Showing 81001 words to 84000 words out of 157517 words
daren ranar dai ita aka buɗewa dandalin tsokana ga Yaya Auwab da ya dame ta da ƙira ita kuma ta ƙi picking, ganin hakan yasa ya fara sakin messages.
Har ila wannan lokaci kuma Nasreen babu wani wanda ta nuna alamar tana so cikin familyn ko wajensa, sun yi sun yi da ita ta faɗa musu amma koyaushe amsa ɗaya take ba su “Nifah har yanzu Ban ga type na ba a familyn nan, amma akwai wanda na riga nayi falling ma soyayyarsa...sai dai ya riga ya yi min zarra, ba na tunanin ko wata rana zai so Ni tunda akwai wacce yake so,ku dai yi min addu'ar Allah ya zaɓa min mafi alkhairi.”
Sosai take kashe musu jiki da wannan zancen nata, gabaɗaya sai bakinsu ya mutu zukatansu kuma su yi rauni.
*Wannan kenan...react Please my people.*
𝓛𝓸𝓿𝓮 𝔂𝓸𝓾 𝓵𝓸𝓽....
[1/29, 8:19 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 3️⃣7️⃣
﷽
A ɓangaren Aunty Mabruka sosai ta sha jinya watan da ya gabata kamar ta yi yaya, ta tane sosai bayan Dr. Ya zo har gida ya duba ta ya tabbatar da cewa ciki gare ta, kar ku so kuga muna wurin ta, tun mutuwar mijinta take fatan ina ma hakan ta kasance ko za ta samu wanda za ta ke kalla a madadinsa taji daɗi sai ga shi Ubangiji ya azurta ta da ciki. Sosai kuma Mamah ke ba ta kulawa, ranar da Mommah tazo bayan labarin ya isa kunnenta kamar ta saɓa Aunty Mabrukan ta goya a baya har sai da ta sa mata jin kunyarta mai tsanani, sosi tayi mata addu'a da fatan Allah ya raya musu babyn.
Bayan Mommah ta wuce a ranar Hajiya Babba ta tari Alhaji Babba da zancen Mommah, da farko ya ce a'a yana kunyar ɗan'uwansa bai san da yaya zai fahimci batun ba daga baya da ta nusar da shi ya amince ya kuma yi mata alƙawarin in sha Allah in da zama tsakaninsu za ta dawo gidanta, daga haka ta masa godiya sosai.
Alhamdulillah! A yau juma'a Daddy ya sauƙo daga dokin fushi da ya hau ya kuma amince Mommah ta dawo ɗakinta bayan yadda ya sha nasiha daga masoyan ƴan uwanshi, daga haka ya ƙira Hajja a waya yace ta sanar da Mommah yana kan hanyar zuwa. Zo U ga murna Mommah sai da ta taka rawa, ko ba komai ta jigata ai, kafin isowarsa ta sheƙa wankanta ta baza turare.
Da yake Hajja ta san batun komawar Tata yasa ta saka su gaba tayi musu nasiha emphasizing mainly on haƙuri a rayuwar aure da kuma biyayya ga miji, Mommah har ɗan hawayen ta na farin ciki daga haka kuma suka wuce bayan ta yi wa sauran matan gidan sallama.
Da suka isa ma sai da suka biya suka gaida Hajjaty, itama ta ɗaura da nata nasihar, Alhaji Baba yayi, daga nan ta wuce part ɗinta Wanda ga mamakinta ya sha gyara sosai kamar wanda aka sauya shi. Lallai yau Mommah take amarya fa, komai na gidan tsaf kuma sabo yake.
*Midnight, Devil's klans palace*
Sosai yau ma suka gabatar da meeting Wanda har kusan faɗa ya kusa kaurewa tsakani daga ƙarshe dai uwargijiya ta sadaukar da jinin baƙaƙen kuliyoyi guda goma sannan ta sha jinin karnuka biyar, kafin ka farga wani irin hadiri da guguwa sun tashi, walƙiya ta ko'ina....fahimtar cewa ƙarfin ikon ta na ƙaruwa yasa sauran jama'ar ƙungiyar ɓacewa ɓat saboda gudun samun mishkila.
