Showing 138001 words to 141000 words out of 157517 words

Chapter 47 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5152

san ba kowa ne yaji zai yadda ba sai mu da muka gani."


"Ina jinki my heartbeat...just to the point."
"Yaya Dama tun kafin ka tafi kwanaki nake son maka magana a kai but I was afraid ka ƙi yarda da Ni, kwanan nan kuma Sister Nasreen itama ta ci karo da kwatankwacin hakan....." Tas ta kwashe komai tun daga ranar da tayi wa DEVILS KLANS 😈 laɓe har sau biyu, fafatawar da suka yi, zuwa wadda Nasreen ta jiyo game da fasa aurenta da aka yi da Ya Ishaq, jin ya yi shiru yasa ta ƙara da
"Yaya ina jin tsoron wani mummunan abu ya faru da wasu daga cikin wannan ahali bayan na san me yake faruwa, tabbas cikinmu akwai Baragurbi da suke sanya rigar mutunci su fito bayan kuma cikinsu ba shi da kyau. Ka ga lokacin da Aunty Mabruka ma ta rasu na zargi wani abun, ba ka nan lokacin Yaya, da za ka yadda, haka ranar ma ba a san waye ba ya ba wa Little poisonous drink, Allah ya so bai masa illa ba an taro abun da wuri, kafin nan ma tun yana ƙarami an taɓa faɗo da shi daga bed... something fishy happened and Is still happening... please do as much as you can to save this family.."

Numfashi Yaya Sadauki ya sauƙe yana jinjina kai, abunda ya jima yana masa ƙaiƙayi kenan cikin ransa, ya jima yana hasaso cewa akwai miyagu a familyn nan tun ba yanzu ba, hatta sharrin da aka yi wa Aunty Mabruka yana sane da cewa sharri ne tunda ya yi bincike a kai.
"Wannan shine kike roƙo na nayi miki my lady?" Kai ta gyaɗa masa yace "in dai wannan ne, consider it done, Nima na daɗe ina hasaso wasu abubuwa amma ban kai su ga mahangar cultists cikin ahalina ba, na rantse miki da Allah ko da kuwa hakan zai yi silar rasa raina sai na gano komai. Kin san irin wannan al'amuran sai an haɗo da great Islamic scholar waɗanda suka yi ƙaurin sunan fannin lalata sihiri da ayyukan shaiɗanu. Daga nan sai mu saka ma'aikatan mu cikin harƙar, lada ki damu, zan ƙira Imam Nasir, shahararre ne kuma ƙwararre a wannan fanni."

"Thank you so much Yaya, I'm very proud of you, kaima ka cancanci tukuicina, ina roƙon Allah da ya ba mu nasara akan waɗannan shaiɗanu."
"Amin my charming angel. Yanzu dai da mun gama da wannan case ɗin I'll present your gifts before you."
"Thank you Yaya na"
Ɓata fuska yayi yace "Yaya ko? I don't want to hear this name anymore, I need one that's romantic." A shagwaɓe tace
"To wanne an ke faɗa maka?"
"Huh!" Ya sauƙe numfashi "Wannan shagwabar taki tana sanya Ni cikin yanayi na shauki da buƙatar son kasancewa da ke..just romantic one, ki zaɓa min, in ba haka ba if you dare call me with Yayan nan, sai na yayo ki" bakinta ta turo tana gunguni. Sai da ya bari ta gama ya cafke lips ɗin nata ya fara kissing ɗinta....daga haka na basu waje gani za su yi babban al'amarin.

Bayan wani lokaci sai ga Yaya Sadauki da Zahrah a hannunsa kamar wata baby ta wani lafe jikinsa sai wani kukan shagwaɓa take shi kuma yana aikin sorry, I'm sorry, is ok, sorry. Toilet suka nufa a tare can suka fito ɗaure da towel alamun wanka suka yi. Kaya marasa nauyi suka sa, nan Zahrah tace itafa ya zauna girki za ta je tayi, ƙin yadda yayi yace suje tare, tare suka shige kitchen ɗin suka yi girkin yana kama mata wani abun. Bayan sun gama suka yi wanka suka yi sallar Azahar sannan suka yi lunch. Yinin ranar tare suka yini, kusan komai tare suke suna shan love ɗinsu.


