Showing 12001 words to 15000 words out of 157517 words

Chapter 5 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5131

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*


Wattpad: @diamond_bhatool
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._



*PAGE* 0️⃣6️⃣

_Dedicated to Moonlight writer's Association_

_Masu neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu_






Hira suke sosai abunsu, tuni Zahrah ta saki jiki kamar ba ita ba. Suna cikin hirarsu Nasreen ta ce “Zahrah ajinki nawa ne yanzu?”
Sai a lokacin Zahrah ta tuna da batun wata makaranta. Cikin raunin murya tace “Eh da ina zuwa lokacin da Mama na nan, mun kai SS 2 kuma sai na daina zuwa sosai, amma dai ban gama ba?”
Fuskar Nasreen ɗauke da ayar tambaya tace “Ban gane ba Zahrah?”
Kau da kai gefe Zahrah tayi tana faɗin “Mance kawai Nasreen”
Sauran da basu faɗin komai tun bayan introducing kansu suka haɗa baki wurin faɗin “Haba Zahrah, a mance kuma”

Haka kawai ta ji wani iri ganin sun nuna concern Nasu a kanta, At least sun cancanci su san komai nata.
“Kinyi shiru” Nainarh ta ƙara fada fuakarta fal damuwa.
“Eh am dama fita nayi a makarantar”
Dafa kafaɗarta Zakiyya tayi tace “Feel free, mu nan duka ƴan uwa ki ne Zahrah ”
Rumaysa ta ƙara da faɗin “Ki ɗauke mu kamar yadda muka ɗauke ki Please, mu dukkanmu ƴan uwa kuma ƙawaye muke gare ki, don Allah Zahrah ki faɗa mana”
Zuciyarta ne ta karaya da yadda suke maganar, hakan yasa ta basu labarin Dalilin barinta makaranta.

Sun tausaya mata sosai. Nasreen ta ce “Kada ki damu Zahrah, zaki koma makaranta, makarantar ma wacce ba'a yi tsammani ba, kiyi haƙuri kin ji?” kai ta gyaɗa sai Nainarh ta ce “Ni fa Zahrah wallahi kin matuƙar yi min kama da wata yarinya wacce da take trending a social media, what's that her name?, Rumaysa kin gano yarinyar nan da kwanaki muka ga video nata tana speech lokacin muna JSS three ne kamar dai”
Rumaysa ta ce “Ƙwarai kuwa Nainarh, nima na fuskanci hakan, sunan ta Zahrah ne kamar dai?”
Zakiyya ta ce “Kai wallahi inaga wannan Zahrahn ce, kun san me yasa?”
Duk suka jijjiga kai banda Zahrah da ke binsu da ido.

“Kun tuna lokacin da muka ga news na best in BECE a Bauchi State a parlourn Alhaji Baba?”
Kansu suka ƙara gyaɗa mata.
“To wallahi lokacin nan sai da Alhaji Baba yace anya wannan ba jininsa bace?, amma ke Zahrah daga wane gari kika taho?”
“Bauchi” ta basu amsa a gajarce.
Baki haɗe suka ce “Wallahi ke ce yarinyar nan!”
Ɗan harararsu tayi tace “Sannu manya”
Dariya dukkansu suka yi. Nainarh ta ce “Kada ki damu Zahrah Kinga muma a SS 3 muke yanzu, Kinga sai muyi paper tare kawai, nasan zaki iya ko don irin yadda kwanaki muka ga kina trending a media da gani ke gifted ce”
“Uhm ba wani nan fa”
“Da gaske wallahi ” Zakiyya ta faɗa.

Haka suka yi ta hirarsu nan Zahrah ta basu labarin makarantar su ta da, da yadda aka yi ta fara zuwa. Yadda ta fara haskawa da kuma yadda ta bar makarantar. Sun matuƙar jinjina mata kuma sun mata alƙawarin kasancewa kamar Ƙawarta Badi'a a gare ta. Sosai suka ƙara jin ƙaunar junansu duk da cewa cikin ransu kowa tsoro yake, don zasu iya cewa a iya sashen Hajjaty ne suke samun wannan kusanci da kuma tattaunawa da juna.


