Showing 141001 words to 144000 words out of 157517 words

Chapter 48 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5162

"Shi ne ƙarfinki, da shi kika dogara, ƙir ki yi shiru ki gani ki kuma ajiye littafin hannunki."
Jin Abunda Muryar ta faɗa yasa Zahrah ƙara ƙaimi wurin karanto ayoyin tsari a bakinta yayin da ta ƙanƙame Alqur'anin a ƙurjinta kamar wani zai ƙwace mata shi.

Cike da karaya Muryar tace "Zan dawo Zahrah, zan dawo gareki, babu wanda ya isa ya min shamaki da abun hari na ko da kuwa wanene, a halin yanzu zan iya komai wurin mallakar Abunda nake so, ki jirayi dawowata a karo na gaba, ina rantsuwa da Gutsurito da kuma uwargijiyata sai na shafe tarihinki, ba iya ke kaɗai ba gabaɗaya ahalinku, mutum ɗaya zan bari shima saboda amfanin rayuwata, shima in ya fara ƙoƙarin kawo min cikas babu shakka sai na kawar da shi, ahalinku sai ya zama kamar mahauta...a turance ina nufin abattoir don ki gane da kyau, zai zama kogin jini wannan estate ɗin da kuke ji da shi. Ki jirayi dawowata na faɗa miki a karo na biyu.!"

*Share as much as you can, react please, ina son ku min lokes ne daga zuciyarku.*
[06/05, 5:50 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 6️⃣7️⃣






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*


Daga haka kuma shiru ya mamaye ɗakin, a hankali haske ya fara bayyana har dukka bulbs na ɗakin suka dawo da haskensu. Zahrah da ke tsaye a wuri guda jikinta na ɓari yayinda ta jiƙe sharƙaf da gumi ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya tana ƙara ƙanƙame Alqur'anin da ke hannunta. Fitsarin da take riƙewa ne yake ƙokarin zubowa, hakan yasa ta tafi toilet da gudu tare da ajiye Qur'an ɗin a kan mirror, har za ta shige ta tuna da addu'ar shiga bayi, da sauri ta taka birki ta karanto addu'ar kafin ta shiga. Tana fitowa ta fara leƙe-leƙe, ganin babu kowa yasa ta fito da sauri ta ƙara ɗaukar Alqur'anin ta manna shi da chest ɗinta.

Idanuwanta ne suka sauƙa kan wayarta, hakan yasa ta ƙarasa da sauri ta wawurota, manta PIN code ɗin tayi tsabagen firgici, a hankali ta ajiye wayar. Kiraye-kirayen sallar Isha' yasa ta ƙara komawa toilet a tsorace tayi alwala, tana fitowa ta tada Sallah. Bayan idar da sallar Isha' da tayi ƙin zama tayi sai ta fara jero nafilfilu don gani take da ta idar da sallar za a ƙara dawowa ga shi rabonta da ta ga mahaifiyarta tun ranar Dinner ɗinsu, tana buƙatar da ganta Koo da kuwa mutuwar ce da gaske ke tunkararta.

Ta idar da sallama tana shirin tayar da wata sallar ta ji alamun taɓa handle na ƙofa, tuni hantar cikinta ta kaɗa har wani irin sauti cikin nata ke yi. Ba ta yi yunƙurin waiwayowa ba ta ɗaga hannun za ta kabbara sallah. Sassanyar muryarsa mai sanya nutsuwa ga mai saurare ita tasa hannunta tsayawa yadda ta ɗaga ba tare da ta sauƙe ba. Cike da son confirming ta ɗan ƙyalla idonta ta gefe, tana ganin shine ta nufe shi da gudu tana sakin Marayan kuka tare da kanannaɗe shi. Duk wani sautin kuka da muryarta za ta fitar jinsa yake cikin ransa, ji yake wani abun na sukan ransa, ba tare da ya dakatar da ita ba ya ƙara haɗata da ƙirjinsa. Sai da ta yi mai isarta ta fara sakin ajiyar zuciya tukun ya jawota tare da musu masauƙi bakin bed. Kanta ya ɗaura kan ƙirjinsa yace "kin ji yadda zuciyata ke bugawa ko? Don Allah ki daina kukan ki faɗa min what's wrong?"

