Showing 30001 words to 33000 words out of 157517 words

Chapter 11 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5136

da veil suka tsira mata ido.
She look so awnn and breathtaking. Ganin ta Yi Shirin fita yasa Zakiyya faɗin
“Bari na je na ɗan huta Please, xan dawo anjima kafin nan kun dawo.”

“Nan ɗin ba wurin hutawa ne sai kin koma can?” Zahrah ta tambaya.

“Tsaya muje Zakiyya nima zan wuce, Mommah ta ce min Yaya Sadauki ya dawo, In ya koma bai tarar da Ni ba zai hukunta ni.”

Nan suka wuce suna ɗagawa Zahrah hannu “Ki kawo mana tsaraba kuma.”

Nasreen da Rumaysa zamansu suka yi nan Bedroom ɗin Zahrah ita kuma ta fito parlour tana jiransa.
Few minutes sai ga Yaya Sadauki cikin takunsa na ƙasaita, sanye yake cikin wata back expensive T-shirt gaban an rubuta SPORT sai Kuma blue-black jeans Wanda ya ɗan kama shi kaɗan. Black takalmi ne a ƙafarsa, taku yake kamar wani basarake yayin da ƙamshin turarensa ke isa wuri kafin shi.

Agogonsa da ke ɗaure a tsintsiyar hannu ya duba ganin da sauran lokaci yasa kai tsaye ya nufi Bedroom ɗin Hajjaty ya mata sallama kan sun tafi. Ko da ya fito bai ce mata uffan ba sai yayi waje, ta riga ta gane cewa miskilanci a jininsa ne hakan yasa ta miƙe tabi bayansa.

Motar da ya nufa ta ƙarewa kallo tana ƙara yaba kyanta, horn ɗin da yayi mata yasa ta Zabura ta nufi motar, gidan baya ta buɗe da niyyar shiga ta tsinkayi muryarsa yana faɗin.
“Ni drivern ki ne?” ai tuni ta rufe ta koma front seat ta Zauna.

Wani makeken shopping mall ya nufa da ita yayinda kowannensu ya ƙunshe bakinsa in Banda sautin karatun Minshawiy babu abinda ke tashi yayin da Zahrah ke ɗan satar kallonsa time to time tana ayyana irin nutsuwarsa.

15minutes suka share kafin suka isa, bayan ya daidaita parking ne ya juyo gareta

“Let's go” daga haka ya buɗe side ɗin da yake haka nata ɓangaren ma. Tunda duka fito mutane ke kallonsu musamman Yaya Sadauki da ya shahara a faɗin ƙasar ba don saboda tarin dukiyar da yake da shi ba sai don ƙwazo da ubangiji yayi masa, he's the head as well as founder of NIC, mutumin da ya samu ƙwarewa a fannin bincike sannan kuma the whole CEO of Abatcha Automobiles Wanda ke ji da kuma tashe da samartaka.

A tare suka nufi entrance na makeken mall ɗin, wasu na faɗin
“Anya wannan ba ALIYU UMAR ABATCHA ba ne?” others are worried about the lady he's with Suna fatan ba aure yayi ba, wasu ƴanmatan kuma na faɗin ai ko ya yi aure suna son shi, mathna wa thulatha wa rubā', wasu kuma na faɗin maybe ƙanwarsa ce don da gani ba aure tsakaninsu. To shi ya ma san suna yi ne?”

Kallon Zahrah yayi bayan sun shiga yace
“Go round and pick anything you like, kada ki damu da ya yake just pick it ok?”

Kai ta gyaɗa Masa daga haka ta nufi ciki, tsawon mintuna amma ta kasa zaɓar komai, kamar ya sani kuwa sai ya bi bayanta, ganin babu abunda ta ɗauka yasa ya ɗan ja ƙaramin tsaki.

Komawa yayi sai ga shi tare da ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin, pointing ma Mai aikin Zahrah yayi wacce ke tsaye still ko uban me take. Ban ji me yace masa ba sai ga Zahrah ta dawo wurin sa da zuwan mutumin. Daga nan Yaya Sadauki yace su fito su jira a mota.

Ba musu tabi bayansa suka koma. Kusan 10 minutes sai ga mutumin nan da wasu masu irin kayansa sun fito su uku yayin da hannuns kowannensu ke ɗauke da akwati. Motar su Yaya Sadauki suka nufa, dama booth a buɗe yake, so basu sha wahala ba suka ajiye kana mutumin yazo ta saitin da Yaya Sadauki yake ya miƙa masa ATM card ɗinsa, har ya karɓa mutumin na shirin juyawa ya tsayar da shi sannan ya miƙa masa wasu kuɗaɗe masu ɗan yawa.
“Thank you” mutumin ya fara godiya kenan Yaya Sadauki ya ɗaga masa hannu. Nan ya basu hanya su kuma suka wuce abun su.

