Showing 75001 words to 78000 words out of 157517 words
hakan yasa ta 'dauka waya da system nata da ta ajiye tun ranar da ta gama shirya komai nasu.
Sosai ta sha kukanta bayan ta 'dauko su, thank God she's alone, haka ta zauna bayan ta gama kukan tana 'yan surutai ita 'daya kamar wata zautacciya, Mamah da ta ji shirun Zahrah ya yi yawa bayan kuma ta ga shigowar Zahrah ya sa ta nufi 'dakinta don duba ta, surutan da Mamah taji Zahrah na yi ne suka 'dan tayar mata da hankali, ba tare da 'bata lokaci ba ta fahimci cewa Zahrah kenan son marigayi take. Ba tare da ta yi abun da ya kai ta ba ta juya a hankali ta koma tana 'kara nanata abun a kanta.
Bayan an sha ruwa Aunty Mabruka ta dawo wurin Mamah, Zahrah dai yau ba ta sha ruwa a part 'din Hajiya Babba ba, target 'dinta 'daya shine yau kam za su sha hirarsu da Mama ba tare da ta san yanzu Mamah ta Aunty Mabruka ba ce, a lokacin da ta fito da niyyar zama tare da Mamah ta ga an mata shigen layi sai ta koma ta fara amsa past Q tunda dama Jamb ta matso kusa.
Bayan sallar Isha su Daddy, Alhaji Babba, Abba, Papa, Affa da kuma Abie suka shogo tare da Alhaji Baba, sosai suka 'kara jajanta batun Mamah sannan suka mata nasiha sosai, bayan sun gama ita ma ta musu ta'aziyyar rashin Yaya Sadauki, sai a lokacin su ma suka san dalilin zuwansa Bauchi, a nan aka 'kara yi masa addu'a da fatan dacewa.
*YAU DA GOBE SAI ALLAH*
Bahaushe yace Yau da gobe sai Allah, ni kuma nace Hande idjango sai djomirawo, haka rayuwar ta ci gaba da kasancewa ba tare da Yaya Sadauki ba har aka yi azumi ashirin da biyar, a lokacin yana da rai duk yadda azumi yayi ashirin da biyar to zai yi wa kowa kayan sallah, babba da yaro kowa za a bi a raba a ba shi nasa, ba iya cikin family ba hatta orphanage 'dinsa na sirri wanda babu wanda ya san yana da shi sai Yaya Khalil haka zai ma yaran nan kayan sallah, yanzu shikenan kuma ya tafi.
Bayan an kai azumin ranar sai ga Yaya Khalil, kayan sallar da ake yi bai fasa ba ya wakilci 'dan'uwansa, bayan an ba wa kowa nasa da daddare ne yake fa'dawa iyayen nasa cewa yana bu'katar ku'di daga gare su, ko da suka tambaye shi me zai yi da wa'dannan ma'kudan ku'da'de 'kin fa'da yayi daga 'karshe Alhaji Babba ya hau shi da fa'da.
"Rabu da shi Yaya, ai ba a san uzurin da zai yi ba, ba ni account numbern ka, kowa zai saka maka kaji?" Daddy ya fa'da yana kwantar masa da hankali. Nan Alhaji Babba ya dake yace ai ba za a ba da ku'din ba sai Yaya Khalil ya fa'di me zai yi.
Hak babu yadda ya iya yace "Ku gafarce ni ni da 'dan'uwana Allah ya ji 'kan sa, 'dan'uwa na yana da wani gidan marayu da ya kafa kusan shekaru biyar baya, a daidai wannan lokaci tsawon shekarun da ya bu'de yana 'dawainiya da marayu bai ta'ba fashin sanya su farin ciki a salla ba, zai musu kaya kaya masu sunan kaya kamar kowa, Don Allah kada ku ce a'a, ina so a ci gaba da ayyukan da yake yi har zuwa lokacin da mu ma zamu tafi, ku zuba hannun jarinku wajen taimakawa marayu, shi kuma ubangiji zai biya ku da abun da ba ku yi tsammani ba." Daga haka yayi shiru tare da goge 'kwallarsa.