Ita kaɗai ce tsaye cikin wasu halayen kaya ɗinkin doguwar riga wacce kamar wuya kaɗai aka fitar daga jikin yadin, ba a iya ganin fuskarta sakamakon ta juya wa gabas baya ɗauke da ƙwarya a kanta sai kuma wata ƙaramar kuliya baƙa dake hannunta. Tsawon wasu daƙiƙu tana karanta wasu dalasimai daga baya kuma wannan hadiri ya ɓace ɓat kamar bi wanzu ba, haka zalika wannan guguwa ta tsaya cak.
Wani mahaukacin ihu mai kama da dariya uwargijiya ta sake wanda illahirin filin ke amsa ƙuwwarsa. Bayan wani lokaci kuma da wannan ihu tsit kake ji. Ba tare da ta juyo ba tace
“Ya kai dodon tsafi! Gutsirito ma cika mana buri, ina fatan zuwa yanzu ka wadata Ni da isasshen ƙarfin da zan tunkari abubuwan hari na, zan ci gaba da zubar maka da jini kai kuma ka ƙara min ƙarfi.” shiru tayi tare da rintse idanuwanta sannan ta fara motsa bakinta tana jujjuya hannunta sai kuma ta haɗe hannaye biyun wuri ɗaya, wani irin makeken madubi ne ya bayyana kan hannunta, kafin ka ce me shi da kansa ya samarwa kansa matsugni a gabanta.
Shafa madubin tayi tana mai motsa baki, sai ga hoton Aunty Mabruka ya bayyana kan madubin kwance a kan gadonta. Ci gaba da motsa baki uwar gijiya tayi kana tace “Tashi tsinanniyar katangar da ta min shamaki da wasu abubuwan! Tashi!” Kamar wasa sai ga Aunty Mabruka ta miƙe daga kwance tana duba ko'ina na ɗakin da take.
“Lallai ma, na gama kwashe duk wata dukiya ta maceccen mijinki, abinda ya rage na fara lahanta wannan dangi tun daga yau kamar yadda suka yi silar mutuwar kaka na da kuma mahaifiya ta.”
Shafa fuskar Aunty Mabruka ta fara yi tsawon wasu sakanni, kamar ta taɓa wuta lokaci guda ta janye hannunta daga jikin madubin tare da miƙewa tsaye a zabure.
“Me? Ciki? Ciki a jikinta?, a'a Gutsirito ba mu yi haka da kai ba, dole ta mutu ita da ɗan cikinta sai dai ba na so wani cikin ahalin nan yayi mutuwa mai sauƙi irin ta wancan maceccen,na fi so na wahalar da su, na azabtar da su kafin na sadaukar da jininsu gareka Gutsirito.”
Kwance daga cikin madubin Aunty Mabruka ta koma tare da fara juyi kan gado tana mai dafe cikinta.
Shafe madubin ta kuma yi kana Alhaji Babba ya bayyana ƙatoto sai kuma ƴaƴansa ƙanana a jiki har da Mamah wacce ita ma ke kwance sai dai akwai wani haske a tattare da ita.
“Dole na kassara rayuwarku musamman wannan tsohon da ya kasance sila...ku ɗin kuma za ku taya ubanku girbe abun da ya shuka ne...hhhhhh” ta faɗa tana kecewa da wata mahaukaciyar dariya. Kafin wani lokaci ta shafe nasu shafin sai kuma ga jikokin gidan ɗaya bayan ɗaya amma banda ƴaƴanta.
Haka su ma ta sha alwashi a kan su kafin lokaci guda kuma ta saki wani irin ihu mai matuƙar razanarwa, lokaci ɗaya wannan baƙar guguwa ta fara tashi, hadiri ya gangamo ta yadda iya hasken walƙiyar kawai mutum zai iya gani lokaci bayan lokaci. A lokaci guda d haske ya bayyana babu ko alama bare burbushin uwargijiya a wannan wuri.