*A week later (Bayan sati ɗaya)*

Kasancewar Yaya Sadauki hutunsa ya ƙare yau yake shirin komawa bakin aikinsa. Cikin shigar maroon coat with white inner, Sai maroon trouser da necktie, sosai yayi fresh abunsa ga wani sheƙi da sumar kansa da ta sha gyara take. Biye da shi Zahrah ce ɗauke da briefcase ɗinsa maroon colour sai kuma glasses ɗinsa. Tafe suke suna murmushi zahrah na faɗin "shi ne ba za ka jira Ni ba ko? Allah Allah ma kake ta tafi ka bar gidan ko Azizy?" Kamar motar da aka takawa birki yace "I'm so sorry Charming Angel, kada ki min sharri." Wani irin kallo da ya kusa Zauta shi ta aika masa. "You're forgiven Azizy, yanzu ficewa za ka yi ka bar Ni Ni kaɗai a gidan ka bar Ni da kewarka?"
Kalar tausayi ya koma lokaci guda yace "Nima ba don raina bane, ina so na samar muku da jin daɗi a duniya ta yadda ba zan gaza muku a kowanne fanni na rayuwa ba, amma ji nake kamar na dawo na zauna, anya ma zan iya aikin nan ba kya a jiki na?"

"Kar ka min zaƙin baki, za ka iya mana, na yarda da kai na yarda da kaina, babu wata mace da za ta shiga tsakaninmu, duk wacce ta kalleka ban yafe mata ba."
Dariya yayi yace "idan ma ta kalle Ni ke kaɗai idanuwana ke kallo, so relax my baby girl, ba zan jima ba."

Isowarsu parking space yasa ta ɗan dakata da tafiyar ta wani shagwaɓe fuska tace "I'll miss you badly Darling, Allah ya tsare min kai ya ba ka nasara kan kowanne al'amari da zai ɓullowa rayuwarka, Allah ya kare min kai daga sharrin masu sharri, ya haɗa ka da alkhairai masu tarin yawa."
Yana shirin shiga motar ya dakata tare da dafe chest ɗinsa yace "Amiiin my precious, your prayers were answered bi'ithnillah." Shiga motar yayi ta miƙa masa briefcase ɗinsa sannan ta rufe motar. Kunna motar da yayi yasa ta fara waving masa hand har ya fice. Gateman na rufe gate ɗin ta juya cike da kewar mijin nata.

*Yaya Sadauki*

Tunda ya isa office nasu na NIC yake amsar gaisuwa da fatan alkhairi haɗi da Barka da dawowa aiki. Yana shiga office ɗinsa ya fara solving abubuwan da ke gabansa, ba shi ya tashi ba sai around 12pm, lokacin ma saboda kusantowar sallah ne. Sai da yayi Sallah ya dawo kan aikinsa babu ji babu gani.

An hour after Yaya Ishaq yazo wurin yaya Sadauki, aikin ya ajiye saboda muhimmiyar magana yake so yayi. Tuntuɓarsa yayi akan labarin fasa aurensa, amsar da ya ba shi yasa ya yarda cewa lallai abun babba ne kuma babu shakka akwai lauje cikin naɗi.
Yaya Sadauki yace "Amma ta yaya aka samu ka dawo daidai?"
"Akwai SHEIKH Imam Nasir, shi yayi wannan aikin tuƙuru wajen ganin an tarwatsa aikin."
"Ma sha Allah, abunda nake son sani kenan. Allah ya kiyaye gaba, yanzu dai fatan ba ka jin komai game da aukuwar al'amarin?"
Murmusawa Yaya Ishaq yayi yace
"Ai babu komai yanzu kam, na amshi ƙaddarata har ma na samu sabuwar catch, Allah yasa ba za ku hana ni ba?"
Da ayar tambaya Yaya Sadauki ya kalli Yaya Ishaq yana jiran karin bayani.
"Eh fa officer, Nasreen nake so ku ba ni."
Cikin jin daɗi Yaya sadauki yace "Babu komai ku daidaita kanku mu zha biki."

