Showing 27001 words to 30000 words out of 157517 words
baya son kuka musamman na ɗiya mace, macen ma wacce tayi silar zuwan sa duniya. Sanyaya murya yayi kana ya ƙara hugging nata tightly, he so much love her, yana son mahaifiyarsa ko yaya take, amma kuma ɗabi'unta kawai yake so ta gyara.
“Ba haka bane Mommah, ina jin zafin abun da ke faruwa indeed na ma Fi ki jin zafi amma ke har yau kin kasa fahimtar cewa masu zuga ki kina aikata ire-iren abubuwan nan wallahi ba son ki suke ba illa iyaka son su ga mutuncin ki ya zube.”
Ba tare da ta yadda ba sai dai kawai tana tsoron wannan damar ta kuɓuce mata yasa ta ce
“Is alright sit down let's talk.” ba musu ya zauna gefenta kamar yadda ta umarce shi.
“Na ji wata magana da Alhaji Baba yayi ɗazu amma ina so ka tabbatar min ba haka bane”
Tsaf ya fahimci a kan me take magana amma sai ya kame ya ce
“Me kenan Mommah?”
“He Said that zai haɗa auren ka da yarinyar nan da tayi kwantai har take bin maza don na tabbata abun da ya faru ma shirin ta ne”
Kamar zai yi kuka yake kallon Mommah. Tabbas wanda yayi nisa ba ya jin kira amma sai ya kame ya ce
“Yea haka ne Mommah, akwai matsala ne?”
“Tambaya ta ma kake akwt matsala Haidar?” ta faɗa a ɗan zafafe.
Ba tare da ya ce komai ba ya riƙo hannunta ya haɗa da nasa.
“Mommah Please understand, ba Wai Alhaji Baba ne ke da laifi ba, hakan da yayi adalci ne, ki ƙiyasta a ce Nainarh ce haka ta faru da ita kuma kawai sharri aka mata, kina tunanin zata samu wadda zai aure ta ne? No Mommah kada ki ce zaki ja da wannan hukunci, Ni na riga nayi accepting ma kawai kema ki share, and Zan faɗa miki wani abu da baki sani ba wallahi Mommah mutanen da ke ɗaura ki hanya ba mutanen kirki bane, kuma ki sani abinda ya faru ma suna daga cikin waɗanda suka shirya shi, ki yi tunani a kai.”
Cikin rasa Madafa ta ƙara duban yaya Sadauki sannan tace “Ba wai bana son ka yi auren nan bane, yarinyar da aka Baka ne, ɗiyar Hajiya Babba fa, matar da ke ƙwace duk wani abu da zan mallaka, kai kanka ƙoƙarin raba Ni take da kai son, Ina ga in ka auri ɗiyar ta, get something here son, in ma zaka yi auren ka auri ɗiyar masu ƙauna ta mana, ga ƴaƴan Hajiya Baraka da Saudatu amma sai ƴaƴan Hajiya Babba?”
“Mommah, ki fahimci wani abu, Hajiya Babba ba ta nufin ki da sharri ke ce ba ki fahimce ta ba saboda huɗubar da ake miki, Mommah don Allah ki gane gaskiya ki gane masu son ki tun kafin ki yi nadama lokacin da babu amfani.”
Ita fa duk iri wahalar da ta bashi na yin doguwar magana bata gamsu ba da saboda ta riga da ta yi nisa. Cikin ransa yake mata addu'ar Allah ya sa ta fahimci gaskiya.
Daga haka ya miƙe yace bari ya je ya bawa Alhaji Baba haƙuri, Bata Hana shi ba duk da bata so hakan ba, sai ta amsa da to amma ya dawo Please za ta gyara masa Bedroom ɗinsa. Shi har mamaki yau ta bashi, wai yau shi ne yake samun irin wannan kulawar daga Mommah? Lallai ta yi laushi kam.
Shi kam murmushi yayi sannan ya nufi kofa zuwa ɓangaren Hajjaty ya bar ta parlourn tana saƙawa da warwarewa.
_Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, yanzu muka fara wasan fata na dai zaku bani haɗin kai mu kammala tare da ku ta hanyar reacting, commenting da Kuma sharing. Na gode_
*Comment, react and share fisabilillah*
[12/27, 8:06 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣3️⃣
_Not edited_
﷽
Hajjaty ce sai Zahrah a parlourn, Alhaji Baba Kuwa yana can Bedroom ɗinsa tun da ya baro part din Hajiya Babba ya dawo bai ƙara leƙowa. Saƙawa da warwarewa kawai yake game da family crisis da ke samu.
“Assalamu alaikum”
Zahrah ta amsa masa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da ƴaƴan yatsunta. Lura da yadda ta suƙure da shigowarsa sai yaji babu daɗi amma hakan bai sa ya saki ransa ba sai ma ƙara haɗesa da yayi.
Ita ta fara gaishe shi kanta ƙasa, bata ma yi tunanin zai amsa mata da ta tuna da korarta da jiya yayi. Jin ya amsa yasa ta ɗan turo baki wanda caraf a kan idon sa ne, bai ce uffan ba ya zauna gefenta Hajjaty sannan suka gaisa.
“Ai na ɗauka ka tafi yawon naka da naga shiru baka zo ka yi breakfast ba.”
Harara ya bankawa Zahrah ai ba shiri ta miƙe, cikin ransa yace “Wannan da ganinta zata yi rashin kunya sai dai kuma tana da shegen tsoro da alama”.
Ganin ta bar wajen yasa yace
“Ina nan, ban samu bacci bane jiya shi yasa ban fito da wuri ba.”
“Ayya, baka karya ba ma kenan?”
“Uhm”
“Bari Zahrah tazo ta haɗa naka wani abu Mai sauƙi...” bata kai ga kiran Zahrahn ba ya yamutsa fuska yana faɗin
“Haba Hajjaty yarinyar nan ne za ta min girki ai sai dai jagwalgwale, ki bar shi na ci lunch kawai.”
Baki riƙe Hajjaty ta ce
“Sannu Sadauki, to bari ka ji, girki jiya zan iya cewa ita tayi tunda gurasar ka ma ita tayi ta haɗa maka, Zahrah! Zahrah”
“Na'am, ga Ni nan zuwa. Ga Ni Hajjaty”
“Zaki ɗan haɗawa Yayanku abun karyawa ne mai ɗan sauƙi”
“Tooo Yaya me za a yi?”
“Something simple” ya faɗa a saman laɓɓansa. Nan Zahrah ta wuce kitchen don Samar Masa breakfast shi kuma ta bar shi suna ɗan taɓa hira da Hajjaty wacce duk rabin hirar nasiha da jan hankali take masa.
Within 10minutes Zahrah ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da good flask da kuma thermoflask, tana gama ajiye masa a dining table dawo parlourn looking at his innocent face tace
“I'm done yaya.”
Shiru can kuma ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba yace
“You wait for me there ko Ni zan yi serving Kai na?”
Kai ta jijjiga sannan ta koma dining area Tana jiran zuwansa. Ya share kusan 3minutes kafin ya zo ya zauna. Serving nasa fried potatoes with egg tayi sannan ta fara ƙokarin zuba bread ɗin da ta soya da ƙwai cikin wani bowl. Hannu ya ɗaga mata hakan yasa ta tsaya tana jiran umarni.
“Have You taken yours?” ba ƙaramin mamaki taji ba jin tambayarsa amma sai tayi ƙoƙarin ɓoye hakan ta girgiza kai.
“Oya serve yourself now!”
Babu yadda ta iya ta zuba nata sai dai ta kasa ci saboda kunyarsa da kuma nauyinsa da take ji but can ɓangarensa hankali kwance ya ci abun sa yana korawa da shayin da ta haɗa masa.
Bayan ya gama ya goge bakinsa da tissue sannan ya ɗan kai dubansa ga ɓangaren da take. Ganin ba a sake take ba yasa ya murmusa kana yace
“Why Are You not eating?, Ain't you hungry?”
“Ina....Ina ci fa Yaya.” ta faɗa a rarrabe. Wani iri yake ji idan ta ƙira shi da Yaya, ji yake kamar yadda take faɗa ba kamar yadda sauran family members ɗin ke faɗi ba ne.
“Alright, ajiye zamu yi magana In na tashi sai ki ƙarasa.”
