Showing 42001 words to 45000 words out of 157517 words
his children muma ya bar mu muyi iko da namu!” ta idasa tana share ƙwallar da ke zubo mata.
Handkerchief ɗin sa ya ɗauko yana share mata hawayen
“Is ok Mommah, ya isa kukan kada ki ja ma kanki ciwo, ina riƙon ki da Allah ku kwantar da hankalin ki kada ki yi abun da za ki zubar da ƙimarki cikin gidan nan.”
A ɗan zafafe tace
“Aliyu ƙima? Maganar ƙima naji kana yi? To ai already ba Ni da ita a gidan nan, Im da a ce ina da ita ai da ba za a yanke hukunci a kan dab na ba tare da an bani damar amincewa ko akasin hakan ba. Wallahi Aliyu ko igiyoyin aure na za su tsinke wallahi ba zan bari a yi auren nan ba.”
Tana faɗin haka ta tashi fuu ta nufi Bedroom ɗinta yayin da ta bar Yaya Sadauki kamar statue. Miƙewa shima yayi jiki ba ƙwari ya fice. Direct Masjid ya tafi ko da aka isar kamar kullum ya biyo su Alhaji Baba suka taho tare da sauran Uncles ɗin shi har da waɗanda bai yi tsammanin gani ba. Ko da suka isa a an parlourn suka yada zango har Hajjaty ta fito suka gaisa sannan shima da ke zaune kan carpet ya gaida Uncles ɗin nashi.
Alhaji Baba ne ya unarve su da su tashi a ci abinci sai a lokacin Hajjaty ta lura da ba Zahrah a wajen. Ba ta ce komai ba ta je ta kira Zahrah. A tare suka ƙaraso Zahrah ta ja ma Hajjaty kujera, bayan ya zauna ta fara gaida Uncles ɗin ta suka amsa fuska sake, nan ya Yi serving kowa including her Heart's desire 😳.
*Na san kuna da tarin tambayoyi gare Ni my esteem readers, ku dai kawai mu je zuwa.*
_React and share please._
[12/31/2024, 10:17 PM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣0️⃣
﷽
Bayan sun gama dinner dukkan su suka dawo parlourn kamar yadda yake. Alhaji Baba bai ware kowa ba, kai tsaye ya fara magana kan dalilin tara su.
“Kamar yadda kuka sani irin wannan kira na gaggawa na ɗauke da ma'anoni mabanbanta, haka zalika yau ma dai na ƙara tara ku saboda wani muhimmin batu, ɓarakar da aka samu a kwanakin baya tsakanin Sadauki da kuma Mabruka ƴar wajen Sadiƙu, na san dukkan ku abun ha jijjiga ku musamman iyaye a ɓangare biyun, ko da ba su nuna wa juna ba tabbas zukatan su sun munana. Dalilin haka ya sa na yanke hukuncin ɗaura aure a tsakaninsu bayan tabbatar da cewa babu komai ɗin da ya faru kawai shiri ne na maƙiya, sai na ga mu toshe bakin maƙiya ta hanyar haɗa auren su zai fi. Ya kuke gani a matsayin ku na iyaye?”
Cike da biyayya kowannensu yayi na'am da hukuncin Alhaji Baba, Nan ya ƙara da faɗin.
“Ma sha Allah, ina ƙara godewa Allah da ya bani ƴaƴa masu tarbiyya waɗanda ba su taɓa ja da hukuncin da na zartar, Ubangiji ya baku masu yi muku biyayya kwatankwacin yadda kuka min.”
Nan suka amsa da “Amin!” Alhaji Baba ya ɗaura da
“Saboda gabatowar azumi nan da wata ɗaya, na yanke ranar bikin cikin makonni biyu ma su zuwa, kowa sai ya fara shirye-shirye.”
Nan gaba ɗaya su Daddy, Appa, Abie da sauran suka fara addu'ar Allah ya sanya alkhairi. Daga nan kuma suka fara taɗin su na ƴaƴan da iyaye.
*Ina Zahrah?*
Tun da ta fahimci akwai abun da za a tattauna ta fara tashi daga dining ɗin sai ta fice daga apartment ɗin ta tsaya bakin ƙofar saboda ta samu damar ji. (Babu kyau gulma fa Zahrah?”