Duk wannan surutun da Yaya Sadauki yayi ya yi ne saboda ya kau da hankalin ya Ishaq kar ya fahimci cewa akwai sa hannun wani daga cikin familynsa a fasa aurensa da Zahrah. Bai daɗe ba ya tafi, shi kuma ya koma kan aikinsa bayan ya ƙira Sheikh Imam Nasir sun yi magana sun kuma tsaida ta ina za su fara.

*Toh jama'a, da alamun za a yi walƙiya..kuma za mu gani magautan cikin familyn, to jama'a kar a manta a ci gaba da reacting da sharing fisabilillah.*
[01/05, 8:59 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 6️⃣6️⃣






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*

Sai da ya ga ya ci rabin aikin da ke gabansa ya fara haɗa briefcase nasa, komai da ya san ya zo da su ya kwashe, har ya kusa fita ya tuna da phone ɗinsa da ya bari a kan cupboard, da sauri ya juyo ya ɗauka sannan ya fice, gaisuwar ma'aikatan yake amsawa fuska babu yabo ba fallasa yayin da ya nufi parking lot, motarsa ya shiga sannan ya ja ta sai gida.

Tun da ta jiyo ƙarar buɗe get ta miƙe tsaye tare da ƙarewa kanta kallo gaban mirror. Ɗan juyi tayi tukun ta murmusa har kumatunta na lotsawa, ba ta ankara ba taji an taɓa handle na ƙofar, da sauri ta daidaita tsayuwar ta tare da ƙoƙarin nufar door ɗin. Tana ƙarasawa tayi hugging nasa yayin da shi ma yayi hugging nata tightly, they spend some minutes maintaining their contact kafin tace "You're welcome My Noor, sannu da dawowa."
Ƙamshin da gashin kanta ke fitarwa ya shaƙa tare sauƙe numfashi yana mai cusa kansa a tsakanin wuyanta, actually the scent nearly make him fall, cike da kasala yace "I missed you terribly My charming angel, the distance make me feel like we're apart for long, if not because of money ba zan ke fita ko ina ba, just staying by your side will make me survive."
A hankali ta fara ƙoƙarin raba jikinta da nasa tana faɗin "the house seems to be so dull because you're apart, I missed you more." Ta faɗa tare da ranƙwafo da kansa ƙasa tayi kissing face ɗinsa.
"Na san ka gaji da yawa, bari na fara haɗa maka ruwan wanka sai ka ci abinci, ko abincin za ka fara ci?"
"Nope, lemme fresh up first Sai in ci daddaɗan girkin matata."

Briefcase ɗinsa ta amsa daga nan ta wuce closet ta ajiye masa. Toilet ta nufa ta haɗa mai ruwan, lokacin da ta fito already ya rage kayan jikinsa daga shi sai towel sai kuma phone ɗinsa da ke hannunsa. Miƙa mata phone ɗin yayi ya ja ya tsaya, kan bedside drawer ta ajiye, juyowar da za ta yi ta gan shi tsaye ya harɗe hannayensa kamar me jiran abokin faɗa. Ɗauke da maɗaukakin mamaki tace "Noor??" Gira ya ɗage mata yana faɗin "uhm?"
"Na haɗa maka ruwan fa" ta faɗa a shagwaɓe.
Yadda tayi maganar ya kwaikwaya sannan yace "To ai ba ke nake jira ba?" Shagwaɓa? She asked herself, sosai jikinta yayi sanyi kamar ta shiga ruwan sanyi, a hankali tace "Ni kuma Noor?"
"Yea, ke mana" ya faɗa cikin halin ko in kula.

A shagwaɓe tace "nifa na yi wanka na, ba ka ga har na yi kwalliya ba?"
Ta faɗa tana dudduba jikinta tare da son ya fahimta.
In his naughty voice yace "Allah Nikam ki zo mu yi, in ba haka ba yau ba zan yi wanka ba kuma abincin ma ba zan ci ba."
Dafa kanta tayi tana faɗin "Ya salaam" babu yadda ta iya haka ta haƙura ta fara ƙokarin rage kayan jikinta, da sauri ya matso kusa da ita yana ƙoƙarin tayata...abunka da wanda yake hannu, tun kan a shiga toilet ɗin ya fara lalubata, konda suka shiga wankan ma dai ba a samu tsinana wankan ba dai....can kusan rabin sa'a sai ga su sun fito tare hannunsu sarƙafe da na juna.

