Showing 126001 words to 129000 words out of 157517 words
yana can gaba, kuma ba a buɗe dabbobin.
Yanzu ya fara mamaki don kuwa a kan idonsa wannan akuya ta rikiɗa izuwa siffar mace mai ciki.
Zaro idanunsa yayi cikin ransa yana karanto addu'ar neman tsari, yana gamawa a zahiri kuma ya fara karanto ayatul kursiyyu yana tofa iskar saitin matar da ke tsaye wacce ba ya iya tantance fuskarta. Cikin ikon Ubangiji lokaci guda wannan mata ta ɓace ɓat kamar babu ita a duniyar wurin. Da haka ya koma motar yaja, horn yayi masu gadi suka buɗe, hakan yasa ya shige ciki, yau dai saboda abunda ya gani ko Good one hour Bai yi ba ya fito bayan ya sallami ma'aikatan.
*FRIDAY.*
A yau juma'a aka yi walima wacce ta mugun ƙayatar ta kuma ƙara tunzura Rumana kan bakarta na warware auren da aka yi, sai dai zakaran da Allah ya nufa da cara...a daren ranar kuma Yaya Ishaq ya zo gidan tare da Yaya Sadauki, ba ta wani yi mamaki saboda ta ba shi labarin gudunmowar da Yaya Ishaq ɗin yayi wa rayuwarta, bayan sun gaisa Yaya Sadauki yace "Lily, ku gaisa ina zuwa."
Shaye da mamaki ta bi shi da kallo har ya fice a parlourn.
Ganin haka yasa Yaya Ishaq gyara murya yace "Congratulations Zahrah, Allah ya muku albarka ya sanya Tarayyar ku ta zamo alkhairi. Allah ya ba ku zaman lafiya." Da "Amin" ta amsa tare da jan bakinta ta tsuke, sosai yayi mata waɗansu tunatarwa game da aure daga nan yayi mata sallamar zai wuce, har ya miƙe kuma ya koma ya zauna tare da faɗin "Ehm na manta muhimmin abun da ya kawo Ni ma, yauwah Zahrah taimako na zo nema wurinki"
"Taimako kuma?"
"Ƙwarai taimako dai."
A sanyaye tace "Allah ya sa ina da iko."
"Amin, kina ma da shi....dama dai batun ƴar'uwarki ne don Allah, ina so ki taya Ni neman soyayyar ta duk da na san ba lallai ta amince ba."
"Wacce ƴar'uwata kenan?"
"Ƴar'uwarmu mana, Nasreen nake nufi, don Allah kada ki duba abun da ya faru don har yau ina blaming kaina sai dai babu yadda zan yi haka Allah ya ƙaddara."
Jin ya ambaci Nasreen yasa taji wani sanyi a ranta. Numfashi ta sauƙe tare da faɗin "Babu komai, Allah yasa ta amince ɗin, amma zan so ku fara magana da ita kafin nayi da ita, inaga hakan zai fi ko?"
"Eh kuma fa, to ai ba Ni da contact nata."
"Bari na saka maka." Mika mata phone ɗinshi tayi bayan ta saka, karba yayi yana faɗin "Thanks amarya, sai mun zo dinner gobe."
Murmushi kawai tayi shi kuma ya fita, sai da yayi wa Ya Sadauki sallama tukun ya wuce.
*Morning*
*10:00am*
Da yake yau gidan cike yake ga su Nainarh duk an bazo sai suka tare a bedroom ɗin Zahrah banda surutu babu abunda suke. Around 10am suka wuce wurin saloon bayan an dawo suka ɗaura a yadda suka tsaya. Nainarh da ke wani ladabin ƙarya ta dubi Zahrah tace, "lallai wannan amarya ta Yayana ta musamman ce, gyaran amarcin har sau biyu aka miki?"
