Showing 60001 words to 63000 words out of 157517 words
shima suna mutunci da shi). Da suka faɗa masa addu'a kawai ya mata yace In sun je su gaida masa ita.
Su Yaya Khalil da Detective Hamad, Prince Bello su suka raka ango, Prince na driving Amarya da ango su kuma su Yaya Khalil suka tsaya suka saya kaji da youghurt. Daga nan kuma suka take motar and thank God suna Isa Suma suka isa.
Ƙememe Yaya Sadauki yace ai ba a isa a raka su ba, daga nan ya isa ya gode haka. Dariya suka yi suna tafa hannu, Yaya Khalil ya dakatar da shi, a kunnensa ya raɗa masa
“Ka bi min ƙanwata a hankali ka ji ko?”
Wani kallo ya cilla masa yana faɗin
“Dallah ku bar min gida, gaurayen banza, In kun ji haushi kuma gobe a ɗaura naku.” daga haka ya shige ciki ya ajiye Ladar da suka bashi.
Dawowa yayi ya rufe ƙofa kafin ya koma. Lokacin da ya shiga bai tarar da ita ba, ƙarar ruwan da yaji yasa ya fahimci cewa tana toilet, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya tafi ɗaya Bedroom ɗin yayi wanka sannan ya saka wasu milk pyjamas masu tsananin taushi. Bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito ya nufi Bedroom ɗin da take, lokacin har ta haye Bed ta ja Blanket.
Sallamar da yayi yasa ta mike tana zare ido. Ba tare da ya kalle ta ba ya zube kan lallausan carpet ɗin dake ɗakin. Ledar ya fara buɗewa tuni ƙamshi ya cika hancinta, yunwar da ta tara a lokacin ta tashi tace ba ta san zama ba. Fara ci yayi bayan ya saka a plate, can taga bai kula ta ba da alamar ba zai ce ta zo ta ci ba kawai sai ta saƙƙo kanta ƙasa ta zauna ita ma ta saka ba tare da ta ce da shi komai ba, ita ta fara tashi ta nufi toilet, bayan ta yi brush ta dawo ta haye Bed sai lokacin Yaya Sadauki ya gama cin nasa. Korawa yayi da youghurt ɗin da ta bari daga nan shima ya mike.
Ƙasa-ƙasa yace
“Ki yi alwala ina zuwa” Sauran kazar ya fice da ita zuwa kitchen kana ya wuce ɗaya Bedroom ɗin da ya mallaka wa kansa. Brush yayi daga nan ya ɗauro alwala. Lokacin da ya koma ita ma alwalar tayi ta saka ƙaroton hijabi, babbar praying mat ta shimfiɗa musu. Yana zuwa suka tada sahu kamar yadda ma'aiki ya koyar don nuna godiyar su ga Allah. Raka'a biyu suka yi sannan ya dafa goshinta ya karanta addu'ar da Manzon Allah ya yi umarnin kowanne ango ya karanta ta ga matarsa a daren su na farko.
Daga nan kuma yayi mata tambayoyi kamar yadda addini ya shar'anta, ta bashi amsoshin yadda ya kamata hakan yasa ya ƙara godewa Allah da kyautar macen da ya bashi, fatansa Allah yasa zamansu ya kasance alkhairi. Daga nan kuma yace ta tashi ta kwanta, sai da ta kwanta daga nan kuma shima ya naɗe praying mat ɗin bayan yayi shafa'i da witr nasa kamar kullum tukun ya nufi Bed ɗin ya kwanta.
(To amarya da ango, safiya mai albarka) nan na ja musu ƙofar da suka manta ba su rufe ba.
*Mommah*
Yau kwanan baƙin ciki tayi musamman idan ta tuna shikenan an daura auren ɗanta da wannan shegiyar yarinyar. Da ƙyar bacci ya ɗauke ta ga shi kuma kuɗaɗen da ke hannunta sun ƙare, kayan abinci da ta siyo ma yanzu saura kaɗan, tunani take da ina za ta samu kuɗi ga shi Daddy har yau bai je biko ba bare ta sa ran zai bar ta ta koma. Daga ƙarshe dai haka bacci ɓarawo ya sace ta.