Jikinsu ne yayi sanyi gaba'daya suna 'kara mamakin hali irin na marigayin, tabbas suna kyautata masa dacewa musamman da wa'dansu ayyukan alkhairinsa da suke bayyana garesu yanzu bayan ba ya nan. Sosai suka saka ku'di, Alhaji Baba kuwa a lokacin ya sadaukar da tasa dukiyar wurin ganin ya kafa tasa sada'katul jariya 'din tun kafin mutuwarsa.
Tabbas duk wanda ya sa wani farin ciki ubangiji zai faranta masa, Ranar da aka 'dauki azumi na ashirin da shida aka kai wa marayun kayan sallarsu su ma, sun yi farin ciki sosai, Yaya Khalil na shirin tafiya yaji muryar wasu daga cikin su na fa'din
"Uncle yau ba ku zo da Daddy ba, Uncle ina Daddy yau ka zo kai 'daya? Daddy ba ya zuwa sosai ka ce masa mun yi fushi da shi Uncle"
Sai da yayi jim kafin ya juyo ya fuskanci Yaran yace.
"Daga yau nine Daddy kun ji ko? Daddy ya yi tafiya mai nisa ba lallai ku 'kara ganinsa ba, ku dai kuna yi masa addu'a Allah ya yi masa rahama"
"Shima ya tafi wurin da iyayenmu suka tafi ko?" Wata yarinya ta fa'da
"Ya rasu shima?" Kowa da tambayar da yake jefowa, ganin sun riga sun fahimci komai yasa su gaba da lallashi don kuwa kuka sosai suke shikenan Daddynsu ma ya mutu, da 'kyar ya sha kansu shima ka'dan ya hana yayi kukan, jiki sukwane ya musu sallamar sai ranar sallh zai zo su tafi masallaci tare kum tare za su yini, daga nan y musu sallama ya tafi ya bar su zukatansu babu da'di.
A cikin kayan da aka raba babu Mamah saboda kafin dawowarta marigayi ya yi booking kayan, hakan yasa Yaya Khalil yace mata gobe ta shirya za su je tayi siyayya da yake ba da wasu kaya dama ta zo ba, sosai Mamah ta ji da'di tana jerawa Yaya Khalil addu'a cikin ransa yana fa'din "Da ace 'dan'uwa na nan da ya gama cika rayuwarki da farin ciki Mamah musamma saboda son da Yake wa 'diyarki ba tare da ya sani ba."
Su Zahrah kuwa duk ba sa nan da yake yau 'din hutun kwana biyar da aka ba su ya fara, wankin kai suka je daga nan aka musu kitso, ba su yi jan lalle ba saboda bayan salla da kwana 'daya za su rubuta Jamb 'din su sai aka zana musu ba'ki kawai.
Washegari Yaya bayan an sha ruwa Yaya Khalil, Zahrah Nainarh da Nasreen suka raka Mamah siyayya, sun gama siyayyar komai wanda duk su suka 'daukawa Mamahn,bayan an yi payment ma'aikatan wurin suka kai musu mota. Nasreen da Nainarh na tsaye suna surutu sai kuma Zahrah da ke gefensu kanta sama tana kallon taurarin da ke jere a sararin samaniya yayin da hankalinta gaba'daya ya bar jikinta zuwa can wata duniya.
Har aka gama shirya kayan Mamah Nainarh da Nasreeen suka shige Zahrah na waje, Mamah ce ta hango ta hakan yasa ba tare da ta ce komai ba ta nufi wurin Zahrah,kafin ta kai ga 'karasawa wurin Zahrah taji an ambaci sunanta.
"Mamah"
A 'dan tsorace ta 'dago don ganin waye wannan.
Ido waje Mamah tace "Ishaq?" Tana mai ri'ke ha'barta tana mamaki.
Da yake space 'din da ke tsakinsu da Zahrah ba wani mai yawa ba ne jin sunan da Mamah ta ambata yasa ta sau'ke kanta 'kasa tare da juyowa a hankali tana mai mayar da kallonta ga wurin da Mamah ke tsaye. "Da gaske ne? Yaya Ishaq ne?" Ta tambayi kanta cike da kokonto sai kuma ta ba wa kanta amsa da "No he can't be the one, ya mutu ai". Tana shirin juyawa Mamah ta 'kira sunanta "Zahrah". Juyawar da bata yi ba ta 'karasa wurin da Mamahn ke tsaye ga mamakinta dai Yaya Ishaq 'din dai shi ne!
