Showing 150001 words to 153000 words out of 157517 words

Chapter 51 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5157

Wayarsa keypad ya ɗauko ya ɗauki hoton sassan jikin ɗaya bayan ɗaya sannan ya mayar da wayar cike da tsoro.

Takawa ya fara yi cikin takunsa na ƙasaita ya nufi ƙofar da ya gani, subhanallah!!! Me zai gani, ƙwaryayyaki ne sun fi goma jere a jikin ginin da aka rufe bangonsa da Jan ƙyalle ta ko'ina, jan carpet ne shimfiɗe a ƙasa sai kuma mutum lulluɓe da jan ƙyalle a zaune da ƙwaryayyaki cike da jini a gabansa. Jiki na rawa Alhaji Baba ya ƙara ciro wayarsa ya fara ɗaukar komai a hoto, Allahn da ya taimake shi babu ƙara a wayar, yana gamawa ya juya saɗaf-saɗaf ya fice a ɗakin, da sauri ya bar gidan ya shiga motarsa cikin rashin hankali ya koma wancan gidan Babatunde.

Daidaita kansa yayi yace wa mai gadi shi fa bai gane gidan ba, bai ma ga irin gidan da ya kwatanta masa ba, mai gadin yace, "ba kai kaɗai bane, duk wanda na kwatantawa sai ya dawo ya ce bai gaba ba, amma akwai gidan," waigawa ya fara yi ganin babu kowa yasa yace "Ni kaina sau ɗaya na taɓa ganin gidan, kuma na kasa yarda da cewa abun ba rufa ido ba ne."
Dama ashe mai gadi neman abokin zance yake da yake shi bahaushe ne, su kuma masu gidan ba sa Hausa da Hausawa amma sarai sun iya.

Nan yace "Ina yawan ganin an shigo da yara gidan nan, haka mata, amma ba na ganin fitarsu, gidan yana ba Ni tsoro, Alaji gaskiya ba na tunanin lafiya."
Kamar Alhaji Baba bai san komai ba yace "Kuma ba ka taɓa shiga cikin gidan ba?"
"Ban taɓa ba Alaji, gaji na bakin ƙofar can" ya nuna masa ƙofar parlour, "Ina ganin akwai wani abu a gidan nan, kuma fa ba a taɓa yin baƙi a gidan ba, kai ne baƙo na farko da ya zo gidan nan."

Kai Alhaji Baba ya jinjina tare da ƙiran wayar Babatunde.
Bai ɗaga ba sai da ya ƙira sau uku, cikin wata iriyar murya Babatunde yace "Aminina, kwana biyu" gaban Alhaji Baba ya buga jin yanayin da yayi magana, amma sai ya waske yace "Ah nawan, lafiya ƙalau, shiru kwana biyu ban ji ka ba yasa na zo gidanka, ga Ni nan mai gadi ya hana Ni shiga"
"Ya hana ka shiga kuma?"
"Eh"
"Ba shi wayar, in Banda iskanci bai ga shigarka ba ne da zai hanaka shiga?"
Miƙawa mai gadi wayar Alhaji Baba yayi ya masa alama da ido. Mai gadi yasa wayar a amsa ƙuwwa.
"Kai me ya hana ka barin Aboki na ya shiga?"
Cikin rawar murya mai gadi yace "Alaji kai kace kar na bari ko waye yazo ya shigar maka gida..." Katse shi tayi yana rage murya yace "Yanzu dai kana ina? Koma gefe "
Da ido Alhaji Baba yace masa eh yaje.
"Yanzu yanzu ka shigar da shi ciki, dama jiran zuwansa nake, ka fara yi wa matar gidan magana, in ta fito kace ga Harrau!"
"To"
Daga haka yace "Kai masa wayar"
Karawa yayi a kunnensa "yi haƙuri nawa Alajin, yanzu zai maka iso cikin gidan."
"To" daga haka kiran ya tsinke.

