Showing 102001 words to 105000 words out of 157517 words

Chapter 35 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5140

Bayan an kammala kuma akayi packaging snacks din a manyan randunan roba biyu, wannan al'adarsu ce matsawar za a aurar da ɗiye ga bare ɗan waje.
Yammacin ranar bayan sallar la'asar motocin dangin miji suka faro kutsowa cikin estate ɗin, a daidai part ɗin Hajjaty suka tsaya, nan aka ba su damar shiga. Sai da manyan mata masu ji da kansu da kuma dukiya suka gama shiga tukun motocin da suka kwaso lefen suka iso. Sosai aka tarbi baƙin da abinci da sha mabanbanta, hakan da aka yi kuma yasa sun tabbatarwa kansu cewa ɗansu ya ɗauko ƴar BABBAN GIDA ne, kuma babu shakka irin wannan tarba ba lallai su same ta ba sai A BABBAN GIDA. Bayan sun ci sun sha ne suka ba da izinin a shigo da kayayyakin, ikon Allah! Wato dai ana ɓarnar kuɗi a bikin ƴaƴan masu hannu da shuni, sai da aka ɓata wasu daƙiƙu kafon aka kammala shigowa da kayan. Da bismillah suka fara buɗewa ɗaya bayan ɗaya har suka kammala buɗe akwatunan, duk da yadda rayuwa tayi tsada, talakawa na jin jiki ta yadda wanda yayi tozali da waɗannan akwatuna zai ce almobazzaranci ne tunda ga mabuƙata, akwatuna set ɗaya ɗaya har set set 30, kuma dukka kayan da aka zuba a ciki babu na wasa.

Bayan an gama kallon kaya ne Hajiya Babba ta roƙi ɓaki da su jira a kwashe kayan akwai sauran kayayyakin ƴan'uwan yarinyar da za a kawo, ba su musa ba duba da yadda suka ga kwarjijinin tsohuwar, nan aka shigo da kayan Nainarh, Zakiyya, da kuma Rumaysa kowa sai son barka yake yi. Bayan an gama gani duba da ƙuratowar maghrib dangin ango suka buƙaci wucewa, nan aka fara shigar musu da tsarabar snacks ɗin da aka yi. Mommy Salaha da wannan damar tayi amfani ta samu damar ganawa da amarya, bayan tambayoyin da ta mata ta ba ta dukkanin amsoshi kamar yadda ta buƙata, daga nan ta bar ta tana tunani cikin ranta.
Bayan dangin Ya Ishaq sun koma, Mommy Salaha ta nunawa Mom lallai akwai matsala, ya kamata ta binciki ɗanta matsawar dai tana so bikin na ya tafi daidai in ba haka ba kuma mutuncinsu zai iya zubewa a idanun BABBAN GIDA. Daga haka itama ta wuce zuwa nata gidan.

***********************************************

Tsawon sati guda kenan aka ci gaba da yi wa amaren gyara, gyara kuma da yaci sunansa gyara sai dai i zuwa wannan lokaci Zahrah still na cikin muguwar damuwar rashin sanin makomarta a wurin husband to be ɗinta. Hakan yasa damuwar ta fara bayyana kanta a fuskarta sai dai ta gagara sanar da kowa duk da cewa iyayen nata da ƴan'uwan ta kowa cikin tambayarta yake musamman Mommah da yanzu take ji da Zahrah ɗin fiye da kowanne yaro cikin familyn tunda ta gama mata komai, ita ta raini little Sadaukin ta. To me kuma ya rage da ba za ta nuna mata ƙauna ba?.

Shirye-shirye sosai ake A BABBAN GIDA babu kama ƙafar yaro, kowanne sashe na gidan ya amsa da hakan ga yadda aka ƙara gyara da ƙayata gidan kai da gani ka san ba a taɓa bikin da ake ji da shi ba kamar wannan.
Ranar Talata ya kama da ranar da aka saka amaren a lalle, ranar laraba aka yi traditonal day wanda event ɗin sosai ya ƙayatar musamman yadda aka nuna al'adu, Ranar Alhamis kuma aka gabatar da Mother's ev. Sosai aka soshale domin kuwa kowa dai a zahiri cikin farin ciki yake hatta Rumana da yanzu tsakaninta da zahrah ya rage murmushi, duk lokacin da za su haɗa sai ta murmusawa Zahrah wanda hakan ke matuƙar ba wa Zahrahn Mamaki.