*Prince Bello*
Ko da suka koma daren nan hana su bacci yayi, ko mutum ya fara bacci sai ya tayar da shi yana faɗin “I'm In love” sai kuma yayi murmushi. Samun sauƙinsu da bacci ɓarawo ya sace shi tukun suka samu suka rintsa.
*Devil Klans*
A daren yau sai da suka gabatar da meeting na musamman don taimakawa uwargijiyarsu ta cimma burinta. Akuyoyi da tauruna goma aka ba ta ta sha jininsu a lokacin saboda ƙarfin ikon ta ya ƙaru, daga ƙarshe dai suka rufe taron kowa ya ɓace ɓat kamar ba a halicci mutane a wurin ba.
*ZAHRAH'S POV*
Lokacin da su Nasreen suka dawo already ta yi bacci, tayar da ita suka yi suna mitar me yasa bata faɗa musu ba ta da lafiya ba. Tunani ta yi can tace musu su yi haƙuri. Dandalin hira suka tayar su ma. Nasreen tace
“Zahrah kika tafi aka sha da rabin ki, ina baki labari Yaya Khalil.....”
Nainarh ce ta katse ta tana rufe mata baki
Zahrah ta harari Nainarh tace
“Dalla Malama meye Hakan? Nasreen ina jin ki”
Bakinta ta janye tana dariya tace
“Wato Zahrah ashe Nainarh tun ba yau ba raina mana hankalin take, ashe ita da Yaya Khalil love suke sha ba mu sani ba”
Zaro ido Zahrah tayi tace
“Lallai Nainarh! Kin shammace mu ashe”
Zakiyya tace
“Wai kina nufin kice min ba ki san Nainarh ba, Ni tun ba yau ba na fara jiyo ƙamshi-ƙamshin hakan, shiyasa koyaushe za ki ga tana rubuta letter K a littattafanta Ashe Yaya Khalil take nufi, O Ni Fadimatu!”
Dariya Zahrah da Nasreen suka yi, Zahrah tace
“Oh Ni Zahrah'u ashe dai su Nainarh an tafasa!”
Harararta Nainarh tayi tana kai mata dukan wasa tace
“To ina ruwan ku da Ni ne, naga kema Zahrahn kina yi?”
“Niiii Zahrah?” rufa min asiri ban kai ba tukunna”
Harararta tayi a karo na biyu sannan ta kalli su Rumaysa.
“Wai ku har yanzu ba ku san Zahrah ma tana yi ba?”
Cike da zumuɗi Rumaysa tace
“Ba mu mu sha”
Dariya Nainarh tayi sannan tace
“Ban tabbatar ba, I'm joking Amma na San cewa dukkanku akwai waɗanda ke burge ku cikin familyn nan, In za ku fito ku fito kawai, don ni dai da na gama secondary school Zan auri Yaya Khalil ɗina”
Dukan wasa suka kai mata
Zakiyya tace
“Uhmm Ni fa ba zan yi auren gida ba, duk da cewa Yaya Taj na mugun burge Ni amma ba na jin zan iya aurensa ko da ace ya furta kalmar so gare ni”
Kama baki Nasreen tayi tace “Baki dai falling ma soyayyarsa ba, tuni kuka ba da kai, ku dai duk ina ganin ku, kowa zan ga ina zai je”
“Lallai Zakiyya ɗan'uwan nawa ne kika cewa ba za ki aura ba?” Rumaysa ta faɗa
“Ni kuwa kinga Ya Auwab yana matuƙar burge Ni wallahi, da zai ce yana so na da gudu zan yadda, mu yi auren mu da mun yi candy”
Baki buɗe Nasreen ke kallon su tace
“Allah ya shirya min ku ƙanne na, amma kun ba Ni kunya, Ni dai har Yanzu ban fara tunanin wani aure ba, la'alla sai zuwa nan gaba. Ke kuma Zahrah yauwah”
Gyara zama suka yi don jin me Nasreen ɗin za ta ce
“Wannan guy ɗin da yayi miki liƙi daga ina rai?”
Rau-rau da ido Zahrah tayi tace
“Wanne kenan?”
Dariya dukkansu suka yi, Rumaysa tace
“Ƴar rainin sense wannan abokin Yaya Sadauki ɗan Sarkin Adamawa.”