Ba tare da Yaya Sadauki ya kalli Zahrah ba yace
“Why didn't you pick anything? Ko babu abun da ya burge ki a wurin ne?”.

Har ta jijjiga kai ta tuna da ba ya so, da sauri ta buɗe baki tace
“A'a ban san ya kuɗin abubuwan zai kasance ba, kada na ɗauki masu tsada da yawa na karar maka da kuɗinka.”

Statement ɗinta na ƙarshe ne ya bashi dariya har sai da ya murmusa ita kuma sai kallonsa take ganin yadda wani sihirtaccen kyau ke fitowa daga gare shi cikin ranta ta furta “Tabarakallahu Ahsanul Khaliqin”.

“An ce miki kuɗi na zai ƙare ne for common shopping da zaki yi? Ai ko mall ɗin zan siye babu wani giɓi da kuɗaɗe na zasu samu.”

A ba zata ta furta
“Ka ji daɗin ka”

“Ke ma kina son kuɗin ne?”

Dariya Zahrah ta kwashe da ita jin ya mata wata irin tambaya har sai da dimples ɗinta suka lotsa, duk irin yadda yaso ya kauda kansa kasawa yayi, sai ya tsinci kansa da faɗin
“Kina da kyau” tukun ya mayar da dubansa ga titi.

“Kai Yaya ai kuwa ka fi Ni, duk duniyar nan ban taɓa ganin kyakkyawa kamar ka ba, da ina cewa Yaya Ishaq ne amma tun da na ganka na tabbatar babu ya kai.”

Kalamanta sun masa daɗi ta ɗaya ɓangaren kuma sun bashi dariya amma a wannan karan dariyarsa yayi ga yadda fararen haƙwarensa suka bayyana, Zahrah kam kasa daina kallonsa tayi.

“You're funny Zahrah, Wai kina nufin na fi kowa da, to ina batun Indian”

“Allah Yaya ka fi su musamman when you smile, sai ka ƙara kyau.”

“Uhm” kawai yace ganin sun doso katafaren gate na estate ɗin su. Bayan sun iso yayi parking a apartment ɗin Hajjaty.
A hankali ya furta “You can go, Ni zan wuce part ɗin mu, Please in baki gaji ba cook something for me.”

“Ok Yaya thank you, may God bless your wealth and Grant you jannah.”
Ya ji daɗi sosai da addu'arta har sai da ya murmusa sannan yace
“Amin Lily, Zan sa a shigo da kayanki yanzu, take care.”
“Ok bye” ta faɗa tana waving hand ɗinta sannan ta shige ciki shi kuma ya ja motarsa zuwa part ɗin su.

Ashe duk abun da ke faruwa a idon Rumana ne wacce ta kusa mutuwa don mamaki da tsananin kishi, wai a wannan yarinyar Yaya Sadauki yake wa murmushi? Yaushe ma yazo?, Tsabagen yadda zuciyarta ke tafasa da gudu ta tafi tana kuka har part ɗinsu without minding the distance.

Ita kuwa Zahrah tana shiga ta tarar da Hajjaty na zaune ita da Ya Auwab, Ya Taj, Ya Aufa da kuma ya Faruq, kan ta ƙasa ta ƙarasa. Fuska sake Hajjaty tace
“A'a Zahrah'u an dawo kenan, ina shi Sadaukin?”

“E Hajjaty ya wuce part ɗin Mommah.”

Shaye da mamaki Ya Auwab ke kallon Hajjatyn kana yace
“Hajjaty wane Sadaukin? Wai Yaya dodon mu?”
Sosai Zahrah ta dara duk da cewa she's not comfortable being in-between them saboda yawan kallo irin na Ya Auwab.

“Shi dai, ai tun jiya ya iso shi da Halilu.”
Zahrah dai wucewa tayi zuwa Bedroom ɗinta, kamar yadda tayi zato none of them was there. Wanka ta Yi ta ɗauro alwala, tana idar da Sallah ta yi zikirorinta sannan ta nufi kitchen don haɗawa Yaya Sadauki abinci.