Bayan an tashi a mother's ev, kowa ya koma kan shirye-shiryen washegari, a daren nan ne Nasreen ta tsare Zahrah ala dole tana son sanin me ke faruwa da ita? Duk yadda tayi Zahrah ta ƙi sanar da ita komai. A raunane Nasreen ɗin tace "May be it's because ni ban yi aure ba yasa kike damuwa, right?"
Da sauri Zahrah tace "No sister"
"Then why?" ta tambayeta. A wannan karon sosai Zahrah ta yi rauni, ace ango ya ƙauracewa ganinta tsawon makonni biyu da kwanaki?, tuni ta fashe da matsanancin kuka. Lallashinta Nasreen tayi da ƙyar ta iya faɗa mata dalilin damuwarta da sharaɗin ba za ta faɗawa kowa ba. Sosai Ran Nasreen ya ɓaci kan abunda Ya Ishaq yayi wa ƴar'uwarta kuma ta ɗau alwashin sai ta tabbatar masa da kuskurensa. Jawo ta Zahrah tayi tana faɗin "Remember kin yi alƙawarin ba za ki yi confronting nasa ba." cike da ɓacin rai Nasreen tace "Babu wanda ya isa dakatar da ni wallahi, ba a yi halittar da za ta....."
Ba ta kai ga ƙarasawa ba Hajjaty ta shigo ɗakin tana ƙwalla ƙiran Zahrah. Tare da Nasreen suka fita don amsa ƙiran. "Yauwah Zahrah'u, maza sauri ki zo parlour."
Da "To" duk su biyun suka amsa suna bin bayan hajjatyn. Turus! Zahrah ta ja ta tsaya ganin fuskar da ba za ta taɓa mantawa da ita ba a parlourn.

*In har kuna so na ci gaba fa ya kamata kuna reacting tare da sharing, in ba haka ba zan ji kamar ba kwa ƙaunata. Help me and show me love by reacting please.*

[15/04, 11:23 AM] Diamond Bhatool: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 4⃣8⃣




*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*


Ɓangaren hagu ta kai dubanta nan ta ga Mamah sai sharar ƙwalla take, hakan ne ya tabbatar mata da cewa shi ɗin ne bai gizo ya mata ba. Daga wurin da take tayi pointing ɗinsa da yatsa a tsorace tana faɗin "you? What brought you here?". Hannunta taji an ja hakan yasa ta bi mai jan nata, zaunar da ita Hajjaty tayi tare da zama itama har zuwa lokacin kuma mutumin bai daina bin Zahrah da kallo ba yana jijjiga kansa yayin da fuskarsa ke nuna tsantsar mamaki da al'ajabi.

Gyaran murya Alhaji Baba yayi wanda yayi daidai da shigowar Daddy da Alhaji Babba, bayan sun zauna Alhaji Baba ya fara magana yana mai duban Mamah dake famar share ƙwalla sannan ya dubi Malam Babayo da ya rako mutumin.
"To Malam Babayo muna sauraronka, grin ya kuka bar wannan mutumin ya shigo ne?"
Cike da girmamawa yace "Ranka shi daɗe ai wannan mutumin in ba a bar shi ya shigo ba inaga mutuwa zai yi, sojoji sun hana shi shiga amma ya kafe yana kuka yana faɗin ko za su kashe shi wallahi ba zai koma ba sai ya ga Ƴar sa, da ƙyar da siɗin goshi ya yadda ya koma inda ya fita jiya amma yau sai ya fara burburuwa hakan yasa suka ce na rako shi ya shigo idan ya so kowanne hukunci kuka yanke ya wadatar." ya idasa tare da sunkuyar da kansa ƙasa.

