Showing 36001 words to 39000 words out of 157517 words
a buɗe take.*
*Please react and share fisabilillah.*
# LilynYaya
# YayanLily
# Kausar
# Rumana
[12/29, 9:56 PM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣7️⃣
﷽
*ZAHRAH*
Baiwar Allah daren juma'a dai bacci gagararta yayi, ta rasa ina zata jefa kanta, ga shi yanzu magana ma wahala take bata bare a zo gandun hira, Nasreen ma ta yi ta gaji, har kuka sai da ta yi wa Zahrah amma ƙyam ta ƙeƙashe idanun ta. A haka har bacci ya ɗauke Nasreen ɗin.
Haka ta yi ta jera sallolints har dare ya tsala, cikin daren ta fara jin ihu sama-sama, a hankali kuma ihun ke ƙaruwa har ya kai ga ya fara damun kunnuwanta. A hankali ta miƙe tare da switching bulb Amma ba abun da ta gani, siɗaf-siɗaf ta buɗe ƙofa ta fice parlourn tana waige-waige kamar tsohuwar munafuka.
Still dai babu kowa a parlourn amma ihun nan didn't disappear. Cike da tsoro ta nufi entrance door ɗin ta buɗe ta a hankali bakinta ɗauke da addu'ar neman kariya a wurin ubangiji. Hararbar gidan ma dai babu kowa, sannan har wa lokacin nan tana jin ihun kamar a cikin kunnenta.
Ba ta gushe ba tana mai ambaton sunan Ubangiji a haka ta fara takawa tana kewaya ko'ina but nothing to be found. Da ta gaji da zagayawar kuma kunnenta ya ƙi ya daina jiyo ihun kawai ta yanke shawarar fita waje ta duba.
Duk irin tsoron da take ji haka ta kawar da shi ta murɗa lock ɗin jikin ƙofar a hankali, Allahn da ya so ta kuma ƙofar ba ta yi ƙara ba, ajiyar zuciya ta sauke tana mai ƙara ninka addu'o'in tsari bisa harshen ta. A haka ta fice ba tare da takalmi ba tana tafe tana waiwaye.
Kamar wacce aka ce wa tsaya sai ta tsaya cak da tafiyar tana mai lashe kunne don gano direction ɗin da sautin ke fitowa wanda a yanzu ya sauya amo i zuwa wani irin abu maras daɗin ji ko sauraro.
Wurin da take tsammanin daga nan sautin ke fitowa ta nufa har lokacin zuciyarta ba ta daina lugude ba amma ambaton sunam Ubangiji da take yi yasa take jin ƙarfin tunkarar wurin wanda fili ne tarwal sai kuma bishiyoyi da ciyayi masu tsayi da suka gama cike wurin.
Dakatawa ta yi tana zaro ido saboda hango wasu mutane da tayi daga nesa, mamaki sai da ya so kashe ta, ko su waye ne? Ta faɗa cikin zuciyarta. Cike da ƙarfin hali ta fara takawa cikin sanɗa har ta kusa isa ga mutanen sai kuma ta kwanta cikin ciyayin da suka fara bushewa ai kuwa wani sauti ya ɗan bayyana. Nan ta rufe bakinta da tafin hannunta tana roƙon Allah yasa ba su ji ta ba, sai dai kash sun riga sun ji.
Nan take suka waiwayo a tare. Nan take wurin yayi shiru kamar ba a wurin ake zabga wannan ihun ba.
Daga can ta ji ana faɗin
“Motsi nake ji, da alama someone is here.”
Sauran ma suka amsa da
“Muma mun ji.”
“A kewaya a bincika, idan har hakan ta tabbata ko waye yake mana laɓe zan yi sadaukarwa ga Gutsirito don ƙara samun ƙarfin iko na samu na kammala aikin da nake kai.”
“Maza a nemo ko waye”
Tunda Zahrah ta ji waɗannan maganganu hankalin ta yayi mummunan tashi, tsoro da fargaba suka yi mata dirar mikiya, banda rawa babu abun da jikinta ke yi har ta kai ga bakinta ba ya iya furta komai bare ta yi addu'a, haƙwarenta na sama da ƙasa sai karo suke ci da juna suna bada sautin ƙaƙas-ƙaƙas.
