Showing 9001 words to 12000 words out of 157517 words

Chapter 4 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5135

ɗaura kan Bibalo a kan cinyarta.


**********************


*ABATCHA ESTATE*
*FCT ABUJA*
*8:05am*

Sai da ta ƙara wanka kafin ta ɗauki wannan kayan da Hajjaty ta nuna mata, cikin wata Black expensive Abaya da ta ji stones wanda ke zuba ƙyalƙyali ta shirya, ba ta yi wata kwalliya ba coz farar powder da ke gaban Mirro ɗin ta shafa, sannan ta shafa wet leaves, ko kwalli bata saka ba ta yafa Black veil da ke haɗe da abayar ta yafa. “Masha Allah ” sosai suka karɓi farar fatarta sai ta fito a ainihin balarabiya amma fa mai jin Hausa 😂.

Hajjaty ma cikin wata atamafar ta ja da baƙa ta shirya, tayi kyau kamar ba ita ta haifi Daddy ba. Ganin ƙarfe 8:10 yasa Hajjaty ɗauko Mayafinta ta yafa “Yi maza ki fito Zahrau lokaci ya kusa cika”
Da “To” ta amsa tana ajiye turaren da ta ke fesawa tare da bin bayan Hajjaty da ke ƙoƙarin barin bedroom ɗin.

Basu ɓata lokaci ba kau tsaye suka nufi Family Hall da ke ɗan kusa sosai da ɓangaren Hajjaty. A wannan lokacin kuma da yawa sun iso, saboda su al'adar su babu African time Shiyasa in an saka lokacin taro da wuya ba'a fara shi yadda ya kamata ba.

*Shin kun sa cewa?:*
_1. Duk wanda ya tashi daga bacci ba'a so ya miƙe immediately as he wake up?, Ana so idan mutum ya farka daga bacci kada ya miƙe a lokacin, an fi so ya ɗan ci gaba da kwanciya na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya miƙe tsaye, hakan zai ƙara improving level of wellness na mutum musamman ta bangaren ƙwaƙwalwa da kuma tunani, psychologically one will be more stable_
_On the other hand miƙewa tsaye da zarar mutum ya tashi daga bacci kan haifar da matsalolin lafiya da dama, ciki yana jawo sauƙar jini (hypotension), yana kawo rashin dai-daiton tunani ta yadda zaka ga mutum a zabure kamar wani abun tsoro ya sako shi gaba. Hakan har ila yau kan iya haifar da matsalolin da suka shafi ƙwaƙwalwar ɗan Adam._
_So You guys should be more careful, in an tashi daga bacci a daina miƙewa tsaye a take, ayi ƙoƙarin jinkirtawa na wani lokaci ko don inganta lafiya._
_Haka nan tashi tsaye bayan dogon Zama, shima yana sanya jinin mutum sauƙa. Ba'a fiye son yin dogon Zama ba saboda gudun hakan, ku sani Sauƙar jini (hypotension) ya fi hawan jini illa, sannan yafi wahalar magancewa fiye da hawan jinin. A kula sosai da lafiya my esteem fans._

_2. Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi yakan fara kowanne aiki da bismillah_
_Manzon Allah ya kasance yakan ambaci sunan Allah a farkon kowanne abu da zai yi hatta a cin abinci, habibties kada a manta a ke yin bismillah kafin yin kowanne irin abu. Sannan ake yawaita godewa Allah bisa kowacce ni'ima komai ƙarancinta. Allah ya sa mu dace._

*Ku kasance da alkalami na don jin yadda zata kaya, masu cewa kansu ya kulle ku ƙara haƙuri ku ci gaba da bibiyar alƙalami na, komai zaku fahimta ne da sauƙi, ku tuna _A babban gida_ muke, so everything there supposed to be somehow complicated.*

*A karɓa da haƙuri my esteem fans, manage this!, ina ƙara Baku haƙuri in sha Allah komai zai daidaita. I've been busier than before that's why, Amma zan ƙoƙarta komai ya saitu. Make sure that you guys react! React!! React!!! & React har sai na gaji da ganin reactions. I love you guys😘, group members ayi comments Please sannan ayi sharing don Allah, much ƙauna 💕.*

[10/18, 5:24 AM] Diamond Bhatool:

*Typing 📲*

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*


Wattpad: @diamond_bhatool
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._



*PAGE* 0️⃣5️⃣

_Dedicated to my superhero, father, mentor and role model in person of JS Yakubu, Allah ya ƙara maka lafiya baba._

_Masu neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu_






Gaban Zahrah ne ya buga suna kaiwa gaban makeken block ɗin da aka maƙala mishi signboard na Family Hall wanda ke ƙyalƙyali da dare kuma ya ke fitar da haske kala kala. Hajjaty da ke riƙe da hannunta ne ta fahimci hakan. Cike da kulawa ta ce “Kin ga Zahrau muje duka ƴan uwanki ne ba wani bare, kar ki ji tsoro kin ji?”
Kai ta gyaɗa sannan suka fara takawa izuwa steps ɗin da zai sada ka da hall ɗin. Suna tsayawa glass ɗin ya zuge nan suka shiga ciki.

Mutane ne sosai suka halarci taron, manya da yara, sai dai babu iyaye mata da alama iya mazan ne a ciki. Shigowar Hajjaty yasa hankalin su komawa ga saitin ƙofar, mamaki sosai ya cika su ganin wata baƙuwar fuska wacce ko makaho ya shafa ta zai sai jinin gidan ce, but to them abun ya ɗaure kanunsu. Ko da yake lokacin Alhaji Baba ne kaɗai bai shigo ba sai kuma Daddy yasa suka nemi wuri suka zauna. Few minutes sai ga Alhaji Baba tare da Daddy wanda ke riƙe da shi. Har wurin zamansa aka kai shi bayan ya zauna Daddy ma ya nemi nasa wurin ya zauna.

Babu alamar motsi cikin hall ɗin tun shigowar Alhaji Baba. Kowa yayi tsit yana sauraran me za'a ce, wadanda suka kula da shigowar Hajjaty ma suna jira a kammala su ji wacece wannan kyakkyawar yarinya da suka shigo tare.

Alhaji Babba wanda a kodayaushe in za'a yi wani taro yake fara magana kamar yadda ya kasance babba cikin Abatcha family. Microphone 🎤 ɗin ya ɗauka da fara magana.
“Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatouh”
Gabaɗaya Hall ɗin ya ɗauka da “Wa Alaikumussalam”
Nan ya ɗaura da faɗin “Iyayen mu masu daraja, ƴan uwa na da kuma ƴaƴan mu, barkan ku da wannan safiya mai Albarka” sai ya ɗan tsagaita kafin ya ci gaba
“Kamar yadda na gani akan fuskokin ku na ƙara tabbatar wa da kaina cewa kuna mamakin wannan unexpected meeting, so Kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara magana akan abinda ya tara mu. Sai dai kafin nan kamar yadda muka saba za'a bude taron da addu'a, Bismillah Qasim”

Wani kyakkyawan saurayi ne ya mike ya amshi microphone ɗin daga hannun Alhaji Babba, fuskar matashin sake wacce da ke nuna zallar kamala da kwarjini ya fara magana, khudhbatul hajah ya fara daga nan yayi addu'o'i sannan ya mikawa Alhaji Babba da ke zaune microphone daga nan ya koma mazauninsa.

Alhaji Babba ya ci gaba da magana “Masha Allah, Allah yayi Albarka Qasim, kai tsaye zan fara magana akan abinda ya tara mu. Idan baku manta ba wasu lokutan zaku ji ƴan uwana wato iyayenku suna magana akan ƴar uwarsu wacce ta ɓata tsawon wasu shekaru masu yawa” sai kuma yayi shiru. Nan hankalin kowa ya ƙara komawa jin me Alhaji Babban zai ce? An same ta ne ko kuma ta mutu ne? They're all earger to know.
“Alhamdulillah” Alhaji Baba ya ci gaba “Cikin ikon Allah Ubangiji ya nuna mana gudan jininta, sai dai ta ɗaya bangaren har yanzu dai ita Madina babu labarin ta, saboda haka a ƙara ƙaimi wurin Addu'a Allah ya bayyana ta.”

Nan da nan Hall ɗin ya kaure da hayaniyarsu wannan na cewa kaza wannan kuma na faɗin kaza har ta kai ga Zahrah da ke gefen Hajjaty shan jinin jikinta, tuni wani tsoro ya ɗan kamata kar dai taje she's not welcome by her cousins.