*Yaya Sadauki*

Lokacin da ya isa ma an fara kiraye-kirayen sallah, hakan yasa ya haye sama don yin alwala, kamar yadda Mommah tayi alƙawari ta sa na gyara masa Bedroom ɗinsa. A gaggauce yayi wanka sannan ya ɗauro alwala, yana saka kaya ya fito sai sauri yake jin an shiga sallah a masallaci.

Bai wani tsaya ba da aka idar kuma bai bi su Alhaji Baba ba sai ya juya zuwa ɓangarensu don samarwa mahaifiyarsa lafiya. Ita ma lokacin tana parlourn ita da Nainarh sai kuma auta Ra'ees. Da gudu Rarrashi ya nufi Yayan nasa yana ihun murna
“Oyoyo Yaya, oyoyo Yaya.”

Hugging nasa yayi shima yana murmushi coz he so much adore that little creature.
Tare suka ƙarasa. Cike da farin ciki Nainarh ta gaishe shi tana faɗin yaushe ya dawo?, Kallon da ya aika mata yasa ta miƙe tsaye ta nufi Bedroom ɗinta. Kallon Ra'ees yayi yace
“My Man, maza ka bi Aunty Nainarh ka ce ta koya maka karatu.”
A shagwaɓe Ra'ees ɗin yace
“Yanzu Aunty Nainarh duka na zata yi, da ba ka nan ma kullum sai ta je wajen Aunty Zahrah da Mommah ta hana naje na ganta,kuma Aunty Nainarh tace kyakkyawa ce, wai haka ne Yaya?”

“Uhm, yanzu kace Ni na aiko ka ba zata dake ka ba kaji.” daga haka Ra'ees ɗin ya wuce shi kuma ya maida dubansa ga Mommah. Cike da girmamawa ya gaida ta ta amsa fuska babu yabo babu fallasa.

Suna gama gaisawa tace
“Aliyu ya zancen aurenka da yarinyar can? Ka samu ka shawo hankalin Alhaji Baba?” dariyar takaici yayi cikin ransa yana ƙara nema mata shiriya.

“Mommah ai babu fashi auren nan, nima ina so fa”
A zabure tace
“Uban me suka ba ka Aliyu, yaushe ma kake kula matan ballantana har ka ce kana son ta, wallahi ƙarya kake kuma baka isa ka auri ɗiyar Hajiya Babba ba.”

Ganin yadda ta ɗau zafi yasa ya kwantar da murya yace
“I'm sorry Mommah, calm down please” tea ɗin da ke ajiye kan Centre table ya miƙa mata
“Shikenan mu bar zancen tunda baki so, mu yi wani daban.”
Haka suka sha hirar su daga nan kuma ya fice saboda lokacin salla da yayi. Bayan an idar kuma ya wuce da Alhaji Baba.

Shi da kansa ya shiga da akwatinan da ya manta bai sa an miƙa mata su ba tun ɗazu. Laraba da ta Ganshi da sauri ta karɓa nan ya faɗa nata inda zata kai. Dayan ya koma ya ɗauko sannan ya nufi ciki.

Nan suka yada zango a parlourn ana ƴar hira. Sallamar Yaya Khalil ne ta dakatar da su daga maganar. Bayan ya shigo gefen Man ɗinsa ya zauna, suna gaisawa da Hajjaty da kuma Alhaji Baba aka ci gaba da hira.

“Nifa abinci ne ya kawo Ni nan bayan gaida tsofin nan, a tashi a ci abinci Please.”

“To foodie, you'll never change.”
Dama aikin Yaya Khalil ne In dai an fara hirar nan shi ke tuna musu da abinci. Babu musu kuwa Hajjaty ta ƙwala ƙiran Zahrah.

Ita tayi serving ɗin su ganin bata sakawa Yaya Sadaukin ba yasa Yaya Khalil faɗin
“Ke Zahrah abun naku har ya kai haka? Ni na haƙura da nawa ki miƙawa Sadauki.”
Ƴar bazawarar dariya tayi har sai da sautin ta ya fita.

“Haba Yaya Khalil, ci naka kawai, na Yaya na ai daban yake da na kowa.” ba iya Yaya Khalil ba har Yaya Sadauki sai da ya kafe ta da ido. Su dai tsofin abincinsu suka ci gaba da ci. Ganin yadda suka kafe ta da ido yasa ta ɗan kau da kanta gefe sannan ta buɗe foodflask tayi serving nashi.

