Showing 117001 words to 120000 words out of 157517 words
shiru haka, shegen Suratu kamar aku."
"Ɗaya muke Ni da ke."
"Kin ga ba wannan ba, gobe don Allah ki shirya ki je gidan Aunty Humairah ki karɓo min little, wallahi na yi missing nasa sosai."
"Ai ke ba ki da ƙafa ko?"
Kwaɓe fuska Zahrah tayi tace "Min manta Ni matar aure ce?"
*FEW DAYS LATER...*
Kwanci tashi Babu wuya a wurin mai rai, rana ba ta ƙarya in ji hausawa, sai dai uwar ɗiya taji kunya. Yau ta kama Alhamis, yau ne ranar da aka sanya don gabatar da family meeting wanda ya ƙunshi kowa da kowa, har da iyaye mata da ba a yi da su. Sosai aka shirya family hall ɗin ya tsaru.
Da misalin sha ɗaya daidai kowa ya hallara tun daga kan babba zuwa mafi ƙaranta hatta Aunty Madina ta zo duk da cewa kwananta biyu ne da komawa KD. Amare ma cas, kowa ya zo tare da mijinsa. Babu shakka wannan taro da ba su san a kan me za a yi ba ya sa zuciyar wasu cikin waswasi yayinda wasu kuma suka ƙagu su ji ko ma menene za a tattauna a kai.
Shaɗaya da minti goma sha biyu 11:22am aka ɗunguma zuwa katafaren hall ɗin, decoration ɗin da aka yi yasa suka tabbatarwa kansu cewa akwai wani muhimmin abu da za a yi. Bayan kowa ya Zauna Zahrah da Nasreen suka shigo da sauri kamar wasu munafukai ganin sun makara, idon da Zahrah ta ɗaga ya sauƙa kan Rumana, gefenta kuma Aunty Humairah ce, ai ba shiri Zahrah ta nufi wurin tare da ɗaukar Little da ke cinyar Aunty Humairahn tana faɗin "Sannu Aunty, na ɗau ajiyata."
Daga haka suka yi can baya, shi kuwa sai ɓaɓɓaka dariya yake yana gwalatunsa wanda ba komai mutum ke ganewa ba sai ɗaɗɗaya.
Kamar ko yaushe sai da aka buɗe taron da Addu'a tukun Alhaji Baba ya karɓi abun magana kana yayi welcoming kowa da kowa.
*React and share.*
Diamond 💎 Bhatool 🦋
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣6️⃣
﷽
"To Kamar yadda kuka sani kuma kuka gani wannan taron na musamman ne, don zan iya cewa a tarihin wannan ahali ba a taɓa yin kwatankwacinsa ba."
Nan ya kwashe batun fasa auren ɗaya daga cikin amaren da aka yi, sannan yace "Da yake Allah ya barwa kansa sani sai dai auren bai fasayu ba, an ɗaura shi da wani mijin."
Gaban wasu daga cikin mutanen da ke parlourn ne ya fara bugawa jin sai da aka ɗaura auren, wasu kuwa har da kukansu, nan ya kwashe zuwan su Yaya Ishaq tas. Lokaci guda ɗakin taron ya cika da surutu sai zagin wanda yayi siddabarun nan ake da ƙyar aka koma tsit kamar da.
Murmushi irin na dattijai Alhaji Baba yayi kafin yace "Sai kuma wani ƙarin abun farin cikin..." Bai kai ga faɗa ba Yaya Sadauki ya kutso cikin hall ɗin cikin takunsa na ƙasaita. Kamar an ɗauke wuta haka hall ɗin ya koma daga bisani kuma kowa ya tsorata da al'amarin. Nan wasu suka yin baya wai suna neman wurin fakewa wasu kuma na faɗin fatalwa ne. Sai da Yaya Qasim ya ɗan ɗaga murya kafin aka yi shiru, shi kuwa Yaya Sadauki ko ta kan su bai bi direct gefen Alhaji Baba ya nufa ya zaune ya naɗe hannu yana bin su da ido.