"Anya kuwa shi ne?" Ta tsura masa ido tana mai son tabbatarwa.
Ganin kallon da Zahrah ke masa yasa Mamah 'ko'karin barin wajen tana fa'din "Zahrah muna jiranki a mota, Ishaq ina zba idon ganin ka fa"
Ba tare da jin ya Ishaq 'din da ke fa'din "To Mamah In sha Allah Zan zo" ba ta wuce mota. Ganin Mamah ta ba su wuri yasa yayi wani irin murmushi. Zai iya cewa bai ta'ba shiga wani farin ciki ba a rayuwarsa sama da wannan ko dan irin wahalar da ya sha a baya ne ba tare da tunanin farin cikinsa zai dawo ba?
Tsayuwarsa ya gyara ya 'kara zuba sexy eyes nasa ga Zahrah wacce ta kasa 'dauke idanuwanta daga nasa and all this tana so ta gama confirming shi 'din ne ko kuwa?.
"Kallon ya isa haka ko Cutie?"
Jin abun da ya fa'da yasa Zahrah kwa'be fuska tana yatsinawa sai kuma ta turo bakinta gaba, huh! She nearly killed Ya Ishaq da wannan kallo bai san sanda ya furta "Wow! Damn cute.." sai kuma yayi murmushi. 'Bata fuska ta kuma yi tan fa'din "Ni ba kai nake kallo ba Ya Ishaq, i just want to confirm kai 'din ne ko kuwa, and tunda na tabbatar i can say bye, saboda na yi fushi da kai." Ta idasa a shagwa'be tana mai shirin juyawa. Caraf taji ya ambaci sunanta cikin wani irin salo da za ta iya rantsewa a duniyar nan babu wanda zai iya fitar da sautin tamkar yadda yayi. Shiru tayi ba tare da ta juyo ba amma ta kasa 'daga 'kafarta ta wuce.
"Cutieeee" ya 'kara fa'di yana jan 'karshen sunan. Da sauri ta juyo tana kallonsa, lokaci guda kuma idanuwansu suka ha'de da juna tuni kowa ya zuciyarsa ta 'kame wuri 'daya, ita Zahrah a 'bangarenta tana mamakin ganinsa ne zallah musamman yadda ya sauya, ya yi kyau abunsa kamar ba a Nigeria yake rayuwa ba, he looks so breathtaking and more matured, yanayin shigarsa zai 'kara tabbatarwa mai karatu ya ji'ku kuma yana jin da'di.
'Bangaren Yaya Ishaq kallon da yake yi wa Zahrah tunaninsa ya lula ne ga irin rayuwar da za su shimfi'da da ita tunda yanzu dai finally ta dawo garesa ba ya ma tunanin ko tana da aure? Tana son sa ne kamar Yadda shima yake son ta?.
Nasreen da ta 'dan 'kosa da zaman jiran Yaya Khalil ne ta mintsini Nainarh, nan ta fahimci me take nufi, su biyun a lokacon kowacce ta fice daga motar, to their suprise, Zahrah suka hango tsaye da wani santalelen guy daga wurin da suke har sun harbo irin kallon da yake aikawa Zahrahn. Kallon-Kallo suka aikawa junansu wamda lokaci guda kuma zuciyar Nasreen ta ba da wani irin sauti. Kanta ta kawar gefe tace "Nainarh! Gizo ido na yake ko kuwa?"
ita ma Nainarh tambayar ta aika a maimakon amsa "Nima dai kamaer abun da kika gani na gani?" Nasreen ta amsa da "Of course yes, Zahrah is in love...amma ta gagara sanar da mu? Mu je mu gani." Daga haka suka 'daga 'kafafunsu don ganewa idanun su who's that lucky guy da Zahrah ke tsaye da shi.