"Ah to, ɗaya kike so a min kamar ke? Ko kin manta mijin na daban ne? Kinga dole kuwa komai namu ya zama unique." Dariyar shaƙiyyanci suka yi Zakiyya na faɗin "Eh lallai Zahrah, wuyan ki ya yi ƙwari tunda har wani fiffika kike mana, daɗinta ma dai kowa da mijinsa, a to."
Dariyar suka kuma yi banda Nasreen da tayi kici-kicin da fuska tana bin su da kallon tuhuma sannan tace
"Na ga alama da Ni kuke saboda Ni ɗaya ce single." Tana faɗa ta miƙe za ta fice daga bedroom ɗin, da sauri suka mike ana rige-rigen tarota.
"Haba Aunty Nasreen ɗinmu? Yi haƙuri kin ji, ba haka muke nufi ba."
Da haka ta juyo tana gwaliyonsu. Rumaysa wacce ta kame wuri guda tace "Kun ga Ni yanzu na daina wannan yarintar, babyna ya hana." Ta faɗa tana shafa empty belly nata.
Ido waje suke kallonta, Zahrah da bakinta ke buɗe ta rasa me za ta ce ta ce "Lallai ba shakka, wai kina nufin har an ƙaru?"
"Ah to?"
Ɗaya bayan ɗaya take bin sisters ɗin nata da kallo baki riƙe
"To sai me?" Nainarh ta tambaya. Daƙuwa Nasreen ta aika mata "Sai gidanku, ku fa naga alamar yanzu kunya ta ƙaranta a gunku, to kowa ta aje rashin kunyarta sai ta je gidanta." Ta faɗa tana kame fuska a nata na babba.
Dariyar da suka yi yasa itama tayi. Haka suka ƙarashi surutansu har wuraren Azahar tukun suka miƙe, sai lokacin Zahrah ta tunkari Nasreen da batun Ya Ishaq, Nasreen tace "mun riga mun yi magana, amma na ce masa sai na yi tunani...yauwah jan aji kenan." Dariya suka yi daga haka suka yi shirin sallah dukkansu.
Suna idar da salla Mai lalle ta ƙaraso... Nan aka sheƙawa amarya jan lalle a ƙafafunta da hannayenta, sannan aka yi wa Nasreen, Nainarh da Zakiyya, Rumaysa aka yi wa ƙarshe sai mita take. Lokacin da aka gama musu already na Zahrah ya gama ja...ya yi maroon gwanin ban sha'awa abunka da farar fata, cirewa tayi ta fara sallar laasar ita da Zee mai lallen ƴan gayu. Suna salla aka fara shatawa zahrah zanen lalle baƙi, kai jama'a, sosai zanen yayi kyau, ga maroon ga baƙi a kan farar fata, ku kwatanta irin kyan da zai yi. Bayan an gama mata aka ɗan zanawa sauran ma sama-sama (kun san komai na amarya daban yake.)
Sai around 5pm Mai lalle ta gama, Yaya Sadauki da kansa ya sa Drivernsa na office ya kai Aunty Zee mai lalle har gida bayan goma sha tara na arziƙi da ya loda mata.
Sai da aka yi sallar Isha' aka fara shirye-shiryen tafiya wurin dinner, babu babba babu yaro kowa ka gani adonsa na musamman ne, ƙawayen amarya sun kece shiga mai kyau kamar su ne amaren, haka nan angwayensu ma ba a bar su a baya ba. Nan dai suka ɗauki amarya suka wuce da ita wurin kwalliya, ma sha Allah kawai za a ce, make up dai ta hau, sosai Zahrah tayi kyau kamar ba ita ba, abun ku da mai kyau kuma ya ƙara da kyau, sai kyan ya ƙaru kan na da. Daidai lokacin da aka gama mazajen suka iso coz already masu halartar dinner duk sun wuce event venue ɗin.