A lokacin da ta ji Alhaji Baba ya ce an yanke ranar bikin Yayanta in 2weeks time ji ta yi kamar an ɗiga mata wani tafasasshen ruwa a zuciyarta. A zabure ta fice ta zagaya ta ƙofar baya, da ƙyar da taimakon Ubangiji ta isa Bedroom ɗinta.
Tana shiga ta faɗa kan Bed ɗin ta tare da fashewa da wani matsanancin kuka, ta rasa ina za ta jefa ranta ta ji sanyi a duniyar nan, ga shi babu kafaɗar wanda za ta kwanta ta zubda ƙwallarta. Nan zuciyarta ta fara tariyo mata moments ɗin da yayanta, why ta yi sauri falling in to his love? Ashe son sa take tsawon lokacin nan?
“No, ba na sonsa, kawai dai ɗan'uwa na ne!” ta faɗa a bayyane.
Da sauri zuciyarta ta ƙaryata ta da faɗin
“Idan har you're not in love with him why kike jin kishinsa?”
Da sauri ta furta
“Kishi? Kishinsa nake?, Noooooo!” ta faɗa tana buga pillown da ke hannunta
“That's impossible!”
Zuciyarta ta ƙara ce mata “Is Possible Zahrah, ki dawo hankalin ki, idan ba kishi ba ne why kike jin zafin aurensa?”
“Wayyooo Allah...” ta faɗa tana dafe kanta da hannayen ta biyu sakamakon yadda kan nata ke juyawa. Daga haka kuma ta yi luuuu ta koma ta baya kamar wacce aka zarewa rai.
Hot love kenan! Su Zahrah yau an yi ƙaramar hauka.
**************************************
Fitowa yayi daga motar kamar wadda aka zarewa laka, a haka ya shiga ciki, Thanks to Allah bai tarar da kowa ba kamar yadda yayi tsammani, a haka ya fara haye benen har ƙafarsa na harɗewa. Daidai Bedroom ɗin da ke nuna mallakinsa ne ya murɗa handle tare da shigewa. Ba tare da ya zare mask ɗin sa ba ya faɗa Bed ɗin.
Numfashin sa ne ke ƙoƙarin kokawa yana shirin barin gangar jikinsa, da ƙyar ya iya cire mask ɗin. Ai ba shiri mai ɗauko report ta ja baya ganin fuskarsa.
Yaya Ishaq ne tabbas sai dai ba wancan Ishaq ɗin da mai karatu ya sani a baya ba ne, wannan Ishaq ɗin wayewa ta bayyana tsantsa a fuskarsa duk da yana cikin tashin hankali.
Wani irin numfashi yake ja tare da fesarwa yana kuma juyi kan katafaren Bed ɗin sa.
“Why angel? Why? Ina kika tafi kika bar Ni? Angel angel! Ko'ina kike in dai a doron duniya kike sai na nemo ki, ke ɗin rayuwa ta ce, na so ko tun baki san kanki ba, ina sonki har yanzu kuma zan kasance mai cigaba da son ki har zuwa numfashi na na ƙarshe, to my last breath angel.!” ya idasa yana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
Wai dama haka so yake? Haka so yake dama? Idan haka so yake baya yi wa wasu mutanen adalci a rayuwa duba da yadda yake kai su ga rasa jin daɗi, da yawa sun rasa nutsuwarsu saboda so, wasu sukan rasa hankalin su su koma tamkar mahaukata, wasu sukan rasa dukiyarsu da muƙamin su saboda so, wasu kuma iyalinsu da abokai kan juya musu baya dalilin so, so so! Wasu kuma sukan rasa wani sashe daga jikinsu, wani so kan zama sanadiyyar makancewarsa, wani kuma sanadiyyar kurumcewarsa, wani sanadiyyar rasa ɗanɗanon bakinsa wani kuma kan rasa rayuwar sa gaba ɗaya. Tabbas so cuta ce ga duk wanda bai yi dace ba ko kuma ɗaya daga cikin abubuwan nan suka same shi silar sa.
