Showing 93001 words to 96000 words out of 157517 words

Chapter 32 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5160

kafin lokacin sai ki girma ai, in kuma ba ki son auren da Ni ne lemme know!”
Zaro idanuwa wace tayi tace “Nii?” tare da dafa chest ɗinta. “Yes, you!” ya faɗa yana jijjiga kansa.

A matuƙar shagwaɓe tace “Ni dai ban ce haka ba Yaya Ishaq, kuma ai ba ma hakan bane.” kamar zai yi dariya ya make don baya son wargi ya shiga zancen kana yace “Kin tabbata?”
Kai ta gyaɗa masa tana kallon ƙasa.
“Is alright, na yarda da ke Aminaty...saura in an tambaye ki kice ba haka ba ke Yaya kike so?”
Dim! Gabanta ya buga, “Yaya? Which Yaya?” ta tambayi kanta. Jin shirin ta yasa ya ɗago don ya ganta, ganin kamar tunani take yasa yace “uhm Queen, tunanin me kike yi ne?”
Cikin inda-inda tace “Nothing oo, gobe Are You coming?”
“Yes! But..”
“What?” ta tambaya.
“Ban gaji da kallon ki ba.”

A hankali ta furta “To in zauna sai ka gama kallon nawa mana.”
“Me ma kika ce?”
“I Don't say anything, idan mun yi auren ai sai ka gaji da kallo na.”
Da sauri yace “What? WHO tell you so? Ai ba zan taɓa gajiyawa da kallon ki ba Cutie, in zan shekara ina kallon ki ba zan taɓa gajiyawa ba ko da na daƙiƙa ɗaya ne.”
“Uhm?” tace don tabbatarwa.
“For sure, kinga ki koma ciki kar Hajjaty ta tambaye ki ina kika je.” sai a lokacin ta tuna ta yaya ta fito, nan ta fara ciccila ido kamar maras gaskiya.

“What's wrong?” ya tambaya ganin yadda ta sauya, rau-rau da ido tayi tana faɗin “Ka san ta yaya na fito kuwa?, to cewa nayi zan amso saƙo and.” ta dakata tana duba agogon dake ɗaure a wrist nata “Kusan 35minutes ban koma ba, shikenan!”
“Calm down.” ya faɗa yana kallonta, cikin kwantar da hankali yace “Sai ki ce kin karɓo kina dawowa kika gan ni, sai kika tsaya muka gaisa, does this work?”
“I don't think so” yace “Hakan za ki faɗa, it's the only solution, ki wuce ciki, see you tomorrow, bye” waving hand nasa yayi tare da kallonta har ta wuce ba tare da ta ce uffan ba. Murmushi ya saki ganin ta shige ciki, kana ya juya tare da nufar motarsa dake fake.

Lokacin da ta shiga Allah ya taimake ta babu kowa a parlourn sai Nasreen wacce har lokacin take riƙe da Little Sadauki, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da nufar wurin Nasreen ɗin, a hankali ta furta “Allah ya taimake ni.”
Jiyowa Nasreen ɗin tayi ta kalleta sai kuma ta maida kanta ga kallon Little Sadauki ba tare da ta ce komai ba.
Jin ta yi shiru kuma yasa Zahrah sakin ajiyar zuciya ta nufi bedroom nata har lokacin Nasreen na zaune.

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*








*💎💍ELITE DIAMOND*
*WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_




*Of*👇👇👇







_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 4️⃣3️⃣




Sai da ta tabbatar Zahrah ta shige kana ta miƙe tare da nufar bedroom nata, lokacin da ta shiga Zahrah har ta sauya zuwa kayan bacci tana shirin kunna system nata da ke gabanta don yin assignment. Ba tare da ta kalleta ba ta ajiye Little a wurin da ta tabbatar ba zai fadi ba kana ta juya don ta wuce part ɗinsu. Ta kai bakin ƙofa Zahrah tace
“Sister” ba tare da ta juyo ba ta tsaya tana jiran me Zahrah za ta ce mata.
Ganin ta ƙi ko da juyowa yasa Zahrah miƙewa ta nufe ta.