“Ya isa haka!” Alhaji Baba ya. Faɗa da ɗan ƙarfi, nan Hall ɗin yayi shiru kamar ba dai yanzu aka gama cin kasuwa cikinsa ba.
“Yanzu ba tare da ɓata lokaci ba kowa zai introducing kansa saboda ta ƙara fahimtar ku, amma ita bari ta fara sanar da ku sunan ta, Bismillah” rass gabanta ya faɗi, hannun Hajjaty ta ɗan ƙanƙame, ƙasa ƙasa Hajjaty ta ce mata “Ki nutsu Zahrah, maza tashi ki je”

It's not her first time to speak in public but this time is different, zuciyarta ne ke tsalle tana kai kawo. A hankali ta miƙe ta nufi stage ɗin, hannunta na ɗan rawa ta ɗau mike ɗin. A hankali zuciyarta Kuma ta fara saituwa, cike da ƙwarewa da magana a cikin mutane ta ce “Assalamu Alaikum, good morning my lovely grannies and parents, good day my esteem sisters and brothers, da farko suna na Zahrah Abdulkarim Kuru, ɗiya ga Madina Abatcha wacce aka riga aka sanar da ku komai game da ita. Naji daɗin shigowa cikin ku kuma ina fatan kuma kun ji daɗin kasancewa ta da ku.” sai kuma ta yi shiru tare da ajiye microphone ɗin. Babu laifi kowa was impressed with her speech, though wasu daga ciki were disgusted by her speech. A nutse ta taka ta koma gefen Hajjaty tana sauƙe ajiyar zuciya.

Alhaji Baba ya ce “Now!, Qasim zo ka ɗau abun magana a fara ta kanka, let everyone introduce himself to her now.”
Ya Qasim ne ya miƙe a nutse ya fara magana “wa Alaikimussalam, morning, Ni suna na Qasim Abubakar Abatcha.” daga nan ya miƙawa sauran mutanen, ɗaya bayan ɗaya kowa yayi introducing kansa, daga nan kuma suma iyayen suka yi. Nan Alhaji Babba ya ce gobe za'a zaga da ita ta ga sauran mutanen gidan.

Ya Qasim ne ya rufe taron da Addu'a nan manya suka fara fita kafin maza sai kuma matan kowa na ƙara tattaunawa akan yarinyar.

Wasu Ƴan mata guda uku da zasu kai 24years ne ke tafe suma suna magana akan Zahrah. Ɗaya daga cikinsu wacce fatarta ke da haske sosai ta ce “Ke Rumana Ni fa yarinyar nan ta burge Ni wallahi, see how courageous she's, ga ta kyakkyawa, kina ganinta kamar Hajjaty ce tayi kaki ta tofar. Wacce aka ƙira da Rumana ce ta yamutsa fuska tare da tofar da yawu gefe. “Ke Hibba matsala ta da ke, you're so local, don Allah wannan yarinyar what's that her name!” ta ɗan ɗaga kai sama tana ymutsa fuska sai kuma ta ce “Zahrah take ko wa! Wallahi haka kawai yarinyar bata mun ba, daga gani zata yi rawar kai, ga ta da shegen kyau kamar aljana”

Ɗan taɓe baki ta ukun nasu tayi ta ce “Kya ji dai da wannan banzan halin naki, Ni dai tunda jini na ce dole ba zan ƙyamace ta ba, kyau kuma da kike magana ke ma ai kina da shi, duk cikin familyn nan babu wadda za'a cewa mummuna.”
“Faɗa mata kam Jidda, Ni na rasa wane irin hali ne da Rumana, mutum bai Miki komai ba kawai ki ce kin tsane shi” Hibba ta faɗa tana faɗin “Kun ga Ni nayi ciki, sai mun haɗu kuma”. Ta faɗa tana shigewa apartment ɗin su da yafi kusa da na Hajjaty.

Tsaki Rumana ta ja ta nufi apartment ɗinsu ranta duk babu daɗi, tana shigar ta tarar da Mai aiki na mopping Parlour, harara ta cilla mata tace “Ke Jennifer kin gyara min ɗaki na ko?”
“E Eh ranki ya daɗe, ta faɗa tana sunkuyar da kai gudun masifar Rumana, tsaki kawai ta ja ta haye stairs ɗin sannan ta shige room nata tana sakin tsaki a kai a kai.