Mai gadi ya dubi Alhaji Baba yace "Alaji me ka fahimta da hakan? Ya ce na maka iso in matar ta zo na ce mata Harrau ne!"
"Harrau?" Alhaji Baba ya maimaita cikin sigar tambaya.
Kai mai gadi ya jinjina masa.
Cike da tausayawa Alhaji Baba yace "kana son ranka da lafiyarka?"
Kai ya gyaɗa masa
"To ka tattara inaka inaka ka bar gidan kafin Mai gidan ya dawo kaima ya shiga ciki da kai kamar yadda yake shiga da wasu." A rikice mai gadin yace
"ALAJI ba ni da wurin zuwa"
"Kana da iyali ne?"
"A'a"
"To alhamdulillah, ta zo gidan sauƙi, yi maza ka biyo NI mu tafi kawai."

Babu ɓata lokaci su biyun suka fice suka shiga Mota, daga nan suka fara tsula guda, few hours suka koma Abuja.
Police station kai tsaye suka wuce sannan suka ba da information ɗin Babatunde da pictures ɗin duk da ba su fito da kyau ba saboda Camera irin ta da. Nan suka wuce gidan Alhaji Baba, shi kuma Alhaji Baba sanin cewa Babatunde zai neme shi yasa ya kashe wayoyinsa gabaɗaya.
Daga nan ya ba wa mai gadi ɗaki ya sauƙa.

Bayan nan shi kuma ya koma gurin matarsa, nan ya labarta mata komai, murmushi kawai tayi, ɗauke da ayar tambaya yace "ya kike murmushi?"
Hajjaty tace "Na gode Allah da ka gani da idonka, Ni tun ba yau ba nake zargin wannan Babatunde ɗin, na san ba ya son ka Wollah, na kuma san cewa yana son kawo ƙarshen mu ne, da sauƙi tunda yanzu ka gano shi, nifa dama can Yaren nan ba sonsu nake ba, don mugaye ne na ajin ƙarshe."
"Me kike nufi?"
Nan ta ba shi labarin kayan sunan da ya kawo a haihuwar Sadiqu, ta ƙara da faɗin "Dama wannan dukiyar tasa Ni tun ba yau ba na san cewa ta jini ce, shege, Wollah ƙarshensa dai ya zo da izinin Allah, don irinsu ba su cancanci ci gaba da rayuwa ba."

*React and share fisabilillah.*


[10/05, 12:50 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 7️⃣2️⃣






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*

A can ɓangarn Babatunde tunda abokinsa ya ƙira shi ya shiga tashin hankali, to me ya kawo shi? Ganin babu mai ba shi amsa yasa ya fara ƙoƙarin bincika allon tsafinsa cike da farin ciki yau dai kam zai kawo karshen Alhaji Baba tunda ya haɗa shi da Gabriella. Yana gama ibadar da yake ya sha jininsa ya ƙoshi sannan ya koma ɗakin farko, wannan jikin matar da aka lanƙaya ya sauƙo sannan ya tuɓe ya hau kai yana karanto wasu kalmomi da ban san me suke nufi ba.

*POLICE STATION, KADUNA*

Lokacin da suka samu ƙira daga babban ofishin ƴan sanda na FCT suka haɗa gayya suka nufi address ɗin da aka ba su, ko da suka zo unguwar sai suka kashe jiniyarsu, ta sama suka haura gidan, suna shiga suka nufi ƙofar da suka gani a buɗe, Abunda suka gani ya tsoratar da su, mutum yana jima'i da gutsirarren jikin mace, hasubunallahu wani'imal wakeel! Kusan dukkansu sandarewa suka yi suna ganin ikon Allah, Ogansu ne ya dawo da su cikin hayyacinsu ta hanyar daka musu tsawa, shi kansa Babatunde sai lokacin ya dawo hayyacinsa. Ganin mutane cikin kakin ƴan sanda yasa ya ɗan tsorata amma bai nuna musu hakan ba.
"You're under arrest"
Bai konɗago ya dubi ogan ƴan sandan da ke magana ba sai da ya kai ƙarshe ya miƙe tsaye yana shafa abarsa. Kallon shaƙiyyanci ya aika musu ya saki wani malalacin murmushi.
"Ya?"
Ogan ƴan sandan yace "you're under arrest!"