Zaro idonta tayi tace “Na shiga uku, rufa min asiri Rumaysa wallahi ban san wani ɗan sarki ba, ku yadda da Ni ƙarya take.” ta faɗa tana bin kowannensu da kallo.
“Is ok, na yadda da Zahrah, Please to sleep don ni na gaji”
Da haka aka rufe zancen kowa ya kwanta.
Washegari around eleven pm sai ga ango da abokansa sun fito gaisuwa, Prince Bello dai ƙyalla ido yake yaga ta ina tauraruwar tasa za ta ɓullo. Part ɗin Hajjaty suka fara zuwa, lokacin da suka shigo kuma Zahrah ta biyo Zakiyya da gudu kan ta ba ta lip balm ai ta riga ta yin wanka. Ba su yi tsammani ba kawai suka ji muryar Yaya Khalil yana faɗin
“Hey girls”
A zabure suka juyo duka su biyun daidai lokacin da Prince yayi tozali da abar begensa.
Cike da kunya suka gaishe su, da sauri Zakiyya ta koma bayan ta faki idonsu, Zahrah na shirin wucewa taji Yaya Sadauki ya ce
“Zahrah Please ki sanar da Hajjaty zuwan nu”
Kai ta gyaɗa tare da wucewa Bedroom ɗin Hajjaty.
Shi kuwa Prince sai maimaita sunan yake a ransa. Murmushi yayi yace
“She must be Zahrah, kyanta, komai nata daban yake da na sauran, i love you”
Tunanin sa ya katse ne da fitowar Hajjaty Zahrah na biye da ita. Kitchen ta nufa ta kawo musu drinks da snacks daga nan ta koma Bedroom nata tana cika tana batsewa wai Rumaysa ta jawo musu Yaya Sadauki ya gan su suna gudu.
Dariya suka yi don ba su ga abun ɓata ran ba, Nainarh ta ajiye wata killer smile kan fuskarta tace “Saura kaɗan”
A tare suka ce “A yi me?” waskewa tayi tace “Nithing ooo, kun san dai this week za a Fara registration na jamb ko?”
“E eh haka fa, wallahi har na manta”
Zahrah tace “Nima dai na manta, ya kamata mu ci serious mu fara karatu don mu samu na tafiya jami'a, au ashe ku kunce daga nan shikenan, to Allah ya kiyaye”
Kallon banza suka bi ta da shi. Nainarh tace “Sai aka ce miki kuma mun gama, ai za mu yi a gidan mazajen mu ko?”
“Allah???” ta ba ta amsa tana sakin dariya daga haka ta janyo school bag nata ta fara fidda littattafai, duk mai son cin serious sai ya min magana don na sa shi a layi, su ooo kuma zan ce Yaya ya siyo muku littafin soyayya ya yi?” ta idasa tana ɗage musu gira.
Shigowar Aunty Na'eema yasa Zahrah tasowa da sauri ta ɗauki babu Aryan sai washe mata baki yake. Da harara Aunty Na'eema ta bi Nainarh
“Shi ne kika bar Ni Ni ɗaya a can ko?”
Dariya Nainarh tayi tace
“Naga Yaya Junaid yana nan”
*React and share please*
[1/16, 5:19 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣8️⃣
﷽
Tun da suka fito yake damun Yaya Sadauki akan Zahrah amma ko ƙala bai ce masa ba, kamar maye haka yake ta masa magana.
“Allah AU Abatcha I'm in love with her, and aurenta zan yi, don Allah ka haɗa Ni da ita”
Banza ya ƙara masa amma an ce akan abun da kake so ba ka fushi. Da ya gaji sai ya dawo gun Yaya Khalil,
“Aboki ko ina da wani hali ne da yasa ba za ku bani ita ba, wallahi i do love her with all my heart!”
“Ai ga ka ga ta, babu wanda yayi maka Shamaki da ita”
Amsar da Yaya Khalil ya bayar yasa Yaya Sadauki juyowa ya aika masa da wani irin kallo.