"Ya isa haka mana, a saurara."
Tsit hall ɗin Yayi kowa ya ƙagu ya fahimci abun da idanunsa ke gane masa.
"To Kamar dai yadda kuka gani, wannan" Alhaji Baba ya faɗa yana nuna Ya Sadauki da ya haɗe girar sama da ƙasa ganin abun nasu kamar ma hauka ne.
"Cikin sahalewa da ikon Ubangiji ya dawo garemu, dama can Allah bai ɗau ransa ba tunda sanin kanku ne wanda ya mutu dai ba zai dawo ba. Saboda haka ne ma yasa na haɗa taron nan kowa ya ganshi a nan kada ya kawo ziyara ku fara gudu kamar mahaukata, irin dai yadda kuka yi yanzun nan. Saboda haka ina umartar kowa ya tattara ya nasa ya nasa ya bar ɗakin taron nan."
Sum-sum aka fara miƙewa ana ficewa banda Mommah da ke jin kamar ta furga wurin da Yaya Sadaukin ke zaune, haka Yaya Khalil ma dai ƙin fita yayi, Zahrah kam ta kasa ko da ƙifta idanunta don gani take da zarar ta ƙifta zai iya ɓacewa ɓat daga nan kuma ba za ta ƙara ganinsa ba, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dawo da kallonta ga Little wanda shima idanunsa suna ga Yaya Sadaukin.
Ganin duk an fice ya rage iya matasan ne, iyaye yasa Alhaji Baba murmusawa yace "ma sha Allahu, marasa hankalin sun fice, ku masu hankalin ku matso kusa, Qasim, ungo ajiye amsa ƙuwwar nan."
Ko da suka matso kusa dai kowa kasa ɓoye farin cikinsa yayi musamman su Mommah wadda take ganin kamar mafarki take, haka ta sha kukanta. Su iya Zahrah da Little kam an maƙale a baya ana sauraron ikon Allah. Sai da aka gama gaggaisawa tukun Alhaji Baba ya dubi shalelen jikan nasa yace "Sadauki Sadauki, Sadaukin Abatcha Sadaukin duniya, ai ba ka san wani abu ba mu nan har mun binne gawarka ashe ba kai ba ne, to ya aka yi bayan kuma an tabbatar da cewa kana cikin jirgin da yayi haɗarin?"
Kamar ba zai tanka ba yace "Allah ne mai yin yadda taso haƙiƙa, babu shakka ranar zan je Bauchi ne don cika muku muradinku game da ɗiyarku kuma Babata Mamah wacce na gano yadda take ta hanyar wani bawan Allah. Na so a ce ta hannuna ta dawo gare ku sai dai Allah shi ke yadda ya so, a ranar da muka tafi na yi sallama da matata tukun na wuce ba tare da wani ya san na tafi ba bayan ita. Ba zan ce ga abun da ya faru ba tunda a sararin samaniya ne sai dai zan iya tuna lokacin da jirgin mu ya kama da wuta tare da tarwatsewa gabadayansa. Ba zan iya tuna komai ba amma dai.." dakatawa yayi tare da miƙewa ya bude door ɗin hall ɗin, wani ɗan matashin da ba zai wuce Sa'an Yaya Sadaukin ba ya kalla tare da masa alamar ya shigo, wuri ya ba shi ya zauna tukun ya dubi su Alhaji Baba da suka yi tsit suna kallon su kana ya dubi mutumin yace "Wannan shine Junaidu, abokina ne a can kuma shine wanda ya taimaka min a lokacin da al'amarin ya faru, Aboki ko za ka iya ba mu labarin gabaɗayanmu."
Gyaran murya Junaidu yayi yana gyara zama, "To da farko dai alhamdulillah, kamar yadda ya faɗa Junaidu sunana, Ni mutumin garin Zubo ne, da ke jahar Bauchi, sai dai kuma Ni gidana yana bayan gari kusa da kogi saboda kasncewata masinci."
