Showing 57001 words to 60000 words out of 157517 words
guda kenan da kawo ki nan ana ta fama kan matsalar sai yau ɗin Allah ya kawo ƙarshen ta, Alhandulillah”
Shiru yayi jin Madina na kuka Inna Kuma sai lallashin ta take kan ta godewa Allah ba kuka ya kamata tayi ba. Sai da kukan y tsagaita Malam ya ci gaba da magana.
“Haƙiƙanin gaskiya na ji daɗi sosai, ba kuka za ki yi ba Madina, godiya za ki yi wa Ubangiji da ya sa kina da sauran rayuwa a matsayin mai hankali. Domin kuwa da ace ba a nema miki magani ba babu shakka a haka za ki dauwama, sai dai buwayar Allah gagara misali ce.”
“Abokiyar zamanki ita ta aikata miki hakan, shine aka haɗa ki da wani shaiɗani wanda ya juyar da tunanin ki ya mayar da ke maras amfani. Amma tunda kin dawo dai-dai ina roƙon wata alfarma a gare ki, ko da kin koma can gidanki ki bar ta da halinta kada ki ce za ki ɗau mataki.”
Cikin Muryar kuka da al'ajabi Mama tace “Ai ko ba ka nemi alfarmar nan ba Mallam ba zan yi magana ba, Nima Zan koma ne ga ahali na saboda......”
Nan ta kwashe tas tarihin rayuwarta ta sanar da su. Inna kam har da kukanta tana share hanci sai Allah wadai take da Kawu da Baba Amarya. Nan Mallam ya ɗaura da nasiha wa Mamah kan guduwa da tayi ta bar ahalinta ba tare da ta ƙara waiwayarsu ba. Inna ma tayi Tata kafin a tsayar da sai Mamah ta murmure tukun su je a mayar da ita, don Inna cewa tayi tare da ita za su tafi in lokacin yayi. Daga haka suka koma cikin gida.
*Don Allah a yi sharing, kuma a yi reacting*
*I love you people*
[1/16, 5:16 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣6️⃣
﷽
*Friday*
*ABATCHA ESTATE MOSQUE*
A yau juma'a, dubban mutane suka shaida auren ALIYU UMAR ABATCHA da kuma amaryarsa MABRUKA ABUBAKAR ABATCHA akan sadaki dubu 500 Alhaji Babba shi ne ya biya kuɗin a matsayinsa na waliyyin ango yayin da Papa ya amsa matsayinsa na waliyyin amarya. Allah ya ba da zaman lafiya.
Fuskar kowanne ɗaya daga cikin alhalin ɗauke da hasken farin ciki musamman Alhaji Baba da kuma ƴaƴansa. Ta can gefe ango ne zaune kansa ƙasa coz ya ma kasa tashi saboda yadda jikinsa yayi mugun sanyi. Prince Bello ne da Yaya Khalil suka yo kansa fuskarsu sake. Ganin kamar bai san da zuwansu ba yasa Yaya Khalil ya ɗan zungure shi, a ɗan rikice ya ɗago, ganin yadda suka ɗan tsoratar da shi yasa ya banka musu harara.
“Ango ka sha ƙamshi” Prince ya faɗa yana miƙa masa hannu. A zahiri ba za ka taɓa fahimtar wane yanayi Yaya Sadauki yake ciki ba kasancewar fuskarsa ba ta bayyana hakan ba, but deep down wani irin tsoro ne ya shige shi lokaci ɗaya daidai lokacin da auren ya gama ɗauruwa. Murmushin da ya yafa a fuskarsa yasa Yaya Khalil jin sanyi cikin ransa.
“Ya! Man, mu je waje, friends namu na waje sai neman ka suke” babu yadda ya iya ya miƙe, a tare suka taho suna ta yi masa shaƙiyyanci shi bai ma san suna yi ba coz hankalinsa ba ya wurin. Sosai aka shiga gaisawa suna masa fatan alheri da addu'ar zaman lafiya tukun aka fara wucewa for reception da za a yi a makeken hall na estate ɗin.