Gyaran murya Alhaji Baba ya kuma yi a karo na biyu yana duban mutumin "Malam, ka ce wurin ƴarka kazo, wacece ƴar taka?" kamar wadda yake jira a ba shi damar magana ya nuna Zahrah da yatsa yana fadin "Ga ta nan, ga ta nan Zahrah, ai ƴata ce."
"Too ana wata ga wata, ke Zahrah'u kin san mutumin nan ne?"
Caraf yace "Ta ma isa ta manta da ni ina ubanta?"
Tsawa Daddy ya masa yana faɗin "ba ka da damar magana sai an ba ka dama!"
Murmushi irin na manya yayi yace "Zahra'u muna saurarar ki."
Cike da zafin rai ta nuna Kawu da ke sakin murmushi tace "Alhaji wannan shine Kawu Idrisu, mutumin nan dai da ya cutar da rayuwar ɗiyarku ya kuma sanya ta a ƙangin wahala, wallahi Alhaji na tsani mutumin nan kuma..."
"Ya isa haka Zahrah, zauna" Alhaji Baba ya dakatar da ita.
"To Bawan Allah idan na fahimta daidai kai ne Idrisu ɗan'uwan Abdulkarim, ba za mu yi saurin yanke maka hukunci ba har sai ka faɗa mana da me kake tafe."
"Eh to gaskiya dama tun ranar da na ga wannan baiwar Allah Madina da kuma ɗan'uwana naji ina son kasancewa da ita, hakan yasa nabi duk wata hanya da za ta sa na raba su sai dai ban ci nasara ba, daga ƙarshe kuma na kashe ɗan'uwan nawa saboda son zuciya da ƙaunar abun duniya." ƙwalla ya share sannan ya ci gaba "Bayan na kashe shi sai da na haɗa da siddabu irin na tsafi tukun ta amince da aure na kuma na sanya tsanar duk wanda zai kawo mata zancen gida tare da mantar da ita gida da ahalinta. Tun daga wannan lokaci da na ga na mallake ta na fara dasa ta kan ƙangin wahala har sai da ta jigata amma daidai da rana ɗaya ba ta taɓa yunƙurin neman haƙƙinta daga gare ni ba, hakan kuma bai sa na saduda ba, a lokacin da ɗiyarta Zahrah ta fara tashi ne ma take yunƙurin samar mata ƴanci...."
Nan ya ba su labarin irin wahalarwa da izayar da ya gana musu tsawon zamansu sannan ya ba su labarin Aunty Amarya da asirin da ta masa, shima lokacin da asirin ya sake shi da ya dawo gidan bai tarar da su ba sai ma kwaɗo da ya gani garƙame da gidan, lokacin da ya bincika kuma sun riga sun sayar da gidan shi kuma ya tashi a babin zero da kuma ƙudirinsa na nemo Mamah da Zahrah a ko'ina suke a faɗin duniya.
"A lokacin da na dawo na ci gaba da sana'ar da nake yi ina ci gaba da neman Madina, sai dai sam babu buɗi, a haka wasu ƴan jagaliya suka ja ni cikin team ɗinsu na ɓarayi, da farko dai akwai samu a harƙar sosai kwatsam ƙaddara ta faɗo min, wata rana mun Kai hari gidan wani ɗan siyasa a can Bauchi tsautsayi ya afko kaina, har mun yi satar muna shirin ficewa sai ga ƴan sanda sun mana ƙawanya, a ƙoƙarina na tserewa ne suka harbe ni a ƙafa amma na sha yayin da sauran ƴan'uwana kuma duk aka tafi da su, bayan an cire min harsashi ne wajen ya zama gyambo wasa-wasa har cancer ta shiga wurin ban sani ba saboda samun abun da zan ci ma matsala bare kuma zuwa wani asibiti a haka har dai abun ya ci tura daga ƙarshe aka yanke ƙafar wanda da ƙyar aka samu kuɗin aikin daga wurin wani ɗan siyasa. Bayan ciwon ya ware ma haka na ci gaba da shan wahalar rayuwa, hakan yasa na shiga cikin miskinai don samun abunda zan ci ashe ban sani ba ɗaya ƙafar ma ta kamu, babu jimawa kuwa ta fara nuna alamun hakan, a lokacin da za a cire wannan ƙafar na ci azaba ba dan wata ƙungiya sun kawo agaji ba na tabbata da yanzu ciwon ya riga ya matar da ni." Ajiyar zuciya ya sauƙe yayin da parlourn yayi tsit, masu rauni cikinsu suna tausaya masa a ɓangaren Daddy kuwa Allah Allah yake ya gama labarin nasa domin ya hukunta shi bisa cutar da tilon ƙanwarsu da yayi.

