Showing 105001 words to 108000 words out of 157517 words
siyasa ne mijin.
Rumana ce tafe cikin ado da kwalliya yayinda take taku ɗas ɗas, ɗas kamar mai tsoron taka ƙasa tana tafe tana rangaji da murmusawa da alama dai tana cikin farin ciki. Wata makekiyar mota ta shiga wacce sam ban ma lura da ita ba, tana shiga kuma aka ja motar aka bar estate ɗin da ita.
*ZAHRAH*
Gabanta ne ke tsananta bugu tun safe, yayinda ruɗu da fargaba suka mamaye illahirin rai da ganganar jikinta. Fahimtar hakan yasa Nasreen ta zauna kusa da ita tana mata ƴan labarai don kawar mata da tunanin da ya addabeta amma sam babu ci gaba.
"Sister, don Allah ki cire komai a ranki, duk da na san hakan zai yi wuya duba da yadda kika ɗauki son duniya kika ɗaura kansa amma yayi disappointing naki, ki yi haƙuri ki mayar da komai ba komai ba, fatan mu Allah yasa a samu sauyi in an kai ki gidan."
Hannun Nasreen Zahrah ta riƙe tana ƙanƙamewa kamar an ce da ita Nasreen ɗin za ta gudu ne ta bar ta. A hankali tace
"Do you know what? Na riga na cire damuwar Ya Ishaq na ajiye a gefe, it's only this morning nake ji na ba daidai ba, my heart is beating faster and the rate i respirate also change, ina tunanin akwai abun da ke shirin faruwa da ni yau, sai dai ban san ko mene ne ba, amma believe me Nasreen, something i don't even know is about to happen."
Cikin sigar kwantar da hankali Nasreen ke shafa bayan Zahrahn tace "Calm down Babe, nothing bad will happen in sha Allah, alkhairin Allah ya bibiyi rayuwarki amaryarmu, i'll miss you all" ta faɗi ƙarshen da ƙarfi har sauran suka ji.
Nainarh ce ta juyo tare da kallon Nasreen da Zahrah tace "Aunty sama aunty ƙasa, Aunty ya kama bakin yarinyar carrr...few hours dole a martaba ni." dariya dukkansu suka yi, Rumaysa ma ta juya ido ta ƙara da faɗin "Cas abinmu, kowa dai ya martaba kowa tunda abun kusan kowa an taɓo shi, ni bari ma na kame don zuwa jimawa na zama yayar Zakiyya."
Aunty Na'ima ce ta dakatar da su da faɗin "ku kuka sani dai, amare marasa kunya, da a ce lecture nake muku da duk kun yi tsit kuna sunnar da kai, duk za ku yi bayani."
"Kai Aunty Dan Allah, mu meye namu a ciki?"
"Babu komai" ta ba su amsa "Anjima duk za a kai kowacce gidanta sai naga ta iya shege ko?, ungo wannan, ku samu ku shanye anjima ku yi wanka."
Caraf Zakiyya tace "Ni fa Allah Aunty na gaji da wannan jiƙe-jiƙen sai kace wasu..." ba ta ƙarasa ba Aunty Na'ima ta dakatar da ita tana riƙe baki "E..lallai Zakiyya, dole ki gaji kam, duk iya ƙoƙarina na ganin na kai kowacce gidanta a mutunce shine kike ce min kin gaji? Ba shakka, to wallahi sai kin sha, ka ji min yarinya...ke da kan ki za ki min godiya."
Dariya suka kwashe da ita suna pointing Zakiyya da yatsa.
"Maza ku yi ku shanye ku ba ni, kafin Mimie tace ban ba wa ɗiyarta kulawa ba" ƙara fashewa da dariya suka yi kamar cikinsu zai fashe. Haka dai suka ci gaba da shirmensu Aunty Na'ima na taya su har ƙarfe tara tayi, nan aka kawo breakfast ɗinsu wanda fruits ne zalla a menu ɗinsu, bayan sun yi breakfast Zahrah ta ɗauko wayarta da ta kashe ta kunna kamar wanda aka ba ta umarnin hakan.
