Showing 90001 words to 93000 words out of 157517 words

Chapter 31 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5147

Allah yayi mata rahama yasa ta dace, ya kuma sa rayuwar can ta fiye mata nan gidan duniya.

Rashin mai shayarwa a cikin familyn ga kuma yadda Little Sadauki ke kuka alamar yunwa tana addabarsa yasa ZAHRAH ɗauko sauran kuɗaɗen nan da Late Yaya Sadauki ya basu su gama harhaɗa wayoyinsu kana taje ta karɓo Little Sadauki daga wurin Mamah tace ta kawo shi ta jijjiga shi. Tana karɓansa kuma sai ta fice daga gidan ta nufi asibiti da shi, wata ƙwararriyar nutritionist ta samu ta mata bayani cewa yaron mahaifiyarsa ta rasu, babu kuwa mai shayar da shi ga shi kwanansa goma ne a duniya.

Daga ƙarshe dai ta ba da shawarar a haɗa masa formula feeding kawai, nan ta rubuta mata requirements ɗin tace ta suyi kana ta kwatanta mata yadda za ta yi constituting nasu. Daga nan ZAHRAH ta saɓa Little Sadauki a kafaɗa suka wuce mota, sai da ta sayi komai na buƙata kana ta koma gida, lokacin kuma har ya yi bacci abunsa.

Kwantar da shi tayi a bedroom ɗin Hajjaty sannan ta shiga ta fara harhaɗo duk wani shirgi nasa, daga nan kuma ta fara ƙoƙarin constituting formula ɗin, cikin Sa'a ta gama, kamar jira yake ta gama haɗawa ya tashi yana tsalla ihu. Yadda aka kwatanta mata haka ta fara feeding nasa, cikin ikon Allah kuwa sai ga shi yana sha a yunwace, sai da ya ɗauke kansa da kansa tukun Zahrah ta haɗa ruwa ta wanke shi ta saka masa kaya sannan ta goya shi, kafin kace me bacci ya ɗauke shi.

A lokacin da Zahrah ta fito parlour duk sai suka bi ta da kallon mamaki Mamah na tambayar ta ina Little Sadauki? Ta basu amsa da faɗin “Bacci yake?”
“Bcci Kuma?” suka faɗa a tare, nan Zahrah ta musu bayani dalla -dallah, Hajjaty har da hawayen farin ciki tana ƙara sakawa Zahrah albarka don kuwa abun da ya tsaya mata a rai kenan.

*Yaya Ishaq*

Tun ranar sunan Little Sadauki yayi fushi da Zahrah, ya ma riga ya yanke shawarar tunkarar magabatanta da maganar aurensu tun kafin wani ya masa overtaking.

*Life*

Ɓangaren Zahrah kuwa gabaɗaya yanzu sai a hankali, tana dawowa daga school za ta zo ta amshe Little Sadauki, karatun kirki ba ta yi a gida shi yasa ta tsara in sun gama lectures za ta ke tsayawa tayi karatu, in ta dawo kuma lokacin Little ɗinta ne.

A yanzu ma dai kwance yake a gabanta ta zuba masa idanuwanta, kau da kanta tayi gefe ganin mutuwar Yayanta na shirin dawo mata sabuwa yasa ta kunna wayarta tare da shiga videos,ba da son ranta ba ta taɓa waƙar saleem smart 🤓.
Ba tayi ƙoƙarin katsewa ba ta kashe kunne tana saurare.

“Uhm” ta faɗa tana sauƙe ajiyar zuciya, haka kawai sai ta tsinci kanta da dialling numbern Yaya Ishaq, bayan ta gama ringing ya ƙira ta, kamar kada ta dauka sai kuma ta ɗauka.
“Assalamu Alaikum Yayana na kaina”
“Waalaikis Salam my queen, how's your day”
In slow tone tace “So dull...”
“But why?” he asked looking furious
“Saboda ka manta da Ni, did I offended you Yaya Ishaq?” ta tambaya shagwaɓe
“Noo...” ya ba ta amsa “It seems like ina disturbing naki ne Queen, shi yasa na ɗaga miki ƙafa ki huta”