Sake fashewa da kuka tayi tana ƙara ƙanƙame shi.
"Please Raihanatu qalby...save your husband ki yi shiru ki faɗa masa damuwarki."
Ajiyar zuciya ta fara saki, hakan ya tabbatar masa da cewa ta daina kukan.
"Noor..." Ta ƙira sunansa kamar dai wacce in ba ta faɗi ba za a kashe ta like her life depends totally on calling him.
"Ina jinki habibaty."
"Zan koma wurin Hajjaty Yaya, ba zan zauna a gidan nan ba.!" Ta kare tana ƙara sakin wani kukan.
Bayanta ya fara shafawa yana faɗin "Sorry, calm down My precious angel, faɗa min me aka miki" shiru tayi ba ta ce komai ba hakan yasa ya fara tunanin ko ya mata wani abu, tunawa da sun rabu ne ma cikin shaukin juna yasa ya ce "An miki wani abu ne? Na bata miki raine? Na miki laifi ko?"

Sai a lokacin ta fara girgiza masa kai.
"Idan babu ɗaya cikin abinda na lissafo ki faɗa min what's wrong with you? Ko ba ki da lafiya ne?"
"A'a" ta faɗa cikin Muryar da ke bayyana tsantsar tsoro da firgici.
Cikin rashin sanin madafa yace "Kin ga lizard ne?"
A hankali tace "Yaya sun ƙara dawowa, wallahi yanzu suka bar gidan nan, idan kana so nayi tsawon rai ka mayar da Ni gun su Hajjsty don Allah."
"Shikenan zan mai da ki, faɗa min su waye ne suka ƙara zuwa."
Tas ta kwashe Abinda ya faru ta faɗa masa ta ƙara da faɗin "In dai ba ka ɗaukeni ba za su kashe Ni in ba ka nan."

"Shhh, is ok, ɗazu na yi magana da Sheikh Imam Nasir kuma ya ce during weekends zai shigo, ba zai bar gidan nan ba sai ya gano komai ya magance komai da izinin Allah."
A tsorace tace "Noor har sai weekends? Wallahi kafin nan hala sun kashe Ni ma.. shikenan" sai kuma ta saki wani kukan. (Nace dama Zahrah ma tana da tsoro haka ne?"
"Tightly ya riƙeta sannan ya ɗago kanta idanuwanta cikin nasa yace "Babu abinda zai faru da ke Angel, kin manta Allah yana tare da ke kuma shi ke karewa?..." Haka dai ya lallaɓata da ƙyar ya shawo kanta ta haƙura amma da sharaɗin in zai fita aiki sai dai su fita tare.

Kallonta yayi yana ƙara nazartar yanayinta, ta tsorata ƙwarai, hakan yasa yake so ya kawar mata da tsoron. Ranar dai da ƙyar ta iya yin Dinner, haka ta bi ta maƙale masa ko motsawa yayi sai ta yi, tare suka yi wanka suka shirya daga nan kuma suka kwanta.

*WASHEGARI*

Bayan yaya Sadauki ya tafi wurin aiki sai da ya ƙara kiran Sheikh Imam Nasir ya sanar da shi abunda ya tarar jiya da daddare, cike da son kwantar masa da hankali yace "Hakan ba wani abun damuwa ba ne, ku dai ku yi ƙoƙarin kiyaye azkar, babu abun da zai faru, Nima ina ga next tomorrow zan shigo tare da wasu malaman. Komai zai tafi daidai bi'ithnillah."
"Allahu Yashā'" yaya Sadauki ya ba shi amsa. Daga nan suka sallame.