****************

Hajiya Babba ce zaune a parlourn ta cikin shiga ta alfarma wacce ke ƙara bayyanar da kwarjininta a idanun mutane. Sallamar Affan ne tasa ta ɗago idanuwanta tana kallonsa. A gaban ta ya zauna yana faɗin “Barka da safiya Hajiya”
“Barka” ta bashi amsa a gajarce. “An gama meeting ɗin kenan?”
“Eh Hajiya an gama” shiru na ɗan wani lokaci ta ce “Masha Allahu, a kan me aka yi zaman ne?”
Fuska dauke da murmushi ya ce “Hajiya kin san wannan ƴar uwar su Alhaji Babba wacce ta ɓatan nan?, Aunty Madina yauwah kamar dai haka sunan yake!”
“eh me ya faru da ita to?” ta faɗa cike da son sanin abunda ke faruwa.
“Hajiya ai ƴarta ce ta dawo, amma ita ɗin an ce ta ɓata ba'a san yadda take ba.”

Cikin halin ko in kula ta ce “To Allah ya bayyana ta.”
Affan ya ce “Amin Hajiya, kin san mene Hajiya?”
Kai ta jijjiga masa “Yarinyar kina ganinta sai ki ce Hajjaty ce ta haife ta.”
Ba tare da ta ɗago ba ta ce “Ayya, ina Nasreen ne?”
Dariya Affan yayi kafin yace “Hajiya ai ƙafar Zahrah ƙafar Nasreen, tana can part ɗin Hajjaty”
Daga haka bata ƙara ce masa komai ba hakan yasa shima ya tashi ya nufi bedroom ɗinsa.


**************
Su uku ne zaune a katafaren Parlourn da alamu dai suna tattauna wani muhimmin zance ne. Mommah ce ta kalli Ammie da Mami ta ce “Nifah ina cikin matsanancin tashin hankali kwanan nan!”
Ido zare Mami ta ce “Lafiya Hajiya Sughrah?”
“To lafiyar dai, kin san har yanzu Aliyu baya ɗaga kira na?, hankali na ya gama tashi, shi ma wannan yaron Khalil bana samun numbersa, Abu ƙarami Aliyu ya ɗauke shi babba.”
Gyara zama Mami tayi ta ce “Kai Ni na rasa wane irin yaro ne wannan, mutum sai shegen taurin zuciya, gaskiya ina ga da sa hannu akan al'amuran sa fa, dole a duba al'amarin nan.”
Jimm kaɗan Mommah ta ce “Gaskiya ina tunanin hakan, Amma ko yaya za'a yi ai bai ƙarfi na ba, Ni na haife shi, zai dawo ya same ni ne, gabaɗaya kwanan nan da ciwon kai nake kwana, ga BP na ma ya hau wallahi.”
Mamie ce tayi gyaran murya ta ce “Ai kuwa Ni ne fara zargin anya ba Bakin Hajiya Babba cikin wannan al'amari kuwa?”

“Nima na fara zargin haka, ban san yaushe Hajiya Babba zata bar kowa ya shana da ƴaƴansa ba a gidan nan, duk ta bi ta maƙalƙale kowa kamar nata. Gaskiya dole muyi kyakkyawan shiri akan wannan al'amari” Ammie ta ƙara a kai, murmushi Mami tayi ta ce “Ni na rasa wane irin boka take bi haka, kiga fa abokan zaman ma kamar tsoronta su ke yi!”
“Yo ba dole ba!” Mommah ta faɗa “Ai dole su ji tsoronta, gadararta fa ita aka fara aura a gidan, ke su ma Hajjaty da Alhaji Baban ba haka ta bar su ba, duk irin yadda take tsula tsiyarta basa magana.”
“Mtss Allah dai yayi mana tsari da ita, ke Ni fa na fara zargin anya ba ita ce da yaranta ke zagon ƙasa ga Abatcha Automobiles ba?” Mami ta faɗa fuska ɗaure wanda ke nuna tsantsar takaicin abunda ke faruwa.

Kwanaki an saci billions of Naira daga asusun Companyn, sannan an saci motoci Masu tsadar gaske da bikes gashi duk binciken da za'a yi an kasa ganowa waye ya ɗauke su.