Yaya Khalil, Yaya Ishaq, Yaya Auwab, Yaya Taj....so ma sha Allah, tare motocin su suka faka, kamar haɗin baki su huɗun suka fito cikin fararen shaddodinsu da aka yi wa ɗinkin babbar riga wanda aka zuba aiki kamar ba gobe, sun yi kyau sosai sai ƙamshi suke zubawa. Daidai lokacin da Nainarh, Zakiyya da kuma Rumaysa suka fito yayin da Nasreen da Zahrah ke ciki. Kamar abun gadara kowa ya nufi matarshi ya riƙo hannunta sai santin Khan da suka yi suke, haka su ma matan sai santin mazajen nasu suke.
Ya Ishaq ne kawai bai fito ba sai lokacin, yana fitowa ya buɗe back seat, _Tabarakallah ahsanul khaliqin_ kawai Na iya furtawa. Yaya Sadauki ne cikin farar shaddarsa wacce taci aiki na golden colour zars sai dai ko ba a faɗa ba kuɗin nasa da nasu akwai banbanci, sosai yayi kyau cikin shigar manyan kaya da bai saba ba, ciƙe da ƙasaita da ta mamaye jinininsa da jikinsa ya fito, hular kansa wacce itama fara ce da gold colour ta yi kamar za ta faɗi, da sauri ya tare ta. A hankali ya fara takawa don ɗauko tashi amaryar lokacin kuma su Yaya Khalil sun shige nasu motocin, fitowar Zahrah da Nasreen ya yi daidai da isowarsu bakin gate na wurin, so ma sha Allah, Ni na ma rasa gane cikin Zahrah da Yaya Sadauki waye ya fi yin kyau a yau, sosai white wedding gown ɗin da ta sanya wacce aka yi wa ado da gold colour ta yi ɗas jikinta kamar dai a jikinta aka ɗinka shi, lokacin da eyes ɗinsu suka sarƙe da juna kasa ɗaukewa suka yi don ji suka yi ina ma a barsu a haka, irin magnetic force Amma na shauki shi ya riƙe so kowa na yaba irin kyan da ɗan'uwansa yayi.
"They're waiting for U people, ku adana kallon ku, there's time still." Faɗin Yaya Ishaq yana sakin murmushi ganin Nasreen ma ta yi kyau, shima a nashi ɓangaren ji yake kamar ya sace ya gudu da ita.
At a certain spot suka haɗu, ganin hakan yasa Nasreen kamo hannun Zahrah ta damƙa cikin na Yaya Sadauki tana smiling tare da yaba irin dacewar da suka yi, they're meant for each other indeed.
*React and share....an jima akwai update if you people help me share and react. Can't love U less...*
[28/04, 7:53 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 6️⃣0️⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
Tsintar kansa yayi da riƙe hannun gyam kamar za a ƙwace masa ita daga gare shi. A hankali cikin wata cooler voice yace "Let's get going amarya..." A ɗan suƙure tace "uhm" nan suka fara takawa har zuwa wurin motar da already Yaya Ishaq ya buɗe back seat, Yaya Sadauki ne ya fara shiga sai Zahrah waɗanda har yanzu hannayensu cikin na juna yake, ganin sun shiga yasa Ya Ishaq rufewa ya nufi wurin mai zaman banza ya buɗewa tashi princess ɗin, daga nan ya zagaya yayi horn, nan motar Yaya Khalil da Yaya Auwab suka fara tafiya, hakan ya ba motarsu da ke tsakiya damar tashi.
Suna isa kowa ya fara firfitowa, sai da kowa ya shige Ya Ishaq ya fito ya buɗe ƙofa, Bayan Yaya Sadauki ya fito ya zagaya side ɗin da Zahrah take ya buɗe tare da miƙa mata hannunsa, hannunta ta saka cikin nashi soft hand ɗin ta fito, ji kake ƙas! Ƙas! Camera na aiki, dukkansu they're not comfortable da wannan kusancin sakamakon yadda zuciyarsu ke ƙara bugu sai dai yanayin, yanayin ya matuƙar sanya zuciyar tasu sanyaya, how they wish su dauwama a irin wannan yanayi. A nutse suka fara takawa zuwa cikin hall ɗin yayin da masu hoto da videos ke haska su, suna shiga halla ɗin ya ɗau tafi taf-taf taf, MC yace "We're recognising the presence of our latest bride and groom" yana faɗin haka ya saka sautin waƙar Hello wanda ya sanya zaƙamin shauki ya tashi cikin zukatansu while on their face smile ne kawai ke escaping.