Komawa tayi ta miƙe kan sofa tare da sauƙe ajiyar zuciya, kamar dai yadda tayi tsammani babu wani saƙo daga Ya Ishaq, whatsapp, I.G, facebook kai har twitter babu alamar wani saƙo daga gareshi kuma tana da tabbacin yaga saƙonninta. Tsaki ta ja tare da shiga private folder ɗinta kamar yadda take a kowanne lokaci musamman in tana cikin damuwa, kewar Little Sadauki ne ta hanata ci gaba da kallon ta fito waje, kai tsaye parlourn Hajjaty ta ƙarasa tana dudduba Aunty Salma don ta san dai ba zai wuce yana tare da ita ba. Can idonta ya hango shi fuska haɗe kamar ba ya son ganin kowa, "Little" ta ƙira sunansa, kamar wani zararre ya miƙe cikin tafiyarsa irin ta yara ya ƙaraso tare da hugging Zahrah.
Itama murmushin take ta ɗago shi sama tana faɗin "Na yi missing naka, Aunty Salma ta ƙwace min kai, ina Baby Aryan?"
Kamar ya san me take faɗi ya kwaɓe fuska yana gwalatunsa wanda ciki babu abunda ta fahimta, kumatunsa ta riƙe tana shafa kansa "Is ok, ba zan bar kowa ya ƙara ɗauke min kai ba my little, mu tafi tare ko?"
Kai ya gyaɗa daga haka ta juya, matan da ke parlourn sai yabawa suke da ita musamman da aka sanar da su ai ita ke kula da yaron tun mutuwar uwar.
Kasancewar Little a tare da ita ya rage mata abunda take ji sosai. Hakan yasa ta sake kamar babu abunda ke faruwa.
Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe mazajen gidan suka fara shirye-shiryen tafiya ɗaurin aure, da yake ma a masallacin estate ɗin za a yi bayan an dawo daga Jumu'at prayer yasa kowa ya ɗau harama.
Sha biyu daidai motoci suka fara fita daga estate ɗin zuwa masallacin juma'a. Bayan an sauƙo daga jama'a kuma aka fara hallaruwa a masallacin estate, manyan mutane a ƙasar da kewaye har da fararen fata abokan kasuwancin Alhaji Baba sun samu halartar ɗaurin auren.
*ZAHRAH*
Sallar azahar ta gabatar yayin da wayarta ke hannun Little Sadauki yana buga game, tana idarwa ta jiyo shigowar saƙo, sai lokacin ta tuna ashe ta bar data a kunne, ba ta miƙe ba sai da tayi zikirorin bayan sallah tukun ta miƙawa little hannh, kamar ya sani ya miƙo mata phone ɗinta, whatsapp messages, "From who?" ta tambayi kanta.
Yatsarta ta kai ga message ɗin ta shiga, tarin videos ne da kuma pictures from Ya Ishaq, da sauri ta danna kansu suka fara downloading yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri saboda rashin sanin takamaimai me za ta gani.
Ganin sun gama yasa ta danna video na farko sai dai kafin ta ƙarasa kalla ta faɗi ƙasa daga ita har wayar tata a sume, hankalin ƴan'uwanta tuni ya dawo kanta, sai tashinta suke amma shiru, tuni suka fashe da kuka suna faɗin "Ki tashi please sister..". Rasa ma me ya kamata su yi mata suka yi, saboda haka suka kai kallonsu ga wayarta sai dai secreen ɗin ya fashe kuma ma ta ɗauke gabaɗaya. Gabansu ne ya ci gaba da bugawa ga shi kuma sun rasa me ya kamata su yi sai suka saka ta gaba suna kuka a daidai gaɓar Nasreen ta shigo, abunda ta gani ya matuƙar tayar mata da hankali, da gudu ta fita ta nufi Aunty Madina da ke shirin fita daga parlourn.
"Lafiya Nasreen? Ke kan ba za ki taɓa hankali ba." yanayin da ta ga Nasreen ɗin kuma yasa ta ƙara faɗin "Lafiya?" da ƙyar Nasreen ta iya furta "Zahrah" cikin ruɗu ta nuna mata ƙofar ɗakin da suke.