*Amarya*
Gabanta ne ke tsananta Bugu tun da gari ya fara wayewa, haka ta fara safiyar ta jikinta sukuku babu wani ƙarfi. Zaune suke ita da friends ɗin ta Raudha da ma'eesha sai kuma Aunty Na'eema da ta kasa ta tsare amaryar tana counseling nata musamman da ta sanar da ita komai, ta tausaya mata ƙwarai kuma ta ƙuduri kafin su koma Egygt za ta taimaka mata har su daidaita da mijinta. Ita ta shirya amaryar cikin wani expensive lace da ya Sha ɗinki, kana doso ɗakin ƙamshin amarya zai tabbatar maka da wanzuwarta. Sosai tayi kyau abun ta sai dai kuma deep down her heart is beating faster, tsoro da fargaba sun cike zuciyarta.
Aunty Na'eema da kuma su Ma'eesha suka sa ta gaba da surutu hakan yasa ta ware.
Sallamar mahaifinta da ta jiyo tare da wasu mazan yasa gabanta bugawa, wannan fargaba ta zama jiki na kowacce amarya.
Humaira ce ta shigo fuska ɗaure tace “Aunty Mabruka su Alhaji na jiran ki a parlour”
“Ban gane ba” ta tambaya
Kamar ba za ta amsa mata ba amma tunawa da mai faruwa ta faru yasa ta ce
“Ki fita ki ji mana” daga haka ta wuce nata Bedroom ɗin ta saki kukan baƙin cikin rasa nagartaccen miji irin Yaya Sadauki.
Hijabi ta saka tana mai barin iya idanuwanta waje har ta isa parlourn. Tsugunnawa tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Alhaji Uthman ne ya fara buɗe zaman da addu'a sannan ya ɗaura da nasiha ga amaryar tuni kukan da take haɗiyewa ya kufce mata, sosai yayi mata nasiha daga ƙarshe ya damƙa mata sadakinta a hannunta.
Alhaji Baba ya ɗaura da faɗin
“Ki yi shiru haka nan, duk wani abu da ya kamata a faɗa Papanku ya faɗa, a matsayi na na mahaifin ki kuma babu abun da zance illa iyaka ki kasance mace mai haƙuri a gidan aurenki tunda dama ibada ce ta kai ki, kul naji ko na gani kin yi rashin ɗa'a ga mijinki, ki bi shi sau da ƙafa shi ne kaɗai abun da zan roƙa a wurin ki. Kin gane?”
Kai ta gyaɗa ta ci gaba da kukanta.
Bayan su Alhaji Babba sun fita Aunty Na'eema tazo ta ɗaga ta suka shiga ciki, wanka ta sa ta gaba tayi bayan ruwan ƙamshin da ta haɗa mata a toilet. Bayan ta fito ma wasu turaruka ta ƙara bata ta shafe jikinta da su sannan ta ɗaura wani mai mai Masifar kamshi. Atamfa ta fitar mata ta saka su Raudha sai yaba kyau suke suna santi, ita dai amarya zuciyarta ce ke wani irin bugu kamar zata fasa ƙirjinta ta fito. Bayan ta saka aka ɗaura mata alkyabba a kai sai ta fito kamar wata gimbiya, kai tsaye ɗakin Hajiya Babba suka nufa, nan iyaye mata ma suka mata nasiha, Hajiya Babba dai addu'a kawai take mata cikin ranta kan Allah ya basu zaman lafiya. Daga nan suka wuce Part ɗin Hajjaty bisa umarnin Alhaji Baba, daga nan kuma za a wuce da ita ɗakin mijinta.
A can Part ɗin Hajjaty ma ta sha nasiha sosai, Aunty Madina dai da ido ta bi ƙanwar Tata ƙasan ranta tana mata addu'ar Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta su yi rayuwa mai inganci, daga nan kuma Papa ya sa ta a Mota bai tsaya da ita ko'ina ba sai gidan mijinta wanda Daddynsa ya masa kyautarsa. Ma sha Allah, nan ya kara jan kunnenta kafin ya fito. Yana tafiya sai ga su Aunty Na'eema, Raudha, Ma'eesha, Aunty Madina sun iso.