Suna zama MC ya dakatar da sautin yana faɗin "Well seated is our latest bride and her groom, you're all welcome to the programm" Sai tafi taf-taf. "Alhamdulillah for this special day, you're all welcome to this remarkable occasion...kafin mu nutsa cikin taron, kai tsaye za a fara da refreshmet saboda ku samu karsashi.. " bai rufe baki ba sai ga ma'aikatan _Al'imaan Restaurant_ sun fara shigowa, nan aka yi serving kowa. Sai da aka gama ciye-ciye da shaye-shaye tukun aka fara kiciniyar rausayawa.
At first MC ya buƙaci best friend Na ango da ya fito ya ba da brief history Na angon, babu ɓata lokaci Yaya Khalil ya fito, tafi aka masa sannan ya amshi microphone daga hannun MC, cikin dakakkiyar muryarsa ya fara magana cikin harshen turanci.
"Assalamu alaikum everyone, thank you all for answering our invitation, you are all welcome. I'm Ibrahim Abubakar Abatcha, the best friend of our latest groom as well as brother to him...let me start by giving you a brief history of my friend.. He's Aliyu Umar Abatcha, a.k.a Sadauki, he's born on...attended his primary, secondary and tertiary education in London, he has a Batchelor in Cyber security and forensics analysis, he's the CEO of ABATCHA Automobiles also..the founder and president of NIC...not only that, he's the owner of Noor Orphanage." Aya ya ɗan sauƙe sannan yaci gaba.
"My brother is unique having so many qualities others lack, he's kind, generous and...I don't have enough words to express who my brother is, all I know is that he's special, our latest bride congratulations for having such wonderful guy by your side, congratulations once again, indeed you're very lucky to have him as your life partner hope you will love him endlessly, take good care of him in every situation. I'm wishing you people all the best in your marriage life. Thank you!"
Sosai ya burge mutane, tun lokacin da ya fara magana Hajiya Nainarh aka fito ana masa liƙi, haka su Aunty Salmah ma suka yi masa liƙi. MC yace "Ma sha Allahu, we have heard about the groom from his real bestie, now it's turn for the bride, we need her best friend on the stage..."
Haka Nasreen ta fito cikin takunta mai ɗaukar hankali ta amshi microphone daga hannun MC. In her sweet voice ta fara magana cikin harshen turanci itama wanda yake fita tamkar wata baturiyar gaske aka ajiye
"Hi everyone, firstly I'll like to give a huge appreciation to you for answering our invitation, thanks." Ta fada tare da haɗe hannayenta alamar godiya, tafi kake ji, sai ga Yaya Ishaq ya fito yana liƙi sai smiling yake.
"Here with you on this golden stage is Nasreen Abubakar Abatcha, bestie and sister to the latest bride Zahrah Abdulkarim Kuru. She's born on....and raised by her mom and uncle in Bauchi State, she attended both her primary and secondary education at Bauchi State from Almunawwara Academy Bauchi being their overall best student ever, she won so many crowns at that stage, the best part of her is that... she's Quranic reciter, how I wish my friend will recite even a single Aya for you, subhanallah!! I'm sure you people will take your wives, your sisters and daughters to Quranic school just to be like her."
"Recently my sister now is Law student at Nile University. Mr groom, I'm so happy for you as you took the precious jewel as your wife, she's damn generous, calm and kind, congratulations again and again for you Mr groom, I can say you're the luckiest man ever because you're with my precious darling sis as your wife, hope you'll take good care of her like a newborn baby, I'm wishing you Allah's Khair in your marriage life, more Barakat and happier life. Thanks.."
