Showing 69001 words to 72000 words out of 157517 words

Chapter 24 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5169

sahur na azumin washegari ya gagara har alfijr ya keto. Bayan sallar asuba kai tsaye iyaye mazan banda Daddy da ke tare da Alhaji Baba suka fice daga gidan don nemo gawarsa shima a masa sutura a mi'ka shi gidansa na gaskiya. Allah ya masa rahama.

Washegari da safe su Aunty Madina suka diro, su Yaya Haidar da Yaya Junaid tare da ahalinsu su ma suna hanyarsu ta zuwa tunda sa'kon ya kai gare su, sai dai ba su wani 'daga hankali akai ba saboda ba su yadda da zancen mutuwar tasa ba.

Yaya Junaid da kansa ya 'kira Hajja a waya ya sanar mata. Sosai Hajja ta yi tawakkali sai dai damuwarta 'daya bata san ya za ta tunkari Momma da zancen ba, haka dai ta 'kira gaba'daya 'yan uwan Mommah ta sanar da su, kafin kace me duk sun hallara ana ta koke-koke, Mommah da ta fito don ganin su waye ke kukan ganin ahalinta yasa gabanta fa'duwa tana addu'ar Allah yasa ba Hajja ba ce ta rasu suke wannan kuka. 'karasawa tayi kusa da su tana rage girmn idanuwanta
"Bayin Allah kun sa mu gaba da kuka, don Allah me ya faru"

Ganin Hajja ta fito itama tana hawayen yasa ta 'dan sau'ke ajiyar zuciya sai dai kuma hawayen Hajja sun sanya mata ru'dani da bugawar zuciya mai tsanani da ba za ta iya jurewa ba, 'karasawa tayi ta rungume Mommah . Sosai 'yan'uwanta suka tausayawa yanayin da ta shiga sai dai har lokacin Mommah ba ta san me yake faruwa ba.
"Ki shirya Shughrah za mu fita ne."
Hajja ta fa'da tana sakin Mommah tare da share 'kwallarta.
"Ina za mu je ne haka Hajja? Sai kuka kuke kun 'ki fa'dama min dalili, don Allah ku fa'da min kada zuciyata ta tarwatse" Momma ta fa'da tana 'dan kawar da kanta gefe.
"Ki ai shirya kawai Sughrah, idan mun je za ki ji me yake faruwa, sai dai kuma kafin nan ina ro'konki da ki yi ha'kuri da abunda za ki ji, kada ki yi tunanin ubangijin da ya salla'da hakan bai son ki ne, kin ji ni?" kai Mommah ta gya'da zuciyarta na 'kara karyewa.
"Maza je ki yi wanka ki karya, ku kuma kukan ya isa, addu'a ce kawai mafita a yanzu."

*HOSPITAL*

Babu laifi Hajjaty da ta farka safiyar yau ta fauwala ubangiji komai ta kuma 'daura da yiwa shalelen marigayin jikanta addu'a, hakan ne ma yasa Dr. Muba da ke famar 'dawainiyar jinyarsu yayi discharging Hajjatyn, atleast in ta koma can ra'da'din will be relieved, Yaya Khalil ne yazo ya mayar da ita can aka ci gaba da zaman jiran tsammani tare da addu'oi.

*MOMMAH*

Drivern Mommy Nasiba ne ya 'dauko su Mommah, su Aunty Rahina da mazajensu suka taho da motar Yaya Kabiru, gaban Mommah bai daina yankewa ba lokaci bayan lokaci kuma takan le'ka fuskokinsu taga suna share 'kwalla. Mamaki ne ya cika ta ganinsu a Abatcha Estate yayinda tsoro da fargaba suka yi wa zuciyarta 'kawanya, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai take maimaitawa har motarsu ta daidaita parking, bayan sun fito suka shiga part 'din Hajjaty.

A lokacin an dawo da Hajjaty, parlourn nan kuwa cike yake da jama'a everywhere and every angle, abunda ya 'daure kan Mommah shine yadda kusan duk mutanen cikin ke share 'kwalla.
"Tabbas mutuwa aka yi" ta fa'dawa kanta "Amma waye?" Babu mai ba ta amsa yasa tayi wa Hajjaty Ya ha'kuri ba tare da ta san 'Dan da ya wahala da miyagun halayenta ne ya bar mata duniyar da ta shana ba.