Bayan ta isa ta dafa kafaɗarta tana shirin juyo da ita ta fuskance ta Nasreen ta dake tare da cijewa. Jiki sanyaye Zahrah tace “Sister, what's wrong? Kin juya min baya ko na miki wani abun ne?” banza tayi da ita hakan kuma sai ya ba wa Zahrah mamaki musamman da ta tuna hakan bai taɓa faruwa tsakaninsu ba. A matuƙar sanyaye ta koma ta gabanta amma still Nasreen turns her head to side, a sanyaye Zahrah tace “Haba sister na, fushi kike da Ni? Na miki laifi ko? I'm sorry”

Still dai Nasreen remains quite kamar babu wata halitta mai kama da ita a wurin. Hakan ya ƙara ba wa Zahrah mamaki, ba tare da gajiyawa ba tace “Don Allah pardon me sister.”
Nasreen dai kamar gunki har lokacin kuma kanta na gefe, kan Zahrah sosai ta ɗaure ta ma rasa me za ta yi. Tsugunnawa tayi ƙasa on her kneels kamar za ta yi kuka tace. “Don Allah ki yi haƙuri, ban san me na miki ba amma ki yafe min.” shiruuu still.

Ganin hakan ma ya ƙi aiki yasa Zahrah ta langwaɓar da kai duk da Nasreen ɗin ba ta kallonta.

_Ƙawata kina ji? In dai kika bar Ni sai na sha wuya._

_Sai na zam kamar tsokar da babu jijiya._

_In ba da ke ba sai dai rijiya_

_Rijiyar ma mai ɗauke da ƙugiya._

Kafin Zahrah ta ƙarasa Nasreen ta juyo tana kallonta, dariya ta yafa kan fuskarta tace “Kin ci Sa'a kin waƙe Ni, ban waje na wuce.”
Da sauri Zahrah ta miƙe tana hugging Nasreen ɗin tace “You're going nowhere madam, ki zo mu kwanta.” fuska ɗaure Nasreen tace “I'm going home, ki ba Ni hanya ko ranki ya ɓaci.” ta ƙarasa sounding so intensed.

Ido waje Zahrah ke kallonta tana ƙara mamakin Nasreen ɗin, cikin ranta take tambayar kanta “Is she that tough?”
Without minding on how she sound Zahrah ta marairaice fuska tace “Yi haƙuri Yayis ɗina, dawo mu kwanta mana.”
Da ƙyar da siɗin goshi Nasreen ta haƙura yayin da ta bar Zahrah da mamakin yadda ta sauya, ta sa Zahrah cikin alhinin wane laifi ma tayi mata, da yake babu mai ba ta amsa yasa ta ci gaba da karatunta bayan ta yi assignment, can dai bacci ya fara kamata sai yawning take, hakan yasa ta rufe system ɗin ta ajiye ta kan bedside drawer kana ta miƙe ɗauke da addu'ar bacci a bakinta.

*Morning...*

Duk da cewa it's weekend tana son ta tashi da sassafe coz akwai muhimman abubuwa a gabanta amma hakan bai yiwu ba saboda ba ta samu kyakkyawan bacci ba da daddare. Zuciyarta ta gama karaya da abubuwan da ke bibiyar rayuwarta, first masifar Kawu da matarsa, aka Kai ga rashin Yayanta ga kuma yanzu wani hali da ta fuskanta daga ƴar'uwarta wanda ta tabbatarwa kanta cewa akwai lauje cikin naɗi, sai dai za ta saka ido domin gano matsalar da ke tattare da mai damuwa da ita. Baccinta sosai ta sha ba tare da gajiyawa ba, ba ita ta tashi ba sai ƙarfe goma na safe.