Nan Yaya Khalil ya tubure ala dole shima wancan zai ci, Yaya Sadauki yace ai ba wannan zance kowa yaci nasa. Da ƙyar dai ya bari Zahrah tayi serving Yaya Khalil ɗin karo na biyu sannan ita ma ta zauna tana ci.
Ko da suka gama Yaya Khalil sai mitar wariyar da Zahrah ta nuna yake, ita kam abun ma dariya yake bata.


*React and Comment Please, Diamond 💎 Bhatool 🦋 taku ce.*


[12/28, 9:19 PM] Diamond Bhatool:

*🏡A BABBAN GIDA*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*




*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_


_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow

*PAGE* 1️⃣5️⃣

_Gabaɗaya sannan shafin sadaukarwa ne ta musamman gare ku mutanen channel ɗina ~Diamond Bhatool Reading Club (DBRC)~ alkairin Ubangiji ya kai gare ku a duk inda kuke. Ku sani ina matuƙar godiya da yadda kuke nuna min ƙauna, wallahi ina don ku irin da yawan nan. ILYSM🦋💞_

                                  ﷽

Sai da kowa ya tashi a wurin ga rage iya Yaya Sadauki ne da Zahrah wacce ke jira tayi masa godiyar kayayyakin da ya sa aka jida mata. Fahimtar hakan yasa ya ɗago ya kalle ta yana goge bakinsa da tissue.

“Ehn” yace yana ɗage mata gira.
“Yaya, thank you so much, words ain't enough to express how much deeper I appreciated, you are not only a brother but a father himself. Jazakallahu khairan Yaya na.”

“Uhm Ameen Babu komai, bana son godiyar nan ma, all I did na Yi ne saboda Allah, and you indeed deserve it. Thanks for the food.”

Tura baki tayi tace “I don't like the thank you also, Nima na Yi ne saboda Allah and you deserve the tasty and handsome food from me.” (Kun ji wai handsome food😳🤣)

“Ey? Who say your food is tasty? Wai ma handsome, hhhhh I'm only managing to take it saboda kar ki ji babu daɗi, amma sam baki iya girki ba.”

Zaro ido Zahrah tayi tana kuma shagwaɓe fuska lokaci guda
“To In haka ne nima ka biya ni kuma ka daina ci tunda ba daɗi ai su Hajjaty zasu ci.”

“Waye ya ce miki zasu iya ci?, Tab! Lallai baki san duk wanda ya kai girkin nan naki bakinsa ba lallai ya iya ƙara sha'awar abinci ba har ya mutu?.”

“A'a a'a wallahi I know that I prepare the tasty and delicious meal you ever tasted, you're only beating around the bush, Kuma daga yau ban ƙara yi maka.” ta faɗa tana miƙewa tsaye bakin nan gaba kamar shantu, shi abun nata ma dariya ya bashi. Buguzum ta ja kujerar baya tana shirin ficewa taji ya dakatar da ita cikin murya mai cike da umarni.

“Don't You dare add a step in ba Haka ba sai na ɓalla ƙafar, come back.”
Juyowa tayi kamar zata yi kuka saboda takaici.

Muryarsa ya sanyaya yace
“I'm sorry Lily, kin ga wasa nake, girkin ki ba dai daɗi ba, Mamah dai ta yi raino mai kyau don duk ƴanmatan gidan nan babu wanda zai iya irin girkin nan naki.”

Lokaci guda Zahrah ta saki wani murmushi tana faɗin.
“Ai dama na sani, Babu wadda zai ci girkin Zahrahn Mamah bai yaba ba. Thank you Yaya na.”

“Uhm nace ba”

Hankalinta kwacakom ta mayar gareshi

“In na yi aure zan ɗauke ki kike mana girki Ni da mata ta.”

Dimm! Zuciyarta ta buga, sai kuma ta zaro ido gudun kar ya gano ma ta tsoratan nan.

“Tab ɗin, Zahrahn Mamah ce zata muku girki?, Allah ya sauwaƙe Barrister Zahrah ta muku girki?”
Ido waje shima yake kallonta musamman yadda tayi kici-kicin da fuska.

“Do You mean ba Zaki yi min ba kenan har kike faɗin Allah ya sauwaƙe?” baki ta turo bata ce komai ba

“Shikenan tunda ba zaki min ba ai. Tun yanzu Gara na daina ci kada na saba kuma daga baya na sha wahala.”
Da sauri tace
“Ni fa ban ce haka ba Yaya, kawai dai sai nayi muku girki kai da wata gardiya?”

Ido ya zaro yana kallonta musamman yadda hankalinta kwance take magana babu wani shakkar sa kamar yadda sauran mutanen gidan ke ji.