Maganarsa tasa taji babu daɗi, cikin Muryar kwantar da hankali tace “I'm sorry Yaya na, ba haka bane, kawai har yanzu ina cikin moaning na rashin Aunty Mabruka ne.”
“Ayyaah sorry Rouhy, addu'ar mu take buƙata, Allah ya mata rahama.”
“Amin” ta amsa a hankali.
“Uhm...mine?”
A ɗan shagwaɓe tace “I'm all ears”
“Kika ce bana takura miki ko?”
“Uhm” ta ba shi amsar a gajarce.
“That's good of you, I love you”

Ƙasa-ƙasa tace “I love You too” sai kuma ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana leƙa fuskar Little Sadauki da ke bacci ta tsakanin yatsunta. Murmushi mai sauti yayi har tana iya jiyowa.
“Alhamdulillah! Yau dole nayi sadaƙa...first in history Queenie ta ce tana so na, Allah na gode maka.” cike da shagwaɓa tace “Uhm Ni Yaya ka bari, shiyasa kullum ban son faɗi, duk sai ka sa mutum jin kunya.”
“I'm sorry, shikenan na daina, yanzu yaushe ne auren namu?”

Kamar tana gabansa ta rufe fuska tana Turi baki gaba.
“Kin yi shiruu”
“Ni Ni Ni ba yanzu ba, Ni fa yarinya ce.” dariya Yaya Ishaq yayi, sai da yayi mai isarsa kana ya dakata. “Kika ce ke yarinya ce Queen?” “Uhm”
“Ai kuwa get ready and speedy your growth, ki zama Babba, in not more than 6,7,8,9, months by now ko? Hmm you'll be my one.”
Kunyarsa sosai take ji hakan yasa tayi shiru, shima da ya fahimci hakan sai ya mata sallama yana sakin wani murmushi, atleast dai ta faɗa mata.

A haka rayuwar ta ci gaba da tafiya, yau ne gobe ne wasa-wasa yanzu kusan sati biyu da rasuwar Aunty Mabruka, sosai Little Sadauki ke samun kulawa daga wurin Mamah, Hajiya Babba, Mommah da kuma uwa-uba Zahrah wacce ke ganin za ta iya sadaukar da komai nata saboda shi. Sosai ya fara girma kuma jikinsa bai nuna alamar yunwa ko rashin ƙoshi ba.

A daidai wannan lokaci Yaya Ishaq ya tunkari Mom ɗinsa da batun aurensa da Zahrah, sai da ya gama faɗa mata kuma ya fara sosai kai wai kunya yake ji. Murmushi tayi tare da ɗan ranƙwasar kansa tace
“Look at him, see how shameless he's ” sai kuma ta ɗan harare shi, shagwaɓe fuska yayi kamar zai yi kuka. Mom tace
“Dube ka, U be like...Mom in na rasa ta i can't live, ina sonta Mom...” sai kuma tayi dariya. Miƙewa tsaye yayi yana buga ƙafa kamar wani 4years old boy. Dariya Mom ta kuma yi tare da miƙewa tsaye tana faɗin “Bari Daddynka ya shigo sai muyi magana, Allah sanya alkhairi.”
“Amin Mom” ya faɗa yana hayewa sama zuciyarsa wasai.

Yana shiga bedroom nasa yayi dialling numbern ta duk da bai da tabbacin za ta ɗaga kiran sai dai yana fara ringing tayi picking.
“Hi my Yaya” ta faɗa tana sakin murmushi kamar yana gabanta.
“Malikatu albi...”. A yadda ya furta sunan sai da tsinci kanta cikin wani irin yanayi. Jin ta yi shiru yasa ya murmusa tare da faɗin “Are You there? Hello?”
“Uhm” ta faɗa a gajarce.
“I just call to check upon your health...kuma ina so naji Muryar ki tunda kin hana Ni ganinki.”
Jiki a sanyaye tace “It be no like this Hubby, kawai abubuwa ne suka min yawa amma ina lafiya, hope Kai ma haka.” Sosai ya cika da mamaki jin yau ta ƙira shi da Hubby, he feels like ya daka tsalle don murna.