Can gida kuma Zahrah duk a tsorace take, tun fitarsa ta kunna TV, AfricaTV Qur'an ta saka, sannan ta dadira a parlourn ta zauna, ai duk sharrin aljani da shaiɗani ba za su zo wurin ba. Da za ta shiga kitchen yin lunch kuma ta saka karatun a wayarta. Ba ta jima da farawa ba Nasreen ta kawo mata ziyara tare da ba ta saƙon Aunty Na'ima ita kuma ta karɓa tana godiya.
Tsabagen tsoro irin na Zahrah ko labarin abinda ya faru ba ta ba wa Nasreen ba, wai tsoro take kada taje suna jinta. Hirarsu ta rayuwa kawai suka yi, ashe Nasreen da ya Ishaq kam sun gama daidaitawa abunsu, wai yau ma za a zo nema wa Ya Ishaq ɗin aurenta. Abun sosai yayi wa Zahrah dadi sai son Barka take. Nasreen ba ta tafi ba har Yaya Sadauki ya dawo. Yadda yake nunawa Zahrah soyayya babu kunya yasa duk ta bi ta suƙure, ko da tace za ta tafi ma hanata yayi, wai ta bari in zai fita sai ya ajiye ta.

Yana ajiye ta ya nufi part ɗin Hajjaty, ganin Mamah kaɗai a Parlour yasa yayi hamdalam cike da girmamawa suka gaisa. Bayan sun gaisa yace "Ehm Mommy Madina (kamar yadda yake ƙiranta) dama ina son numbern wannan malamin ne da kika zauna a gidansa a can Toro, Allah yasa akwai."
"Eh to, ba zan ce babu ba, bari na duba maka."
Ya amsa da "To Allah dai yasa a samu." Dubawa tayi can tace "Alhamdulillah, an ma samu. Ga ta nan" ta miƙo masa wayar.
"Ma sha Allah" ya amsa tare da amsar wayar, cikin ƙanƙanin lokaci ya kwashe numbern ya miƙa mata ta amsa tana tambayarsa "lafiya?"
"Lafiya lau Mama" ya ba ta amsa a taƙaice. Bai wani jima ba saboda condition ɗin Zahrah da ke ransa, hakan yasa ya koma to continue taking care of her.

Sai da ya koma tukun ya ƙira Malam Sadi (Kawu Sadi). Bayan sun gaisa yayi introducing kansa, daga suna zuwa alakarsu da Mamah. Daga nan yace masa yana kan hanyar zuwa TORO zuwa gobe don maganar da yake so su yi ba ƙarama bace. Wayar da yake Zahrah na jinsa, yana ajiye wayar ta fashe da kuka wiwiwiwiwi.
Da ƙyar ya rarrasheta ta yi shiru hakan ma don ya ce tare za su tafi ne. Babu yadda ya iya haka ya sa aka yi musu booking flight tare, Ranar ma ba ta bar shi ya yi nesa da ita ba, duk inda zai je haka za ta riƙe hannunsa kada ya barta.

*WASHEGARI*

At early as seven suka shirya, Abaya ce maroon colour a jikinta sai veil ɗin shima maroon da adon black a jiki, Black flat Gucci shoe ta saka sannan ta ɗauko Black handbag ɗinta na Gucci brand ta ɗaura a kafaɗa. Shima dai irin shigar Tata yayi na wasu expensive coat, sosai suka yi kyau kamar ka ɗauke ka ɓoye su. Suna gama shiri suka fito, da Yaya Khalil suka ci karo a bakin gate yana tsaye jikin motarsa sai duba agogon hannunsa yake alamar dai akwai wanda yake jira. Tare suka ƙarasa suka gaisa, motar tasa suka shiga daga nan suka wuce Hajjaty's apartment. Ba su yi doguwar gaisuwa ba suka musu sallama, daga nan su Hajjatyn including Mommah suka bi su da addu'ar Allah ya dawo da su lafiya. 7:30 Flight ɗinsu zai tashi, hakan yasa suka nufi airport nan take, isarsu kenan aka kira sunansu...in few minutes kowa ya gama shiga, first in history da Zahrah ta shiga jirgi. Nan aka sanar da kowa da ya shirya jirgi zai tashi, duk da cewa gabanta faduwa yake amma haka ta dake, ganin ba ta saka belt ba yasa ya saka mata, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kwantowa jikinsa wanda yayi daidai ta tashin jirgin, runtse idanuwanta tayi yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, fahimtar hakan yasa ya sauƙe mata cool peck a face ɗinta, idanuwanta ta buɗe tana ƙare masa kallo, gira ya ɗage mata yana faɗin "Ya dai?"