Miƙewa Yaya Ishaq yayi da ƙyar saboda yadda yake ganin dishi-dishi, wayarsa ce ta nuna buƙatar agaji yayin da sautin ringing ɗin ya karaɗe ɗakin, waƙar Saleem Smart ne dai-dai wurin da yake cewa.
Haka so yake dama, ya maida kai bawa.......
Sauraran waƙar ya ci gaba da yi har ƙiran ya yanke.
_Flash back_
Masu karatu za su ce tun da Yaya Ishaq ya tafi bai ƙara neman Zahrah ba tsawon waɗannan shekaru! Abun da ya faru shine, bayan tafiyarsa karatu bai taɓa mancewa da Zahrah ba tsawon wannan lokaci, kullum cikin tunani da kewarta yake ga shi ba shi da wani abu nata da zai ɗebe masa kewa sai pictures ɗin ta guda uku.
Bayan ya kammala karatu kuma Daddynsa tare da Mom ɗinsa suka yi residing a can saboda hare-haren da ake kaiwa mahaifin nasa, ya kuma kafa masa dokar babu shi babu Nigeria har sai In tare za su je, shi kuma ba shi da ranar zuwa.
A haka soyayyar Zahrah ta ci gaba da kama zuciyarsa har ta kai ga ta yi masa kamun da ba zai iya cire kansa ba, tun yana ɓoyewa har abun ya fara yawa har da su kwanciya jinya.
Wannan karon ma ganin in har ba su bar shi ya zo ya ga angel ɗin sa ba za a samu matsala saboda likitan da je kula da shi ya sanar da su lallai in ba a Masa abun da yake so ba zai iya rasa ransa.
Hakan ya sa babu shiri Daddynsa yayi booking Musu flight suka diro Nigeria duka kuma sauƙa gidansa da ke GRA, a ranar ya so ya tafi don ganin Angel ɗin sa amma suka ba shi haƙuri ya bari sai washe gari.
Wannan shi ne taƙaitaccen bayanin abun da ya faru bayan tafiyar ya Ishaq.
_To the story...._
*SADAUKI'S POV*
Tunda Alhaji Baba ya gama magana ya sulale ya bar parlourn ba tare da sun kula ba, kai tsaye part ɗin su ya wuce don ya kwanta in b haka ba yada zuciyarsa ke wani irin mahaukacin bugu da sauri da sauri ba lallai gangar jikinsa ta iya ɗaukar sa ba, the amazing part of it is that Sam ba ya so ko kaɗan iyayensa su fahimci cewar kawai sadaukarwa ce yake son yi musamman Alhaji Babba, wanda duk cikin gidan babu mai ƙaunarsa kwatankwacin yadda yake kai har mahaifin da ya haife shi, idan har ya fahimci baya so to tabbas auren nan sunan sa an fasa.
Ko wankan da ya saba yau bai yi ba, kan Bed ɗin sa ya faɗa yana dafe saitin heart ɗin sa, ba zai ce ba ya son auren ba sai dai kuma yana jin wani iri, yana ji kamar akwai wata zuciyar da ta fi buƙatar aurensa fiye da Mabruka, yana jin anya ya yi wa wannan zuciya adalci?.
“Who's that person?” ya tambayi kansa. Tashin mafita ga kuma tunani da ya sa shi gaba kamar ya haukatar da shi yasa ya miƙe a daddafe ya shiga toilet tare da ɗauro alwala. Nan ya yi ta jera nafilfilu ba adadi yana kai kukansa ga mai sama tare da neman ya masa zaɓi mafi alkhairi.
*MAMI*
Da yake duk matan babu wanda ya san da dawowar Abba ko da ya shigo a main parlour ya sauƙa, lokacin kuma dukka matan na zaune a parlourn kowacce ta hakimce sai hura hanci take.
Small Mom dama can ita ta iya kula da miji da sauri ta miƙe tana masa sannu da dawowa, shi ma ya amsa, ganin dai Mami ko alamar furta A ba ta da shi yasa ya jijjiga kansa yana mata addu'ar shiriya.
“Baraka!” Abba ya ƙira sunanta
Ɗagowa tayi ta kalle shi sannan ta mayar da kanta.
“Kina gani na amma ko sannun da dawowa babu? Kina ganin hakan daidai ne?”