Dariya ya kwashe da ita yace
"Kun taɓa ganin yadda aka kama mutum a cikin ɗakinsa ba tare da an faɗi laifinsa ba?" Sai kuma ya haɗe fuska yace "Ku fice min a gida yanzu yanzu in ba haka ba kuma duk cikinku babu wanda zai bar wajen nan da rai, shashashu kawai."
Yana faɗin haka ya fara ƙoƙarin barin parlour zai koma can uwar ɗaka, da sauri ogan ƴan sanda ya saita shi da bindiga yana faɗin
"In ka kuskura ka ƙara taku guda babu abinda zai hana na harbe ka, idan za ka miƙa wuya tun wuri ka miƙa in ba haka har lahira zan aika ka yanzu."
Juyowa yayi yana duban ɗansandan, ko me ya tuna, sai ya dawo ya miƙa hannayensa biyu aka saka masa handcuff, daga nan suka wuce da shi office ɗinsu, aka bar wasu na ƙara bincika ɗakin don samar da shaida.

Wasa wasa abu ya zama babba, don duk yadda yayi tunanin abun zai zo ya wuce yadda yazo, hope ɗinsa ɗaya, itace Gabriella Amma ko sawunta bai gani ba, haka yayansa ma babu wadda ya gani, su kuwa suna gida a garƙame don ba su san me yake faruwa ba, sai da ranar meeting na ƙungiya yayi taga shiru mijinta bai zo ba yasa ta bincika a allon tsafinta, abinda ta gani shi ya ɗaure mata kai, yaushe aka kama shi without her knowledge? Ko ma waye responsible she'll handle it.
Washegari kuwa da sassafe suka nufi police station ɗin, a nan aka ce musu ai gobe za a wuce da shi court tunda an samu wadatattun hujjoji a kansa, amma tunda iyalansa za su iya ganinsa.

Tashin hankali, irin yadda syka ganshi abun ya ɗaure kan su, gabaɗaya ya lalace kamar ya shekara uku a rufe, tsabagen bugun da ya sha kuwa har ƙafarsa ta ji ciwo sosai wurin ya kume ya zama ciwo sosai, rashin kula da wurin duk da ba wani dadewa aka yi ba yasa har wurin ya fara ɗiwa, a matuƙar fusace suka bar police station ɗin zuciyar Gabriella a hasale, kuɗi ne fa da su, yanzu dole ta zuba kuɗi a sakar mata da mijinta. A daren ta nemo lawyer, maƙudan kuɗaɗen da ta zuga masa yasa ya amince da aikin cikin sauƙi.

Washegari kamar yadda aka sanar haka aka fito da Babatunde ƙafarsa na zubar da ruwa mai wari zuwa court, abun mamaki ƴan jarida sun cika fal suna jiran a ba su damar magana da shi aka laifin da ake zarginsa.
Duk wani gidan talabijin zancen ake "A yau talata...23 ga wata Fabrairu, yau za a shigar da ƙarar Hamshaƙin mai kuɗin nan Babatunde Mohammad wanda ake zargi da amfanin da jinin mutane don biyan buƙatunsu, Wakilinmu na can kotu don samar muku da rahoton yadda ƙarar za ta kasance... ku kasance tare da mu.."

Da yake da an yi tunanin babu lauya mai kare wanda aka yi ƙara an yi tunanin shari'ar za ta zo da sauƙi, sai dai kwatsam sai ga Lauya ya bayyana a matsayin mai kare wanda aka yi ƙara. An fafata sosai a ranar yadda lauya wanda ake ƙara yake aikinsa cike da ƙwarewa kamar babu wani abu da Babatunde ya aikata. Tafiyar da lokaci yayi yasa aka ɗaga sauraran ƙarar zuwa ranar 3 ga wata Maris. Gabriella Babu abunda take sai sakarwa lauya kuɗi har zuwa ranar 3 ga wata, cikar da kotun tayi a wannan ranar ya wuce tunani, nan aka ci gaba da amsar ƙarar, abunka da ƙara da shaidu, tuni waɗanda suka yi ƙara suka yi winning case ɗin, nan alƙali ya yanke hukuncin ƙwace duk wata kadara da kuɗi da Babatunde ya mallaka ba bisa ƙa'ida ba, sannan kuma an yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na rai da rai tare da aiki mai tsanani. Daga nan aka rufe case ɗin shi kuma aka wuce da shi prison, Gabriella ta shiga tashin hankali sosai da wannan ɗanyen hukuncin da aka yanke masa ga shi ta yi wadaƙa da nata kuɗin wajen ganin ba a ɗaure shi ba. Haka Joy da Amaka, sosai suke kuka ganin an wuce da babansu prison.