"Me ya faru da Zahrah?" at this time Nasreen can't reply, saboda haka ta ja hannun Aunty Madina zuwa bedroom ɗin nasu. Abun da ta gani itama sosai ya kaɗar mata da hankali, da ƙyar ta samu ƙwarin guiwar furta "Help me pick her to car." haba, tashin hankali wai ba a sa masa date, Nasreen ce kawai ta fahimci saƙon Aunty Madinah saboda haka ta fara kiciniyar ɗaga Zahrah amma sun gagara, shigowar Aunty Na'ima da Aunty Salma yasa suka taimaka aka fito da Zahrah wacce ke a halin rayuwa ko mutuwa.
Aunty Madina da kanta tayi driving yayin da ta sa Aunty Na'ima komawa ta kula da amaren ita da Aunty Salma kuma suka wuce asibiti da Zahrah. Yanayin da likitoci suka gan ta yasa suka amshe ta da gaggawa kan gadon marasa lafiya aka yi ciki da ita zuwa A&E don ba ta taimakon gaggawa su kuma su Aunty Madina suka tsaya a bakin ward ɗin sai kai da komawa suke suna fatan Allah yasa dai lafiya.
Kafin ka ce me tuni labarin faɗuwar Zahrah ya karaɗe estate ɗin sai dai bai kai ga isa kunnen mazajen gidan ba tunda yanzu suka fara dawowa daga sallar juma'a kuma kai tsaye masallacin estate suke wucewa. Hajjaty da hankalinta ya gama tashi haka ta sa Nuwairah jikar ƙawarta ta ɗaukota zuwa asibitin, Nasreen dai da sauran ƴan'uwanta hankalinsu tashe yake haka nan uwarɗakin nasu ma da ke ƙoƙarin kwantar musu da hankali ba a daidai take ba. Nasreen ce ma ta kula da wayar Zahrah ta ɗauke ta ta ajiye ƙasan wardrobe.
*ABATCHA ESTATE MOSQUE*
Sosai masallacin ya cika maƙil, haka nan sararin masallacin ma cike yake da mutane masu shaida ɗaurin auren, masallacin ya tara iyalan Alhaji Baba da kuma angwaye da masu karɓa musu aure. Ganin kowa ya hallara yasa aka fara shirye-shiryen ɗaurin aurarraki. Babu ɓata lokaci aka ɗaura auren Ya Auwab da Rumaysa, Ya Taj da Zakiyya, Kausar da Zahid, Jidda da Humaid, Hibba da Ashir......
*Show me love please*
*React and Share Fisabilillah.*
[17/04, 8:46 AM] Diamond Bhatool:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣0⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
Nan aka buƙaci ango ko mai karɓan auren Zahrah amma shiru kake ji babu wanda ya fito, can dai Dad ɗin Ya Ishaq ya turo shi gaba shi kuma sai nonnoƙewa yake, mamaki da al'ajabi suka cika ɗaukakin mutanen da ke cikin masallacin.
"Wuce ka je mana, shashasha kawai!"
Dad ya faɗa ya zungura ƙeyar Ya Ishaq da ke famar haɗe rai yana huci kamar wani fusataccen zaki. Daddy ne ya dakatar da shi yana faɗin
"Lafiya dai? Ko ba ya so ne?"
Cikin jin kunya Dad yace "Rabu da shi lafiya ƙalau, zallar iskanci ne. Mu ƙarasa a ɗaura."
Ƙara noƙewa Ya Ishaq yayi hakan ya ƙara ɓata ran Dad, tas! Kake ji ya wanke shi da wani zazzafan mari ganin yana so ya ɓata masa suna a idon duniya. Kallon kallo aka fara aikawa juna cikin masallaci yayin da kowa ya zaro ido waje ɗauke da tarin tambayoyi a fuskokinsu. Zafin marin ne yasa Ya Ishaq babu shiri ƙarasawa ga maɗaurin auren yayin da mamaki da al'ajabi suka cika ransa, wai yau shi Dad ya mara a bainannas?.