Tana komawa seat nata aka buƙaci ƙawayen ango da su fito stage su ɗan taka, they do as they're called tunda most of them are not Nigerians, haka aka bukaci ƙawayen amarya, some of her course mate represent the team. Ango da amarya aka buƙata da su hau stage, Ya Salam! They worn it wollah, sun matuƙar sanya nishaɗi a zukatan jama'a har wasu ma suna Allah Allah su ma su yi aure suna kuma fatan Allah ya ba su mata na gari kamar dai Zahrah. Sosai dai taro ya ƙayatar kuma kowa ya gwangwaje abun sa, ba su suka bar event centre ɗin ba sai around 12:30am.
Kai tsaye dama an sallama Zahrah ga angonta, Alhaji Baba luma ya ce da sun gama taron su su wuce kawai, masu buƙatar zuwa washegari sa leƙa tunda a cikin estate ɗin gidan yake. Yadda suka taho haka suka wuce gidan amarya don musu rakiya. Ganin dare yayi yasa Suna kai su suka fito, Yaya Khalil ya damƙawa abokinsa leda nan ya masa sallama and they all dispersed leaving only the groom and his bride.
Zahrah wacce ke zaune a Parlour cike da ƙosawa da kayan jikinta don a takure take da su. Shigowarsa yasa ta sunkuyar da kanta, tsakani da Allah nauyinsa take ji kamar za ta yi yaya. Lura da hakan da yayi yasa wata cool smile tayi escaping kan face nashi. Ƙamshin turarensa da ya cika mata hanci yasa ta ɗan ɗago tana satar kallonshi, suna haɗa ido tayi saurin sauƙe nata ƙasa. Murmusawa ya ƙara yi tare da miƙa mata hannunsa saying "Let's get in Zaujaty.." manta wata kunya da take ji tayi tare da ɗago kanta tana mamakin sunan da taji ya ƙira ta da shi yayin da wani daɗi kuma ya lulluɓe heart nata.
"Zaujaty...." Ya ƙara maimaitawa a karo na biyu, da sauri ta kawar da kan ta gefe tare da sanya nata hannun cikin nasa. Daga haka ta miƙe tsaye, a haka suka fara takawa, shi da kansa ya musu jagora zuwa wani bedroom da ke kallon west, buɗe kofar yayi sannan yace "Bismillah" tsintar kanta itama tayi da basmalar sannan suka taka a tare suka shige, with full concern ya dubeta yace "Dare ya yi and I know this textiles sun takura ki, ki yi wanka ki sauya kaya, bari na ba ki wuri ko?" Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ɗaga kanta alamar eh.
Da haka ya fito tafkeken parlourn yana sakin wani murmushi da shi kansa bai san dalilin fitowarsa ba, hakan yasa ya shiga bedroom ɗin da ke kallon wancan, shima rage kayansa yayi ya watsa ruwa, bai tsaya shafe-shafe ba ya sanya wasu soft Gucci brand pyjamas white colour,shafa sumar kansa yayi looking directly into the mirror yana faɗin "Alhamdulillah!" Tunawa da ya bar ta ita kaɗai yasa ya fesa turaruka daga nan ya sanya takalman kayan ya nufi parlour. Ledar da Yaya Khalil ya ba shi ya ɗauka sannan ya ɗauko plate da cup ya wuce. Ganinta bakin bed zaune da hijabi yasa yayi murmushi yace "they're all the same" daga haka ya ƙarasa inda take, wata babbar table cloth ya shimfiɗa a kan lallausan carpet ɗin da ke ɗakin sannan ya aje ledar tare da samun wuri ya zauna, duk abinda yake tana kallonsa sai dai nauyinsa na yanzu da take ji yasa tayi kamar ba ta ga shigowarsa ba.
To his surprise kwance ya tarar da ita ta takure guri guda kamar mai baccin gaske, sai dai ba baccin take ba, murmushi kawai yayi cikin ransa yana ƙara mamakin tsoro irin na Zahrah. A haka