*Saturday morning*
*Mabruka's POV*
Asubar yau da ƙyar ta iya miƙewa ta yi ta sakamakon matsanancin ciwon kai da ya kama ta tun farkawar ta ta farko da daddare, a daddare tayi sallar asuba kana ta koma ta kwanta. Ko da gari ya waye sai ta ji sha'awar taje wurin Mamah, hakan ya sa ba tare da shawara da kowa ba ta harhaɗa abun da za ta buƙata cikin trolley, cike da ƙarfin hali ta ja duk da kanta na mata matsanancin ciwo kamar an ɗaura mata wani ƙatoton dutse akai.
*Angels' POV*
Bayan sun gaisa da Hajiya Babba ta umarce su da su je su gaida Mommah, cike da farin ciki suka tafi saboda tsantsan farin ciki. A yau gabaɗayansu tarba mai kyau suka samu daga wurin Mommah, haka ta sa su gaba lallai sai sun tsaya sun yi breakfast a nan, da ƙyar Zahrah ta shawo kanta ta yadda bayan ta ce “Ai mun riga mun yi breakfast Mommah, da zarar mun dawo dai nan za mu dira tunda marmarinmu kike sai a yi lunch da mu.”
“To shikenan Allah ya tsare hanya”
Da “Ameen” suka amsa kana suka wuce school abun su.
*Alhaji Baba*
Yau ko sallar asuba bai fita ba duba da cewa ba ya bari ta kuɓuce masa duk da jiki irin na tsufa sai dai yau ko sallar bai yi ba har gari ya waye sakamakon ciwon ƙafa da ya zo masa ba tare da ya kwanta da shi ba, lokacin da Mamah ta shiga duba shi saboda yanzu ta ɗauki ɗawainiyarsa gabaɗaya a cewar ta yanzu juyi yake buƙata. Shigar ta don haɗa masa ruwan zafin wanka ta Ganshi kwance saɓannin yadda ta saba za ta Ganshi sanye da gilashinsa either yana azkar ko karatun Alkur'ani a irin wannan lokaci.
Da saurinta ta ƙarasa kusa da shi ta tsugunna gabansa, ga mamakinta hawaye ne ke tsiyaya daga idanuwansa yasa ta miƙe tsaye babu shiri tare da ja baya, tana shirin fita taji muryarsa ta nufi kunnenta.
“Madina..” ba tare da ta fita ɗin ba ta juyo, sai da ta zo wurin da yake yace “Taimaka ki ɗauko waya ta a can ki ƙira min layin Qasim, in ya ɗaga kice masa ya zo maza maza ina nemansa.”
Umarninsa ta cika bayan ya ɗaga ta isar da saƙon Alhaji Baba sannan ta ajiye wayar a bedside drawer, cike da mamaki da kuma tsoro tace “Alhaji Baba me ya faru kake kuka bayan ban taɓa ganin ka yi ba tun da nake.”
Wani hawayen ya share lokaci guda ya buɗe baki ya fara magana. “Madinatu ban yi sallar subuhi ba har yanzu ga shi idanuwa na biyu amma na ƙasa ɗaga ƙafafu na ga shi har lokaci ya fara ƙurewa, bari Qasim ya zo ya taimaka min na tashi.”
“Alhaji Baba ai da ba ka sa na ƙira shi ba tunda ga Ni, nima zan iya kula da kai ai. Bari na taimaka maka ka miƙe.”
Ba tare da ya Musa mata ba ta fara ƙoƙarin taya shi tashi sai dai kuma hakan ya gagara, sallame Ya Qasim ce ta sa Mamah juyawa, “Yauwah Qasim, samu ka taimakawa Alhaji Baba ya kimtsa yayi sallah”.
Kansa ɗaure yake duban Mamah, a haka ya ƙarasa zuwa wurin da take riƙe da Alhaji Baba, sai da ya taimaka masa ya gyara jikinsa sannan ya masa alwala, daga nan kuma ya dawo da shi shimfiɗarsa da Mamah ta sauya, bayan ya shimfiɗa masa sallaya ya zauna ya gabatar da sallar a zaune sakamakon rashin iya tsayawa.