“Lafiya ba lafiya ba tunda kewarki ta min yawa, ina son ganin ki, kin ba Ni dama na zo?”
A ɗan shagwaɓe tace “Yaya ai ban hana ka zuwa ba kai da gidanku?”
“Za dai kimin daɗin bakinki ko, anyways I'll be coming today with a good news.” gabanta ne ya ɗan buga jin ya mbaci good news Amma sai ta kawar da abun da zuciyarta ke kintsa mata tace. “See You soon.”
“I love you” ya faɗa yana sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya. Can ƙasan maƙoshi tace “Same here husband to be.”

Ɗan zabura yayi har da miƙewa daga kishingiɗe yana ƙara tambayar kansa anya Habibati alb ɗinsa ce, cike da son tabbatarwa yace “Rouhy kamar naji kin ce wani abu?”
Kawar da kanta tayi kamar tana gabansa tace “Ban fa ce komai ba Yaya.”
“No Please Rouhy, Don't say that, please repeat yourself...kar ki ce a'a ”

“Ni fa Yaya i Don't say anything, I only say same.” ta ba shi amsa a shagwaɓe tare da langwaɓar da kanta tana kwaɓe fuska.
“Shikenqn since You don't cherish my happiness at all, sai na zo ɗin, bye...”
Yanayin yadda yayi maganar sai taji kamar ba ta kyauta ba, hakan yasa tace
“Sorry Husband to be, please no vex ”
Sosai yaji daɗin sunan da ta ƙira shi har bai iya ɓoye hakan. Cike da matuƙar farin ciki yace.
“Thank You heartthrob, sunan ya matuƙar yi min daɗi, Please be calling me with it kafin na zama Husband ɗin gasken.” A ɗan kunyace tace “No problem oo, your happiness is mine, bari na dubo Little Sadauki na ji kamar kukansa.” ba don ya gaji da jin muryarta ba ya mata sallama yana ƙara nanata irin ƙaunar da tayiwa wannan Yayan nata da har ɗansa yake samun wannan kulawa daga gare ta, Fatansa dai Allah ya ƙara karkato masa hankalinta gare shi ita ma ta so shi ko da rabin yadda yake sonta ne.

*React and share fisabilillah.*


https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND*
*WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 4️⃣2️⃣




A estate ɗinsu yayi sallar Isha, bayan an idar ya shigo ya gaisa da su Mamah ana raha ana dariya, Hajjaty ta takarkara tace “Yaron nan dai Ishaqa ba dai hankali ba, ka ga da ina da ɗiya mace ai da na baka auren ta.” dariya kowa yayi jin wani batu daga Hajjaty amma ita da da gaske take yi. Nasreen da ke riƙe da Little Sadauki a hannunta tace “Hajjaty sai dai cikin jikokinki ko?”
“Ai kuwa dai ƴar nan Nasreen, kin ma tuna min, ita wannan jikar tawa ina ga da ita za a yi.” Hajjaty ta faɗa baki washe tana mai pointing Nasreen. Caraf kuwa Nasreen tayi ta daidaici saitin kunnen Hajjaty murya ƙasa-ƙasa tace “Rufa min asiri Hajjaty kafin taji, kin san fa Yaya Ishaq yana da mata, auren ne kawai ba a ɗaura ba.”

Buɗe baki Hajjaty tayi tare da riƙe haɓarta da hannunta tace “Ikon Rabbis-samawati, yau nake ganin ikon Allah.” sai kuma ta dubi Yaya Ishaq da ke ɗan hararar Nasreen tace. “Lallai yaon nan ka shammace Ni, to duk da haka dai zan ƙara maka da ƴar jikar nan tawa.” kowa sai da ya dara banda Yaya Ishaq da ya ɗan kawar da kansa gefe yana faɗin “To Hajjaty.”. kallonsa Nasreen tayi tare da nazartar yanayinsa, sai taga kamar ba ta kyauta masa ba. Itama kau da kanta gefe tayi tare da miƙewa tsaye tana saɓa Little Sadauki a kafaɗarta kana ta nufi bedroom ɗin Zahrah.