Kansa ya juyar yayin da Daddy ke faɗin "Ni Alhaji Umar Abatcha na ba ka auren ɗiyata Fatima Abdulkarim Kuru...." bai idasa kammalawa ba Ya Ishaq ya sunkuyar da kai, nan maganganun sabuwar masoyiyarsa suka fara dawo masa "Kada ka yarda ka aureta, ka ce A'a, maza a'a!" kunnensa ya toshe jin ta ko ina sautin muryarta na fitowa, a karo na biyu Daddy ya ƙara maimata abun da ya faɗa sai dai wannan karo a hasale Ya Ishaq ya miƙe yana faɗin "Ba na buƙatar auren ɗiyarku, ba na buƙata, a kai gaba ko da mai so." yana ida faɗin hakan yayi yunƙurin juyawa zai fice, caraf Dad ya cafko wuyan rigarsa "Hauka kake ne Ishaq? Wallahi ba ka isa ba, ba ka isa ka zubar min da mutuncina ba, dole ka aureta ko ba ka so, in ba haka ba ka faɗa mana dalilin sudden change na ra'ayinka gareta kowa yana sauraro."
Juyowa Ya Ishaq yayi yana faɗin "Haka kawai ba zan aureta ba Dad, kada ka tursasa min..."
Tas! Tas! Dad ya wanke shi da mari ta ɓarin fuskarsa ta hagu da dama, a fusace ya ƙara da faɗin "Wallahi ka dawo a ɗaura auren nan, ba ka isa ka mayar da ni ƙaramin mutum ba." ƙara cakwamo Ya Ishaq Dad yayi kamar wanda za su yi dambe, hakan yasa Daddy zuwa ya ɓamɓare hannun Dad daga Ishaq, duk zafin rai irin na Daddy tuni yayi disappearing kamar ba shi ba ya dafa kafaɗar Dad yana faɗin "Ka ga Alhaji wannan ai ba abun rashin hankali ba ne, yaron nan shi ya gani ya ce yana so, to tunda yanzu baya buƙata inaga a bar shi."
"A bar shi fa kace Alhaji Umar, wallahi bai isa ba, da mutuncina ba zai zubar min ba."
Alhaji Baba da ya gagara furta uffan sai lokacin ya dubi Ya Ishaq da ya sunkuyar da kai ƙasa, lokaci guda kuma yaji abun banbaraƙwai, wani namiji da suna Hajara. Cike da son ɓoye ɓacin ransa ya ƙira Daddy da Dad, sai kuma ya ambaci sunan Ishaq a ƙarshe. Kwarjinin Alhaji Baba yasa dukka suka zauna a gabansa nan ya fara magana cikin sanyin murya.
"Babu komai, inaga tunda yaron yanzu ba ya ra'ayi a bar shi hakan zai fi gudun kada a yi abun kunya ko a ɓata zumunci, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."
"Amin" suka amsa a tare yayinda Dad ke aikawa Ya Ishaq kallon za mu haɗu. A kunyace Dad yace "A yi haƙuri Baba, Allah ya ƙara girma, kai kuma" ya maida dubansa ga Ya Ishaq "Sakarai sai ka fice ka ba mu waje, in sha Allah Zahrah ba za ta tozarta a dalilinka, yanzu ba da jimawa ba za a ɗaura aurenta da Shureim, ɗan ɗan'uwa na, kai kuma kaje za ka gani."
Babu kunya sai ga Ya Ishaq ya miƙe sandaran ya yi waje, sosai mamaki da al'ajabi suka ninniƙe zukatan mutanen da ke cikin masallacin, thank God duk makusanta ne da ba a san yadda abun zai munata ba.
Dad ne ya mayar da dubansa ga Alhaji Baba, a kunyace ya fara magana cikin sanyin murya yace
"Baba don Allah a yi haƙuri, ba zan taɓa so dalilin wannan gidahumin yaron a fasa auren yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba, ba zan so dalilinsa zuciyarta ta karye ba, saboda haka.." sai kuma ya ja gauron numfashi kafin ya ci gaba. "Don Allah ina neman alfarmar a ɗaura da ɗan ɗan'uwana Shureim, ina da tabbacin zai riƙeta kuma na isa da shi."
Shiru ne ya ɗan wanzu sakamakon batun da suka tsinkayo daga Dad yayin da can mutanen da ke harabar masallacin suka riga suka fara watsewa, a tunaninsu an kammala ɗaura aurarrakin tunda sun ji shiru.