A lokacin da Aunty Mabruka ta ƙarasa sashen Hajjaty ɗauke da trolleyn ta, ɗakin Mamah kai tsaye ta nufa ta ajiye trolleyn, ganin ba ta ciki yasa ta kwanta kan gadon tana dafe saitin kanta, ta daɗe a kwance tana nazarin wannan ciwon kai, shafa cikinta tayi tana sakin murmushin ƙarfin hali tace “Ubangiji ka raya min wannan ciki, ka sa ya kasance tamkar mahaifinsa ta yadda duniya za ta yi alfahari da shi, ya Allah ka raya shi rayuwa mai inganci ko bayan raina.”
“Amin” Mamah ta amsa mata tana ƙarasawa bakin bed ɗin, shafa kanta tayi tana faɗin “Lafiya Mabruka?”
Fuska yamutse saboda yadda kanta ke sarawa tace “Lafiya Mamah, kai na ke tsanin ciwo tun daren jiya da na farka daga bacci, Mamah anya zan ci gaba da rayu....” bata ƙarasa ba Mamah ta rufe mata baki da faɗin “Kul! Ahir ɗinki, ki daina wannan zance, Bari mu karya sai na raka ki ki ga Doctor saboda yanayin ki dole sai da monitoring.” ba tare da Aunty Mabruka ta ce ƙala ba ta sauƙe ajiyar zuciya.
Bayan Alhaji Baba ya yi sallah, yau breakfast nasa ma Hajjaty da kanta ta kai masa shi ɗaki, bayan ya ci aka taimaka masa ya fito don a tafi asibiti. Wani private hospital da ya kasance na musamman suka wuce, abun ku da abu da kuɗi tuni aka karɓe shi, bayan an ji complain ɗinsa likita ya rubuta masa gwaje-gwajen da za a masa, kai tsaye ma'aikata suka wuce da shi Radiology, daga nan aka ɗauki sample na jininsa, kana aka dawo da shi wurin Dr ɗin.
Within few minutes result ya fito sai dai abun da Dr ya gani ya mugun ɗaure kansa, mutum a ce ba ya iya taka ƙafarsa amma wai wannan result ɗin nasa ne? Da ba don ya yadda da ingancin ayyukan su da ma'aikatan kansu ba babu abinda zai hana ya ƙaryata wannan result. Nan ya musu bayanin ai lafiya ƙalau Alhaji Baba yake, wataƙila gajiya ceta sa ya gagara tafiyar, daga haka Dr ɗin yace su koma gida bayan shawarwarin da Nurse ta bayar kan abubuwan da za su inganta lafiyarsa, daga haka kuma suka dawo gida.
A ɓangaren Aunty Mabruka ita ma dai kusan hakan ne, duk iya binciken ma'aikatan lafiyar wurin gano dalilin ciwon kan abu ya gagara, saboda haka suka mata bayanin cewa lafiyarta da ta yaron da ke cikinta ƙalau, da haka su ma suka koma gida.
Bayan su Zahrah sun dawo daga school suka tarar da batun rashin lafiyar Alhaji Baba da kuma Aunty Mabruka, sai da suka duba jikin kowa tukun suka wuce part ɗin Mommah kamar yadda suka mata alƙawarin zuwa ɗin. A can ranar suka yini, suna shirin wucewa Mommah ta kasa ta tsare lallai sai dai su kwana a nan. Babu yadda za su yi kuwa suka koma don cika umarnin Mommah.
*React and share fisabilillah*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 3️⃣8️⃣
﷽
Haka rayuwar ta ci gaba da wakana tsawon wata uku, a lokacin cikin Aunty Mabruka ya girma sosai sai dai fa ta ƙi lafiya, kullum ciwon kai da ciwon ciki, in an je asibiti kuma lafiya kowanne gwaji da za a yi yake nunawa. Wannan dalilin yasa Hajiya Babba ta sanar da Yaya Haidar batun Aunty Mabruka ɗin, shi kuma yace ta koma wurinsa hala za ta fi ganin ƙwararrun likitoci a can ɗin.
Bayan kammala komai ta keta hazo, sosai take samun kulawa daga Aunty Salmah, sai dai kuma Abun da yanzu yake damunta bai wuce gane-ganen da take yi ba, idan dare yayi kuwa ba ta da sukunin bacci ta ringa ganin dabbobi mabanbanta waɗanda wasun su ma babu su a wannan yanki amma haka za su yi ta razanar da ita.