Aure dai ya riga ya ɗauru, masu farin ciki suna yi, ƴan baƙin ciki ma ana nan ana ƙulla ya za a yi a warware aure, sai dai ta Allah ba tasu ba, abunda Ubangiji ya tsara babu mai iya ja da shi.
*ZAHRAH*
Sosai wannan biki ya mata daɗi ko ba komai ta ƙara sanin wasu ahalinta kuma alaƙa mai kyau ta ƙullu tsakaninsu, Musamman Aunty Madina, tun da aka ce mai sunan Mama ce ta ji tana ƙaunarta ita da yaronta Aamir, Yaya Haidar ma sosai ya nuna kulawarsa gareta har yake cewa in sun gama WAEC& NECO za ta zo musu hutu don tuni sabo ya shiga tsakanin ta da su, Aunty Salma matarsa ma Babu kaifi tana da kirki ga kyakkyawar babynsu mai shekaru huɗu Nihal, yarinyar ba dai shiga rai ba shiyasa Zahrah ta tattare su ita da Aamir da baby Aryan. Tun su Nasreen na mita har suka gaji. Sosai yaran suka ɗebe mata kewa.
*Mommah*
Duk da cewa she can say now she's stable Amma ta rasa yaya za ta yi ta dakatar da auren nan, ganin dai ba riba za ta ci ba tunda an ɗaura yasa ta ajiye makaman yaƙin ta gefe tunda dama can zuga ce ta rufe mata ido har zuciyarta ta makance ta yanke wa kanta wannan mummunan hukunci, yanzu ya za ta yi? Tana buƙatar gidan mijinta a yanzu amma ba ta da kwarin gwiwar tunkararsa.
Ya Junaid ma da yaje Hajja ta feɗe masa komai, sosai yaji zafin hali irin na mahaifiyarsa tasa, nan Hajja ta ja kunnensa kan kada ya kuskura yace zai kashe mata kuɗi, ya bar ta sai ta yi hankali. Bai so hakan ba amma babu yadda ya iya sai ya nema mata waya ƴar keypad yace kafin a gama bikin zai san yadda zai yi da ita.
Da yamma kawai sai ga Ammie da Mamie sun kai mata ziyara, a maimakon da ta gano kuskurenta ta yanke alakar ta sa su sai ma ƙara ɗinkewa da suka yi, yanayin da suka ganta yasa suka fahimci akwai saura fa, hakan yasa suka koma bayan zigin da suka mata amma kafin su fita Hajja sai da ta tare su ta buga musu warning na su fita daga rayuwar ƴarta. Abun ku da ƴan duniya sai Ammie tace
“Ki raba mu da ita tunda ke kika haɗa mu da ita, ka ji tsohuwa da iya shege” daga haka suka cika bujensu da iska.
*9:00pm*
Yaran Zahrah da Zakiyya suka kai wurin Hajjaty saboda su samu su shirya, da ƙyar Ya Aufa yace zai kai su da sharaɗin suka wuce time ɗin da ya sa ba zai kai su ba, nan suka wuce suka fara shiri a gaggauce.
Waɗanda ke gidan amarya tuni aka fara haramar tafiya Dinner, kowa sai kece ado yake kamar ba shi ba. Takanas make-up artist ɗin tazo ta sheƙawa amarya kwalliya, idan ba sanin cewa Aunty Mabruka ba ce ba lallai ka iya gane ta ba, ta yi kyau sosai abunta kamar ka jefa a aljihu ka gudu da ita.
Horn ɗin da suka ji ya tabbatar musu da cewa ango ne ya zo ɗaukar amaryarsa. Yaya Khalil ne ya rako shi har parlourn kana ya maka sallama, hakan yasa su Raudha fitowa suka ba su waje, shi kaɗai ya shiga ciki, “Tabarakallahu Rabbul khalikin” ya samu iya gurtawa can ƙasan maƙoshi yana yaba yadda tayi kyau. Tsinin idanuwansa da ke yawo kanta yasa ta ƙara sunkuyar da kanta, hakan yasa ya ɗan kauda fuska ya nufe ta tare da mika mata hannunsa
“Amarya, Are we good to go?”
