Showing 153001 words to 156000 words out of 157517 words

Chapter 52 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5139

can, ba zan taɓa bari ku yi galaba a kai na ba, Ni ɗin sabon jini ce, kuma fansar kakana da kakata kamar na ɗauketa!"

Hakan bai sa Kawu Sadi yi musu naimsiha yana nuna musu cewa Alhaji Baba ba shi da laifi game da hakan, yana nusar da su illar tsafi da shan jini, amma aka ce wanda yayi nisa ba ya jin ƙira. Dalilin da yasa kuma yake musu nasihar saboda su tuba ne su rabauta da rayuwarsu don a wannan lokacin babu wani tsafi a jikinsu, shi kansa Dodon tsafin nasu ya riga ya ƙone tunda asirinsu ya tonu.

"Shikenan tunda ba za ku tuba ku nemi yafiyar wadanda kuka cutar ba, kun sani a yanzu ba ku da kowa ga shi kuma kun hura wuta A BABBAN GIDA irin wannan, yanzu masu gidan sun yunƙuro, matuƙar ba ku tuba kun nemi tafiyarsu ba zan bar komai a hannunsu su ɗau hukuncin da suke ganin ya yi musu. Ya kuka gani?"

Rumana ta kwashe da dariya tace "An faɗa muku mu sakarkaru ne, a cutar da iyayen mu kuma a ce mu nemi yafiyar wani a cikin gidan? Ina rantsuwa da Dodon...".
"Dakata, nan ba sansani matsafa bane da za ki mana shirka a nan!"
Itama a tsawace tace "Kai ba ka kai matsayin da za ka hana Ni yin Abunda na so ba, Ni ce magajiyar uwar gijiya dole nayi yadda na so, da me kake taƙama ne wai?"
"Da Allah"
"To ya hana mu yin Abunda muka so"

Cike da takaici kowa ke kallonsu yana jijjiga kai, lallai wanda ya ɓata ya ɓata sai dai Allah ya yi da rabon shiryuwarsa. Sheikh Imam ne yayi murmushi yace "Za ku iya yin Abunda kuke so, amma ku sani a halin yanzu ba ku da wani iko tattare da ku sai yadda Mazluman da kuka cutar suka yi da ku." Kamar da wasa suka gwada amfani da tsafinsu don ɓacewa daga wurin amma ina, duk yadda suka yi abu ya ci tura. Maimakon ganin hakan yasa su fahimci cewa Allah ɗaya yake amma saboda taurin kai irin na shaiɗani suka ƙi, sai ma suka fara ƙoƙarin neman abun da za su cutar da wani da shi, ba su yi aune ba suka fara ganin jami'an NIC sun fara shigowa, babu ɓata lokaci kuwa aka wuce da su.

Nan Sheikh Imam ya dawo kan iyalan da suka shiga matsananciyar damuwa musamman Papa da Abba waɗanda ke zubar da hawaye, ashe duk zaman da ake yi na ƙarƙashinsu ne masu haɗa husuma a gidan? Da ƙyae suka yi shiru sannan Sheikh Imam yayi musu nasiha Kawu Sadi ma yayi tasa. Daga nan kuma shelar family meeting ta tashi. A wurin Yaya Sadauki ya nuna musu komai yadda ya faru wanda yayi video gabaɗaya, kuka wiwi ta ko ina yayin da aka fara godewa Allah na bayyana gaskiyar komai, sai tsinewa Mamie da Ammie ake yi ciki har da yaransu. Kafin kace me waɗanda ke gidajen mazajensu mu labari ya kai musu. Sosai suka yi baƙin ciki da wannan rana tare da Allah wadai da iyayen nasu da suka zaɓi gurbatacciyar rayuwar da aka gina su kai.

Lokacin da Yaya Sadauki ya buƙaci yi wa su Sheikh Imam tukuici da ƙyar suka haddasa cewarsu ai duk an zama ɗaya, daga ƙarshe yayi booking ma Kawu Sadi flight zuwa Bauchi sannan ya sa Detective Musa ya masa Alkhairi na ban mamaki ciki har da gina masa sabon gida wanda aka ware masa wurin da zai ke aikin sa na taimakon marasa lafiya, ya siya masa mota tare da ɗaukar masa driver. Shi kuma Sheikh Imam yace lala, shi fa he's satisfied kuma ba ya buƙatar komai.