Haka suka ci gaba da hirarsu sai ga Nainarh ta shigo parlourn, kamar zata yi kuka ganin Mamie da Ammie a part ɗin su. Ta rasa me yake kawo su wurin Mommah ko yaushe, su zo suna zancen waccar masifaffiyar Hajiya Babbar.

Fuska ɗaure ta ƙarasa, ƙasa tayi da murya alamar bata so ta ce “Ina yinin ku”
Baki washe Ammie ta amsa da “Lafiya ƙalau Nainarh, an dawo kenan”. Baki taɓe Nainarh ta ce “Eh” tana ƙoƙarin wucewa. Muryar Mamie ce ta tsayarta tana faɗin “Zo mana Nainarh kamar wacce ake kora?” kamar zata yi kuka ta juya tana faɗin “Gani”
Murmushi Mamie tayi tace “An gama meeting ɗin ne?”
“Laa Kinga Ni har na manta ma da batun meeting ɗin” Ammie ta ƙara.
Kamar bata so ta ce “Eh an gama”
Cike da ƙosawa da tambayar ta ce “Zan ɗan shiga toilet ”
Baki washe Ammie ta ce “Babu komai shiga ki fito mana”

Daga haka Nainarh ta nufi bedroom ɗin ta tana sakin ajiyar zuciya. Tunani sosai take akan rayuwar wannan family nasu, a haka zaka ga kamar cikin farin ciki da ƙaunar juna suke amma a gaskiya babu duka biyun, a da yadda taji ana bada labari ƙalau ake zaune, amma tun wani lokaci da ya shuɗe zaman lafiya ya ƙauracewa wannan family, ga dai duniyar ta samu sai son Barka, abu ɗaya suka rasa shine zaman lafiya da kwanciyar hankali don kuwa daga Wannan sai wancan

Kullum cikin cases ake, yau wannan gobe wancan, an rasa gane ina gaskiya take, saran ɓoyen da ake a gidan ya fara wuce misali. Kowa na zargin kowa, cikin matayen gidan ma babu wata jituwa mai kyau, gidan Alhaji Babba dai suna zamansu ƙalau, amma sauran gidajen kam ba'a magana, wasu kansu haɗe musamman amaren hakan iyayengidajen ma.

Idan muka koma ɓangaren yara kuma Alhamdulillah yawancin su kansu haɗe yake, sai dai wasun ba haka bane. Wasun sun tashi ne kuma an raine su da ƙiyayha da kishin juna, yayinda wasu kuma ke zaune cikin farin ciki da sauran.

A ɓangaren su Mommah tun shigar Nainarh bedroom nata suka ci gaba da hirarsu. Ammie ce ta ce “To yanzu ke Hajiya Sughrah meye hukuncin da kika yanke kan shi Aliyun?”
Gyara zamanta tayi tace “Ni me na San zan yanke ne? Gabaɗaya kai na ya kulle, na tura masa messages ma Bana tunanin ya gani, na ce masa yayi haƙuri ya dawo gida za'a shawo kan matsalar amma ya ƙi.” ta idasa cikin raunin murya.
“Gaskiya ban ji daɗin abinda ya faru ba, shi ma Aliyu me ya kai shi ga neman ƴar gida a cikin gida?,gashi yanzu ba'a san ma wane hukunci Alhaji Baba zai yanke ba.” Ammie ta faɗa cike da kulawa.
“Abun da na gani kenan Hajiya Saudatu, sai dai wani hanzarin ba gudu ba, tunda yanzu dai muna hasashen irin hukuncin da Alhaji Babba dai yanke, ina laifin kawai mu haɗa aurensa da Kausar idan ya so Kinga dole Alhaji Baba ya dakatar da wannan hukunci!” Mamie ta faɗa tana son ƙara nunawa Mommah muhimmanci wannan shawarar sai dai Ammie ji take kamar ta ƙwale ta don ta mata shigar sauri.

Jimm kaɗan Mommah tayi tana tunanin yadda abun zai kasance, idan har tayi wasa da wannan damar za'a samu matsala, amma wani ɓangare na zuciyarta na nuna mata illar hakan, musamman in ta tuna da halin Mazan nata, sai kuma Wani ɓangare na zuciyarta ta ce mata “Cikin ku waye ya haifi wani ne kam?”
Tabbas dole yanzu ta nunawa Ya Sadauki iyakarsa, babu yadda ya iya, dole ya bi wannan sharaɗin nata, tunda gashi ƙiri da muzu dai so ake kowa ya tsane shi a gidan. Kullum tana da burin sanin waye ke musu wannan Zagon ƙasa (Khadija candy). Har yau har yanzu ma bata gamsu da cewar Ya Sadaukin zai aikata abinda aka tuhume shi a kai ba.