*React and share fisabilillah*
[1/27, 8:35 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 3️⃣5️⃣
﷽
Har lokacin da suka isa tsakanin Zahrah da Ya Ishaq kallon kallo ake. Sallamar Nasreen yasa dukkansu suka zabura suna komawa hankulansu. Abunka da namijin duniya sai ya waske ya bar Zahrah sai ciccilla ido take. Ta gefe Nasreen ta saci idon mutumin ta sha'bo bayan rigar Zahrah, da Sauri Zahrah ta fara ta'ba goshinta da yatsunta da suka sha lalle tace "Ehm Nasreen & Nainarh meet Yaya Ishaq wanda nake baku labarinshi kwanaki, and Yaya Ishaq" ta 'fada tana kallonsa tare da pointing Nasreen "Meet my beloved sisters Nasreen and Nainarh" tayi pointing Nainarh. With smile on his face yace
"Ma sha Allah, so pleased to meet you sisters, I'm Ishaq as she said"
Fuska sake suma suka ce "Thanks".
Daga haka suka ji muryar Yaya Khalil yana kwa'da kiran Zahrah, ba shiri suka masa sallama bayan ya amshi numbern Zahrah kan in ya zo sai ya 'kira ta, daga haka suka wuce Yaya Khalil sai fa'da yake hushinsa kuma bai wuce ganinsu da namiji ba musamman da bai san cikin su wace ce aka tsayar ba, fatansa Allah yasa ba Nainarhrsa bace. Mamah tana jinsa kar yace ta barsu yasa tayi gim da bakinta don ta fahimci da biyu yake fa'dan.
Bayan sun koma aka fara kallon kayan Mamah ana yabawa, daga nan girls 'din suka nufi part 'din Hajiya Babba da yanzu suka fiye zama fiye da na Hajjatyn. Suna isa suka tarar da Rumaysa da Zakiyya sai cika suke suna batsewa waian tafi ba a ce musu za a fita ba. Labarin da Nainarh ta sako musu na Zahrah yasa dukkansu suka bar batun fushi suna bu'ktar 'karin bayani. Nasren tace "Wallahi fa, ina wannan Ya Ishaq 'din da Zahrah ta bamu labarin ya saka ta a school lokacin tana Bauchi?"
Rumaysa tace "Eh na gane"
Gyara zama Nasreen tayi tace "Yauwa, yau shi muka gani kuma fa akwai alamun eh eh eh...."
Dariya dukkansu suka yi, Zahrah tace
"Sai kuma ku yi ai tun.." bata rufe baki ba wayarta ta tsala ihu tana bu'ktar agaji, sani ba su ba wa kowa numbers nasu ba hatta mutanen gidan yasa suka zubo mata ido, harara ta cilla musu ta murgu'da baki kana ta shige bedroom nasu ta bar su suna mita. Ba tare da ta san waye ba tayi picking, tsawon wasu lokuta sai ga ta ta fito tana yatsina fuska suna ganin hakan suka kwashe da dariya sai da Hajiya Babba ta sa suka bar parlourn tana fa'dan har 12:00am ba za su kwanta ba.
*DEVIL'S KLANS*
A tsakiyar wannan dare suka tada busarsu da suka saba yi wacce tayi sanyi saboda zuwan azumi, ha'duwar yau kuma ta murnar wucewar watan da ya musu da ayyukansu ne. Sai da suka gama bushe-bushensu tukun suka fara tattaunawa kamar komai. Uwargijiya ce ta saki wani irkn numfashi mai kama da 'karar iska, tuni wata guguwa ta tashi wacce tayi sanadin komawar wurin kamar ba'kin rami kafin daga bisani haske ya mamaye wurin.
Kamar koyaushe yau ma sai da ta yi kirari ta 'kara ta yi ta gaji tukun ta fara magana cikin kakkausar muryarta marar da'din sauti.
"Ina taya mu murnar shu'dewar ba'kin wata mai hana mu sukuni, bayan nan kuma ina mai son 'kara sanar muku akwai muhimmiyar sadaukarwa da za mu yi mai tarin yawa wacce nake fatan in mun yi ta za mu 'kara shahara, 'karfin ikon mu zai dawo kamar yadda ba kwa tunani, abu na gaba za mu shahara mu zama taurari a duniyar tsafiiiiiiii"
"Ye! Ye! Dodon tsafi ya taimake mu"
"Kowa ya tanadi abun sadaukarwarsa, da zarar mutane sun fara murnar salla mu kuma za mu yi murnar shudewar watan, za mu sha jini mu 'koshi ba shakka, in rantsuwa da dodon tsafi zan sadaukar da jinnai marasa adadi a wannan karon, zan shahara fiye da kowa a duniyar tsafi, a yanzu ne zan fara 'daukar fansar kaka na da ya bari a hannun mahaifiya ta wacce ba'kin ciki ya lahanta ta, na rantse da dodon tsafi ba zan bar wannan abu ya wuce haka ba, fansa! Fansata! Dole su ji babu da'di, tunda na rasa mutane biyun nan dole su rasa goma!"