Wata zazzafar ƙwalla kawu ya goge tare da ci gaba da magana "Na san cewa alhakin Abdulkarim ne yake bibiyata da kuma iyalansa da na cutar ido rufe saboda abun duniya wanda ga shi yanzu yadda nake karɓan hukunci na tun a gidan duniya. Amma ko babu komai na yi farin ciki da suka dawo cikin dangi ko ba komai sun ƴantu daga uƙuba ta."
"Tabbas duk wanda ya cutar da wata rai ubangiji ba zai bar shi ba, abunda ba ku sani ba yanzu haka cancer ɗin da nake fama da ita ta jini ce, kuma likita ya tabbatar min da cewa ba zan yi tsawon rai ba. Alhamdulillah da ubangiji ya nuna min ku a wannan gaɓar.." hannunsa biyu ya haɗe alamar neman alfarma sannan ya ce "Ina neman afuwar ku Madina da kuma Zahrah wanda ku nafi cutarwa, haka nan kuma ahalinsu kuma ina roƙonku da ku yafe min bisa cutar da jininku da nayi duk da na san ban cancanci yafiya daga gareku ba, amma ku duba ba don hali na ba ku yafe min, sannan gani nan gabanku ku min duk irin hukuncin da kuke ganin in kunyi zai sa ku huce ko da kuwa raba ni da numfashina ne." nan ya fashe da kuka har lokacin kuma hannayensa suna haɗe wuri guda.

Wannan kare ba iya su Mama bane ke kuka hatta su Zahrah hawayen suke sharewa. Shiru ne ya wanzu tsawon wani lokaci kafin Alhaji Baba ya ci gaba da magana.
"To, Alhamdulillah, ba mu da wani abu da za mu ce sai godiya ga mahaliccinmu, babu shakka mun shiga halin ƙunci na rashin Madina amna lokacin da ta dawo garemu mun yi farin ciki maras iyaka musamman da ta zama biyu, babu shakka abun da ya faru da kowanne bawa ƙaddara ne kuma mun yi imani da hakan, shiyasa ma lokacin da Zahrah ta zo garemu ba mu nemo ka ba, ba wai don ka fi ƙarfin mu ba ko kuma ba za mu iya ba, sai dai mun amshi hakan matsayin ƙaddara, saboda mun san ko ba daɗe ko ba jima sai ka neme su, haƙƙinsu kaɗai ba zai bar ka kaji daɗin duniya ba. Ba ma wannan ba, ni ba zan tursasa waɗanda aka zalunta ba da su yafe maka ba, amma ga ka ga su, idan sun yafe shikenan, in kuma ba su yafe ba ma mu ba zamu hukuntaka ba, sai dai su suka buƙaci hakan don karɓar hakƙinsu."

Mamah ce ta share hawayen da suka jiƙa fuskarta cikin dasasshiyar muryarta tace "Baba ni dai ta ɓangarena na yafe, ubangiji ya yafe mana baki ɗaya."
"Kin yafe kika ce? To wallahi ba za mu bar shi ya ci bulus ba Madinah, sai ya san cewa ya taɓo ƴar dangi.!" Daddy ya faɗa a fusace. Murmushi irin na manya Alhaji Baba yayi kana ya mayar da kallonsa ga Daddy yace "A'a Umaru, tunda har ta yafe ina ga babu wani abu da za a masa, Allah ya yafe mana baki ɗaya, Zahrah me za ki ce?"
Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyin jiki tace "Alhaji nima na yafe, Allah ya yafe mana baki ɗaya."
"Amin" duka mazauna parlourn suka haɗa baki.