Godiya wa Allah babu wanda bai yi ba, washegari kuwa aka shigar da ƙarar su Mamie babu ɓata lokaci, kamar yadda ta kasance da iyayensu haka aka yanke musu hukunci nan fa sai hauka tuburan, duk wanda suka kashe suka sha jininsu haka suke razanar da su, haka dai za ka gansu suna ihu suna cire kayan jikinsu a prison ɗin.

*A WEEK AFTER*

Bayan sati da kammala komai aka ɗaura auren Nasreen da Yaya Ishaq, Zahrah ma ta koma gidanta, a daren ranar sun faranta ran junansu, nan yake sanar da ita abinda yace in an gama case ɗin can zai faɗa mata.
"Am all ears my man!"
"Za mu tafi honeymoon, wace ƙasa da wacce kike so?"
Tace "Uhm ina da mafarkin zuwa Abu Dhabi saboda yadda nake ganin finafinan da aka ɗauka a can, ina son ziyartar Canada, daga nan kuma mu wuce Saudiyya muyi ibada sai mu dawo."

Washegari kuwa aka fara culucukun visa na Zahrah tunda shi already yana da shi, bayan kwana biyu komai ya kammala, ranar Litinin jirginsu ya lula zuwa babban birnin Dubai...Abu Dhabi, satinsu guda suka shan love ɗinsu daga nan suka fita a Canada, nan suka haɗu da su Nasreen waɗanda can suka fara sauƙa su, Nan ma satinsu biyu suka wuce Saudiyya don nuna godiyar su ga Allah. A nan suka haɗu da sauran familynsu gabaɗaya babu babba ba yaro.

Sati biyu suka yi a nan ma suka wuce gida Nigeria, ranar da suka koma aka kawo siyayyar Baby da Yaya Sadauki yayi, ita kanta Zahrah ba ta san cewa tana da ciki ba sai da aka kawo kayan. Tambayarsa tayi
"Zaujeey kayan nan kuma daga ina?"
Shafa cikinta yayi tare da rungume ta ta baya ya zaro kansa ta kafaɗarta yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta mai sanya shi nishaɗi sannan yace
"Na unborn ɗin da ke cikinki"
Cike da mamaki tace "Zaujeey Ni kuma? Ta yaya kasan ina da ciki bayan Ni na san ba Ni da shi?"
Murmushi yayi yace "Haba My Nour, kin san dai Ni ne mijinki, ina kula da ke daidai iyawata, rabonki da ki yi menses tun yaushe?"
Ido zare tace "Tab! Wollah har na manta ana yi ma, inaga tun bikin mu ban ƙara ba."

Ƴar dariya yayi yace "This means you're pregnant Nour" yana faɗin haka ya juyo da ita suna fuskantar juna tare da hugging nata tightly, sun daɗe a haka sannan ya sake ta yace "Thank you so much My Nour, ke ce rayuwata kuma numfashi na, kasancewarki a tare da Ni yasa na fara ingantacciyar rayuwa, ke ce bangona, matata kuma sirri na, ina matuƙar ƙaunarki, kin ba Ni farin ciki maras misaltuwa, kin haskaka Rayuwata da ta ahalinmu sannan kin min tukuicin da Allah kadai zai iya biyanki. I love you!" Ya idasa sounding romantic and kissed her passionately, the kiss that make both of them forgot everything, it took them several minutes before they stopped everything, ba tare da ta sake shi ba ta sanya kyawawan idanuwanta cikin nasa, cike da saukin so tace "Ina ƙaunarka my One and only, I called you one and only because you're the only one that lights my life, kai ɗaya ne ka gyara rayuwata bayan rugujewar da tayi, ka so Ni da ranka da zuciyarka, ka kula da Ni kamar jaririya, waye zai iya min hakan in ba kai ba?"
Ba tare da ta jira amsar saba tayi kissing nasa tace "Only you my 1&only, I cherished every moment we share, I'm wishing well be together forever and ever, make death take us together when our time reach, ba zan iya rayuwa babu kai ba My king"