Ihu suka fara suna fa'din
"Sai kin yi, uwargijiya ce sai kin yi!"
Shiru na wasu da'ki'ku aka samu sai kuma ta ci gaba "Zan 'karawa 'diya ta kuma magajiya ta Taizana 'karfi domin kammaluwar aikin mu, kowa ya tanadi kayan sadaukarwarsa!" Daga haka kuma suka fara wasu zantukansu da kai tsaye za a ce yarensu ne na matsafa ba kuma yaren duniya ba.
*MORNING*
Sassafiya su Aunty Mabrukan Mamah ta faki ido ta gudo wurin Mamahnta, sosai take jin da'din mu'amala da Mamah, ganin kowa sai shogowa yake da kayan sallarsa musamma little girls 'din nan suna nuna wa Mamah wacce lokaci guda kowa ya san da zamanta kuma ake girmama ta. Aunty Mabruka sai da ta zub da 'kwalla da ta tuna ban da ita za a je Eid bana tunda tana takaba.
*ZAHRAH*
Yau tunda ta tashi take jinta wani iri musamman da ta tuna mafarkin da ta yi a yau 'din. Ta rasa gane me yasa Yaya yake zuwa cikin mafarkinta, gashi kullum tayi mafarkinsa sai ya sa mata shakka akan mutuwarsa. Jiki sanyaye ta fice ta gaida Hajjaty da Mamah, wayarta ta 'dauko don za su fita amso 'dinkinsu da suka kai ita da su Nainarh. Tana bu'dewa taga message, a heart melting love message da ya sa gabanta bugawa, who's that sender? Tunawa da jiya har waya ashe sun yi da Yaya Ishaq yasa gabanta bugawa, babu shakka shine.
Babu shiri hawaye suka fara zarya kan fuskarta, wayarta ta 'kan'kame a 'kirjinta tana fa'din "My heart can't love you Ya Ishaq, she'd already fall for one, ta fa'da ma soyayyar mamaci, Allah sarki Yaya na, he be like...Lilyn Yaya this and that, ba zan so kowa ba bayan shi infact ba ma zan yi aure ba sai a aljanna." Ta idasa tana murmushi, lokaci 'daya kuma ta gimtse fuska tana 'fa'din "I can't reject your love in ka bu'kaci hakan, zan iya zama a hakan amma Ya Ishaq zuciya ta ba za ta so ka ba a matsayin masoyi, zan ci gaba da maka kallon 'dan'uwa to my last breath."
Fuskarta ta gyara tana kallon mirror kafin ta cire wyan ta fito. A parlour ta ci karo da Yaya Khalil yana aika mata wani mugun kallo. Kan ta 'kasa ta gaida shi sannan ta bi gini za ta fice, dakatar da ita yayi yana fa'din
"Jiya da wa kuka tsaya?"
Saura ka'dan tayi dariya don ta gano jirgin nasa sai kuma ta kafse tare da ba shi amsa.
"Yaya Ishaq ne, Yaya na ne, Mamahma ta san shi ka tambaye ta" ba tare da ya yadda ba yace "Zancen me kuke da shi to?" Kamar za ta yi kuka tace "Yaya Khalil mun kusa 7-8years ba mu ha'du ba shine fa nake tambayarsa dama bai mutu ba? Su Sis Nainarh kuma Mamah ce tace su zo su 'kira ni."
Wata ajiyar zuciya da ya sau'ke sai da Zahrah ta 'kara dubansa karo na biyu tana jinjina hali irin nasa. Ko da suka ha'de da 'yan'uwanta ta basu labarin ha'duwarta da Yaya Khalil