Ko da ta tashi ba ta ga Nasreen ba ba ta yi mamaki ba, Little Sadauki also was no where to be found, ta san dai ba zai wuce yana wurin Mamah ba. Ko da ta tashi ruwa ta watsa ta wanke bakinta kana ta fito parlourn, babu kowa hakan yasa ta nufi dining, bayan ta yi breakfast taje ta gaisar da Alhaji Baba, daga nan ta wuce gaida Hajjaty da Mamah sannan ta dawo bedroom nata.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da zama bakin bed ɗinta tana faɗin “Ya Allah!
Buɗe ƙofar da aka yi yasa ta mai da dara-daran idanuwanta ga mai shigowa, Nasreen ce ta shigo, ɗan kawar da kanta Zaharh tayi, ba ta yi ƙoƙarin yi wa Nasreen ɗin magana ba saboda tuna irin famar da suka sha jiya, hakan da tayi yasa Nasreen ɗin jin babu daɗi, cikin sanyin murya tace.
“I'm sorry Sister for behaving odd yesternight, ban san me yazo kaina ba amma ki yi haƙuri.”
Fuska sake Zahrah tace “Babu komai ƴar'uwa, na san ban kyauta miki ba nima, amma ba ta haka ya kamata ki hukunta ni ba in na yi ba daidai ba, you should have let me know me na aikata so that i'll apologize, don Allah kar hakan ta ƙara shiga tsakaninmu, zuciya ta ba za ta jure hakan ba, ke kanki kin san how valuable you are to me.”

“In sha Allah ba zan kuma ba, i'm so sorry dear, forgive me!”
“Babu komai.” daga haka suka koma sabgoginsu kamar ba abunda ya faru tsakaninsu. Bayan su Zakiyya sun shigo haka suka yi ta hirarsu gwanin burgewa.
Nainarh ce ta buɗe musu sabon shafin hirar da faɗin
“Babes! Kun san wani abu?”
A tare suka amsa mata da faɗin “Sai kin faɗa.“
Gyara zama tayi tace “Wai Yaya Khalil ne jiya yace min zai yi wa su Daddy magana kan auren mu.”
“Ke kuma kika ce masa me?”
Fuska yamutse tace “Kuna tunanin zan yadda ne? Ai na fi son dukkanmu a ɗaura aurenmu rana guda, in har kuna so na amince dole kuma ku sanar da Babes ɗin ku.“

Jinjina kai Zahrah tayi tare da faɗin “Lallai Nainarh ba ki da lafiya ma, to meye don kin fara auren?”
“Shi dai na gani." Faɗin Zakiyya tana yamutsa fuska
“Ke in banda abunki meye na ce masa a'a? To wallahi innza ki ce masa ma yayi magana ki faɗa, idan kuma kika bari har ya ɗau zafi wallahi sai ya wana ki, lokacin mu da kike cewa za ki jira hala mun turo namu.“
Dukan wasa ta kai wa Zakiyya wacce ke dariya, “Lallai Zakiyya ke muguwa ce, Allah sa Yaya Taj yace ba yanzu ba.”
"To sai me?“
"Sai na riga ki yin aure."

"Lallai yaran nan" Nasreen ta faɗa "To ku duka da kuke zancen nan kun shiryawa auren ne?"
Zahrah tace "Sister ai ba sai an shirya ba, shi aure lokaci ne."
"Hakane" ta ba ta amsa cike da gamsuwa.
Rumaysa da ke wani jujjuya ido tace "Wallahi duk ku shirya, ba na jin za mu ƙara ko 5months a gidan nan, in ma za ku ware ku ware, ni dai Ya Auwab na min magana zan ce mishi ok."
Dariya dukkansu suka yi ganin yadda tayi maganar.
"Allah ya kyauta to, na ga alamar ku ɗin nan auren kuke so, ba dama a zauna sai kun kawo zancen aure?" zahrah ta faɗa tana gyara zamanta.
"To bamu kai auren ba ne Mrs Ishaq to be?" Zakiyya ta faɗa tana kanne mata ido.
Da sauri Zahrah tace "Ni dai ban ce ba, rufa min asiri, ku da kuke so kuma kuka kai Allah ba da sa'a don ni kam ba yanzu ba."