"Ranar wata juma'a da yamma na dawo gida daga cikin garinmu da yake in na yi su na kan kai cikin gari ne a saye, ina dawowa na sauya tufafi domin komawa nayi su, a lokacin da na kafa tulu na a cikin kogin sai na ji kamar na zunguri abu, a tunanina ma wani ƙaton kifi ne hakan yasa na fito na zara sangen da nake amfani da shi, abun mamaki kuma sai Na ci karo da wani ɓangare na abun hawa da ba zan iya fayyace menene ba, hakan ya sanya ruɗu da al'ajabi cikin raina. Hannuna na sa na janyo amma hankalina ya ƙi kwanciya da abun sai nake jin kamar akwai wata halitta tare da ɓangaren abun hawan, hakan ne yasa kawai na shiga kogin kamar mai wanka, ba tare da na zata ba na ci karo da abu, abun ka da ƙwararre na jawo abun take muka yo sama, ga mamaki na me zan gani? Mutum, mutum ne gwarzo a siffa kuma kyakkyawa, a lokacin na san cewa ba ƙaramin mutum bane, kalar fatarsa yasa nayi tunanin ko dai ba ɗan ƙasar bane? Da haka na ciro shi kusa da tutu na na shimfiɗe shi tare da matse ruwan da ke cikinsa, cikin ikon Allah ashe akwai sauran numfashi a tattare da shi. Sosai na godewa Allah, saboda yadda na fahimci akwai jigata a tattare da shi yasa na saɓa shi a baya na muka shiga cikin gidana, ɗaya ɗakin da muke ajiye kayan abinci na nufa da shi, da yake lokacin abincin ya ja baya kawai sai na gyara ɗakin tare da kwantar da shi bisa tabarmar kabar da uwarɗaki na ta kawo min."
"Bayan nan na sa ta tafasa ruwa masu zafi, Ni na taimaki bawan Allahn nan yayi wanka, sannan na ɗauko suturata na ba shi ɗaya, bai ji ƙyanƙyami ba kawai naga ya amsa ya saka. Ganin hakan yasa na koma wurin su ɗi na bayan izinin daga wurinsa da na karɓa, ina komawa ban kama wasu kifaye masu yawa ba na dawo na ba wa uwargidan ta yi abinci da shi. Nan ta tsare Ni da tambaya, ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita, abun ku da mace tuni tausayinsa ya kama ta itama. Bayan ya ci abincin bai wani jima ba ya kwanta sai bacci."
"Washegari tare muka karya, bayan mun karya nake tambayarsa daga ina yake, amma sai yayi shiru da alamun dai ba ya cikin hankalinsa hakan yasa na haƙura na tambayi sunansa, abun mamaki a take ya amsa min da Sadauki. Mamaki sosai na shiga ganin ya iya Hausa, sai dai tsawon kwanaki uku in na tambaye shi daga ina yake ba ya cewa komai duk da za mu zauna mu ɗan taba taɗi da shi, daga haka na fahimci cewa ya manta abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa. A ranar ne kuma na je cikin gari naji ana zancen haɗarin jirgin sama da aka yi daga wurin jama'ar gari, wanda su ma labarin ya Riske su ne ta hanyar sauraran rediyo."
"A haka muka ci gaba da zama, sannu a hankali shima ya koyi su har ma ya fi Ni iyawa, cikin ƙanƙanin lokaci sai ya kama kifayen da a rana iya adadin su nake iya kamawa. Nan da kasuwa ta ta bunƙasa, har aka fara zuwa daga wasu ƙauyukan kusa da mu ana sarin kifi wurin mu. Daga baya ma dai sai muka fara fita har wasu wuraren muna kai kifi, ganin ƙwarewa irin tasa yasa na nemi shawarar uwargidan nawa Ni da shi muke tafiya jama'are yin su ɗin, ai kuwa mun samu alkhairi ba kaɗan ba, tuni arziƙina ya bunƙasa sai dai damuwata ɗaya har yau wannan bawan Allah bai tuna wani abu ba daga rayuwarsa."