“Haba Abban Faruq, ya za a yi ka titsiye Ni gaban wannan matar hakan daidai ne?”
“Ka ga Alhaji na, ka ƙyale ta kada ta ɓata maka ranarka while you look so happy I can see, mu je ka watsa ruwa ka ci abinci.”
“To ƴar'iska! A gaba na kike karuwancin naki ko? Hehehehe! Sai ki faɗa min wane dare ne jamage bai gani ba!”
Small Mom ba ta bi ta kanta ba ta ja hannun mijinta ta bar Mami sai harare harare take tana magana ita ɗaya kamar mahaukaciya.
Ba ta bar parlourn ba kuma sai da ta suka fito. Nan taji Abban na faɗawa Small Mom cewa an saka bikin Sadauki da Mabruka, sosai ta yi murna yayin da Mami ta miƙe tsaye a zafafe tace
“Ba zai yiwu ba! Dole na tarwatsa auren nan don Sadauki ba shi da matar da ta wuce Kausar”
Kallon ba ki da hankali Abba ya cilla mata sannan yace
“Dama can ke ba hankali gare ki ba Baraka, sai ki tarwatsa auren, nace bismillah ki tarwatsa auren in kin cika ƴar halak” rai ɓace kuma ya wuce zuwa turakarsa da ke jikin main parlourn.
Da harara Mami ta bi shi tana faɗin
“Zan kuwa tabbatar maka Ni na cika Baraka Abban Faruq!”
Cike da mamaki Small Mom ke kallonta sannan ta miƙe tsaye tana faɗin
“To iyayen haddasa, a dai sano hassada ga mai rabi taki ce! Mtsss” daga haka ta bi bayan Abba. Ita kuwa Mami kamar mahaukaciya ta fice ta nufi part ɗin ta tana tunanin ta ya za ta yi ta tarwatsa wannan aure!
*Ammie*
Wani lukutin bala'i, Part ɗin Papa ma dai haka aka gwabza bala'i don Ammie rasa nutsuwarta ta yi bayan jin bayani daga bakin Papa, ita dai Mimie fatan alkairi tayi musu tana nuna tsantsar farin cikin ta, tun da Papa ya ga yadda ta yi reacting tare da ficewa a hasale ya sa Ayar tambaya kan ta.
Haka ta faru a sauran sassan gidan kuma ko ina shigen abun da ke faruwa, sauran matan da ba su ƙulli kowacce da sharri ba taya su murna tare da musu fatan alheri.
*Hajiya Babba*
A lokacin da Alhaji Babba ya shigo gidan fuska sake ya tadda su a main parlourn gidan ne saɓanin sauran sassan gidan, a nan hirarsu suke gaba-dayan su, yaran kuma na wasan su.
Shigowarsa yasa yaran suka nutsu, ƙananan cikin su suka rungume shi suna oyoyooo Alhaji. Da farin ciki ga amsa musu sannan ya yi wa kansa mazauni a parlourn, nan duk matansa suka masa sannu da dawowa.
Hajiya Babba ya kalla yace
“Ina Mabruka ne?”
Hajiya Amina da ta kasance uwar ɗakin ta tace
“Tana ciki, Meerah, maza kira Auntynku ki ce mata Alhaji na kiranta.”
Da gudu ta zuwa parlourn Hajiya Amina don kiranta.
Kallonsa suka yi ganin yadda fuskarsa ke nuna farin ciki Hajiya Karima ta ce
“Babbansu yau dai alamun kana cikin farin ciki” ta ƙarasa cikin sigar zolaya.
Murmushi yayi yana faɗin
“Ba shakka, ina cikin farin ciki maras musaltuwa.....” katsewa yayi sakamakon shigowar Mabruka parlourn wacce ta tsugunna gabansa kan ta ƙasa.
“Sannu da dawowa Alhaji, An yini lafiya?”
Fuska sake ya amsa mata da
“Lafiya ƙalau Mabruka, ya aikin?”
“Alhamdulillah” ta ba shi amsa. Shiru parlourn ya ɗauka na wani lokacin kafin Alhaji Babba ya gyara zamansa tare da gyaran murya.
💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃
_Yanzu ma aka fara! Yanzu ma aka fara, kuna jin wata lukurar Masifa kuwa people? Gaskiya akwai ban tausayi sosai musamman ga love birds ɗin nan, fatan mu Allah ya sa abun ya zo da sauƙi._
*Masoya littafin A babban Gida musamman followers ɗin ~DBRC~ waɗanda ke ƙarfafa min guiwa da reacting wadda ke nuna zallar soyayyar su gare Ni da alƙalami na ina godiya, alkhairin Ubangiji ya kai gare ku a duk yadda kuke, tabbas ina ƙaunar ku ƙauna ta gaskiya kuma saboda Allah.*
*Sannan waɗanda ke min comments daga wasu groups ɗin da kuma na musamman masu min ta PC Allah ya saka muku da alkhairi, kar ku manta ko yaushe ƙofar gyara a buɗe take Habibties, zaku iya samu na kai tsaye ta +2347061707238 ina godiya sosai*
*Love You all.*
[1/11, 7:14 PM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣1️⃣
_For those willing to be updated about this book should kindly follow my channel, a can kaɗai nake update yanzu._
﷽
“Hajiya Ruƙayya, Hajiya Karima da kuma Hajiya Amina.”
“Sai kuma ke Mabruka na tara ku ne a nan ba don komai ba sai don na sanar da ku abun farin ciki da ya tunkaro mu.”
Gaban Mabruka ne ya bada wani irin sauti mai karfin gaske wanda har fuskarta sai da ta bayyana hakan. Babu wanda yace komai hakan ya ba wa Alhaji Babba damar cigaba da jawabinsa.
“A matsayin ku na iyaye ga yarinya ina fatan za ku yi farin ciki da abun da zan faɗa, ke kuma Mabruka” ya nuna ta da hannunsa wanda har lokacin kanta ke duƙe.
“Ina fatan za ki biyayya a kan wannan hukunci.” nan gabanta ya ƙara bugawa
“A yau Alhaji Baba ya yanke auren Mabruka da kuma Sadauki cikin makonni biyu masu zuwa in Sha Allah, sai ku fara shirye-shiryen bikin, zan tura muku kuɗi ta a account ɗin Ruƙayya, In da buƙatar ƙari sai ku min magana.
A hankali ta ɗago jajayen idanuwanta ta dubi Alhaji Babba ta furta “Allah ya Ƙara girma Alhaji.” daga haka kuma ta bar parlourn da gudu har tana shirin faɗuwa sakamakon karo da Humaira da suka yi. Da kallon mamaki Humaira ta bi ta wondering why is Aunty Mabruka acting so strange, Nan ita ma gaban ta ya ba da wani irin sauti, daga nan ta ƙaraso, a lokacin su Hajiya Babba duk sun tashi, iya su Meerah ne zaune. Fuska ɗaure Humaira ta kalli Meerah tace
“Meerah me ya samu Mabruka?”
Meerah ta amsa mata da
“Albishir Aunty Humaira! Saura sati biyu bikin Aunty Mabruka da Yaya Sadauki.”
Gaban Humaira ne ya ba da wani irin sauti, bata tsaya idasa jin zancen Meerah ba ta wuce Bedroom ɗin Hajiya Babba da sauri yayin da numfashin ta ke kokawa don ya bar gangar jikinta.
Da taimakon Allah ta idasa shiga, yanayin yadda ta tura kofar ne ma ya sa Hajiya Babba juyowa don ganin waye. Yanayin da ta ga Humaira ya ɗaga mata hankali amma sai ta dake tana bin ta da kallo har ta iso wurin da take. Kanta ta ɗaura kan cinyar Hajiya Babba tare da fashewa da wani irin azababben kuka.
Cike da kulawa Hajiya Babba ke shafa bayanta ba tare da ta ce mata komai ba, sai da ta yi kukan ta ta fara sauƙe ajiyar zuciya tukun Hajiya Babba ta ɗago ta yayin da fuskar su ke kallon ta juna.
“Lafiya Humaira?” kamar jira dama take taji an tambaye ta sai ta ƙara fashewa da wani kukan, ba tare da ta yi shiru ba ta fara magana wacce ba a gane me take faɗi.
“Kin ga calm down Humaira, faɗa min me ke damun ki Please!” Hajiya Babba ta faɗa