Showing 78001 words to 81000 words out of 157517 words

Chapter 27 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5165

nan suka saka Nainarh gaba da tsokala wai har kishinta ake yi? Duk bakinta yau kam shiru ta musu coz ba za su gane yadda ake ji ba since ba su fa'da kogin ba.

Basu 'bata lokaci ba driver ya mi'ka su wurin 'Dan Amana, ai kuwa ya ci sunansa, nan ya mi'ko musu 'dinkunansu da already ya gama kamar yadda ya fa'da daga nan kuma suka dawo gida.

Tun yammacin ranar aka fara aikin sallah, shiga kawai ake da kaji ana gyara su ta kowanne 'bangare na gidan, aiki kuwa babu 'ya'ya babu ma'aikata haka aka fara, bayan an sha ruwa kuma aka 'daura, ba su suka kwanta ba sai 12:43 na dare. Ba tare da sun gaji da baccin ba Hajiya Babba ta tayar dasu, kamar za su yi hauka haka suka mi'ke, suna yi salla suka 'daura kan aikin da ba a kammala ba, zuwa wayewar gari tuni sun gama komai an yi preserving a manya manyar flasks tukun Hajiya Babba ta sa suka shirya.

Sallah babbar rana, misalin 7:46am na safiya ta ko'ina ka juya cikin estate 'din Yara ne cikin shiga ta alfarma kowa sai murna yake, a yau kusan kowacce mota da ke gidan an wanke ta tas don tafiya Masallaci.

Sai da su Zahrah suka yi breakfast sannan suka fito jere gwanin ban sha'awa cikin wasu expensive Atamfofi kowacce da kalar tata amma sun yi ankon Hijab babba har yana share 'kasa, takalmasu ma mabanbanta ne. Suka sake dukkansu suka fara aikin 'yan mata na snapping pictures har Yaya Khalil ya fito tunda dama tare da shi suza su fita, ba tare da 'bata masa lokaci ba suka nufi motarsa wacce ke zuba uban she'ki suka shige, yana 'karasawa shima ya shige ciki,bayan sun gaisa shiru kake ji banda tasbih 'din da ya kunna kowa kuma na bibiya cikin zuciyarsa.

Sai da suka fara biyawa ta orphanage tukun, lokacin yaran an shirya su tsaf,manyan su ma sun shirya gwanin ban sha'awa tamkar ba su rasa wani sashe na jininsu ba cikin shigar alfarma. Suna ganin motarsa suka yo wurin da gudu suna fa'din "Daddy! New Daddy! New Daddy!" Fuskarsa sake ya bu'de motar ya isa garesu, gaba'dayansu suka masa 'kawanya ba tare da kula da mutanen da suka fito daga motar ba wa'danda ransu yake cike fal da mamaki.

Pictures aka yi snapping nasu kowa fuskarsa sake daga nan aka saka yaran a motoci don tafiya masallaci, a nan yace da su Zahrah su kula da matan, kada su bari wani ya bar wurin, da to suka amsa bayan isar su masallacin suka shimfi'da 'katuwar praying mat suka zaunar da yaran wa'danda tuni sun fara sabawa da su. Bayan an idar ma motocinsu da ke pake wuri guda suka nufa, direct sai orphanage.

Ko da suka isa bayan kowa ya fito aka fara 'dauke-'dauken pictures ba tare da sun farga ba har wuraren 11:54am, daga nan Yaya Khalil yace da su ya kamata su ci abinci tukun. Nan suka nufi dining room 'din orphanage wanda ya kasance mai fa'di da tsawo mai 'dauke dogon table mai tsayi sosai. Bayn Yaya Kkalil ya zauna yaran suka fara zama, maza layi guda matan ma layinsu guda, sauran spaces da ba mutane nan su Zahrah suka zaune ba 'bata lokaci aka yi serving nasu.

Cike da farin ciki suka kammala cin abincin kana aka koma common room aka zauna. Tamkar mahaifinsu haka suka zaune ana 'yan labarai har yamma tayi, hakan yasa yace zai wuce kowa ya shirya gobe za su je zaga gari ne kawai. Cike da farin ciki yaran suka musu addu'ar Allah ya kiyaye, daga nan suka koma gida.
A gajiye suka koma, bayan isha duk suka mi'ke sai bacci saboda gobe za su rubuta jamb 'dinsu in Allah ya kai.