Lokaci guda mutanen da za su kai kimanin su goma suka tunkaro wurin da suka ji sautin ai kuwa nan take suka ja da baya. A dai-dai lokacin Zahrah ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin “Alhamdulillah” sakamakon ƙwarin guiwar tunkarar mutanen da ta samu, lokaci ɗaya ta furta
“Allahu Akbar” da ƙarfi ta yadda duk wanda ke kusa zai iya jin sautin hakan. Nan kuma ta miƙe tsaye tana ƙara maimaita kabbarta, a lokacin mutanen suka fara ja da baya saboda furucin ta na kabbara.
*(Me ya dakatar da mutanen su tunkari Zahrah a lokacin da suka gano maɓoyarta?)*
Abun da ya faru shi ne, suna tunkaro wurin da take wani irin haske mai ƙarfin gaske ya yi musu Shamaki da ita har ya kai ga idanunsu ba sa iya ganin komai sai hasken.
“Ku ƙarasa gare ta!”
Wata murya ta faɗa, lokacin kuma mutanen suka yunƙuro da nufin su ƙara tunkaro ta sai dai wannan karan gani ta yi an cilla su baya kamar wasu duwatsu, ba kuma su faɗa ko'ina ba sai gaban mai ba su umarnin.
Duk da haka Zahrah ba ta yi shiru ba, duk Ayar da ta zo bakinta karanta ta take, tsoron da take ji kuwa kamar an ɗauke mata shi. Ƙara ƙarfin karatun tayi saboda jin umarnin da aka kuma basu na su yi amfani da ƙarfin ikonsu.
Ai kuwa nan suka fara furta wasu dalasimai irin wadda matsafa ke yi, ganin haka ita ma sai ta fara rairo Alqur'ani. Ƙaf suka ji na su ya tsaya saboda ita Allah ke a tare da ita ba kamar su ba. Haka suka kwashe kusan mintuna Ashirin amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, a harzuƙe mai bada umarnin ita ma ta zo amma hasken da ta gani yasa gabanta ya faɗi, ganin nasara na shirin kuɓuce musu ga shi kuma faɗuwa na tunkaro su yasa ta fara gwada Tata basirar sai dai ina abun fa ya ci tura.
Wannan dakikin yasa Black-devil ta fara tariyo abun da ta gani cikin madubin tsafinta wasu kwanakin da suka gabata. “Haske biyu!!” ta furta tana mai dage ƙirji, kar dai a ce duk sadaukarwa da suka yi don daƙile su ba su yi aiki ba?.
Cikin zafin rai ta umarci mutanen ta da su dawo kada ƙarfin ikon su ya ragu don fafatawa da irin waɗannan kan iya jawo hasara mafi ƙolo'uwa ga ƙungiyarsu. Bayan sun dakata ta dubi wurin da babu alamar bil'adama sai haske tace.
“Ya Isa! Mun janye makamin mu”
Cike da jarumta Zahrah tace
“Shi ke nan, su waye ku? Kuma me kuke taƙama da shi? Me kuke yi cikin gidan nan?”
“Keeee! Ya isa haka, ke ko kai waye da zaki ki za ka mana wannan tambaya?”
“Kai tsaye ki kira Ni da mace, Ni ɗin baiwar Allah ce wacce tayi imani da cewa Allah ke bayarwa, ku ma ku bani amsa ta.”
“Kin ci Sa'a da yau sai na ƙwamushe ki, na sha wani kaso daga jikinki na kuma sadaukar da sauran ga Dodo na, amma duk da haka ba zan ƙyale ki ba, ke ɗin ba kowa bace Ni nan Black-devil sai na nuna miki ke banza ce.”
“Haka kika ce ko?, To mu zuba, ko ke wacece Nima Zan gano ki da kuma ƙudirin ki! Sai kuma na san dalilin da ya kawo ku gonar mutane kuna shuka sharri!”
“Dakata!”
Matar ta faɗa a tsawace.
“Kar ki ƙara faɗin abun da kika faɗa, Ni Black-devil ba gonar wasu nazo ba, nan ɗin masarauta ta ce! Kuma ki ajiye sai na sadaukar da jininki na gasa naman jikinli mun yi watanda da ke tunda kika ruguza min wannan rana!”