“Me kika ce?”

“Wallahi suɓutul kalam ne Yaya na, ai matarka kam ƴar suwalwala ce kamar yadda kake ɗan suwalwali.”

Ɗan suwalwalin da tace ya sa shi dariya sai da ya dara, yana ƙara mamakin yadda take. Lokaci ɗaya kuma ya dakatar da dariyar da yake yi ya kalle ta.
“Lily? Are You that talkative?”
Da hannunta ta ƙunshe bakinta tana dariya.

Wayarsa da tayi ringing ya fitar, ganin Yaya Khalil ne yasa ya ɗan ja tsaki, sai a lokacin ya tuna da cewa a dining area suke, kallonsa ya kai ga parlourn babu kowa sai Hajjaty da Yaya Khalil, Alhaji Baba already ya shiga ciki. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da katse kiran. Kallonsa ya mayar gare ta yana faɗin.

“Ni zan wuce Lily, kar ki manta gobe zan kai ki school and I dislike African time.”

“Zan shirya da wuri in Sha Allah, Bye Yaya na.” daga haka ya wuce ita ma ta nufi Bedroom ɗin ta.

Nan ta fara buɗe kayayyakin da ya sa aka kwaaa mata wanda tunda take bata taɓa tsammanin ko rabinsu zata samu ba a rayuwa. Sosai ta yaba da kyansu tana ƙara godewa Allah tare da addu'ar Allah ya bayyana Mamah, Thank you thank you kam Yaya Sadauki ya sha ta, tunda ta fara buɗewa take faɗa har ta gama. Tana gamawa ta fitar da kayan kwalliya ta jera kan mirror, masu buƙatar a kai su toilet ma ta agaza Musu zuwa masauƙinsu.

Nan ta fito kayan ta jera cikin closet, sannan ta ware waɗanda zata saka gobe tare da takalmi da handbag. Toilet ta faɗa tayi wanka sannan ta saka night dress daga cikin sabbin da tayi daga nan ta faɗa gado tana Allah Allah gobe tayi.
(Sweetest dreams Zahrah.)

A nasa ɓangaren ko da ya ƙarasa parlourn bai bi ta kan Yaya Khalil ba saboda ya san halin kayansa, yanzu zai tusa shi gaba da zolaya. Gefen Hajjaty ya zauna yana faɗin
“Tsohuwar nan ina mijinki ne?”

“Ungo nan” tayi masa daƙuwa

“Ai yau ba wajensa kazo hira ba.”

Harara ya bankawa Yaya Khalil da yayi magana kana ya ce
“Hajjaty daga tambaya kuma? To bari na tafi kawai.”

Hajjaty tace “Ai dama ba wurin mu kazo ba yau kam, Allah ya tsare hanya.”

Kwaɓe fuska yayi yana kallon Hajjatyn wacce ta haɗe rai, shi dariya ma ta bashi Wallahi.
“Tuba nake, kaina bisa wuya, a yafe min sarauniya ɗaya a gidan Alhaji Muhammad Abatcha, tsohuwa mai ran ƙarfe kuma.”

Lokaci ɗaya Hajjaty ta fashe da dariya tana faɗin
“Allah ya shirye ka Sadauki, kwanan nan naga alamar ka fara barin mugayen ɗabi'unka na miskilancin, ai yafi maka ma. Ni kaga bacci ma nake ji, bari na wuce sai da safe.”

Dariya shima yayi yace
“To a tashi lafiya Hajjaty”

“Kai kuma...” ya faɗa yana jefawa Yaya Khalil wani mugun kallo mai bayyana zuwa haɗu daga haka ya nufi Bedroom ɗin Alhaji Baba. Yaya Khalil kuwa dariya ya yi daga nan shima ya wuce zuwa part ɗinsu.

Lokacin da Yaya Sadauki ya shiga ciki Alhaji Baba har ya gaji da jiransa ya fara gyangyaɗi. Sallamarsa ne tasa ya wartsake. Yau basu daɗe ba sosai coz tattaunawar gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne ga batun auren Yaya Sadauki da Aunty Mabruka, Nan Alhaji Baba ya ƙara gaining consent ɗin Yaya Sadaukin lokaci ɗaya shima ya nuna goyon bayansa tare da fatan Allah yasa hakan shine mafi alheri garesu. Fatansa dai a yanzu bai wuce ya maida hankali wurin gano masu yiwa ahalin zagon ƙasa da kuma ƙulla sharruka ba.

Ganin dare ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login