*WASHEGARI*

Da wurwuri suka shirya lokacin wasu ko tashi basu yi ba, sai da suka biya wurin Hajiya Babba, Mimie, Ummin Rumaysa, kana suka je wurin Hajjaty da Mamah suka bi su da addu'ar Allah ya ba da sa'a, daga nan driver ya ja su kowacce aka kaita centre din da za ta yi.

Da misalin 12:00pm. Duk sun fito, 'daya bayan 'daya Baba Driver ya 'dauko su ya mayar da su gida. Suna isa suka yi wanka suka ci abinci daga nan Nainarh ta fa'da musu sa'kon Yaya Khalil na in suna son komawa Orphanage in ta ga sa'kon ta 'kira shi zai aiko a 'dauke su. Cike da zumu'di suka ce eh ta 'kira shi. Babu jimawa kuwa sai ga shi an zo 'daukar su, yau kam ba Hijab suka saka ba sosai suka yi kyau kamar ba gobe, dukkansu Abaya suka saka different colours amma from expensive brands sannan suka yi rollong veils nasu, handbang ne a hannun kowaccewacce ta shiga da kayan jikinta. In ka gansu kai ka ce daga sama aka jefo su Nigeria, they look so beautiful.

A can orphange suka tarar da Yaran har an fita da su, bisa umarnin Yaya Khalil aka kai su Park 'din da aka kai yaran, karashen yinin dai a yawace yawace suka yi, Zahrah kam in banda 'daura status babu abunda ke ha'da ta da wayarta, basu suka dawo ba sai bayan maghrib, ko ta kan abinci ba su bi ba ana sallar isha duk suka baje sai bacci.
Hajiya Babba sai fa'da take wai Yaya Khalil 'karfi da yaji na son koya wa yaran yawo... ji fa? Kamar ba su suka ce za su ba.

*Masu bi na ta private suna cewa Yaya Sadauki bai dace a ce ya mutu ba ya kamata kusan cewa in mutuwa tazo ba a dakatar da ita, duk wanda kuka ga ya mutu time 'dinsa ne Yayi, masu cewa kuma Yaya Ishaq bai cancanci ya auri Zahrah ba muje zuwa, ni kaina ban san konzai aure ta ba ko a'a, a dai gani na ko ya aure ta ai babu laifi shima ya ba wa rayuwarta gudunmawa. Allah yasa mu dace.*
*Devil klans fa sun farfa'do...nan ba da jimawa ba zan warwarw muku komai da ya tsaya muku a rai, ku dai ku ci gaba da reacting da kuma sharing.*

[1/29, 7:52 AM] Diamond Bhatool:











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*











*


*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 3️⃣6️⃣




Washegari around 11:00am sau ga Yaya Ishaq da Mom 'dinsa sun tunkaro estate 'din Abatcha, lallai babu shakka Zahrah yanzu kam tana cikin gata, tun daga matsu tsaron katafaren gate 'din ya tabbatar da haka, fuskar nan tasa sake take kamar ance an ba shi auren Zahrah ne ma, Ita kanta Mom 'dinsa ta 'kara jinjina al'amarin ubangiji musamman da ta tuna gidan da su Zahrah suka rayu a can Bauchi, rayuwar 'kuncin da suka yi har suka bar Bauchi da zama, lallai al'amarin ubangiji na da fa'di da yalwa, 'kudirarsa kuwa ba ta 'karewa.