Nan Alhaji ya ci gaba da magana "To Idrisu, ina fatan za ka gyara rayuwarka a sauran lokacin da ya rage maka ka zama mutumin kirki wanda duniya za ta yi alfahari da shi, ba za mu hana ka ɗaukan ƴar ɗan'uwanka ba saboda addini ya ba ka iko da ita fiye da mu, saboda haka in ka buƙaci hakan babu yadda za mu yi sai ka tafi da ɗiyarka."
Dum! Gaban Mamah ya buga jin wani batu daga Alhaji Baba sai dai amsar da ta ji Kawu ya fara bayarwa yasa ta sauƙe ajiyar zuciya.
"A'a Alhaji, ai babu wannan batu kuma, zan fi so Zahrah ta ci gaba da zama ƙarƙashin ku saboda ku ne gatanta, me na taɓa tsinanawa rayuwarta da shi na alkhairi??" hawayen da suka silalo ya goge yace "Wallahi ba zan taɓa raba ta da ku ba ko da a ce ba ni da wannan ciwo na cancer ta jini, saboda haka na mallaka muku ita halak malak ta ci gaba da kasancewa da ku." ya idasa cikin raunin murya.

Sosai jikin kowa yayi sanyi ciki kuwa har da Daddy a wannan karan, Alhaji Baba ne ya ƙara murmusawa yace "To madallah, muna godiya sosai Idrisu, in sha Allah za mu riƙe amanar ka ko da kuwa bayan ranka ne duk da ba mu san waye gawar fari ba. Sannan kuma na yi farin ciki da zuwanka don gobe jama'a za a ɗaura auren Zahrah."
Muruushi Kawu yayi tare da faɗin "Ma sha Allah, Allah ya ba mu ikon shaidawa ya biya ku da gidan Aljanna."
"Amin" suka amsa a jumlace.
"Ban san ko cikinku akwai mai magana ba, in babu inaga a kai Idrisu masauƙi."
Shiru suka yi alamar babu mai magana, daga nan aka raka Kawu masauƙi sannan su ma kowa ya kama wurin zamansa.

Nan Zahrah ma ta koma cikin ƴan'uwanta tana mai tausayawa Kawu irin sosai ɗin nan, abun da ya faru ya sa ta manta da wani batun damuwar da ita kanta take ciki. A daren kwana Zahrah tayi tana sallah tare da roƙar ubangiji waraka da kuma samun sauƙi daga damuwar namiji. A kan sallayar ma bacci ya ɗauketa ba ita ta tashi ba sai da aka fara assalatu.

#A_babban_gida
#diamond_bhatool

*Lots of love my people, Share and react fisabilillah.*


[16/04, 5:16 PM] Diamond Bhatool:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 4⃣9⃣




*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*

*MORNING*
Asussubahi aka Fara aikace aikacen biki, masu aminci tuni suka Fara ɗaura tukwane suna sauƙewa, ta kowanne sashe na gidan mutane ne ke kai kawo, gida ya cika babu masakar tsinke duk kuwa irin yalwa da faɗin gidan fal baƙi suka cika da waɗanda aka gayyata da ƴan gayyar soɗi irin su Maryam Muhammad, su Ummee, kai har da Maman Khalifa ma duk fa don su samu su ci abincin ƴan gayu ne.

Haka ta kasance a sashen Mamie taron jama'a kamar su yi yaya sai gutsiri tsoma suke kan lefen jiya, Kausar sai cika take tana batsewa kayanta ba su kai na waɗancan shegu huɗun ba duk da irin zaɓin mijin da tayi. Wasu na ƙara yaba kaya musamman na Zahrah da ya fita daban yayin da mahassada ke faɗin ai kuɗin sata ne tunda jinin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login