“Mrs Ishaq to be...your Romeo is waiting.”
Ɗan harararta Zahrah tayi tana fesa turare, hakan ba ƙaramin dariya ya ba wa Nasreen ba har ta gagara riƙe dariyar. Sai da tayi mai isarsa tace “Lallai, irin wannan wanka haka ai sai ki zauta Romeo ɗin naki, eh” ta faɗa tana ɗage mata gira. Ba tare da Zahrah ta ce da ita komai ba ta ɗan keɓe ta za ta wuce. Baki riƙe Nasreen tace
“To ai sai ki yi, kya fita ai, to bari kiji su Mamah na parlour.”
“To sai me? Ba dai wurin Yaya Ishaq zan je ba?” ta faɗa tana aikawa Nasreen kallon hadarin kaji. Ba kaɗan ba Nasreen ta shaƙa amma sai ta tsinci kanta da sakin murmushi irin wadda ake ƙira da yaƙe kana ta ɗan murza idanuwanta.

Ko da Zahrah ta isa parlour ba ta hango shi ba hakan yasa ta tabbatarwa kanta ya fita, ba tare da ta dubi su Hajjaty ba ta sa kai za ta wuce maganar Mamah ta tsayar da ita. “Ina ne za ki je haka Zahrah?” kamar za ta yi kuka haka ta juyo tana kwaɓe fuska. “Mamah saƙo zan amso yanzu zan dawo.” ba tare da Mamahn ta yarda ba tace “To.” daga haka Zahrah ta saki wani irin killer smile ta fice.

Tana fita ta fara waigawa ta ko'ina Amma to her surprise Babu shi babu alamarsa, kamar za ta yi kuka ta ɗauko wayarta daga cikin pocket ɗin fitted atamfarta da ta mugun amsar jikinta. Numbern shi tayi dialling bayan ya shiga kuma sai ta jiyo ringing ɗin wayar kusa da ita, juyawa ta fara yi to detect from where is the sound coming, Babu zato babu tsammani ta hango shi jikin flowers ɗin da ke jikin gini.

Daga wurin ta turo baki gaba tare da fara takawa a hankali, takunta kaɗai ɗaukar hankali gareshi bare kuma a zo batun ado da kwalliya, even without makeup Zahrah is a classic and beautiful lady bare kuma ta ɗau kwalliyar ma. Kallonta yake cike da soyayya yana sakin wani irin murmushi, tunda ta fara takawa ya kusa rasa hankalinsa, the way she walks....uhm, tana taku majestically kamar wacce ta fito daga royal fam, har lokacin kuma bakinta gaba yake, shi dai yau ya rasa ta kansa coz Zahrah is trying to kill him with this steps, cike da shaukin ƙaunarta ya ci gaba da aika mata da kallon da ke bayyanar da ma'anoni daban daban.

Duk da cewa she's not comfortable with the way he looks at her Amma hakan bai sa ta daina takunta ba wadda ya kasance ɗabi'arta tun kafin ta cika budurwa bare kuma yanzu da jinin ƴan matancin ya mamaye ta. Har ta isa wurin da yake ta ɗan ja gefensa ta tsaya bai dawo duniyarmu ba, hakan yasa ta waving hand ɗinta a saitin idanuwansa. Caraf ya zabura kamar wani munafiki yana ƙiƙƙifta ido wanda hakan ya matuƙar ba ta dariya, ba tare da ta sani ba ta fara dariyar, shi kuwa banda aikin kallo babu abun da yake aika mata musamman cheeks nata da suka lotsa sai yaji kamar ya kai yatsanshi ya taɓa.

Sai da ta gaji da dariyar kana ta daidaita kanta, Yaya Ishaq dai anya lafiya yake? Idanunsa still yawo suke a kanta. Sai a lokacin kuma wata kunyarsa ta kama ta, hakan yasa ta kawar da kanta gefe sai kuma ta duniyar da kan nata ƙasa. A daidai lokacin da fuskarta ta kubucewa kallonsa ne kuma ya dawo dai-dai, gyara tsayuwarsa yayi yana saka both hands nashi a cikin pocket ɗinsa.
Cikin wata irin murya mai daɗin amo da sanyin saurara yace “Ba zan taɓa gajiyawa da kallon ki ba my Queen, kinga gaba ɗaya na susuce ko?”