Ba ta amsa masa ba sai ta miƙa masa nata hannun a kan nasa. Gaban su ne ya buga a tare.
Ganin za su ɓata musu lokaci yasa Yaya Khalil yin gyaran murya, da sauri ya ɗago ta tsaye har suna iya jin numfashin junansu.
“Mu je” ya faɗa a hankali. Suna fitowa su Raudha suka rangaɗa guɗa, murmushin da iyakacin sa kan fuska ta saki har suka bar parlourn, nan masu hoto suka fara kashe musu aiki. Net ɗin da aka makala mata a ka ta take ta ƙasa sai tayi tagal-tagal kamar za ta faɗi, caraf ya riƙe ta sai ta ɗan kwanto jikinsa. Habaaaa ai pictures da videos ɗin da aka yi ba a magana a lokacin.
“Ki kula da hanya” kai ta gyaɗa masa, nan suka wuce, shi ya buɗe mata motar ta fara shiga sannan ya rufe mata, ya zagayo ya shiga ɗaya side ɗin. Nan Prince Bello ya ja motar zuwa event center ɗin.
Lokacin da motarsu ta tsaya shi ya fara fitowa ya buɗe mata, bayan ta fito ya riƙe hannunta suka shige hall ɗin, daidai isowar su Zahrah da squad ɗin ta. Ma sha Allah, the growing ƴanmata kenan! Sun sha kyau abun su duk da cewa ba kwalliyar da suka yi, ɗinkin ya amshi jikinsu kamar dai an gwada su aka yi.
Tare da Ya Aufa suka shige yana gaba suna bayansa. Cikin mintuna uku aka fara shagali.
Nan aka ƙira amarya da ango stage, kamar dai kowanne masoya haka suka fito suka ɗan taka, zo ku ga yadda ake watsa kuɗi kamar na tsugunna na kwashe amma babu dama, bayan sun koma aka ba wa ƙawayen amarya dama da su fito su ma, Raudha, Ma'eesha sai Aunty Na'eema suka fito, sosai su ma aka watsa musu kuɗi, me zan ga, daf da za su koma Yaya Junaid ma yazo ya gwangwaje amaryarsa da dollars, Ni ko nace har yanzu dama ana watsa dollars?.
Dangin miji aka fara kira, shiru kowa yaƙi fita sai ga su Jidda, Hibba an fito, kafin kace me sai ga su Zahrah an fito fili. Aka sa musu sauti su gwangwaje ai kuwa nan aka san an zo Dinner, bayin Allah rawa suke kamar an aiko su, nan fa hankalin jama'a ya dawo kan su, ashe tun fitowarsu Prince Bello ya ƙyalla idonsa kan Zahrah, hohoho abun da ake kira da love at first sight shi ya faru, yadda take rawa ana mata liƙi yasa yaji wani iri, da sauri ya fita, within a minute Sai ga shi ya dawo, dollars ya shiga liƙawa Zahrah wacce bata ma san yana yi ba.
Babu zato babu tsammani taji an ja hannunta da ƙarfi, ɗagowar da za ta yi idon ta ya sauƙa akan Yaya Sadauki. Gwalo idanuwa tayi ta ma kasa magana saboda yadda taga fuskarsa a ɗaure. Bai tsaya ko ina da ita ba sai da suka bar hall ɗin, a jikin wata bishiya ya tsaya yana aika mata wani mugun kallo, kanta ƙasa taji yace
“Are You out of your senses Lily? Za ki shiga fili kina rawa ana miki liƙi saboda ba ki da kunya?”
Mamakinsa ne ya kama ta, ko ina ruwan sa da rawar ta?
Murya shagwaɓe tace
“Haba Yaya, bikin ka fa ake yi kuma sai kar nayi farin ciki? Naga...”
“Shut up!” ya dakatar da ita
“Don ana biki na baki ga maza ne cike a hall ɗin ba?”