Bayan sun gama da Estate ɗin suka nufi gidan Mommy Nasiba da gida Hajja, sosai Hajja tayi farin ciki da ganin jikan nata sai zuba masa addu'a take yi. Kamar daga sama Mommah ta jiyo muryarsa, su da sauri ta fito don tabbatarwa. Ganin shi ne da gaske cikin manyan kaya da suka mugun yi masa kyau ga wani fresh da yayi yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Ƙarasowa tayi suka gaida ta cike da girmamawa sai ta tsinci kanta da kasa yi masa magana kamar yadda ta kudurta da ta gan shi. Jan ta ƙasa ta juya za ta koma Yaya Khalil yace
“Mommah” ba tare da ta juyo ba tsaya, ko da ya isa sai ya ce “Don Allah Mommah magana nake so mu yi” kasa yi masa musu tayi sai ta nuna masa ɗakinta, gaba tayi ya bi bayanta.
Bayan sun shiga ya sunkuyar da kansa ƙasa sannan ya tsugunna gabanta yace
“Mommah don Allah ki yi haƙuri ki dawo, sai jiya naji ashe kin baro gida, ki yi wa Allah da Manzonsa ki taimaka ki dawo ko dan saboda su Ra'ees, yaron har ya rame saboda rashin ki, don Allah Mommah ki dawo” ta yi niyyar ta hau shi da Masifa ne amma sai ta kasa, hawaye na zubo mata tace
“Ai ba Ni na taho da kai na ba, Daddynsu ne ya ce na dawo, la'alla an gama zaman tunda har yau bai zo ba, In na Kira shi ba ya ɗagawa.”
Kamar zai yi kuka shima yace
“Ki yi haƙuri Mommah, In Sha Allah zan yi wa Alhaji Baba magana za ki dawo, za mu wuce ga wannan.” ya ajiye mata bunch na 1k da ba ta san bawa bane sannan ya wuce. Kuɗin ta ɗaga tana hawaye tace
“Shi ma ya bar Ni, sai abokinsa ne ma ya damu da Ni!”
*Couple of weeks later*
Sosai Yaya Sadauki da Aunty Mabruka suke zaune lafiya, tana ba shi girmansa yadda ya kamata shima kuma yana ganin kimarta, sosai duk su biyun suka yi fresh kamar ba su ba. A safiyar yau yake so ya gana da mutumin da yace ya san yadda Mama take, itama kuma yau take son komawa bakin aikinta, da wuri suka shirya, bayan sun yi breakfast ta fito ɗauke da briefcase nasa a hannunta cikin shigar ta ta lauyoyi. Ganin har ya shiga Mota yasa tayi sauri ta ajiye briefcase ɗin nasa a back seat ta koma ta ɗauko laptop Bata da basket ɗin da ta haɗa masa abinci ko zai ji yunwa tunda yace ba lallai ya dawo da wuri ba. Entrance door ɗin ta rufe sannan ta shiga motar, bayan gateman ya buɗe suka wuce.
Ita ya fara sauƙewa kafin ya tafi ta tuna masa da briefcase nasa da abincin a back seat tukun ta fice tana waving Masa hand. Ko da ta shiga ciki ta haɗu da su Barrister Raudha da Ma'eesha sosai aka buɗe banin hira daga ƙarshe suka buge da zolayarta ko har an samu rabo, murmushi kawai tayi tace “Tukunna dai”
Raudha tace “Allah wannan freshness ya Yi yawa, gaskiya ba ke ɗaya ba.” shashantar da zancen tayi ta mai da hankalinta kan aikin da ke gabanta.
*Zahrah*
Sosai suka mayar da hankalinsu kan karatu, Islamiyya already sun yi sauƙarsu, Zahrah har an ɗauke ta koyarwa a can, kullum Yaya ya kan shigo, idan ta fita ya shigo zai bar sakon zuwansa a hannun Hajjaty. Hidimar da yake mata bai daina ba har yanzu, In ya ga abu zai siya huɗu yace a basu. Ba don ta daina son shi ba haka ta danne zuciyarta ta hakura da shi, ta kuma yi alkawarin ko da wasa ba za ta ƙara barin so ya yaudare ta ba, In fact ba ma za tai sake ba, babu ruwan ta da kowa, karatun ta shine a gabanta.