Ƙirjin ta ne ya bada sautin dimm jin maganar sa. Da sauri ta ture bowl ɗin gefe kana ta sauƙar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta, hakan kuma ya zama mata ɗabi'a matsawar zata magantu da wani babba.
“Me yasa jiya kika min dariya?”
Shiru tayi tana zaro idanuwanta.
“Bana so ina ina magana ana shiru musamman magana mai muhimmanci.”
Cikin sanyin murya tace
“A'a ba da kai nake ba Yaya, Ina tuna Bibalo ne fa...”
Hannu ya ɗaga mata yace
“Ba na magana sau biyu, kuma ba na maimaita tambaya, just tell me the truth.”
Tsoro ne ya ɗarsu cikin ranta ai kuwa sai taji kawai faɗan gaskiyar ne alkairi.
“Dama Yaya...dama zare idonka kayi kana hararar Yaya Khalil shine fa.”
“Dama kallo na kike kenan?”
Tambayarsa tazo mata a ba zata.
Cikin in'ina tace
“A'a e a'a dama iya lokacin ne na ɗago.”
Fuska kame yace
“Is alright kada ki ƙara, bana son ina waje ma ake yin dariya, Thank God kin bani haƙuri jiya wallahi I'll have smash you into pieces.”
“Kayi haƙuri Yaya, ba Zan ƙara ba.”
“Is alright, Deal?” Kai ta gyaɗa Masa
“In ina magana ba a amsa min da kai, ko ke kurmiya ce?”
“A'a, na yi”
“in kin ƙara na miki me?”
“Punish me.”
“Ok, now about the issue of your Mom. Ina so ki faɗa min yadda komai ya faru.”
Hawayen da suka fara wanke mata fuska ta share, ta buɗe baki zata yi magana ya dakatar da ita
“Na duka ki ne?” da kai ta bashi amsa.
“Ba kya jin magana, ba na ce bana son a amsa min magana da kai ba?”
“I'm sorry” ta faɗa da sauri.
“Ina jin ki.”
Nan ta bashi labari tas har da ƙara wasu abubuwan da ta manta bata faɗa wa su Hajjaty ba. Cike da tausayawa yake kallon ta musamman yadda take kuka tana magana cikin raunin murya.
“Is ok, wipe your tears” ya faɗa yana miƙa mata handkerchief ɗinsa wadda kamar an yi masa wanka da ruwan turare ne. Amsa ta yi ta goge kana ta miƙa masa.
Kai ya jijjiga mata yana faɗin “No, ki riƙe shi a tare da ke, believe In me Zahrah.” sai da ta ɗago ta kalle shi jin ya ambaci sunan ta.
“In har Mamah na raye zan yi iyakar iyawa ta na binciko ta, kuma zan ɗauki hukunci a kan mutanen da suka cutar da ku da sannu. Ki daina kuka kinji? Ki zama jaruma kamar ni, na fi ki tarin damuwoyi amma ba na bari a fahimci hakan a tattare da Ni.”
“Is he that simple?” ta tambayi kanta, a zahiri kuma tace “In sha Allah Yaya, Thank you”
Without minding on her appreciation yace
“Alhaji Baba ya yi magana a kan karatunki ma, aji nawa kike?”
“S.S.S 2 ne sai na daina zuwa.”
“Ok zaki koma kin ji? Ki shirya gobe da safe I'll be taking you to school, Zaki koma final year ne kiyi SSCE.”
Jin maganar sa yasa Zahrah jin wani irin daɗi cikin ranta tana faɗin ashe haka ɗan'uwa yake?.
“Thank You so much Yaya, zuciyarka tana da kyau, kamar yadda ka faranta min Ubangiji ya yaye maka damuwoyin ka kaima ka rayu cikin farin ciki.”
“Amin” daga haka ya fara ƙoƙarin miƙewa.
“Yaya Thank you.”
Murmushi yayi wanda ya jefa ta cikin mamakin dama yana yi? Ganin kallonsa da take yasa ya ce
“Ki kula da kan ki, In kina da damuwa feel free ki same ni, and I promise to be there for you.”
“In Sha Allah, thank you.” daga haka ya bar dining ɗin ya koma parlour, ita kuma Zahrah na tsaye tana mamakin how simple he is tare da yaba kyakkyawar zuciyarsa. Murmushi tayi tana shafa fuskarta kana ta koma dining ɗin taci abincinta hankali kwance sai murmushi take yi.