Kallonta yayi yana murmushi tare da ɗaga ta gabaɗaya kamar yarinya ita kuma take ta lafe a jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa da ba ya isarta, kan bed ya dire ta yace "Make Dad check his baby."
Bayan wani lokaci suka nufi toilet tare sannan suka yi wanka, daga nan suka fito, shi da kansa ya shirya Baby Queen ɗin nasa ya kai ta bed ya ajiye sannan ya shirya.

Washegari suka shirya suka kai wa su Mamie Ziyara a prison, cike da raunin zuciya suka dawo musamman yadda suka ga duk sun sauya kamar ba mutane ba, everything about them changed, kamar wasu aljanu haka suka koma ga shi duk sun Rame, ga rashin hankali da tsoratarwar da suke fuskanta daga mutanen ɗakin da kuma rayukan da suka hallaka uwa uba wasu ƙuraje da suka mamaye jikinsu. Dalilin hakan ya buƙaci da a raba musu ɗaki kada su shafawa lafiyayyu cuta. Da haka suka koma a sanyaye.

Sosai Yaya Sadauki ke kula da cikin nan kamar shi ne na fari duk da cewa little ma na samun kulawa daga gare shi amma yadda yake ɗaukin unborn ɗin nan abun har mamaki yake ba wa mutane, Mommah kuwa kullum cikin kuran Zahrah take asking for me take a girka mata, me take kwaɗayi? Babu kunya haka zahrah za ta faɗa, in few minutes Kuma za a aiko mata, Hajjaty , Mamah, duk ba a bar su baya ba, irin wannan kulawar da take samu daga kowanne ɓangare yasa ta tabbatar wa kanta cewa ita ɗin ta musamman ce, tuni ciki ya fara bayyana kansa ga kuma wani kyau da take ƙara yi kamar ka ɗauke ka gudu.

A yau cikin Zahrah ya cika wata takwas Cir, yayinda ya zama ƙatoto har da ƙyar take tafiya, kai da gani za ka san cewa ba ɗa ɗaya ne ciki ba, kowa kuka ya ganta haka yake faɗi, ita dai murmushi kawai take yi tace "ɗaya ne fa". Zaune take bararraje a Parlour ta saka plate ɗin gurasa a gaba tana ci tana shishitun yaji ga kuma watermelon juice tana korawa, shigowar Yaya Sadauki yasa ta fara ƙoƙarin miƙewa ta mishi sannu da dawowa. Da sauri ya ƙaraso ya mayar da ita zaune yace "kada ki wahalar min da kanki da baby, ba sai kin tashi ba" zumɓura baki tayi tace "Ka bi ka damu da Babyn nan, ai dama na ga yadda kake rawar ƙafa kansa na san ka fi son sa, ai Shikenan sai mu je a cire shi!"
Ta faɗa tare da fashewa da kuka, da sauri yayi hugging nata ta yadda ba zai takura mata ba yace "Haba Zaujaty, ai kin san yadda nake son ki ya wuce kwatance, babu kuma wadda nake so yake, ki yi shiru kin ji" haka dai ya samu ya lallaɓa ta don yanzu haka take, abu kaɗan sai ta fassara shi sannan ta fara kuka.