Tana rufe baki sauran jama'ar parlourn suka hau yi mata ta'aziyya saboda kowa ya san Mommah. Da kallon mamaki take binsu can dai ganin duk wanda ya le'ko sai ya mata ta'aziyya yasa ha'kurinta 'karewa ta tambaya. A wannan karon Hajjaty ce ta ba ta amsa da fa'din
"Wanda kika cutar 'din dai Sughrah yau Allah ya kar'bi kayansa, sai ki huta ki kwa'da duniyar ki lashe ta." Tana mai share 'kwallar da ke sintiri daga idanuwanta.
"Ban gane ba Hajjaty ki min bayani" Mommah ta fa'da cike da tsoro.
Ba tare da jin wani abu ba Hajjaty ta ba ta amsa kamar yadda ta bu'kata
"Sadauki dai, Sadauki shi ne yayi ha'darin jirgin sama jiya da safe, Allah ya...." kasa 'karasawa Hajjaty tayi tana mai share 'kwallarta da in har ta ci gaba da maganar kuka zai iya kufce mata.

A matu'kar firgice Mommah ta mi'ke tana sakin wani malalacin murmushi
"Lallai Hajjaty, Sadauki ba zai mutu yanzu ba, bari ki ga yanzu yanzu zan kira wayarsa kuma zai 'daga"
ganin ba ta cikin hayyacinta yasa kowaya fara jijjiga kai yana tausaya mata, Hajjaty ne ta nuna wa Mommah 'kofa tace
"Sughrah ki je 'bangarenki, wasu ba'kin za su shigo" ba tare da fahimtar me Hajjatyn tace ba ta nufi 'kofa, su Mommy Nasiba suka bi bayanta to aid her with psychotherapy.

Abunda kuke tunani ya wuci hakan,tun fitarsu Mommah ba ta 'kara cewa uffan ba, ana tunanin mutuwar ba za ta ta'ba ta ba sai gashi ita lokaci 'daya hankalinta ya riga ya gushe, da ido kawai take amsar gaisuwar sai dai su Hajja su amsa da baki. Allah sarki Mommah, 'dan da take gadara da nata ne, 'dan da take fifita son zuciyarta a kansa yau Allah ya kar'be shi.

*Zahrah & Aunty Mabruka*

Hajiya Babba wacce itama hankalinta yake tashe ita ke jinyarsu, Allahn da yayi taimako Aunty Mabruka ma around 12pm ta farka kamar mahaukaciya, amma bayan nasiha da tunatarwar da Hajiya Babba ta mata ta 'dan risina, hakan yasa Dr ita ma yace ta koma gida za ta fi jin sau'kin ra'da'din mutuwar.

Zahrah ce dai ko sau 'daya ba ta farka ba tun jiya da sa'kon ya doki kunnuwanta, haka Hajiya Babba za ta tofa addu'o'i a cup ta shafa mata amma shiru. Tsawon wannan lokaci dai ba a samu wani update daga mutanen Bauchi ba. Can wuraren Asr ta farfa'do, Alhamdulillah itama a hankalinta ta tashi sai dai kuma banda hawaye ba abunda ke zarya kan fuskarta, 'kunci da damuwasun dabaibaye zuciyarta, ya ma za a yi a ce Yaya Sadauki is nomore alive a yi tunanin ita za ta rayu? That's impossible. Duk irin yadda Hajiya Babba ke ba ta baki tana mata nasiha babu abunda ya sauya coz Zahrah is not fully concious, physically dai ga ta amma mentally she's not there, tunaninta ya tafi can ga begensa tare da fatan wani ya tayar da ita daga nauyayyan baccin da ya 'dauke ta ko za ta samu ta farka daga wannan mummunan mafarki, a haka dai har aka mayar da ita gida ba ta magana sai dai kallo, kowa ya ganta ya san ta ta'bu da wannan rashi, sosai kowa ya tausaya mata.