"Mun shafe shekaru biyu zuwa uku da shi a wannan halin, kwatsam sati biyu da suka wuce mun je jama'are a Babban titin garin wata jibgegiyar mota ta zo wucewa, nan fa Sadauki ya ƙi biyoni muje su wai shi wannan baron yake so yake kalla, ganin tuburan dai ba zai biyo NI ba yasa muka tsaya gindin wat bishiya muna kallon motocin ɗaya bayan ɗaya har yamma. Hakan yasa na fara lallaminsa yazo mu koma amma ya ƙi, ƙarshe dai cewa yayi na tafi, shi motarsa zai hau ya tafi."
"Jin kalamansa yasa na fahimci cewa akwai wani abu da ya fara tunawa da ganin motocin, hakan yasa na zauna tare da shi, can wajajen ƙarfe biyar na Yamma naga ya zabura ya miƙe tsaye, sai kuma ya faɗo ƙasa sumamme. Hankali tashe na ɗauke shi nayi haramar sama mana abun hawa, muna samu kuwa muka wuce gida kai tsaye. "
"Lokacin da ya farfaɗo na sha mamaki ƙwarai jin yana furta wasu maganganu kamar haka _A'a Mubaraka ki bar Ni haka da rashin jin ki, dole yau zan taho da Mamah._" can kuma yace _Zahrah, ki taya Ni da addu'a, ina tabbatar miki da cewa Yayanki will not disappoint you, in sha Allahu yau zuwa gobe in muna da rai za ki yi farin ciki sosai._ _Mommah na ita ce matsalata a rayuwa, na gaji da hulɗa da mutanen banzan nan da take, Mommah wallahi ba son ki suke ba, don Allah ki fita hidimarsu._
"Zantuka makamantan waɗannan yake yi yayin da kuma idanuwansa ke rufe. Kalmar shahadar da ya rangaɗa yasa na tsorata a tunanina ma ko mutuwa zai yi, sai dai lokaci guda kuma ya miƙe ya zauna yana bin ko'ina da kallo. Can dai na dubeshi nace, Mallam Sadauki ka tashi? Sannu. Kallona kawai yake yi daga bisani yace Malam lafiya? Ina ne nan? Me nake yi a nan? WHERE'S my wife and family? Da kyar na lallaɓa shi sannan nace masa yayi haƙuri jikinsa yayi ƙarfi kafin ya koma gida amma ya tubure shi fa dole ya taho, da ƙyar dai ya yadda ya zauna, bayan sati ɗaya da kwanaki shida kuma yace zai tafi, nan dai muka yanke shawara da maiɗaki na akan na raka shi har zuwa ga ahalinsa tunda ya riga ya dawo daidai. Shine muka taho, zuwan mu na yi mamakin ganin ashe shi ɗan babban gida ne irin wannan, taron da muka ga yasa muka yi tunanin ko mutuwa aka yi ashe aure ake ɗaurawa."
Daga haka Junaidu masinci yayi shiru can yace "wannan shine abun da ya faru." Mamaki da al'ajabi sun cika kowa yayin da shi kuma hankalinsa yanzu gabaɗaya yana ga matarsa da ya bari tsawon shekaru, ko ta yi aure bayan takaba? Oho.
Sosai su Alhaji Baba suka yi ta jajanta abun, Mommah sai kuka take tana jin kamar ta janyo shi ta rungume shi, nan suka yi wa Junaidu godiya bisa taimakon da yayi wa Yaya Sadaukin, daga nan Alhaji ya ba shi labarin lokacin da aka gano yayi hatsari har da gawar da suka je aka ɗauko aka yi jana'izarta. Sosai yayi mamaki tare da godewa mahallicinsa. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan yace "What about her?"
Yaya Khalil da ke bayansa yace "Who?"