Tana gamawa ta fito parlourn, lokacin har Yaya Sadauki ya tafi iya Hajjaty je zaune, murmushi tayi tana mai ƙarasawa jikin Hajjatyn ta kwanta.
Hajjaty ma murmushi tayi tace
“Zahrah'u Yayanku yace a faɗa miki da yamma ki shirya zai miƙa ki ki yi shopping.”
Zaune ta miƙe tana duban Hajjaty da mamaki. Ganin hakan kuma yasa Hajjatyn ƙara faɗaɗa murmushinta tace
“Dama na ce miki shi nake jira ya dawo ya kai ki, ban ma masa maganar ba ya tunkare Ni, yana son ƴan'uwansa shi kam, Zahrah naga wasu abubuwa tattare da shi game da ke, Please be with him, ki kula da shi kuma ki ƙarfafe shi a kowanne hali ok?”
Kai Zahrah ta gyaɗa daga nan suka ci gaba da hirarsu wacce yawanci Zahrah ke bawa Hajjaty labarin Mamah da kuma tsohuwar rayuwar su, haka kawai take jin daɗin hakan duk da ba labarin jin daɗi bane amma tana enjoying when narrating it to others, atleast yana rage mata damuwar rashin Mamah duk da cewa yanzu ma bata rasa komai ba, she's sorrounded by supporters everywhere. Fatanta Allah ta bayyana Mamah itama ta rayu da ahalinta.
Sun daɗe suna hirarsu har lokacin azahar, yau dai Zahrah ba a shiga kitchen girkin Rana ba. Ko da suka yi sallah bata fito ba sai da ta watsa ruwa. Bayan ta dawo parlourn bata ga Hajjaty ba sai ta bi ta Bedroom ɗinta. A lokacin kuma Hajjaty ta ajiye wayarta alamar dai ƙira ta amsa.
“Ƴar halak ga ki nan ma, dama Yayanku ne yace wai ki taimaka ki masa girki amma ba yanzu ba sai around 3:00pm zai shigo.”
“To Hajjaty.”
Bayan sun yi lunch Zahrah ta ɗan kwanta, bata yi aune ba taji hayaniyar su ai kuwa ta miƙe da sauri tana dirowa sannan ta nufe su da gudu tana rungume su.
“Kai sisters, daga school duk sai ku daina nema na?, Na yi fushi ma.” ta faɗa tana zame jikinta daga nasu lokaci ɗaya.
“Haba sister, ba haka bane wallahi, yanzu dai mu zauna sai ki hukunta mu.”
Zakiyya ta faɗa tana kwaɓe fuska har sai da gabaɗayansu suka dara.
“Ke dai Zakiyya ba kya rabuwa da ban dariya wallahi.”
“Ba wannan ba dai, tun da na sanya murmushi kan fuskarki na cancanci Ni kaɗai ki yafe min, kowa ta sa ta fisshe shi.” ta faɗa tana ƙara sakin dariya.
Dukan wasa suka kai mata ai kuwa Zahrah ta tare tana faɗin
“Kwa dake ta kuma? Kowa tasa ta fisshe shi. Jama'ar nan dan kun koka school sai ku mance Ni?”
“Sorry Zahrah kin san ko kowa ya manta da ke Ni ba zan manta da ke ba, ina matuƙar ji da ke shalelen hajjaty.”
Nainarh ta faɗa ita ma tana addu'ar Allah yasa ta kauce. Ƴar harara Zahrah ta banka mata kana tace
“Kin ci Sa'a ina ji da ke ai.”
Dariya ita ma tayi ta dawo ɓangaren da Zahrah da Zakiyya suke tana yi wa su Nasreen gwalo.
“Yanzu Sis Zahrah kina gani har gwalo Nainarh ke min saboda mun ɓata, dom Allah mu bawa maraɗa kunya.” Nasreen ta faɗa tana ɗagewa Zahrah gira.
“Kin ci Sa'a kema.” Zahrah ta faɗa tana janyo hannun Nasreen zuwa ɓangarensu ya rage iya Rumaysa wacce ta kwaɓe fuska tace
“Shikenan tunda Ni kaɗai ce ba a so, bari na koma kawai.” ƙofa ta nufa kamar zata fita, caraf dukkansu suka taho suka rungume juna.