Lokaci guda yanayin fuskar Nasreen ya sauya, shiru tayi ba ta ƙara cewa uffan ba saboda kar wani ya fahimci yanayin da take ciki, amma ko ta yaya wadda ke ƙaunar ka zai fahimci kowanne irun sauyi daga gare ka, kowa ya dan fahimta amma taƙamaimai babu wadda zai ce ga dalili, hakan yasa suka yi shiru tunda ba ta sanar da su ba.

Wayar Zahrah ce da ke kan mirror ta fara neman agaji, Nasreen da ke ta site ɗin ta dago da wayar don miƙa mata, wani dum taji zuciyarta na ba da makamancin sautin, da sauri ta miƙa mata tare da miƙewa ta nufi toilet.

Ko da Zahrah taga ya Ishaq sai da ta murmusa, gabadayansu ashe idanuwansu na kanta, a tare suka kwashe da dariya suna faɗin _Love birds_. Bata biye su ba ta kara wayar a kunnenta, bayan sun gaisa Suka sha hirarsu, daga ƙarshe ya tuna mata appointment ɗinsu na fita yau wadda ita har ta manta ma, daga ƙarshe dai suka yi sallama.

Bayan sun yi sallama Zahrah ta duba wayam taga babu Nasreen babu alamarta, kamar za ta yi magana sai kuma tayi shiru suka ci gaba da surutunsu. Kiran sallar da aka fara yasa Zakiyya miƙewa don tayi alwala but to her suprise tana murɗa handle na door ɗin ta ji shi locked, knocking door ɗin tayi tana faɗin “who's in?“
Jin babu amsa yasa ta juyo ta duba waye babu, ganin babu Nasreen yasa tace
"Nasreen please jiranki muke, duk kin bi kin zauna a toilet kamar mai naƙuda, please ki fito mu yi alwala sai ki koma ki haife yaran naki."

Tsaye Zakiyya na jiran Nasreen amma shiru, hakan yasa ta ƙara murɗa handle ɗin tare da banging door din tace "Malama ina jiranki fa."
Duk abunda ke faruwa Zaharh na kula, nan ta kara tabbatarwa kanta da zargin da take. A hankali ta taso zuwa bakin toilet din tace “Sister wai me kike a toilet?"
Shiru tayi ba ta ce komai ba, su ma sai suka tsinci kansu da yin shirun, Nainarh wacce ta sauke wayarta daga kunne daga wurin da take kwance ta ƙwala ma Nasreen ƙira ta yadda za ta jiyo ta.
"Wai Nasreen me kike yi ne haka?"

Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe tare da faɗin "Kun ga muje toilet din Mamah mu yi sai mu dawo, it seems like tana buƙatar kaɗaici din Allah kada mu takura mata"
Babu wadda yace uffan sai ma mikewa da suka yi suka fice a tare.

Jin shirun Ya yi yawa yasa ta tabbatar sun fice, a hankali ta buɗe ƙofar toilet ɗin ta fito fuskarta jiƙe da ruwa har yana ɗisa yayin da idanuwanta suka ƙanƙance kuma suka yi ja alamar ta sha kuka, ba ta tsaya ba siɗaf, siɗaf ta fice daga bedroom ɗin ta bi back door ta fice zuwa part ɗinsu zuciyarta babu daɗi.

*MOMMAH & DADDY*

Bayan Hajiya Babba ta yi wa Alhaji Babba magana bai samu damar yi wa Daddy magana ba, kamar wadda aka tsikara yau ya tunkare shi da maganar Mommah, da farko nuna bai da buƙata yayi har sai da Alhaji Babban ya takura masa, nan ya sanar da dhi cewa ba wai ba za ta dawo bane kawai dai yana so ta nutsu ne. A fusace Alhaji Babba ya fara faɗa ta yadda yake hawa ba ta nan yake sauƙa ba, wadda daga ƙarshe dai Daddy ya ba shi haƙuri tare da faɗin zai neme ta in sha Allah ta dawo gidanta, nan Alhaji Babba ya bar shi yana mai ƙara jin ƙaunar ɗan'uwan nasa musamman yadda bai fiye ja da shi ba idan ya yanke hukunci.