*React and share fisabilillah*
*𝓓𝓲𝓪𝓶𝓸𝓷𝓭 𝓑𝓱𝓪𝓽𝓸𝓸𝓵'𝓼 𝓹𝓮𝓷*


[1/23, 9:11 AM] Diamond Bhatool:











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 3️⃣2️⃣




Zahrah ba ta jima da dawowa ba su Nasreen suka dawo part 'din Hajjaty don kasancewa da ita, ba wai su mutuwar ba ta shafe su bane sai dai babu shakka sun an cewa Zahrah feels the pain more than them. Suna zaune su Aunty Na'eemah ma suka iso, tabbas na gaskata son da ake yi wa Yaya Sadauki, in-law 'dinsa ce amma how she looks will define the actuall pain she's in, Allah ya ma Yaya Sadauki Rahama.

Duk da tsananin 'kunci da suke ciki bai sa an dakatar da duk wani aikin alkhairi da ake yi a gidan ba, hasali ma shirin 'karawa ake yi, daf da maghrib aka kammal girkin da ake yi kai tsaye aka fara ficewa da maka-makan kuloli daga estate 'din zuwa masallatai mabanbanta kafin a kwashi abun sha a wuce da su. Ko da aka sha ruwa ma babu wani mahalukida ya bi ta kan abinci bayan ruwa da dabino da suka saka a bakinsu.

Sai da aka yi isha'i su Alhaji Baba suka dawo, hankalin kowa a tashe yake, a lokacin wa'danda suka 'karyata mutuwar suka yi surrender, tabbas ta tabbata. A part 'din Alhaji Baba aka aje gawar da nufi zuwa safiya a kai shi makwancinsa. Bayan sun huta ne su Hajja suka zo suka yi musu ta'aziyya, kan Mommah 'kasa ba ta bari sun ha'da ido da su ba, gani take kamar idon kowa a kanta yake ga abubuwan da ta aikata baya. Aunty Madina mai dauriyar itace ta sanar da Daddy yanayin da aka yini a ciki bayan tafiyarsa, sosai yayi fa'da kamar zai yi kuka.
"Me yasa ba za ku amshi 'kaddararku ba? Shin kun fi mahaliccinsa 'kaunarsa ne? Ya kamata zuwa yanzu mu fauwalawa ubangiji komai, mu sani babu wani cikin mu da zai 'kara ko da second 'daya ne idan wa'adinsa ya cika, a yanzu addu'arku kawai Aliyu yake bu'kata ba wai kuka ba, 'kuncin da kuka yafawa zukatanku da wa kuke? Da ubangijin da ya 'dauke shi?" Shiru suka yi babu wanda yace 'kala.
"Rashin cin abincin da kuke kuna tunanin in yana raye zai ji 'dadi ne? Kuna tunanin hakan zai dawo muku da shi ne? Kowa ya 'dan'dani mutuwar nan cikin ransa, amma 'kuncin da kuke jefa kanku ba dawowa da shi zai yi ba, ku yi ha'kuri don Allah, ku yi wa Aliyu Addu'a shine ka'dai maslaha." Daga haka ya mi'ke ya fice daga parlourn don ba ya bu'katar rauninsa ya bayyana garesu. Daga nan kuma su Hajja suka wuce da Mommah idan ya so sassafe sa dawo washegari.

Saboda Nasihar Daddy ne yasa aka 'dan ta'ba abincin, Zahrah dai ba ta ci ba saboda ba ta ma san ina take ba har lokacin. Haka wannan dare ahalin nan suka riske shi idanuwa bu'de sai dai kusancinsu da mahallicinsu da ya 'karu, sosai suke sanya marigayin cikin addu'o'insu.

Tun daren aka sanar da jana'izar Yaya Sadauki da za a yi a masallacin estate 'din, hakan ya sa da sassafe aka fara shirin yi masa sutura. Daddy da kansa yayi ma gawar 'dan nasa wanka wacce ta koma tamkar ba shi ba, babu alamar cewa fatar mutum ce wannan saboda yadda ta 'kone bare a zo gandin gane kamanninsa, babu alamar wata halitta kamar hanci a fuskarsa saboda yadda ta kwazazza'be.

Bayan an masa wanka aka shirya shi tamkar yadda ake wa kowacce gawa, sannan aka bar shi a nan 'bangaren saboda ba kowa ake so ya ga gawar ba, in so samu ne ma sai za a fita da shi masallaci za a kai shi in da masu masa addu'a su yi.