Smiling tayi tace "Nothing oo, akwai laifi ne don na kalli Abunda mallakina ne?"
"No" ya ba ta amsa yana jijjiga kansa.
"Is this your first flight?"
Kai ta gyaɗa masa. "Amma ya ba ki tsorata ba?"
"Me yasa zan tsorata bayan ina tare da jarumina kuma majinginata?"
Bai san sadda smile Yayi escaping kan fuskarsa ba jin yadda ta ɗaure shi da kalamai.
Cikin ƙasa da murya yace "You're Special Zaujaty, jaruminki ba zai bari ko ƙuda ya cutar da ke ba...and another albishir" ɗagowa tayi tana saurarensa "That should be after all these issues were resolved."
Bakinta ta tura tace "Shine ka ja min rai?"
Hannunsa biyu ya haɗa yace "I'm sorry wifey"
Ƴar budurwar yarinyar da ke gefensu sai satar kallonsu take lokaci bayan lokaci ganin yadda suka mugun burgeta, duk da cewa ta fahimci matarsa ce amma a hakan fata take inama ya ƙara ta a matsayin ta biyu.

Some minutes later, jirginsu yayi landing a filin jirgi na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchin Najeriya. Bayan jirgi ya gama tsayawa ba a ɓata wani lokaci ba passengers suka fara taka matakalar jirgin suna fitowa. Riƙe da hannun juna Zahrah da Yaya Sadauki suka fito kowanne fuskarsa sake suna ɗan zantawa. Bayan sun sauƙo wayarsa ya ɗauko yayi dialling numbern Detective Musa...tana shiga yayi picking yana faɗin "Sir kuna ta ina ne?" Ba tare da Yaya Sadaukin ya amsa ba ya ja hannun Zahrah zuwa wajen da ya hango Detective Musa.
Suna isa ya fara gaida su cike da girmamawa, ogan dai da kansa ya amsa ita kuma Zahrah ta amsa a kunyace.
Ba su ɓata lokaci ba suka yi mazauni a back seat, nan motar ta tashi. Sai da ya fara tafiya tukun yace "Sir ina muka nufa?"
Kamar ba zai amsa ba yace "TORO LGA, gidan wannan malamin da Mommy Madina ta zauna."
"An gama sir."
Nan motar ta nausa titi sai zuba gudu take.

*React and share please*
[08/05, 3:40 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 6️⃣8️⃣






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*

Tafiya sosai suka yi har ya fara gajiya da tafiyar, can dai suka shigo garin Toro. Ajiyar zuciya ya sauke cikin ransa yana addu'ar Allah ya ba su abun da suka je nema. Har ƙofar gidan Kawu Sadi Detective ya sauƙesu, bayan sun sauƙa ba su buƙaci iso ba kai tsaye Zahrah ta shiga ciki. Goggo na ganinta ta tarbe ta guska sake. Tabarma ta shimfiɗa mata, bayan ta zauna ta ɗebo ruwan da ta ɗura a Jerry can na lemu ta ajiye mata.
Fuska sake zahrah tace "Ehm Goggo ba Ni ɗaya ba ce, tare da maigidan nake." fuska sake Goggo tace "Allah sarki, ai da kin ce ya shigo, maza "Barira, Barira"
"Na'am Inna" ƴar matashiyar budurwar ta amsa tana durƙusawa tare da gaida Zahrah. A kunyace Zahrah ta amsa ganin a girme ba lallai ta girmi Bariran ba.
"Maza saka hijabinki, akwai baƙo a waje ki ce masa ya shigo"
"To Inna" ta faɗa tare da jan hijabinta da ke lanƙaye kan igiya sannan ta nufi hanyar waje.