"I mean she, my wife, Mabruka"
Rasa mai faɗa masa aka yi can dai Mamah ta ba shi labarin rasuwarta tas, ƙwalla kawai ya share tare da mata addu'ar neman rahama, cikin ransa kuma yana alhinin rashi mace ta gari irin Barr. Mabruka. Shiru ne ya wanzu a cikin ɗakin can dai little ya cilla ihu ya fara zillewa daga hannun Zahrah. Sai lokacin hankulansu ya dawo ga Little Sadaukin da ba su sanar da mahaifinsa batunsa ba, kuma ba sa tunanin ya san da samuwarsa.
*React and share*
[24/04, 9:43 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣6️⃣
﷽
"To Kamar yadda kuka sani kuma kuka gani wannan taron na musamman ne, don zan iya cewa a tarihin wannan ahali ba a taɓa yin kwatankwacinsa ba."
Nan ya kwashe batun fasa auren ɗaya daga cikin amaren da aka yi, sannan yace "Da yake Allah ya barwa kansa sani sai dai auren bai fasayu ba, an ɗaura shi da wani mijin."
Gaban wasu daga cikin mutanen da ke parlourn ne ya fara bugawa jin sai da aka ɗaura auren, wasu kuwa har da kukansu, nan ya kwashe zuwan su Yaya Ishaq tas. Lokaci guda ɗakin taron ya cika da surutu sai zagin wanda yayi siddabarun nan ake da ƙyar aka koma tsit kamar da.
Murmushi irin na dattijai Alhaji Baba yayi kafin yace "Sai kuma wani ƙarin abun farin cikin..." Bai kai ga faɗa ba Yaya Sadauki ya kutso cikin hall ɗin cikin takunsa na ƙasaita. Kamar an ɗauke wuta haka hall ɗin ya koma daga bisani kuma kowa ya tsorata da al'amarin. Nan wasu suka yin baya wai suna neman wurin fakewa wasu kuma na faɗin fatalwa ne. Sai da Yaya Qasim ya ɗan ɗaga murya kafin aka yi shiru, shi kuwa Yaya Sadauki ko ta kan su bai bi direct gefen Alhaji Baba ya nufa ya zaune ya naɗe hannu yana bin su da ido.
"Ya isa haka mana, a saurara."
Tsit hall ɗin Yayi kowa ya ƙagu ya fahimci abun da idanunsa ke gane masa.
"To Kamar dai yadda kuka gani, wannan" Alhaji Baba ya faɗa yana nuna Ya Sadauki da ya haɗe girar sama da ƙasa ganin abun nasu kamar ma hauka ne.
"Cikin sahalewa da ikon Ubangiji ya dawo garemu, dama can Allah bai ɗau ransa ba tunda sanin kanku ne wanda ya mutu dai ba zai dawo ba. Saboda haka ne ma yasa na haɗa taron nan kowa ya ganshi a nan kada ya kawo ziyara ku fara gudu kamar mahaukata, irin dai yadda kuka yi yanzun nan. Saboda haka ina umartar kowa ya tattara ya nasa ya nasa ya bar ɗakin taron nan."
Sum-sum aka fara miƙewa ana ficewa banda Mommah da ke jin kamar ta furga wurin da Yaya Sadaukin ke zaune, haka Yaya Khalil ma dai ƙin fita yayi, Zahrah kam ta kasa ko da ƙifta idanunta don gani take da zarar ta ƙifta zai iya ɓacewa ɓat daga nan kuma ba za ta ƙara ganinsa ba, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dawo da kallonta ga Little wanda shima idanunsa suna ga Yaya Sadaukin.
Ganin duk an fice ya rage iya matasan ne, iyaye yasa Alhaji Baba murmusawa yace "ma sha Allahu, marasa hankalin sun fice, ku masu hankalin ku matso kusa, Qasim, ungo ajiye amsa ƙuwwar nan."
Ko da suka matso kusa dai kowa kasa ɓoye farin cikinsa yayi musamman su Mommah wadda take ganin kamar mafarki take, haka ta sha kukanta. Su iya Zahrah da Little kam an maƙale a baya ana sauraron ikon