Mita haɗi da shagwabar da take masa yasa ba yadda ya iya ya haƙura suka shirya cikin kayan shan iska. Kai tsaye dining suka nufa tare, kamar yadda ya fara sabar mata da ci a plate ɗaya haka ta zuba musu sannan ya ja kujera ya zauna. Lap ɗinsa yayi pointing mata ganin tana shirin jan kujera ta zauna, babu yadda za ta yi ta yi matsuguni kan laps ɗinsa. Shi yayi feeding ɗinau su biyun yana ta wasu da sumar kan Zahrah wacce ta ba ta rufe ta ba. Sun shafe wani lokacin kafin suka bar dining suka dawo parlour. A nan ma dai shagalinsu suka sha gwanin ban sha'awa yadda suke nuna ƙauna da tarairayar junansu, abun sai dai ace ma sha Allah.

Zahrah wacce ke kwance a kan chest ɗin Yaya Sadauki shi kuma na jingine da ɗaya daga cikin kujerun parlourn, gyarawa kanta muhalli tayi tana faɗin
"Habiby ka san me?"
Kai ya girgiza mata yana sauraron me za ta ce
"Ɗazu an yi baƙi"
"Su waye?" Ya tambaya da sauri.
"Rumana ce ta zo ɗazu ita da Ammie, sun bar saƙo sun ce a faɗa maka wai ka fara shirye-shiryen ƙara aure, Ni kuma na shirya barin..." Katse ta yayi yana faɗin "What?" Cikin ɗaga murya. Kai ta jinjina masa alamar eh yadda ka ji, sai kuma ta shagwaɓe murya tare da sakin wani ɗan Marayan kuka
"Yaya sati guda ne fa da ƴan kwanaki da aurena, za ka iya auren wata bayan Ni?" Hankalinsa ne ya tashi da yadda take kukan, ɗago ta yayi tare da mannata da jikinsa har suna iya jiyo sautin bugun zuciyar junansu. A hankali ya fara tapping bayanta yana faɗin "Ya Isa my Angel, ki yi shiru mana."
Rage sautin kukan tayi tace "Ni dai ka faɗa min kawai, za ka aureta da gaske Yaya?"
"Ba kya so na aureta ne?" Kai ta gyada masa tana sauƙe ajiyar zuciya.

"Is ok" ya ba ta amsa yana manna mata kiss a lips nata, babu jimawa salon ya sauya....some minutes later bayan sun koma daidai, a tare suka miƙe suka yi wanka, bayan sun fito nan ma ta tada wani sabon kukan wai ya faɗa mata gaskiya.
Murmushi yayi yace "kina tunanin an yi zuciyar Ali ne ba don Zahrah ba? Kina tunanin Ali zai zauna da wata bayan Zahrahn sa? Noooo" ya ba wa kansa amsa "that can never be possible, Ali na Zahrah ne kaɗai, kamar yadda Zahrah ta kasance ta Ali shi kaɗai ko kin manta an yi zukatanmu ne saboda juna?"
Kai ta gyaɗa masa cike da gamsuwa.

"Good girl!' ya ja kuncinta "So my friend, have yourself rest assured that..you've a lover whose love can never be derailed, ki sani bayan ke in dai ba wai a cikin zanen ƙaddarar rayuwarmu ba, ba zan zauna da wata mace ba saboda ke ɗin ɗaya ce tamkar da dubu, kin fiye min duk matan duniya shiyasa na zaɓi dauwama da ke ɗaya a matsayin matata har Aljanna. So ki ajiye batun wata Rumana kinji?"
Kai ta gyada masa sannan yace "kin son ba na son magana da kai ko?" Da sauri tace "I'm sorry "
Cike da so da kuma ƙaunarta yace "duk wanda ya ƙara miki kwatankwacin wannan maganar kice masa don ke kaɗai aka yi Ni, su daina ɓatawa kansu lokaci kin ji?"