********************

*ABATCHA FAMILY*

Kamar yadda ya gabata Alhaji Baba da Kuma matarsa Hajjaty da marigayiya Khadijatu suna da yara bakwai cur.
Alhaji Abubakar Abatcha (Alhaji Babba) shine babban su, matan sa uku ne.
Hajiya Ruƙayya, Hajiya Karima sai kuma Hajiya Balkisu.

Hajiya Ruƙayya (Hajiya Babba) na da yara Bakwai. Aunty Madina ita ce babbar ƴarta, yaron ta ɗaya Aamir kuma suna zaune ne a Kaduna ita da mijinta. Sai Ya Haidar shi kuma ba a Nigeria yake da zama ba shi da matarsa Aunty Salma, yarinya ɗaya gare su, Nihal. Sai kuma Ya Khalil wanda shi bai yi aure ba har yanzu, shi a nan Abatcha estate yake da zama, yayi tafiya ne zuwa London. Akwai Aunty Mabruka yanzu haka ta kammala karatun ta a ɓangaren law, ta fara aiki da Court of Appeal. Sai kuma Humaira, Nasreen da kuma auta Fu'ad.

Hajiya Karima yaranta biyar, Ya Qasim shine babba, sai Ya Auwab sai kuma Hibba, Jalal sai kuma Samha.

Hajiya Amina yaranta uku, Meerah, Jidda sai Naufal.

Alhaji Umar Abatcha (Daddy) matansa biyu, Hajiya Laila (Aunty Amarya) da Kuma Hajiya Sughrah (Mommah).
Hajiya Sughrah ce babba, yaranta biyar, Ya Junaid, Aliyu, Anam, Nainarh sai kuma Ra'ees.

Aunty Amarya yaranta uku, Fadhwah, Adnan, sai kuma Noor.

Alhaji Uthman Abatcha (Papa) shima matansa biyu, Hajiya Saudatu (Ammie) sai kuma Hajiya Ramla (Mimie).
Ammie na da yara biyar, Aufa, Imad, Afifa, Minal, da Kuma Sudais.
Mimie kuma yaranta uku, Affan, Muhibbat, da kuma Zakiyya.

Alhaji Aliyu (Abie) na da mata ɗaya ƙwal. Hajiya Rahila, yaransu uku, Ya Tajudden, Rumaysa, da kuma Auta Mahir.

Alhaji Muhammad (Abba) na da mata biyu, Hajiya Baraka (Mami) da kuma Hajiya Na'ima (Small Mom).
Mami na da yara uku, Ya Faruq, Kausar, da Kuma Asim.
Small mom yaranta biyu, Amna da kuma Aneela.

Alhaji Yusuf (Affa) ma matansa biyu,Hajiya Hauwa (Amma) da kuma Hajiya Hadiyya (Aunty Hadiyya).
Hajiya Hauwa yaranta biyu, Feenah da kuma Reedah. Aunty Hadiyya dai bata da yara ko ɗaya amma tana da ciki.

Wannan sune suka yi making ABATCHA FAMILY.

*Back to story*

Bayan kowa ya fice Hajjaty ta kama hannun Zahrah suka wuce zuwa ɓangarensu. A parlour Zahrah ta yada zango tana sakin nishi “Auh! Wallahi har na gaji Hajjaty”
“Gajiya kuma Zahrau, Kinga yanzu bari na ƙira yaron nan Auwabu ko Tajudden wani ya kai ki kiyo siyayya sai ku tafi tare da Nasreen ta taimaka miki”
Zahrah ta ce “To Hajjaty na gode, amma da mun bari sai yamma fitar zai fi daɗi”
Cike da gamsuwa Hajjaty tace “Eh kuma fa haka ne, yanzu ki huta abunki ”

Ƙara miƙewa Zahrah tayi akan sofa ɗin tana lumshe idanunta tare da tariyo moment ɗin da take ciki, tun daga zuwan ta estate ɗin zuwa yanzu. “Mamah” ta furta har lokacin idanuwan ta na a lumshe. “Yanzu matsala ta kenan! Ita ɗaya ta rage min, ubangiji ka bayyana min ita”
Duk maganar da take yi cikin ranta ne, bata san maganar ta fito fili ba sai da taji an ce “Amin ya Rabbi” a ɗan tsorace ta buɗe lumsassun idanuwanta tana ɗaura su kan wanda ya amsa tambayar.