Bayan rabuwarsu da Alhaji Babba Daddy ya koma part ɗinsa, tunda ya shiga yau ne karo na farko da ya ji wani irin yanayi duba da yadda gidan ya kasance dull, bedroom nata ya shiga bayan shafe wasu daƙiƙu yana tunani ya fito zuwa nasa, sai da ya rufe door ɗin kamar wani na kallonsa kana ya ɗauko wayarsa tare da dubo numbern Mommah, kamar mai shawara da zuciyarsa sai da ya shafe tsawon daƙiƙa tukun ya danna ƙira.

Mommah wacce ke zaune a parlour ita da Hajja suna hira ta jiyo vibration na wayarta wacce ke kan centre table na parloun. Kamar za ta share dai ta miƙa hanu ta janyo wayar, idanu waje take kallon wayar fuskarta na nuna tsananin mamaki, anya ba gizo idanunta ke mata ba?, wayar na shirin yankewa tayi saurin picking tare da miƙewa ta dan ja gefe saboda yadda zuciyarta ke tsananta bugu.

*React, comment and share fisabilillah.*
*Itz Diamond Bhatool*

[4/11, 6:53 PM] bhatooldiamond: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*








*💎💍ELITE DIAMOND*
*WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_













_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 4⃣4⃣




Ko da ta kara wayar a kunneta sai ta tsinci kanta da sakin wata nauyayyar ajiyar zuciya haka ta kasance a ɓangaren Daddy ma. Sallamarsa ce ta sa ta dawo cikin hayyacinta yayin da zuciyarta ke tsananta bugu, wani sashe na zuciyarta na ɗaukin jin me zai ce yayin da ɗaya sashen ke tsananin tsoron da me Daddy yazo. Bayan sun gaisa kamar ba zai ce komai ba jin shirun nata ya yi yawa yasa a gajarce yace “Ehm Ummu Aliyu ki shirya after maghrib i'll be coming." ita kuma sai ta tsinci kanta da gyaɗa kai kamar tana gabansa tace "To Allah ya kawo ka lafiya."
"Amin" ya amsa mata kamar bai son maganar.

*ABATCHA ESTATE*
*NASREEN'S POV*

Kamar wata munafuka haka ta shige bedroom ɗinta, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kwantawa kan gadonta, cikin dasasshiyar muryarta ta furta "Ya Allah!" ƙarar buɗe ƙofa yasa ta ɗan zabura, ganin Hajiya Babba yasa ta ɗan ji kwanciyar hankali. Hakan ya sa ta miƙe tsaye tare da nufarta, wannan ita ce rainon da aka mata.
Kallon ƙurilla da Hajiyya Babba ke bin Nasreen da shi yasa ta tsargu da kanta, kanta ta sunkuyar ƙasa tana watsa da kyawawan yatsunta. Hannun Hajiya Babba ne ya kai ga kafaɗarta, mayar da ita bakin bed ɗin tayi wanda har lokacin idanun Nasreen a ƙasa suke. Cikin wata murya mai nuna tsantsar kulawa Hajiya Babba tace: "Nasreen? Watz wrong, me ya same ki?"
Wani irin kuka ne ya kuɓucewa Nasreen ɗin har tana shaƙewa, tapping bayanta Hajiya Babba tayi ba tare da ta yi ƙoƙarin dakatar da ita ba, sai da ta yi mai isarta kana share hawayenta ta fara sauƙe ajiyar zuciya a jere a jere.

Cike da kulawa Hajiya Babba ta ƙara ƙiran sunanta, ɗagowa tayi tare da kallon Hajiyar tata sannan ta duƙar da kanta."What is wrong Nasreen? Ba ki da lafiya ne?"
Nodding kanta tayi a hankali, Hajiya Babba ta ƙara tambayarta "Ba ki da lafiya ne?" ƙara jijjiga kai tayi, wannan karen a ɗan zafafe Hajiya Babba tace "Open your mouth and talk Nasreen" sai kuma ta sanyaya muryar tata "I'm your mother Nasreen, please feel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login