Daga faɗin haka kuma gaba ɗaya mutanen suka ɓace kamar ba a halicci komai a wurin ba, banda kukan tsuntsaye da ke tashi kuma ba ka jin komai sai sautin numfashin Zahrah wanda ke fita da sauri da sauri.
Ikon Allah! Sai a wannan lokacin Zahrah ta fara jin wani tsoro na kama ta, tana kuma tsoron ta ya zata koma ɓangarensu. Wani tsumtsu ne ya wulga ta gefen ta yana tsi-tsi tsi-tsi, a yadda ta zo a tsorace haka ta fara takawa a tsorace har ta kai bakin gate ɗin, ganin ƙofar still a buɗe bai rufe ba yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, daga nan kuma ta shiga bakinta ɗauke da addu'a. A hankali yadda kowa ba zai ji ta ba ta koma Bedroom ɗin su wanda har lokacin Nasreen baccinta take sheƙawa hankali kwance.
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe sannan ta nufi gadon ita ma don ta kwanta sai kuma kiran salla ya dakatar da ita. Nan ta wuce toilet ta Yo alwala ta zo ta hau sallaya, bayan ta yi raka'atanil fajri ma ba ta koma ba sai ta kama tasbihi har aka shiga salla tukun ta miƙe ta yi Tata sannan ta tayar da Nasreen ma tayi. Daga nan wani mahaukacin bacci ya kwashe ta.
*MORNING*
Kamar kullum Yaya Sadauki ya ɗau wankansa sannan ya fito daga Bedroom ɗinsa, da Mommah suka ci karo wacce ke shirin shiga ta tayar da shi ya yi breakfast.
“Good morning Mommah”
“Morning son, ba dai fita zaka yi ba ko?”
“Sauri nake Mommah, akwai meeting ɗin da zan shiga by 8:00 ne”
Kamar za ta yi kuka tace
“Ok, to bari na sa maka breakfast ɗin sai ka wuce da shi.”
Tsabagen mamaki ma kasa ce mata a'a yayi. Bayan ta haɗa ta bashi, nan yayi mata godiya ya fice. Haka kawai zuciyarsa bata ba shi ya ci ba don haka da ya fita sai yayi discarding gabaɗaya set ɗin including bottle water ɗin cikin bin, daga nan ya wuce part ɗin Hajjaty.
A can yayi breakfast ɗinsa, bayan ya gama ya miƙe har zai fita sai ya tuna da she's off today, ba sa zuwa Fridays, hakan yasa ya janyo wayarsa, Numbern Hajiya Babba ya nemo, take ya doka mata ƙira sai dai bata yi picking ba, kamar dai yayi kuka haka ya ji, amma a yadda yake ji ko me za a yi sai ya magantu da ita kafin ya cigaba da gudanar da al'amuransa.
Vibration ɗin da wayarsa ta yi yasa ya duba, ganin Hajiya Babba yasa ya katse kiran sannan ya kira ta, ko da tayi picking suka gaisa cike da girmamawa, nan yake tambayarta Zahrah. Ce masa tayi tana bacci.
Har zai datse kiran yaji ta ce
“Akwai wani abu ne?”
“A'a dama Hajjaty ce tace In ta tashi a ce da ita tana neman ta.”
Hajiya Babba ta amsa masa da
“To bari na tayar da ita tunda Hajjaty ke kiran.”
Daga haka yayi mata godiya tare da datse kiran.
Hajiya Babba da kanta ta shiga ta tayar da Zahrahn wacce har lokacin bacci bai bar idonta ba.
“Zahrah, ki yi wanka ki karya, Hajjaty na neman ki ”
Cikin Muryar bacci tace
“Tooo, sai na tashi”
Nan ta fara ƙoƙarin komawa baccin, fuska ɗaure Hajiya Babba tace
“Am I not talking to you? Zaki miƙe ne ko kuwa?”
Da sauri ta dira daga Bed ɗin ta nufi toilet.
Bayan ta yi wanka ta yi wanka ta shafa mayukanta da ta tattaro wasu ta taho da su, tana gamawa ta saka wata light blue fitted gown wacce ta matuƙar amsar jikinta, daga nan ta saka hula don ko da wasa ba ta sakaci da saka kwali ko don dukan sa tasha wurin Mamah. Sai da ta fesa turare tukun ta fito parlourn. Babu kowa sai Nasreen wacce ke kallon maimaicin series film na Habibaty man takun2 Wadda ake haskaka a mbc Bollywood.