Ganin shirun da Mommah tayi yasa Ammie jin daɗi ganin dai alamar ƙorafin Mami bai karɓu ba. Ɓangaren Mami ma ras gabanta ya buga, fatan ta dai Allah yasa kar ta bayyana hakan gaban Hajiya Saudatu.
“Kinyi shiru Hajiya Sughrah ”
Wata nauyayyar ajiyar zuciya Mommah ta sauƙe tana faɗin “Gaskiya ne Hajiya Baraka, ina ga shawarar ki ta yi, amma kuna tunanin kuwa Sadauki zai amince da wannan haɗi?”
Cike da son ƙarfafa mata guiwa Mami ta ce “Ƙwarai kuwa ai dolensa ya amince Hajiya Sughrah, ke ce uwar ko shi?”
“Ni ce mana”. Mommah ta bata amsa.
“Idan kuwa ta tabbata hakan ban ga abun tashin hankali ba, yanzu dai amincewar ki kawai nake jira.”

Hararar gefen ido Ammie ta jefawa Mami don ji take kamar ta shaƙo wuyanta ko zata huta, sai dai kawai sai ta danne gudun kada a gani wacece ita ɗin “Ki amince kawai Hajiya, in ba haka ba kuma ki shirya haɗa zuri'a da Hajiya Babba, ta ƙara samun damar mallake ko da ɗan naki tare da dukiyarsa fiye da da .” Ammie ta faɗa yayinda zuciyarta ke ƙuna.

Murmushi Mami tayi jin yadda Ammie ta sauƙaƙa mata plan ɗinta. “Ina sauraron ki Hajiya Sughrah ”
Kamar zata yi kuka tace “Babu komai, yanzu dai Allah yasa ya dawo gidan, in ya dawo ko baya so dole ne ya amince da auren nan, don wallahi ban isa ba haɗa zuri'a da dangin Mayu masu mallake zukatan jama'a ba ”

Cike da farin ciki Mami ta ce “Kar ki wani damu Hajiya Sughrah, akwai malamin da yake min addu'a, gobe goben nan zan samu na je wurinsa, cikin kwana uku zaki ga Sadauki ya dawo gida” fuska sake Mommah ta ce “Da kuwa kin samu kyauta mai tsoka matsayin tukuicin ki.”
“Baki da damuwa Hajiya, Ni dai tunda kin amince zan kula da komai.”

Ammie ce ta fara miƙewa da niyyar wucewa, Mani ta ce “Hajiya Saudatu ki ɗan jira Ni don Allah sai mu wuce”
Fuska sake Ammie ta ce “To kin san ina so ne naji yaya akan me suka tattauna yau, fata na Allah yasa ba batun Sadauki bane ”

Ɗan ƙaramin tsaki Nainarh da ta fito daga bedroom ɗinta tayi, steps ɗin takalminta Ammie ta ji hakan yasa ta waiwayo don ganin ko Hajiya Baraka ce. Ganin Nainarh yasa ta washe baki tana faɗin “Nainarh, kin fito gashi zamu wuce, ko zaki biyo NI ki karɓi kunun gyaɗar ne?, na riga na gama Shiyasa amma na ajiye miki sanin yadda kike son abun.”
Fuska sake Nainarh ta ce “Kai Amma na gode sosai , bari kawai na bi ki na karɓo”
“To kiyi sauri.”
Daga nan Nainarh ta bi bayan Ammie zuwa shashen ta.