Kai ta ƙara gyaɗawa tace "Yaya? Dama kana so na haka? Wallahi ji nayi kamar na haɗiyi zuciya na mutu da suka faɗi haka, ina tsananin kishinka Noor, ba na son wata macen ta raɓeka, na fi so na kasance a tare da kai Ni ɗaya, kai ɗin rayuwata ne, daga ranar da aka ce wani ya shiga tsakaninmu i can lost my..."
"Shhhh.." ya katseta "Ki daina min fatan hakan, in dai babu ke kin san babu Ni, we're two bodies sharing a single heart and life."
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙara lafewa jikinsa
"So you're my soulmate?" Ya gyaɗa mata kai "Then I can sacrife everything I own to see that this Soul remain ours, I want you to be only mine, mine forever. Ana uhibbuka Ya habiburRouhwalqalb.."
Peck ya yi mata kan hancinta sannan yace "love you more wify."

Lokacin laasar da yayi yasa suka yo alwala, shi ya fita mosque ita kuma ta yi Tata a gida. Bayan ya dawo ma soyayyarsu suka sha kamar ba gobe, shirin barin jikinsa da tayi yasa yace "Ya dai? Where do U think you are going leaving your soulmate alone?" Fararen idanuwanta ta juya tana faɗin "I want to prepare tasty something for soulmate" ya ba ta amsa da "if that's the case, then I'll help you do it."
A shagwaɓe tace "Kana son rage min yawan lada Soulmate"
"Ke kuma kina son toshe min hanyar samun lada ko?" Dariya tayi tace "Ai ban ce kada ka yi ba, muje Allah yasa mu yi tarayya cikin ladan"
"Ameen My other half." Ya faɗa yana hugging nata, ajiyar zuciya suka sauƙe a tare tukun suka raba jikinsu, hannunsa sarƙafe da nata suka wuce kitchen ɗin, Apron ta ɗaura masa sannan ta ɗaura, nan suka fara aikin suna shan soyayyarsu, ba su suka gama ba sai ana kiran sallar maghrib, ita ta jera abincin a dining ta bar na Baba mai gadi ya mika masa, sai da suka watsa ruwa tukun suka yi alwala, shi ya wuce masallaci da abincin Baba mai gadi, ita kuma ta tayar da Sallah.

Ba ta sa a ranta cewa zai dawo ba saboda ta san sai ya yi Isha' tukun, hakan yasa ta zauna kan praying mat, Alqur'ani ta buɗe tana karantawa cikin zazzaƙar muryarta, kamar daga sama ta ji wani irin sauti maras daɗi sauraro. Duk da ta tsorata amma sai ta saka a ranta la'alla kunnenta ne ya jiyo haka, dalilin hakan yasa ta ci gaba da karatunta. Aya ɗaya ta ƙara a shafin tilkar-Rusulu (Baqara) gabaɗaya haske ya ɗauke, tsoro ne da firgici suka mamaye zuciyarta lokaci guda, a hankali ta tashi ba tare da ajiye Alqur'anin ba ta fara takawa a hankali tana laluma inda ta ajiye phone ɗinta, ba ta ankara ba taji ta yi karo da abu, "Subhanallah" kawai ta furta, lokaci guda taji abun ya saki ƴar ƙara, a tsorace ta fara tambayar kanta wannan kuma wani irin ƙara ne?"

Dakewa tayi duk da irin tsoron da take ji tace "Waye wannan?" Cikin murya maras daɗin sauraro da ba a iya banbance jinsin mai ita aka ce "Abunda kika tsokano ne"
"Ni kuma?" Ta tambaya
Dariyar shaƙiyyanci aka yi sannan aka ce "A'a Ni, Ni, nace Ni, hhhhh" lokacin kam iya tsoro Zahrah ta gama tsorata don a yanayin nan ta san tana motsawa fitsari za ta saki, cikin ranta ta fara karanto ayoyin tsari har dai harshenta ya tasirantu da kwaikwayon hakan...tana fara yi da ƙarfi taji an ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login