Da misalin 'karfe tara na safe aka fito da gawarsa zuwa parlourn Hajjaty saboda mutane sun riga sun taru za a masa salla. Ko da aka ce Hajjaty ta masa addu'a cike da 'karfin hali ta matso kusa da gawar tasa da ke 'kamshin turare ba tare da ta bu'de fuskar ba ta ha'da hannayenta tana masa addu'a, bayan ta kammala Alhaji Baba ya dubi Mommah yace ita ma in za ta kalle shi to, da sauri ta 'karaso gaban gawar ta tsugunna hawaye na zuba daga idanuwanta ta ha'de nata hannayen ta fara jera masa addu'o'i. Ko da ta gama aka 'daga gawar da niyyar ficewa da ita don a sallace ta kwatsam Zahrah da ke 'dakinta ta fito da gudu ta zube 'kasa tare da ri'ke 'kafar Papa da ke ri'ke da makarar tana fa'din
"Ku yi wa Allah ku yi wa manzon tsira ku ajiye min Yaya na, wallahi bai mutu ba, da ransa kada ku bisne shi. Papa ka duba ka ga Yaya ya ce min zai zo min da dadda'dan labari amma kuce ya rasu? Wallahi Yaya na bai mutu ba, Yaya ka duba Lilynka ce fa" ta fa'da tana sakin wani irin murmushi
"Ka tashi daga makarar nan ba wurin zamanka bane, Yaya ka bar wannan wasan da Lily..."

Fahimtar ba ta cikin hayyacinta yasa su Aunty Na'eemah da su Mimie suka ri'ke ta su kuma su Daddy suka fice da gawar, da 'kyar suka tisa ta gaba ta yadda ta koma bedroom nata wasu irin zafafan hawaye na zuba a idanuwanta.
Nan aka wuce da Yaya Sadauki aka masa sallah sannan aka raka shi makwancinsa.

Tsawon wannan kwanaki biyu na rasuwar Yaya Sadauki, akwai mata da kuma 'ya'yan da ban ga giftawarsu ba cikin ahalin bare a yi tunanin za a yi zaman jimami a tare da su. Bayan kwana uku kuma Alhaji Baba yace kowa ya kama nasa wurin, a ci gaba da yi wa Yaya Sadauki addu'ar Allah yasa ya dace. Babu wanda ya tsallake wannan umarni na Alhaji Baba duk aka watse, Aunty Madina da mijinta da kuma sirkanta suka koma, Yaya Junaid ma ya koma haka Yaya Haidar.

'Bangaren Hajjaty ya rage daga ita sai Alhaji Baba sai kuma Zahrah wacce har yau ba ta farfa'do ba, magana ma ba ta 'kara yi ba tun lokacin da aka fice da gawar Yaya Sadauki. Nainarh wacce yanzu suke kwana tare da Zahrah ta yi iyakar iyawarta wurin ta sa Zahrah ta mance da Yaya amma abun ya fasaya, hakan yasa Hajiya Babba tace daga ita har Nainarh su tattaro su dawo part 'dinta idan ya so Ra'ees ya zauna tare da Hajjatyn.Da haka Zahrah tattara ta koma can 'din ba don ta so hakan ba.

Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya, rashin wani ba zai sa a rasa wani ba, kowa da dalilin da ya sa ubangiji ya busa masa rai. Sati da guda da wannan rashi su Zahrah suka fara shirye-shiryen rubuta JAMB nasu, saboda haka suka koma makaranta kamar dai da amma Zahrah har yanzu ta kasa komawa daidai, gaba 'daya ta rame kamar ba Zahrah ba kuma har yau 'din ta kasa amincewa da cewa Yayanta ya rasu, gani take kamar wata rana zai dawo gare ta.

A matu'kar wahale ta dawo daga school saboda yadda azumi ya fara bata wahala coz sai a yau 'din ne ta fara. A part 'din Hajjaty ta yada zango saboda tana bu'katar hutu, can kuma in ta koma ba za su barta ta rintsa ba don ita ka'dai tasan yadda take ji a jikinta. Wayarta da ba ta iya rabuwa da ita a halin yanzu ta jefa gefe kana ta baje kan bed nata.