_Don Allah masoya ayi reacting, masu complain cewa basu ganin update kuyi haƙuri don Allah, zan rage ɗaura abu bayan update saboda kuna gani, idan baku samu ba kuma zaku iya yi min magana na tura muku ta 08143760764. Please ayi reacting sannan a taya Ni sharing, zan ƙara yawan update a rana in har na ga sauyi, at least 100 reactions nake son gani._
_Thanks my esteem fans, Love you loads.._

[11/9, 11:45 AM] Diamond Bhatool💎:


*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_


*PAGE* 0️⃣7️⃣




Bayan tafiyar su Nainarh ya rage sai iya zahrah wacce ta lula izuwa duniyar tunani, tabbas yanzu ne zata fara gina rayuwarta, amma kuma matsala ɗaya da ta gagara kawar da ita daga ƙwaƙwalwarta shine rashin Mama. Fatanta kullum Allah ya bayyana ta. A wani ɓari na zuciyarta kuma haka kawai take jin wani baƙon yanayi na ziyartarta tun shigowar ta wannan gida, har ta kai ga ta fara tunanin kamar ƙaddarar rayuwarta na shirin canzawa, sai kuma wani abu da ta lura da shi a ƴar hirar da suka yi da cousins nata, amma sai ta kawar jin abun na shirin kai ta wata duniya ta daban.


*****************

*LONDON*

Alhamdulillah zamu iya cewa don a halin yanzu, jikin Ya Sadauki yayi sauƙi sosai, kulawa kam ya same ta daga Ya Khalil da kuma likitansa DR. Arƙam. Abu ɗaya da har yanzu ya kasa fahimta shine tsawon jinyarsa da Ya Khalil yayi bai taɓa ce masa komai ba, idan ya gama masa abunda ya dace a matsayinsa na majinyaci baya ƙara cewa komai, tun yana sharewa saboda miskilanci irin nasa har ya dawo abun ya fara damunsa don tsawon rayuwarsu hakan bata taɓa faruwa ba, sun tashi ne cike da so da ƙaunar juna duk da cewa babu wata alaƙa mai kyau tsakanin iyayensu mata, a irin hali na Ya Khalil, Ya Sadauki kansa ya san shi ke hakuri da shi.

Ganin ba shi da wata mafita kuma hakan na ƙarawa zuciyarsa nauyi yasa yayi niyyar tunkarar ɗan'uwan nasa ya ji wani irin babban kuskure ya tafka haka ne har ya iya fushi da shi, fushin ma irin wadda bai taɓa yi ba.
Lumshe fararen idanuwansa yayi yana sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya.

Shigowar Ya Khalil ne yasa ya buɗe lumsassun idanuwansa da sauri yana kai dubansa gare shi, sai dai abunda ya ƙara bashi mamaki shine yadda Ya Khalil ɗin ya kauda kan sa gefe. Kujerar da ce gefensa ya ja zauna fuskar nan tamau kamar an aika masa da labarin mutuwa. Kamar zai bar maganar sai sun koma sai kuma ya daure, a hankali cikin Muryar da ke nuna cewa mallakinta lafiya bata wadace shi ba ya ce “Dude!”.

Ɓangaren Ya Khalil ya ji sarai sai ya ƙara ɗaure fuska ba tare da ya juyo ba. Zuciyar Ya Sadauki ne ta ɗan karye sai kuma ya tsinci kansa da ƙara ƙiran Ya Khalil ɗin. “Dude!” nan ma ya Khalil bai amsa ba. Hakan ya ƙara tabbatarwa Ya Sadauki irin fushin da ɗan'uwansa yayi da shi. Tunanin yadda za'a yi ya sanyaya zuciyarsa yake amma ya rasa. Karo na farko da murmushi ya sauƙa kan kyakkyawar fuskarsa, alamar dai ya tuna da wani abun ne da ya saka shi nishaɗi.

Lokaci ɗaya kuma ya sarƙafe da tari ba ƙaƙƙautawa, a zabure Yaya Khalil ya miƙe ya nufi yadda yake. “Man! Man!!!, lemme call the Dr.” sai ya juya zai fice a rikice. Dakatawa yayi jin an riƙe shi, tuni ya waigo yana duban Ya Sadaukin da yayi kalar ban tausayi da fuskarsa.
Haɗe fuska Ya Khalil yayi kamar ba shi ya gama nuna kulawarsa ga yanayin ɗan'uwan nasa ba. “Ya dai Malam, let go off me!”
A sanyaye Yaya Sadauki ya ce “Why Dude?” ya idasa cike da raunin murya. “Why all these please?, idan ka juya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login