*Reactions ɗin ku yasa na rage tsayin update, in na ga sauyi zan ci gaba...*
*Thank u so much, Diamond Bhatool loves u.🥰💔*
[19/04, 8:44 PM] Diamond Bhatool:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣1⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
Numfasawa Alhaji Baba yayi bayan nazarin da yayi na tsawon lokaci kana yace, "Ga ɗan'uwan mahaifin yarinyar" nan ya Nuna Kawu da shima ya sanya farar shadda tas, "a yanzu dai ni ba ni da cewa sai abun da yace."
Da sauri Kawu yace "Haba Alhaji, ai duk abunda ka yanke ya yi, yarinyar nan duk kuna da iko kanta."
"To babu damuwa, mun amince za mu ba da auren Zahrah ga ɗan ɗan'uwanka kamar yadda ka buƙata, idan ya so bayan ɗaurin auren sai a zauna."
Fuska ɗauke da murmushi Dad yace "Madallah, na gode Baba, Allah ya ƙara girma."
A zuciyarsa ya amsa daga nan aka fara faɗin siga ta ɗaurin aure sai da aka zo gaɓar karɓan aure wani mutum ya shigo cikin masallacin babu ko sallama a bakinsa, cike da ƙasaita yake taku duk da irin ƙasƙantattun kayan da ke jikinsa yayinda ya rufe fuskarsa da baƙin mask.
Ɗauke da tsantsar mamaki suke kallonsa yayin da Daddy ya gama razana da bayyanar wannan mutumin sai di shi bai bi ta kan kowa ba sai ma wani mugun kallo da ya cillawa Kawu, tuni ya sauƙar da kansa ƙasa. Zama yayi yana fuskantar Alhaji Baba yayinda su kuma suka dakatar da karanto sigar kamar yadda suka fara.
A matuƙar tsorace Daddy ya miƙe, haka Alhaji Babba suna ƙarewa mutumin ido. Tabbas da ba don Ɗansu ya rasu ba, kuma sun tabbatar da hakan ba da sun ce wannan shine, amma ai ɗansu yana da hasken fata, wannan kuma duhun fata gareshi amma ko ma meye dai, bari a gama abunda ake za su bincika. Maganar Alhaji Baba ita tasa suka koma mazauninsu tare da zama.
Shi kansa Alhaji Baba kansa ya gama kullewa haka sauran ƴaƴansa, babu shakka duk wanda ya san waye ne Sadauki babu shakka yaga wannan mutumin zai iya alaƙanta shi da shi, idanuwansa da girarsa sune suka ja hankalinsu, haka kuma ƙirar jiki da yanayin tafiya, abu ɗaya zuwa biyu da za su su cire hakan a ransu shine, Sadauki matacce ne, wannan rayayye ne sai kuma kalar fata da ta banbanta.
"Bawan Allah lafiya za ka shigo mana babu sallama? Ai ko ba don mu don albarkacin masallaci ne ɗakin Allah ka yi sallama." Alhaji Baba ya faɗa yana tsayar da ƙwayar idonsa cikin ta baƙon.
Ba tare da ya ba shi amsa ba ya sa hannunsa wanda shima ya kasance baƙi ƙirin kasancewar wani sashe na hannun ya kasance da haske yasa suka fahimci cewa ba ainihin kalar fatar mutumin ba kenan. Ɗauke da al'ajabi kan fuskarsu da kuma tsoron da ya mamaye zukatansu haɗi da fargaba suke kallon mutumin. A hankali ya fara zare baƙin face mask ɗin da ke fuskarsa. Ba tare da wani ɓata lokaci ba ɗaukakin dattijan familyn suka miƙe tsaye suna dafe ƙirji. Ba su tsinke da mamaki ba sai da suka ga ya zaro white handkerchief daga aljihunsa ya fara goge fuskarsa....kafin ka ce me kuma wannan baƙin gabaɗaya ya ɓace kamar wanda aka wanke tas.
Sosai suka shiga ruɗu har Alhaji Baba na nuna shi da yatsarsa wacce ke karkarwa yayinda ya gagara