Bayan ta yi shiru yace "Albishir?"
Da sauri tace "Goro!" Yace "Nainarh ta haihu ɗazu" cike da murna tace "Don Allah, mace ko namiji?" Yace "Mace" hugging nasa tightly tayi tana faɗin "Wow! Allah ya raya mana, za ka kai Ni naga babyn yau ko?"
"Yau kuma My Nour?." Sakinsa tayi tana turo baki kamar za ta yi kuka tace "Ni dai yau" sanin halinta na yanzu yasa yace "to, zan kai ki sai yamma amma lokacin sun dawo gida ko?" Da haka dai ya taimaka mata ta miƙe tsaye suka wuce ciki.
Da yamma kuma ya cika mata alƙawarinta, tunda ta shiga su Zakiyya ke mata dariyar wai ta ga yadda ta zama Mama kuwa? Cike da masifa tace "Ai kuma cikin ne da ku, yau ko gobe za ku haihu, don kun raina Ni shine za ku ce na zama Mama, ba mana ba Allah yasa kaka"
"Ah! Lallai wannan cikin ya mayar da ke bala'atu to sannu yi haƙuri matar Yaya Sadauki" lokaci daya ta saki murmushi ta zauna, nan suka fara hirarsu, can Zakiyya ta fara yatsina fuska, Rumaysa ta dube ta tace "lafiya Madam?"
Without minding on them tace "Ina jin contractions ne, Allah dai yasa yau nima na sauƙa, EDD na 2weeks Cir da cikarsa." Sannu suka jera mata suna mata addu'ar Allah ya sauƙeta lafiya.

*React and share Fisabilillah*


[10/05, 12:51 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 7️⃣4️⃣






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*

Abu ƙarami fa ya zama babba, babu shiri Zakiyya ta ƙira Ya Taj ta sanar da shi cewa tana jin Labour ta fara, kafin kace me ya zo, har ciki ya shigo ko bi ta kan su bai yi ba ya taimaka mata suka wuce asibitin tukun ya ƙira Mimie ya sanar da ita cewa suna asibiti tare da Zakiyya.
Cikin awanni bakwai ta haihu itama ɗiya mace.

Lokacin da labari ya Riski Zahrah sosai tayi murna. Da sati ya zagayo aka haɗa walimar sunan rana ɗaya, yaron Zakiyya ya ci sunan Daddy (Omar) za a ke ce masa El-Faruq, ta wajen Nainarh kuma ta ci sunan Mommah, Fatima Sughrah, za a ke ce mata "Zuhrah".
An watse a walima lafiya su Zahrah suka koma gida.


Bayan sati biyu da Suna kallon news ita da Yaya Sadauki yayin da take shan farfesun kayan ciki da Mommah ta aiko mata, tura ma Yaya Sadauki plate ɗin tayi tace ya ƙaro mata, bayan ya tafi ne aka saka Daga prison... karo taci da yadda Rumana ta kashe Mamie, kisan gilla ta hanyar amfani da faratunta, a matuƙar tazane Zahrah ta calla ihu tana ƙwala kiran Yaya Sadauki da ya tafi kitchen ɗebo mata abinci. Da gudu ya zo ya tarar da ita kwance alamar suna tayi. Numbern RM. Nadiya Ya ƙira cikin mintuna kaɗan sai ga ta, ganin suma tayi ga kuma blood na bin jikinta yasa tace masa asibiti za a ce, ko nauyin ta bai ji ba ya kwashe ta zuwa mota suka wuce tare da RM. Nadiya.

Zirga-zirga yake ya kasa zaune ya kasa tsaye, 39 minutes after Dr ya bukaci magana da Yaya Sadauki, yanayin da RM. Nadiya ta gan shi ciki yasa ta bi bayansu zuwa office ɗin, ko zama bai yi ba yace "DR. How is my wife? Tana lafiya? Ya baby na dake jikinta?"
Ajiyar zuciya Dr. Ya sauƙe sannan yace "kwantar da hankalinka Mr. Abatcha, your wife and her baby are in good state of health, Sai dai ina recommending a yi inducing labor ɗin saboda yanzu haka za ta iya haihuwa kowane lokaci."
Numfashi yaya Sadauki ya sauƙe yace ban gane ba "She's in labour" RM Nadiya ta ba shi amsa.
"Yanzu ka koma gida ka ɗebo kayayyakin da ake buƙata"