Su Zahrah ma Alhamdulillah duk sun samu gurbin karatu a jami'ar Nile da ke Abuja, Zahrah ta fara Law, Rumaysa Nursing, Nasreen Medicine, Zakiyya Fashion Designing sai Nainarh dake home management. Da yake ba a hostel za su zauna ba yasa Alhaji Baba saya musu danƙara-danƙaran motoci guda biyu, ba su yi two weeks da fara lectures ba Daddy ya ƙaro biyun, kowa kuma ya mallaki tasa. Yara sun zama big girls, cikakkun ƴan mata masu ji da kansu.
Ko da Yaya Haidar yaji hakan babu shiri suka nufi asibiti da ita amma sakamako ɗaya ko yaushe dai ake samu, abun ya fara ɗaure kan likitocin kansu, wani Dr. Henry ne ya ba da shawarar a mata gwadin ƙwaƙwalwa la'alla babu wani abu kawai mental disorders ne suka sa take abu kamar haka, hallucination can lead to such condition likewise delusion.
Amma bayan gwajin ƙwaƙwalwar babu abun da aka gano sai dai sun ci gaba da ba ta kulawa tunda lafiyar Babyn ma ƙalau, a haka har cikin ya kai watanni bakwai babu wani progress a condition ɗin nata.
Ana cikin wannan yanayi kuma ta fara wasu irin ɗabi'u waɗanda ke ƙara tabbatar da cewa ba lafiya ƙalau ɗin take ba, gabaɗaya Aunty Mabruka ta sauya kamar ba ita ba, duk wannan class ɗin nata yanzu in tana abu kamar yarinya, hakan yasa Aunty Salmah ta ƙara rura wutar kulawar da take ba ta musamman da yanzu haka kawai sai Aunty Mabruka ta nufi kitchen ta ɗauko wuƙa za ta cakawa cikin da ke jikinta, taimakon da Allah yake yi duk lokacin da ta ɗauko sai Aunty Salmah ta kama ta, kusan sau uku kenan tana hakan idan Aunty Salamah ta sa ta gaba da tambayar me yasa take hakan sai tace
“Na gaji da cikin, ba na son da Aunty, wallahi in ba a cire shi ba zan kashe shi nikam”
A lokacin da Aunty Salmah ta tunkari Yaya Haidar da zancen ya shiga matsanancin tashin hankali, hakan yasa ya koma asibitin nan ya sanar da Dr ɗin da ke duba ta matsalar da take fama da ita. A ranar aka kai ta asibiti sai dai ta hana kowa taɓa ta including the health personnels, ta kuma ce lallai lallai a mayar da ita gida ita ba za ta zauna a wannan wajen ba, gadon ma makara ce kuma a tsakiyar kogin jini wurin yake.
Zuwa yanzu Aunty Salmah ta fara hasaso cewa wannan jinya ba ta gida ɓace, tana buƙatar interventions na masana addinin Islama, da haka t yanke shawarar yi wa Yaya Haidar bayani.
“Nimah abun da na lura da shi kenan Sweetheart, ya zama dole a ɗau mataki da wuri kafin ta illata kanta, saboda haka gobe zan ajiye aikin ma gabaɗaya tunda Alhamdulillah can ɗin ma ba zan rasa abun yi ba sai mu koma gida kawai, in ta haihu lafiya sai mu dawo, ya kika ga?”
Understandable wife is a gift from God, murmushi tayi tace “Gaskiya hukuncin nan ya yi daidai Soulmate, fatan mu Ubangiji ya ba ta lafiya, amma she's suffering wallahi, Ni gani nake kamar aikin sihiri ne a jikinta.
*ALHAJI BABA*
Condition ɗinsa is even worse than na Aunty Mabruka, daga ciwon ƙafafu kuma sai na jikin gabaɗaya, hakan ya matuƙar tayar da hankalin iyalinsa, nan aka dhirya masa tafiya India don ganin ƙwararrun likitoci, sosai aka shirya tafiyar da Hajjaty, Yaya Auwab, nan jirgin su ya lula, bayan sun isa kuma a gidan Abie da ke can suka sauƙa, washegari aka wuce da shi don ganin likita.
A ranar da suka wuce India