Ba tare da ta ɗago ba tace “Uhmm, you're welcome Yaya, ka zo lafiya?”
“Lafiya Lau my Queen” ya ba ta amsa yana ƙara kallonta, Fatansa Allah yasa idanuwansu su haɗu, cikin rashin Sa'a ta ɗago, suna haɗa ido ta kawar da nata gefe, murmushi yayi yana furta “Yau kuma irin wannan kunya haka Malikat albi? Ba wannan ba, You look so ma sha Allah, I'm indeed lucky to have you as my wife to be, Allah Allah nake wannan lokaci yayi da zan mallake ki, ina ƙara godewa Allah da ya ba Ni ke my Queen, please!” ya haɗe hannayenshi biyu yace “Please ki so Ni Ko da rabin yadda nake son ki ne duk da cewa na san ban kai matsayin ki so Ni ɗin ba, but I'm hoping za ki tausayawa zuciyata.” ya ƙarasa cikin wata irin murya da ke nuna tsantsar roƙo.

A ɗan kunyace tace “Please Husband to be...stop begging me to love you, matsayinka ya wuce hakan, Ni ɗin wace ce da zan ƙi ƙaunarka bayan duk qualities da ake so ka tara?, ka daina tunanin ba na son ka Please, ka manta yadda Cutie ke ƙaunar Yayanta?” ta idasa tare da ɗan ɗago idanuwanta ta dube shi. Ba tare da ta sani ba suka haɗa ido sai dai ba ta janye nata ba a wannan lokacin saboda tana so ya rage damuwarsa na cewa ba ta son shi. Ba tare da ya janye idanunsa ba yace “Are You sure Cutie?”

Kai ta gyaɗa masa cike da tabbatarwa “Yea, 100% sure.” wani irin murmushi ya sake tare da faɗin “Ba ki tarbe Ni ba yau Rouhy, amma iya ƙaunar da kika nuna min kaɗai ta faranta raina, how i wish i have something i can present to you as a gift?” murmusawa tayi ba tare da ta ce da shi komai ba. “Yauwah! Akwai gift ɗin duk da na san ban biya kwatankwacin farin cikin da kika da Ni yau ba amma an ce yaba kyauta tukuici, so gobe Please ki yi wa Mamah magana, we'll be going out together”
A ɗan rikice tace “What?”
Ya bata amsa da “Yes! Ko ba ki son fita da Ni ne?, ban kai ba ko?” ba shiri tace “Ina!” tana mai jan ƙarshen “Ai har ka fi, remember you're my to be husband ”

Gira ya ɗan dage mata just to confirm what she's just said, ita kuma ta jijjiga kanta alamar tabbatarwa. Murmusawa yayi yana faɗin “Alright, Allah ya kai mu. ina ga zan wuce.” ɗagowa tayi ta kalleshi, tunawa da ya ce mata akwai good news da zai faɗa mata in yazo yasa tace “But before..” sai kuma taja numfashi “You've talk about good news? Za kuma ka tafi baka yi casting na ba”
Dariya yayi yana faɗin “Ai na yi tunanin ba ki damu da sani ba, anyways albishirin ki!”


“Goro” ta amsa tana ɗan gyara tsayuwarta coz zuwa yanzu ta ɗan gajiya da tsayuwar. “Fari ko ja?” jin yana kawo abun yara yasa ta ɗan murmusa tace “Fari tas kamar dai Ni ɗin nan?” harararta yayi irin ta wasa ɗin nan yana faɗin “Irin fararen ainihin nan, wani ma ya sani ko na shago ne?”
Haɗe fuska tayi tana furta “Allah ya tsare, natural one ne, Ni kar ka sa na manta, faɗa min.”
“Uhm a nawa zan faɗa miki? Kin san Tinubu ya hana aiki ba biya?” yamutsa fuska tayi tana faɗin “Kyauta mana Husband to be.” jin Husband to be maɗau yasa yace “Ki buɗe kunnuwanki”
“Uhm ina jin ka”
“In sha Allah gobe da Daddy na ya dawo je will be coming ya nema min aurenki ”

Gabanta ne ya bada sautin dam! Amma sai ta ɗan kau da kai tare da yada murmushi akan kyakkyawar fuskarta sai kuma ta turo bakinta gaba. “Yaya fa I'm too young ” ta ƙarasa a shagwaɓe. Sosai ta tafi da imaninsa lokacin da ta faɗi hakan, murmusawa yayi yana faɗin “I'm sorry Rouhy,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login