Ko da suka koma makaranta kowa tsangwamarsu yake yana nuna su da yatsa _su ne ƴaƴan wannan wanda yake da kuɗin jini, dama ai kuɗin ba na Allah bane" kowa sai faɗin albarkacin bakinsa yake wasu kuma na musu dariya. Ko da suka dawo gida suka sanar da Mommynsu, babu shiri ta kwashe su suka tafi prison ɗin, tana buƙatar sanin ta yaya akai hakan ta faru. Bayan sun je aka ba su lokaci. Nan ya fara faɗa mata komai, ya sanar da ita komai tare da faɗa mata cewa ko bayan ransa su ɗaukar masa fansar raba shi da dukiyarsa da ƴancinsa da Alhaji Baba yayi, su hana shi zaman lafiya, ga su Amaka nan, ta san yadda tayi suka zama part of his family, Yana da tabbacin su kaɗai ne za su iya ɗaukar masu fansar Abunda yake faruwa. Haka suka rabu tana kuka, sati mai zuwa ta ɗauko su Amaka ta taho da su suka kai masa ziyara, a ranar sun yi kuka iya kuka, sun koka da halin da suka tsinci mahaifinsu, zuciyarsu ta yi zafi, ta hasala ta kuma tunzura ga ramawa mahaifinsu, sun yi alƙawarin ko wane ne behind this Sai sun rama. Ita dai Gabriella kasa magana tayi a ranar, duk ta susuce da yadda ta tarar da shi, abun da ya fi sa ta damuwa bai wuce ɓacewar tunani da ya kama shi ba, don cewa yayi shi bai san su ba, su tafi ga jarirai za su kama shi, duk kuwa da irin warin da ke fitowa daga cikinsa hakan bai sa sun ƙyamace shi ba, ƙafarsa da ke zubda wani ɗoɗɗoyan ruwa da ba shi da daɗin gani bare kuma ƙamshin shaƙa. A ranar dai haka suka dawo jikinsu sukuku.

A week after that, al'amarin Babatunde ya munana, ma'aikatan prison ɗin kansu ƙyamar kusantarsa suke, ɗaki guda aka ware aka maida shi saboda cutar da na kusa da shi da yake, daga ƙarshe dai aka mika shi asibitin cikin prison ɗin, wanda suka ce babu abinda za su iya game da hakan. A ranar ne kuma aka wuce da shi babban asibitin gwamnati, abun da ya ɗaurewa ma'aikatan asibitin kai bai wuce yadda in sun kai hannu jikinsa da niyyar a wanke wurare masu raunin sai tururin da ke fitowa wanda ba shiri yake sa su janye hannayensu, daga ƙarshe dai haka aka mayar da Babatunde prison tunda abun ya fi ƙarfin ma'aikatan lafiya.

A da yana ƙoƙarin takawa, amma tunda aka dawo da shi tafiya ta gagara, abinci ma ba ya iya ci saboda hannunsa karkarwa yake da zarar ya kai hannu ga robar abincin da ake kai masa, wasa wasa ma sai ya fara zabura, haka kawai zai ta ƙwala ihu yana faɗin a taimaka masa yara za su cinye shi, ba komai bane face irin yaran da ya sha jininsu da suke masa gizo suna calla ihu, haka zai ta toshe kunne amma ba ya daina ji. Bayan wani lokaci kuma sai ya zama useless, numfashi kawai yake ja, amma ba shi da wani amfani, kashi, fitsari duk a jikinsa yake, su kuma ma'aikatan prison suna tsoron kamuwa da wata cutar yasa suka bar shi cikin abunsa. Ranar wata Lahadi da Azahar ya fara ihu, razanannen ihu da ba shi da daɗi sauraro, yayinda ma'aikatan gidan suka zo duba shi, ashe iskokan da yake amfani da su wurin sihiri ne suka cin ubansa, a ranar ne kuma Allah ya ɗauki ran ɗan banza.