Ko da lokacin shan ruwa yayi Zahrah ta koma wurin 'yan'uwanta, bayan an sha ruwa suka gabatar da sallarsu ta maghrib daga nan kuma suka mi'ke don zuwa sannu da shan ruwa ga sauran jama'ar ahalin kamar yadda suka tsara, sai da suka ziyarci kowanne part na gidan, idan akwai squad member nasu sai su ha'du su 'kara gaba, bayan sun zaga ko'ina na gidan suka nufi part 'din Hajjaty. Tun daga door step gaban Zahrah ya buga har sai da ta 'dan dakata. Nainarh ta kalleta tace
"Ya dai Zahrah" kanta ta kawar gefe ba tare da ta ce komai ba ta fara 'ko'karin shigewa, hakan yasa ita ma Nainarh ta bi bayanta suka shige.

Wasu ba'ki ne guda hu'du a zaune a parlourn tare da Hajjaty sai dai ba ka oya gane su wane ne saboda yanayin hasken 'dakin...dim light ne shiyasa. Cike da girmamawa suka 'karasa suna gaida ba'kin sai dai kamar yadda suka shigo ashe cikin ba'kin akwai wacce ba ta gaida Hajjaty ba, still dai ba kuma ta amsa gaisuwar su Zahrah ba a wannan karon. Ra'ees ne da 'dan banzan rigimarsa ya taho da gudu ya kunna light sannan ya yo gurin Hajjaty.

ko da aka kunna hasken abun da Zahrah ta fara cin karo da shi ya matu'kar sa bugun zuciyarta 'kara tsananta bugu, kamar a mafarki! Saboda ta farfa'do daga sumar tsayen da tayi ta murza idanuwanta da hannunta don 'kara confirming abun da idonta ya gani, gaskiya ba daidai ya nuna mata ba wannan karon ma hakan yasa Zahrah ta fara marin fuskarta tana fa'din "Farka farka Zahrah"
Tana 'kara bu'de idanuwanta dai same abu haka take gani.

_Hajjaty_ tun da haske ya gama gauraye parlourn ta kai dubanta ga ba'kin, idan har mai karatu ya san ru'du, to Hajjaty ta shiga wani irin hali na ru'du, waye take gani haka gabanta?
"Nooo that could not be her, ba ita bace" tayi reassuring kanta.

Ihun da Zahrah ta buga tana nufar 'daya daga cikin ba'kin tana ihu tana fa'din
"Mamah na!" Sai kuma ta 'kara hugging nata tightly kamar za a 'kwace ta daga gareta. Wannan ihu da Zahrah tayi shi ya dawo da Hajjaty daga duniyar tunani, tabbas ba gizo Madina take mata ba,'diyarta ce yau ta dawo gareta, nan hawaye suka fara wanke fuskar Hajjaty, Zahrah ce ta raba jikinta da na Mamah ba tare da hawayen fuskarta sun daina zuba ba.
"Mamah yau kam kin dawo..." bata ida fa'din abunda za ta ce ba taga Hajjaty rungume da Mamar dukkansu sai kuka suke. Babu wanda yayi 'ko'karin raba su haka aka bar su suna kukansu, they deserve to cry, kusan shekaru ashirin yanzu rabonsu da juna, dole kuwa su koka.

Nasreen, Nainah, Rumaysa, Zakiyya da yanzu sun fahimci cewa Mamah ce ta dawo yasa suma suka fara zubar da 'kwallar farin ciki tare da dawowa suka rungume Zahrah a tare. Inna, Asma'u da kuma Balkisu wa'danda su suka rako Mama su ma mamaki ya gama cika su musamman yadda suka ga Mama da Hajjaty na kukan farin ciki, hakan ya 'kara tabbatar musu da cewa ba 'karamar soyayya da sha'kuwa bace tsakaninsu.

Bayan an share mintuna goma da wasu sakannin ana kuka suka raba jikinsu koma na duban kowa. Hajjaty tana hawaye tace "Madina yau ke kika dawo? Farin cikin da na rasa tsawon shekarun nan yau ya dawo! Alhamdulillah" sai kuma ta sau'ka ta zube 'kasa tayi sujjada, itama Mamah sai ta bi bayan Hajjaty tayi sujjadar, sosai sauran mutanen suka bi su da murmushi da kuma tausayawa. Hajjaty da ta tashi ta dubi Hajjaty tace "Maza 'diyata tashi ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login