Ba su sha wahala ba tunda kowannen gida cikin estate 'din na da signboard a jiki, ganin _Family root_ yasa ya tabbatar nan ne 'bangaren da Mamah take, driver ya umarta da ya daidaita parking a nan, bisa umarninsa kuma hakan ta faru. Tun kafin motar ta tsaya Ya Ishaq ke shirin bu'dewo Mom da ri'ke hannunsa tana aika masa wani kallo.
"Meye hakan kuma?"
fuska shagwa'be yace "Mooooom"
harararsa tayi tace "Rawar kan ta isa haka mana, ka jira dai motar ta tsaya kafin ka fita, shashasha in ba ka sa na hana su baka ita ba" kamar zai yi kuka yace "I'm Sorry Mom" sai kuma ya gyara zama kamar wani 'karamin yaro yana kwa'be fuska. Da haka Mom ta cilla masa wani kallo tace "Oya mu je ciki, saura kayi rashin kunyar da ka saba, za kaga me zan maka"
"Ba zan ma yi ba" ya ba ta amsa yana bu'de motar ya fito.

Tarba mai kyau suka samu daga Hajjaty saboda sanin za su zo da kuma alkhairin da Ya Ishaq 'din yayi a rayuwar 'yarta. Nan suka zauna ana hira kamar an da'de da sanin juna musamman yadda Hajjaty ta saki jiki da Mom 'din, ita dai Mamah maganarta jefi-jefi ce. Ganin babu amfanin zamansa yasa ya mi'ke. Mama ta dakatar da shi da tambaya "Ina za ka Ishaq?"
Yana 'dan sosa kai yace "La Mamah zan je na jira ta a mota ne"
Hajjaty ta ri'ke bakitana kallonsa kana tace "A yi haka kuma Ishaqa?, bari dai Zahrah'u ta fito ka samu abokan hira, Zahra'u! Nainarh!"
Kunya ce ta kama shi ganin yadda Hajjaty ta ramfo shi, dakewa yayi yana Allah Allah ta fito.

Nainarh da Zahrah ne suka fito daga bedroom 'din Zahrah suna musun wai yau result 'din Jamb zai fito su Nasreen na fa'din 'karya ne, sandarewa suka yi ganinsa tsaye kamar wani gunki, harara Zahrah ta cilla masa tare da 'karasawa tunda sun siga sun fito. Gaida ba'kuwar suka yi ba tare da sanin wacece ba. Zahrah na bu'de baki za ta ce ga ni Hajjaty ta tari numfashinta.
"Ga yaron nan Ishaqa ku kai shi 'daya parlourn sai ku 'dan taya shi hira don na ga alamar ya saba da ke 'din, kira su Nasreen ku je tare" ba don Zahrah ta so ba tace "To Hajjaty"

Daga haka suka wuce can 'din kamar yadda Hajjatyn ta fa'da. Ko da su Rumaysa suka zo su ma suka baje ana hira da su amma Hajiyar tamu ta dake kamar ba ita ba. Haka har wuraren Azahar Yaya Khalil yazo suka fita da Yaya Ishaq zuwa masallaci.

*MOMMAH*

Har ila yau dai Mommah na can gidansu, kullum cikin naci take Daddy ya mayar da ita shi kuwa ya yi kunnen uwar shegu da ita, ta buga duk yadda tayi tunanin za ta yi nasara amma hakan ta fasaya har ta ha'kura da batun ta zubawa sarautar Allah ido. A yanzu dai akwai kyakkyawar Ala'ka tsakaninta da Hajiya Babba,ba kamar da ba.

*ZAHRAH'S POV*

Bayan fitar Yaya Ishaq sai wani cika take tana batsewa kamar ba ita ba ila ala dole ba ta son wargi, gaba'daya haushin Yaya Ishaq ya cika ta, duk tsawon shekarun nan bai neme ta ba yanzu kuma sai wani rawar kai yake.
Sai da Yaya Ishaq ya dawo tukun suka yi lunch, Nainarh hajiyar online ce ta daka tsalle ba tare da ta gama cin abincin ba.
"Wallahi Jamb ta fito, sisters ku tashi mu je mu duba namu"
Fa'da Hajjaty ta fara mata
"Shashasha kawai sai ki tashi kina ihu duk kin tsinkarwa mutane zuciya?"
kwa'be fuska tayi za ta yi magana Mom tace "Ai hajiya haka yaran suke sai ha'kuri, abu ne kuma na jarrabawa irin wacce kowa yake tsumayi, Nainarh ko? Ku je ku duba, Allah sa ku ga mai kyau."
"Amin, thank you understandable Mom"
Dariya gaba'dayansu suka yi banda Hajjaty da ta galla mata harara.