Goggo ta dubu Zahrah tace "Duk yadda aka yi Zahrah'u ce ta wurin Madina ko?"
Kanta ƙasa tace "Eh Goggo Ni ce, ba ki manta fuskata ba kenan?"
"Haba Zahrah'u, ai ke da uwar taki kamar an tsaga ƙara ne, ko na manta ki ai fuskar uwaki na ƙwaƙwalwata."
Sallamar Yaya Sadauki da ke shigowa gidan tare da Mallam yasa Goggo gyara zamanta ta ƙara ware tabarmar da ta shimfiɗawa Zahrah tana faɗin "Lale Maraba da zuwa, zauna ga wuri, ke Barira ƙaro musu ruwan."
"Kai Inna kuɗi kawai za ki kawo naje shagon Ɗan Basi na sayo musu na jarka, kin san fa..."
"A'a Inna ki bar shi, wannan ɗin meye a cikinsa da ba za mu sha ba?" Yaya Sadauki ya dakatar da ita yana miƙa hannunsa ga Jerry can ɗin Coke ɗin gaban Zahrah wacce aka ɗura ruwa."

Da sauri Goggo tace "ka ga Bawan Allah ajiye, bari ta siyo muku na Jarka a shagon Ɗan Basi.."
"Wallahi Inna ki bar shi" ya faɗa tare da kafa kansa ga ruwan ya fara sha...da kallo Inna ta bishi yayin da take jin girmansa a wurinta ganin bai wulaƙanta su ba duk da yadda ta lura da farko kamar zai yi girman kai. Bayan sun sha ruwan Goggo ta sanar da malam cewa ya yi baƙi.
Dama ya riga ya san da zuwan baƙin, hakan yasa ya ce mata ta kawo su Parlournsa. Kamar yadda ya faɗa haka tayi. Bayan sun shiga suka gaida Kawu Sadi cike da mutuntawa. Nan Goggo ta ba su wuri.

Kawu Sadi ne ya Kalli Yaya Sadauki yace "Kun iso da wuri, amma dai ba da mota kuka zo ba?"
Fuska sake Yaya Sadauki yace "A'a Kawu, da jirgi ne"
"Ma sha Allah, ai saurin ya girmi mota, sai jirgi." Ita dai zahrah jinsu kawai take.
Kawu Sadi yace "Yau ɗin za mu wuce can Habujan ko kuwa?"
"A'a Kawu duk yadda ka ce ne mu kam."
Fuska sake Kawu Sadi yace "To madallah, ina ga yau ɗin za mu wuce kar a samu matsala, amma kafin nan ina so ka ƙara buɗaɗa min yadda abun yake faruwa yadda in an je kawai aiki za a hau."
Nan Yaya Sadauki ya kwashe komai ya faɗa masa, Cike da mamaki Kawu Sadi yace "Babu shakka wannan abu na ƴan mafiya ne, kuma dole a cikin gidan naku suke, amma dai Allah wadai da irin mutanen nan. Kada ka damu Ni a shirye ma nake, inaga kawai mu wuce tun yanzu, don akwai abubuwan da za a tanada kafin lokacin aikin."
"To Mallam mun gode. Allah ya ƙara girma." "Amin" Kawu Sadi ya amsa masa tare da shigewa bedroom ɗinsa, few minutes ya fito hannunsa riƙe da jaka, da sauri Yaya Sadauki ya ƙarasa ya karɓi jakar hannunsa. Nan suka fito a tare, Yaya Sadauki ne gaba sai Xahrah biye da shi, Kawu Sadi ne ƙarshen fitowa, ƙofar yaja ya murɗa key tare da cirewa.

Barira da ke tsaye yace wa "Ke ina innarki?"
"Ga ni nan Malam, ya na ga kamar fita za ka yi?"
Kai ya jinjina mata yace "E, zan je Habuja ne, in sha Allahu zuwa gobe ko jibi zan dawo.."
"To Allah dai yasa lahiya."
"Lahiya lau, kin dai tuna abun da nace Miki kwanaki kan Madina, to zan je na kammala aikin ne tunda sun neme Ni"
"To Mallam, Allah ya kiyaye ku, ya dawo mana da ku lafiya ya kuma ba da abun da aka je dominsa."
"Amin Amin sai na dawo"
"Baffa Allah ya tsare hanya"
"Amin Barira."
Daga haka ya fita waje.

Motar da Detective ya kawo su ciki suka koma, Mallam a gefen driver su kuma a back seat. Nan motar ta hau kan hanya....tafiya kam ba kaɗan ba ce, awanni kusan goma suka yi suna tafiya salla kawai ke tsayar da su, jikin kowa ya yi tsami musamman Zahrah da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login