Ba tare da Zahrah ta bi ta kanta ba ta nufi dining tayi breakfast ɗin ta, tana gamawa tayi Hamdala tare da miƙewa, sai da tazo fita ta kalli Nasreen ɗin tace
“Sister, na wuce part ɗin Hajjaty. Idan Aunty Mabruka ta Zo fita tace Ina wayarta yana bedside drawer, bye!” ba ta jira amsar ta ba ta fice.
Tana fita kai tsaye ta nufi part ɗin Hajjatyn zuciyarta na bugawa musamman in ta tuna da yadda lokaci ɗaya tayi musu ƙaura sai lokaci lokaci take shigowa ta gaida su tsawon kwanaki kusan goma, karo na farko da taji bata kyauta musu ba kuma nadama ta sauƙa mata.
A hankali ta fara takawa har ta zo kusa da makeken get ɗin, kamar an ce ta kalli gefe kuma taga motarsa a gefenta, idanuwa ta zaro tana rufe bakinta da hannunta, cikin ranta kuma tana faɗin
“Shi kenan ai!”
Har ta juya zata koma idan ya so bayan ya tafi ta dawo sai wata zuciyar tace
“Why kike nesanta kanki da garkuwarki ne Zahrah?, Saboda zai yi aure?”
“A'a” ɗaya ɓangaren na zuciyarta ta faɗa
“Bana buƙatar kusanci ne da shi saboda kada...”
“A'a Zahrah, baki yiwa kanki adalci ba In kika ce haka, meet him and apologize! That's all!”
Da wannan shawarar ta juya ta nufi ɓangaren zuciyarta na bugawa da sauri da sauri kamar za ta fasa ƙirjinta ta fito don ba shakka in ka Kura wa chest ɗin ta ido za ka ga yadda yake hawa da sauka, an indication of anxiety!
*Good night my esteem fansa, a yi bacci da minshari, saura kuma ku yi mafarkin Black-devil, babu ruwa na!*
*Reat and share Fisabilillah!*
[12/30/2024, 4:31 PM] Diamond Bhatool: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣8️⃣
﷽
A Haka dai ta daure ta shiga ciki, lumshe idanuwanta tayi tana ƙara shaƙar ƙamshin parlourn tare da sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a parlourn...
A hankali ta fara takawa i zuwa ciki, daidai Bedroom ɗin Hajjaty ta ku, daddaɗan ƙamshin turarensa da ke kwantar da hankalin mai shaƙar sa ta jiyo,
Waigawa tayi amma bata ga alamar existence ɗin wata halitta ba.
Gently ta buɗe ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Hajjaty ta amsa mata fuska ɗaure.
“Ina kwana Hajjaty”
“Lafiya” daga haka ta yi shiru. Ganin Hajjatyn ma kamar fushi take da ita yasa ta fara aikin lallami, da ƙyar Hajjaty ta haƙura da sharaɗin za ts tattaro kayayyakin ta dawo. Da haka Zahrah tace
“Yanzu ma zan ɗauko masoyiya kakata.”
“Ke kika sani dai, wato za ki lallame ni ki sa na haƙura, ai ban gama fushin ba Zahrah'u.” ya faɗa tana cilla mata hararar wasa.
“Haba uwargidan Alhaji Baba, naci albarkacin kasancewa ta ɗiyar tilon ƴar ki mace.” daga haka ta fita da sauri da nufin ta kwaso kayanta, bata aune ba taji ta ci karo da mutum. Ƙamshin turarensa tabbatar mata da cewa shi ne.
Da sauri taja baya tana dafe ƙirji yayin da idanuwanta ke zare kamar ta ji karo da zaki. Yadda ta ja bayan ne ya bashi dariya har sai da ya murmusa.
“I'm...i'm... I'm sorryyyy” ta faɗa a rarrabe tare da jan sorry ɗin. Ba tare da ya kalle ta ba ba kuma ta sa ran zai kalle ta ɗin ba.