Wasu kyawawan ƴan mata ne waɗanda ba zasu wuce tsarar ta ba a shekare sai dai bata iya banbance cikinsu wace ce tayi maganar. Murmushi suka yi mata hakan yasa ta ƙara lumshe idanunta sannan ta buɗe ita ma ta mayar musu da murmushin tare da miƙewa zaune tana nuna musu gefenta.
“Thank You”, ɗayarsu ta furta. Murmushi tayi tana ƙara kallonsu sai dai ta kasa tuna sunayensu duk yadda ta so tunawa cikin sauƙi.

Bayan sun zauna, Ɗayarsu wacce ganin fari zaka tabbatar da surutun ta tace “Zahrah, gamu mun biyo ki”
Murmushi tayi tace “Sannun ku da zuwa”
Daga cikin su wata ta ƙara cewa “We're glad that you're back, Barka ƴar uwa!”
“Na gode” zahrah ta bata amsa tana haɗa hannayensu tare.

“Suna na Nasreen” mai surutun ta faɗa “Ga kuma...” “To wa ya saka ki?” ɗayar tayi saurin katse ta “Mu ma muna da baki”.
Ɗayar ce tayi murmushi tace “Ni kuma Nainarh”
Ɗayar ta ce “And I Zakiyya” Ni kuma Rumaysa”.
Da ido take binsu tana ƙara nazartar fuskokinsu fuakarta ɗauke da murmushi.
“Thank You so much sisters, pleased to meet you all!”
“You are welcome ” suka faɗa su ma suna murmushi.

*LONDON*
*Sadauki*

Sun shafe kimanin Awanni biyu a emergency room ɗin kafin aka samu damar ceto numfashinsa, nan Nurse ɗin tayi masa allura tuni bacci yayi awon gaba da shi.

Dr. Arƙam ne yayi saurin tunkarar ma'aikatan yana mai tambayar su ya ake ciki, ɗaya daga cikinsu ne ya dafa kafaɗarsa yana faɗin “Calm down doctor, we're able to rescue his breath, now an mishi allura. In sha Allah he'll be stable but.... let's get inside please”
“Ok” Dr Arƙam ya bashi amsa tare da bin bayansa zuwa office.
Nan Dr ɗin ya ƙara shawartar Dr. Arƙam game da patient ɗin nasa. Daga nan ya fice ya koma wurin Ya Khalil da ke reception cike da zullumi da damuwa, nan yayi ta kwantar masa da hankali, jin ya farka tukun hankalinsa ya ɗan kwanta.

Nan ya laluɓa wayarsa don ya ƙira Gida ya sanar. Jin bata jikinsa yasa ya tuna cewa ya bar wayar ma can gida yasa ya ɗan kawar da kansa gefe yana cije leɓe. Cikin ransa kuma ya riga ya gama yanke shawarar abun yi, don ba zai bari rayuwar abokinsa kuma ɗan uwansa ta salwanta a banza ba, dole ne su koma gida ko yaya ne abun zai fi zuwa da sauƙi.

*Wannan kenan!*
*Na san har yanzu zuciyar readers cike take da ƙaulani! To kada ku damu yanzu ne zamu fara labarin, zuwa yanzu na san kun fahimci wasj abubuwan, yanzu dai mun san babban gida da kuma ahalin by names, da sannu alkalami na zi warware muku komai! Ga Ya Sadauki da. Kuma Ya Khalil! Ku dai ku kasance da Ni kawai don jin yadda zata kaya.*
*Jama'ar Channel ku da nake yaba ko yaushe ku ma kuna son bani kunya, yanzu reacting ɗin ma ba sosai ba, idan baku jin daɗin labarin nd lemme know please*
*Reacting ƙasa da 20 means na daina yin update.*

*My esteem fans a nuna min ƙauna ta hanyar reacting please, Ina son ku da yawa da yawa, kada ku mance ni ɗin taku ce 🤗 😍 😘 💕*

[10/20, 6:12 PM] Diamond Bhatool:
*Typing 📲*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login