“We're sorry” suka kama kunnuwansu “We all love you.”
“I love you too my sisters.”
Duk sai suka kwashe da dariya.
Haka suka yi ta shirmensu, buɗe idon da Zahrah zata yi kan wall clock taga 2:16pm, a zabure ta miƙe tana faɗin “Innalillahi, ashe akwai aiki gaba na”
Da mamaki suke kallonta
Nainarh ta ce
“Aikin me kuma?”
Duk sai suka mayar da kallonsu ga Zahrah seeking for more explanation.
Kanta ta kauda gefe tana faɗin
“Forget it kawai, maza ku tashi mu shiga kitchen.”
“Tab, daga dawowarmu daga school ko hutawa ba muyi ba?” Nainarh da Zakiyya suka faɗa.
“Naga dai ku ne kuka tsayar da Ni da yanzu na gama, Please muje ku taya Ni.”
Babu yadda suka iya haka suka nufi kitchen ɗin, tare suka toya masa sannan suka haɗa miya wacce taji nama sai mitar wai ma ake wa girkin suke, ita dai Zahrah bata ce komai ba illa iyaka ta kalle su ta kauda kai.
Bayan sun gama suka Kai dining suka jera sai ƙorafin sun gaji suke. Daga nan ta ce to su koma su huta abun su ita kuma ta nufi kitchen ɗin ta haɗa Masa fruit salad. Tana gamawa ta kai ta ajiye sannan ya koma Bedroom ɗinta.
A can ta tarar da su sun baje sai hayaniya suke, ita kuwa ta shige toilet ta sheƙa wankanta ta fito. Bata bi ta kansu ba har sai da ta shirya tukun ta zauna.
Hala suka yi ta shirmensu har lokacin da Laraba tazo kiran Zahrah.
A lokacin har Yaya Sadauki ya dawo ashe yana jiran a zo a bashi abinci. Da kanta tayi serving nasa sai surutu take masa shi kuwa ba abun da yake cewa sai dai murmushi ko uhm ko kuma a'a. Cikin ransa kuma yana ƙara yaba mata don girkin nan da yake ci dawowarsa ya tabbatar ba masu aiki ke yi ba kuma ba Hajjaty ba saboda ya san girkinta. Addu'ar sa Allah ya bashi ikon dawo da Mama don kuwa ba ƙaramar gwarzuwa bace, renon da tayi wa ƴar ta ya burge shi musamman ta ɓangaren girki, zai iya cewa cikin familyn nan da wuya a samu wacce ta iya girki ma har manyan ƴan matan gidan.
_Bari na dasa aya a nan, Please kuyi reacting sannan ku taya Ni sharing saboda Allah, in kun yi reacting sosai anjima zan ƙara update. Ina ƙaunar ku my esteem fans._
[12/28, 11:25 AM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣4️⃣
_Wannan shafin kwacakom ɗinsa sadaukarwa ne ga Maman Tajuddeen da kuma Maryam Muhammad, alkhairin Ubangiji ya kai gareku mutanen kirki. Ina matuƙar jin daɗin comments ɗinku wallahi, ILYSM_
﷽
Yana gama ci ta tattare Wurin ta ɗan gyara, nan yace in ya huta zasu fita. Cike da farin ciki ta koma Bedroom ɗinta, har ga Allah ta manta da su Nasreen da ke ciki yayin da murmushin saman fuskarta ya kasa gushewa.
“Ehn Zahrah why this smile?”
Nasreen asked
Ba tare da ta kalle ta ba tace
“Nothing, kawai yau ta kasance rana ta farko da zan fara fita ne.”
“Da wa zaku fita? And where are you guys going?” Rumaysa ta tambaya tana kafe ta ido.
“Ehn knowing where is not important Amma in na dawo zaki gani. Ni da waye shima ban sani ba, Hajjaty dai yanzu take faɗa min cewa in shirya.”
Abayar da Nasreen ta kawo mata ta saka sannan ta fara ƙoƙarin gyara fuskarta, ko da ta gama ta juyo gurin su hannunta riƙe