Da sauri dukkansu suka wuce bedroom 'din Zahrah cike da fargaba. Nasreen ce ta fara bu'dewa ta calla wani ihu tare da fa'duwa 'kasa tana sujjada.
Bayan ta 'dago ta dube su tace "Na samu yadda nake bu'kata wallahi, 199 ku yi ku dubo naku"
"Wayyo Allah nima na samu 205" Nainarh ta fa'da tana sujjada ita ma.
Zakiyya, Rumaysa they all get their requirement saura Zahrah wacce hannunta ke karkarwa ta ma rasa ta ina za ta fara. "Saura Zahrah" Nasreen ta faɗa tana mayar da kallon ta ga Zahrahr. "banjaaaa, ba Ni na buɗe miki nan" Ba tare da jin amsar Zahrah ba ta amshe phone ɗin nata tare da shiga.

Ido waje Nasreen ke kallon Zahrah tace
"Guess what Madam!" Dafe da ƙirji Zahrah tace "Just tell me, na ci ko a'a?”
Kai Nasreen ɗin ta fara juyawa kafin kace me tsoro ya mamaye zuciyarta.
“Please Nasreen ki faɗa min kafin heart ɗina ta daina beating.” jin kalaman Zahrah na ƙarshe yasa Nasreen ta kwashe da dariya tace “Madam congratulations....308 kika ci!”
“What?” Zahrah ta tambaya
Nasreen ta ba ta amsa da “Eh fah, 308 kika samu our champion” ta idasa tana miƙa mata wayar ta duba da kanta. Bayan ta tabbatar da hakan ta miƙawa sauran nan suka yi hugging juna suna taya junansu murna.

Sai da suka gama murnar su a ciki suka koma parlourn and everyone is impressed about their performance nan aka fara taya su murna sai kuma tafiya jami'a, lokacin da Ya Ishaq ya shigo tare da Yaya Khalil suka nuna musu, sosai suka yi farin ciki amma can ƙasan zukatansu fa.....

Sai bayan sallar la'asar su Mom suka wuce bayan Hajjaty ta haɗa ta da tsarabar da ba a rasa ba, har bakin apartment ɗin suka musu rakiya suna faɗin sai sun zo kana suka wuce abun su.

*A gurguje*

Sannu-sannu babu wuya, haka rayuwa ta ci gaba da wakana, yau daɗi gobe akasin haka, yau farin ciki gobe kishiyarsa. Cikin watanni biyu su Zahrah suka fara rubuta jarrabawarsu ta WAEC, a cikin waɗannan watanni Ya Ishaq ya yi ƙoƙarin gina soyayyarsa a zuciyar Cutiensa and Alhamdulillah an ɗan samu sauyi tun lokacin da ya bayyana mata saƙon zuciyarsa, she can't reject it and she promised to remain committed, tsakanin Yaya Khalil da Nainarh kuwa zuwa yanzu manya ma sun fara fahimtar hakan, fatan su Allah yasa hasahensu ya kasance alkhairi.

Zakiyya wacce ita ma yanzu sun ɗinke ita da Yaya Taj Wanda a halin yanzu ya zama cikakken likita yana kuma aiki da National hospital ne da ke Abuja. Sosai suke shan love ɗinsu ba tare da kowa ya farga ba, in suka manne a waya kamar kar su rabu amma idan physically ne Zakiyya ba ta iyawa saboda irin kunyar da take da shi wacce ke ƙara rura wutar son ta a zuciyarsa.

Su Hajiya Rumaysa manya, tuntuni ta fara fahimtar take-taken Yaya Auwab tattare da ita sai dai duk irin yadda yake burge ta sam ba ta jin za ta iya ba shi dama matsawar ba zai tona asirin zuciyarsa ba. Ko irin taɗin nan ake yi idan sun shigo da wuya ku ji bakinta, hakan kuma baya masa daɗi, bayan shawarar da yayi da su Ya Faruq ne suka tisa shi gaba kan ya sanar da ita kafin wani ya riga shi, don samun kamarta ba lallai ba, in ya bari ta kamu da son wani ko wani ya riga shi ya yi da-na-sani.