“Follow me!” ya faɗa a zafafe sannan yayi gaba ita kuma ta bi bayansa zuciyarta na bugawa. Kan ɗaya daga cikin sofas ɗin yayi ma kansa mazauni. Jiki sanyaye ta zauna kan lallausan carpet ɗin don ko giyar wake ta sha ba zata zauna ba whole shima yana zaune ba.
Ta kai mintuna biyar zaune bata samu arziƙin ko da kallo ba. Ganin ƙafarta ta fara gajiya da zaman yasa ta ɗan gyara tare da faɗin
“Yaya ga ni”
Banza yayi da ita har lokacin kuma idanuwansa na lumshe kamar mai bacci. Har ta fara sarewa ga amsawar sa taji ya ce.
“Ai bana gani”
Hannunta biyu ta haɗe tana zaro idanuwa waje fahimtar gatse yake mata.
“I'm sorry, ina kwana.”
“Ashe kin iya gaisuwa.” ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba. Cikin ranta kuma tana ta mamakin yadda ya sauya mata lokaci ɗaya. “Is he that tough?” she asked herself.
Sai da ya gama shan ƙamshinsa tukun ya gyara zamansa. Kallonta yayi yana mai nazartar ta, ganin yadda ta rame sai ya ɗan tausaya mata yana kuma tunanin ko bata da lafiya?. Ba mai bashi amsa hakan yasa yace
“What's wrong with you?” in a pitiful voice., Lokaci ɗaya ta ɗago tana kallonsa jin a irin yanayin da yayi maganar tana kuma ƙara mamakin sauyawarsa kamar ba shi bane ya gama cakume fuska ba.
“Kin san ba na maimaita magana.”
A ɗan kiɗime tace
“A'a eah a'ah ai lafiya ta ƙalau me ka gani?” kallon da yayi mata yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
“Idam lafiyarki ƙalau why do you look so emaciated?”
“Eh dama karatu ne shiyasa”
“Karatun ne ya ramar da ke?” ya faɗa sounding so intensed.
“E Yaya ka san an wuce ni and I want to catch up” ta ba shi amsa a shagwaɓe, yanayin yadda tayi maganar sai da yayi melting heart ɗin sa, a hankali yace
“Is ok....ba wannan ba, me yasa kika raina ni ne Lily?”
“Ni!?” ta nuna kanta da yatsa tana ƙwalalo ido waje...harararta yayi yace
“A'a Ni!”
Shagwaɓe fuska ta ƙara yi tana faɗin
“Am sorry Yaya, wallahi ban raina ka ba, Niii Ƴar Madina na isa?”
Dariya sosai ta bashi fot her last statement Amma ya dake.
“Ga shi nan kuwa In na saka miki doka ba kya bi?, Kin mayar da Ni sa'an wasanki ko?”
“Don Allah Yaya ka yi haƙuri, wallahi ba zan ƙara ba.”
“You will repeat it Lily!” ya faɗa a ɗan kausashe.
Kamar za ta yi kuka tace
“Allah Yaya na tuba na bi Allah, ba Zan ƙara ba.”
“Is ok” ya ba ta amsa “Zan yi haƙuri ne only on a condition.”
Kafin taji condition ɗin ta amsa da
“Ko mene ne na yadda”
“Is alright, the condition is....” sai Kuma yayi shiru.
Ina an excited tone tace “All ears”
Gyara zamansa yayi kana ya fara magana.
“Why na saka miki dokar jira na nayi dropping naki school sannan na ɗaukoki kika mayar da Ni mahaukace? 2. Why kika gudu daga nan ɓangaren zuwa can ɓangaren Hajiya Babba?”
Gabanta ne ya bada wani irin sauti, haɗuwarsu ta yanzu har ta manta damuwarta sai yanzu da yayi maganar, cikin ranta kuma tana gabza muhawara kan ta faɗa masa ne ko a'a? Daga karshe dai ta yanke shawarar binne abun a ranta.
“Don't let me repeat myself Lily.” ya faɗa sounding intensed
“Allaj Yaya ban Yi duk abubuwan da ka lissafo da wata manufa ba, infact na tattara na koma can ne to study harder as I told you earlier?”...
“Abi?”
“Da gaske Yaya!” ta bashi amsa kamar za ta yi kuka.
“You must be very silly Idan har an faɗa miki cewa zan yadda