Few minutes Sai ga shi da trolley ɗauke da kayan baby da na uwarsa. Ko da ya bayar bai iya tafiya ba, a nan ya ƙira Mommah ya sanar da ita. Ba a jima ba suka shigo ita da Hajiya Babba. Ba tare da ya kula da su ba ya ci gaba da zama a reception cikin tagumi yayin da idonsa ke kan Labour room ɗin da take. Ganin dare ya yi yasa yace "Mommah mu je na sauƙe ku dareya yi." Da mamaki kan fuskarta tace "Dare ya yi kake cewa Aliyu?" Sai yanzu ya fahimci ma me yace, kansa ƙasa yace "Mommah, i mean dare ya fara nisa"
"To sai ka kwashe mu ka mayar da mu kaji, matsa ka ba Ni waje"
Babu yadda zai yi ya koma reception ya zauna. Shi ya ma manta da wani abu wani yunwa a rayuwarsa sai da Mommah tace ya koma gida Hajjaty za ta ba shi abu ya kawo. Kafin ya dawo Zahrah ta haifi Baby girl. Bayan an gyara ta ita da Babyn aka fito da baby don su ganta, daidai shigowarsa, da sauri ya ajiye basket ɗin hannunsa ya ƙarasa cikin zafin Nama ya karɓi Babyn da Midwife ɗin ta miƙowa Mommah, ido kawai Mommah ta bi shi da shi tana faɗin Allah ya shirya.

Sosai ya ƙurawa Babyn ido yana kissing nata, "Alhamdulillah!" Muryar Mommah ce ta katse shi "miƙo min ita rasa kunya" ba musu ya miƙa mata "maza ka wuce gida, sai da safe tunda kowa lafiya yake." Babu yadda zai yi haka ya koma gida, sai lokacin ya ɗauki wayarsa, missed calls ne daga ya Faruq rututu, da sauri ya danna ishi kira ba tare da sanin time ba, ganin bai daya ba yasa ya shiga WhatsApp. Saƙonni ne kusan goma kuma dukka videos sai ɗaya daga Yaya Faruq, Voice note ɗin nasa ya kunna. Kuka sosai yaya Faruq yake yana faɗin Yaya Sadauki ya sa baki Abba ya yarda a kawo gawar Mamie a mata salla. Mamie? Me ya sameta, ya tambayi kansa. Ɗaya daga cikin messages ɗin da kai tsaye ya fito daga office nasu ya shiga. Hawaye ya zubar da ya gama kallon video ɗin, al'ajabi da kuma ƙara jaddada ikon Ubangijinmu yayi, duk wanda ya ɗauki duniya da zafi tabbas za ta zo masa kamar wuta, yanzu Shikenan dai Mamie ta mutu, ta mutu kafira, to Allah ya kyauta yasa mu yi kyakkyawan ƙarshe. Jiki babu kwari haka ya kwana, sassafe ya wuce main house ɗinsu. A nan ya tarar ana ta'ajjubin Abunda ya faru da Mamie, ya ji daɗi da yaji an ce a can za a binne ta saboda bai san ta yaya zai tunkari Yaya Faruq ba, Mamie ba Muslima ba ce babu yadda za a yi a mata salla.

Gari na wayewa aka fara kai wa Zahrah ziyara ana ganin Baby, kafin ka ce me kowa status nasa itace in dai yana da alaƙa da familyn, facebook WhatsApp, Instagram da sauran kafafen sada zumunta ta ko ina picture ɗin kyakkyawar yarinyar ne mai kama sak da mahaifinta banbancin su shine ita eyes ɗinta blue ne.

Bayan an binne Mamie haka dai Rumana ta koma kan Ammie, kullum cikin faɗa suke kamar karnuka, a haka dai Ammie ta ci nasara ta kashe Rumana cikin ratar kwanaki uku kacal tsakani da mutuwar Mamie. Itama kuma binne ta aka yi babu sallah, saboda ba su yi imani da Allah ba.

Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya, ranar suna yarinya taci sunan Aunty Mabruka, sai dai Sunan da Little ke kiranta shi ya fara bin bakin mutane "Angel". Sosai aka ci aka sha, aka kashe Naira a wurin event ɗin suna. A couple of month after sunan Angel Rumaysa da Nasreen suka haifi yara mata, ratarsu kwana shida kacal, yarinyar Rumaysa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login