*Yaya Sadauki*
Duk da cewa yana kewar Mommahnsa amma ya yi alkawarin ma Daddy cewa ba zai je gurin ta ba, hak Hajja ma ta sa shi ya ɗau alƙawarin nan. Ko da ya isa kan abinda ya kai shi ya sauƙa. Ko five minutes da zuwansa ba'a yi ba sai ga mutumin ya zo, bayan izinin shiga da ya samu ya shiga ya zauna. Ganin babban mutum ne yasa Yaya Sadauki gaida shi cike da girmamawa. Bayan ya amsa yace
“Baba kai ne aka ce ka san yadda wannan baiwar Allahn take?”
Murmushi tsohon yayi yace
“Ƙwarai kuwa, Madina dai mai masa a kasuwa da naje garin iyaye na can Toro kwana biyu da suka wuce na ganta, har muka gaisa, na tambaye ta yarinyar ta da suke zuwa kasuwar tare tace ai tana tare da iyayenta.”
Ajiyar zuciya Yaya Sadauki ya sauƙe yana faɗin
“To Baba yanzu ma za mu biya maka kuɗin jirgi ka koma, za ku je can ɗin da Detective Musa Wanda yake riƙe da case ɗin, ina dai ka san takamaimai inda take?”
“Ƙwarai kuwa” ya ba shi amsa “Ai da jikokin Cikin umma ta na gan su.”
“Ma sha Allah” Yaya Sadauki ya furta yana murmusawa, zuciyarsa ne tayi wasai kamar an wanke ta. Daɗi ne ya kama shi yasa yace wa baban “Baba ka jira Ni a wannan ɗakin farkon, zan samar maka da jirgin da za ka wuce ko?”
“To to yaro babu damuwa”
Daga haka ya fice. Flight ɗin da zai tashi yau zuwa Bauchi Allah ya so sai 3pm, nan yayi booking Masa sai da ya tabbatar ya gama settling tukun ya fito. A wurin da ya faɗa masa ya same shi. Nan yace ya zo su tafi, restaurant ya Kai shi, bayan ya ci abinci ya tsaya bank ya cire kudi tukun ya nufi Airport da shi. Kuɗin ya damƙa masa Baba Manu yace ai da ya bar shi, da ƙyar ya karɓa saboda rashin nuna jin daɗin da Yaya Sadauki yayi. Bayan ya karɓa ya masa sallama, sannan yace da zarar sun sauƙa ya kira Detective Musa. Da haka suka rabu.
Kai tsaye gaida Hajjaty ya wuce saboda yau bai shiga mata ba. Bayan sun gaisa ya koma gida. Sai around 12:30pm ya ƙira Aunty Mabruka yace mata in ta gama ta kira shi saboda ya riga ya koma gida. A lokacin tace masa ai ta gama da aikin yau, saboda su Raudha sun taimaka mata ta yi clearing na baya. Bayan sun dawo ta ɗaura musu lunch, tana gamawa ta sheƙa wankanta sai baza kamshi take.
Bayan sun ci abincin take tambayarsa yaushe zai kai ta ta gaida Mommah?
Fuska ya haɗe yace “Ba yanzu ba”
A ɗan shagwaɓe tace “Haba Yaya na, In Kai ka yi alƙawarin rashin zuwa ai Ni sai ka bar Ni, ba ka tsoron fushin Allah?, Mahaifiya ba abar wasa bace, na ji in ka kaini sai ka tsaya a waje ko ka tafi, In ma ba za ka mayar da Ni ba zan shiga taxi.” da irin kalaman nan ta lallame shi har ya yarda yace zai barta taje sai weekend.
*Yaya Ishaq*
A halin yanzu ya fara dangana da Zahrah, ya ɗauki soyayyarta a matsayin jarrabawa daga Ubangijinsa, hakan yasa yace da Mom ɗin sa su koma can Abuja babu amfanin zamansu a Bauchin, sosai tayi farin ciki ganin ya fara dawowa daidai, cikin ranta kuma tana masa addu'ar idan Zahrah rabonsa ce Allah ya bashi, idan kuma babu aure tsakaninsu Allah ya haɗa shi da mace ta gari. Nan ta taimaka masa ya haɗa trolleynsa don ita dama a Bauchin nan kamar kan ƙaya take haka take jin kanta.
Da Yamma Yaye Sadauki ya fita don yin siyayya kamar yadda ya saba a kowanne azumi yakan siya kayayyakin abinci