Caraf Zahrah tace “To ai ƴan uwana ne”
A hasale ya ja hannunta jin furucin da tayi, ransa ɓace ya danna ta cikin motarsa da aka kawo su cikin. Tuƙi yake kamar mahaukaci har ya kai Estate ɗin su, a bakin Part ɗin Hajjaty yayi parking sannan ya daidaita kansa tare da juyowa ya kalle ta. Hawaye ne sharkab a idanuwanta, duk takaicin sa ya cika ta. Ko ina ruwan sa da ita da zai katse mata da nishaɗinta? Ta tambayi kanta. Ganin hawayen nata ba karamin karyar masa da zuciya yayi ba amma sai ya dake yace
“Na duka ki ne kike min kuka?”
Sanin halin kayanta yasa ta ce “A'a”
“Oyah wipe your tears or else...” ya faɗa yana miƙa mata handkerchief nasa, lumshe idanuwanta tayi a lokacin da ta ɗaura shi kan fuskarta. The scent is actually unique.
“Lily?” ta ɗago ta kalle shi.
“Why kike son ɓata min Rai? Eh?”
Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta tace
“To ni me nayi yaya?”
“Me kika yi ma kike tambaya? U don't even know abi?”
Turo baki tayi without saying anything.
*React and share fisabilillah*
*Masu taya Ni sharing Ubangiji ya biya ku da gidan Aljannarsa.*
[1/16, 5:17 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣7️⃣
﷽
“Kul kike shiga irin wannan, kin shiga fili kamar ke kika fi kowa iya rawa? Wallahi In aka ƙara biki naga kin dage kina rawa irin wannan sai na saɓa miki” ya faɗa in a terrible voice “kin ji ni ko?”
“E” ta bashi amsa
“Oya! Out of my car” da sauri kuwa ta buɗe ta fice tare da banko ƙofar ta falfala a guje. Murmushi yayi yace
“She'll never change, my headache” sai kuma yaja motar da mugun gudu ya koma hall ɗin, Thank God lokacin ne ake shirin fara ciye-ciye. Kau da kansa gefe yayi daga kallon da ƴan mata ke bin sa da shi ya koma mazauninsa. A hankali ya ɗan ranƙwafo daidai kunnenta yace
“I'm sorry amarya, na fita saboda wani muhimmin uzuri” murmushi kawai Aunty Mabruka tayi, zuwa yanzu zuciyarta tayi sanyi, yadda yake nuna kulawarsa gare ta ya ƙara masa ƙima a idanuwanta. She never dream of such life with Yaya Sadauki.
*Flash back*
Lokacin da ya fizgo hannun Zahrah daga stage yayi waje ashe Detective Hamad na kallonsa, sannan Yaya Khalil da ke liƙawa Nainarh kuɗi shi ma ya gan shi, wanda aka yi wa buƙulun shima akan idonsa hakan ta faru, yayi mamaki sosai ganin Abokinsa ne. Cikin ransa yake tambayar
“Ko me yasa yayi hakan?”
Dawowa yayi ya zauna ba tare da ya cewa sauran komai ba. Ƙwaƙwalwarsa ce ta tariyo masa in bai manta ba wannan ita ce yarinyar da ta kawo musu abinci ashe ba ita ce amaryar ba. Hamdala yayi wa Ubangiji da ya nuna masa wannan fuska, je really loves her, “they called it love at first sight” ya faɗa yana murmushi.
Fuska ta ɗaure yana tambayar kansa meye tsakanin ta da Abokinsa da zai zame ta daga stage ita kaɗai bayan ga wasu sisters ɗin nasa? “There is a question mark here” ya faɗa can ƙasan maƙoshi.
“I love her!” he repeated it uncountably.
Bayan an tashi daga Dinner hankalinsu Nasreen ya tashi ganin sun rasa Zahrah bayan kuma tare da ita suka hau stage. Kai tsaye wurin Yaya Khalil suka je suka sanar da shi. Murmushi kawai yayi don shima zuwa yanzu ya fara fahimtar cewa abokinsa is in love with that creature unknowingly.
“Ka Yi shiru Ya Khalil!” Nainarh ta maimaita
“Kada ku damu ku samu ku koma gida, tun ɗazu aka mayar ta gida bata jin daɗi”
Ba tare da sun yadda da abinda ya faɗa musu ba suka wuce Yaya Aufa ya mayar da su shima kan hanya yana tambayar su ina Parrot (Sunan da ya bata coz sosai