Tun a ranar labari ya karaɗe duniya na yadda gawar tasa ta kasance babu daɗin gani, ga kashi masha-masha ta ko ina a jikinsa. A haukace Gabriella ta Kwaso yara suka zo suka wuce da gawar tasa for burial. Sai dai abun mamaki lokacin da ta gayyaci ƴan uwa da abokan arziƙi zuwa funeral ɗinsa babu wadda ya zo, daga ita sai su Amaka su suka binne gawarsa wanda hakan sosai ya taɓa zuciyarta yayinda ruruwar wutar fansa ya mamaye zuciyarta.

Bayan mutuwar Babatunde ba a jima ba Gabriella ma ta fara jinya sosai ashe ciwon zuciya ne ya kamata na rashin mijinta da tayi, ba ta yi tsawon rai ba itama tayi mummunar mutuwa sai dai kafin mutuwarta tayi ƙoƙarin sanya Amaka da Joy a ƙungiyar asiri, ta kuma ƙara tunatar da su kan ɗaukar fansar mahaifinsu da mahaifiyarsu sannan ta ce su koma musulunci su yi yadda suka yi suka shiga cikin wannan ahali.

Bayan sun musulunta Amaka ta koma Saudatu, ita kuma Joy ta koma Baraka, duk da haka ba su daina shan jini ba musamman Amaka wacce ita nata ya fi shahara har ta shahara a Duniyar tsafi, da tsafinta tayi amfani ta hanyar cusawa Usman (papa) soyayyarta a ransa, a dole ba don iyayen sun so ba haka aka yi auren. Babu jimawa itama Baraka ta auri ɗan'uwan Papa (Abba) ta hanyar rufe bakin kowa a gidan.

*DAWOWA CIKIN LABARI*

Dariya sosai Ammie tayi tare da faɗin "Na san duk cikinku babu wadda zai iya tuna ta yaya aka yi aurenmu saboda aikin iko! Ikon mu da shi muka yi amfani muka sarrafa gabaɗayanku, ga shi duk cikinku babu wadda ya taɓa sanin cewa Ni da Baraka ƴan uwan jiuna ne! Hhhhh ko a haka muka tafi mun muku babban giɓi, mun kashe kuma mun sha jinin jarirai marasa adadi! Ni da hannuna na kashe matarka Sadauki! Na tsaneks kai da mahaifiyarka, amma na ɓoye saboda kuna da abun duniya, matarka ita ke shirin lalata min shirina siyasa na aikata lahira na zuƙe jininta, ɗanka ma na yi iyawata sai dai wannan tsunanniyar ƴar'uwar taka ba ta barinsa babu tsari, itama mun so aikata lahira abun bai yiwu ba!"

Ruwan Zamzam Kawu Sadi ya watso musu take suka razana tare da sakin ihu
"EH, wannan tsinannen tsohon naku shima sai mu gama da shi!" Mamie ta ƙara a kai "Wannan tsinannu biyun, Sadauki da matarsa ku sani kuma ba za mu bar ku ba, mu muka yi sake har kuka yi galaba a kan mu, ashe kune haske biyu da muke gani a jikin allon tsafi..."

"Ya ishe ku haka!" Sheikh Imam ya daka musu tsawa, a take suka yi shiru


*React and share fisabilillah.*


[10/05, 12:50 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 7️⃣3️⃣






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*


"Wato har yanzu ba ku risina ba, kuma ba ku da niyyar tuba ko?"
"Hhhh" Rumana wacce ba ta ce komai ba ta yi dariya "Kai ƙaramik malami, Ni magajiyar uwargijiya ce, kuma ɗiyar Joy wato (Mamie), babu gudu babu ja da baya, kamar yadda na tarwatsa bikin Banzar matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login