Hakan yasa ba shiri ranar da ya shiga part ɗin Hajjaty da gangan saboda ya ja ta su ɗan keɓe ya furta mata saƙon so yasa ya bata ajiyar wasu files da ya taho da su daga court. Ba tare da wani tunani ba ta karɓa. Sai da ya shigo around 8:00pm yayi dialling numbern ta, bayan ta yi picking yace “Please Rumaysa...” sai kuma yayi shiru. Jin hakan yasa ta ɗan ja tsaki ƙasa-ƙasa, ta gaji da wannan shan ƙamshi da Yaya Auwab ke mata, a hankali tace “Eh ina jinka”
Cikin kame-kame ya fara magana “Eh eh am dama wannan files ɗin da na baki za ki taimaka ki miƙo min ina bakin part ɗin Hajjaty zan miƙawa Barr. Ne kuma ina sauri” ba ta kawo komai a ranta ba tace “Ok, I'll be there within few minutes.”

Kamar mai zuwa hira ta gyara fuska har da shafa lip gloss kana ta fesa turare, nan fa su Zahrah suka saka ta gaba, share su tayi ta nufi ƙofa tana faɗin
“Kwa yi ku gama, Ni ba Ni da time ɗin ku” daga haka tayi waje ta bar su suna ta sababi.

Ko da ta fita maimakon ta gan shi a mota tunda ya ce fita zai yi sai ta gan shi tsaye, shaye da mamaki ta ƙarasa garesa tana mai sallama, amsa mata yayi yana ɗan shafa sumarsa da ta sha gyara.
“Kin fito kenan...Barka”
Wani banbaraƙwai taji amma ta dake tare da amsawa “Barka” sannan da miƙa masa files ɗin, yana amsa ta juya don komawa taji ya dakatar da ita da faɗin “Where Are You going again? Magana da na zo mu yi” ya idasa in a weak voice.

Fasa tafiyar tayi ta juyo kana tace “Ok Ya Auwab ina jin ka, ina sauri ne muna karatu kar su wuce ni” jin hakan yasa ya gyara tsayuwa tare da gyara zaman hularsa, ya ma rasa ta ina zai fara coz wannan shine first time da ya fara tsayawa da mace da sunan zance. Jin y yi shiru yasa tace “Bari na shige, gobe in ka tuna sai mu yi maganar”.
“A'a ba a yi haka ba ai Rumy, na san me zance” Kai ta langwaɓar alamar ta gaji da jiransa.

“Eh to dama dai dalilin son magana da ke bai wuce in sanar da ke wasu muhimman abubuwa ba, na farko dai na yaba da halayenki da kuma ɗabi'un ki, sannan batu na gaskiya Rumy wallahi zuciyata ta riga ta kamu da ƙaunarki tun wani lokaci da ya shuɗe, ƙaunar da nake miki kuma ba wai a baki ba, in so samu ne ina da burin na mallake ki a matsayin uwar ƴaƴa na.”
Ba ta ce komai ba sai ta tsinci kanta da jin kunya duk da cewa abun da take jia kenan daga gareshi.

“Kin yi shiru Queen”
“To me kake so nace?” ta tambaya a shagwaɓe wanda hakan ya kusa ya narkar da shi a wurin bai san lokacin da ya ƙara kwantar da murya ba yace “Say You love me too, I'll be happy with this answer ” a ɗan shagwaɓe tace “I'll think about it Yaya, thank you...sai da safe”
Daga haka ta juya da sauri ta koma ciki shi kuma ta bar shi tsaye yana Binta da kallo har ta shige kana ya koma part ɗin su, dama abun da ya kawo shi kenan.

Tana shiga ta faɗa cinyar Zahrah tana famar rufe fuska, baki sake duk suka fara bin ta da kallo.
“Lafiya Rumaysa?” Nainarh ta tambaya.
Sai data gama nuƙu-nuƙunta tukuna ta ba su labarin yadda suka yi da Yaya Auwab, dariya suka yi gabaɗayanu suna faɗin “Wa ya ga? Wai ana so ana kai wa kasuwa”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login