Showing 135001 words to 138000 words out of 157517 words
nasu da suka yi sharing a baya, murmushi ne kawai ke escaping kan lips ɗinsa yayin da yake shafa kwantacciyar sumarsa da ke sheƙi da santsi saboda gyara.
Juyin da tayi yasa ya mayar da hankalinsa kanta, ganin ba tashi tayi ba yasa ya gyara zamansa tare da kwanciya yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta wanda hakan ke haifar masa da nishaɗi maras iyaka, jin sa yake tamkar wani sarki, shafa kansa yayi tare da faɗin "She's unique..."
Wayarsa ya ɗauko tare da browsing _Yadda mutum zai ji idan ya faɗa soyayya_ (oh ku ji wani ikon Allah 🤔) tas ya karance yana murmushi, kenan dai dama can ya daɗe yana son Zahrah? Dama can kulawar da ya ba ta ashe saboda so ne? His heartbeat beating faster when they're together, duka alamun felling for someone ne? Missing her terribly when she's damn apart from him? "Alhamdulillah," ya furta a zahiri tare da shafa sajensa.
"She deserves to be loved....and I madly love her...ba na jin I'll let her leave me don hakan barazana ce ga numfashi na, Ya Allah" ya haɗe hannayensa biyu "Ka bar ni fa ita har ƙarshen numfashi na, ka sanya ta so Ni itama, ka ƙara haɗa kanmu ka wanzar da zaman lafiya a zamanmu da ita..." With this thought shima bacci ya kwashe sa ba tare da ya sani ba.
*React and share please...*
[29/04, 9:57 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 6️⃣4️⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
Kiraye-kirayen sallar Azahar yasa ya farka, har lokacin Zahrah baccinta take sha, a hankali ya kai hannunsa kan wuyanta, jin zazzaɓin ya sauƙa yasa ya sauƙe numfashi, can kusa da ita ya matsa ya ajiye mata peck a face ɗinta, daga nan ya nufi toilet, ruwa ya watsa sannan ya ɗauri alwala. Masallaci ya fita ya bar ta tana bacci, bayan ya yi sallah ya biya ta wurin Hajiya Babba ya karɓa musu abinci, daga nan ya koma gida, hanyarsa ta shiga get ɗin estate nasu suka haɗu da Yaya Khalil.
"Ya, Man kwana biyu?"
"Yaushe ma muka rabu kake wani faɗin kwana biyu? Ba na son iya shege fa."
Taɓe baki Yaya Khalil yayi kamar mace.
"Iya shege ma kace? Eh lallai dole...don ka angwance shine kake wani firirita? To babu laifi ga shi kuwa kwana biyu kacal har ka sauya, ka ga yadda kayi wani fresh abunka?"
Karamin tsaki Yaya Sadauki ya ja yana shirin wucewa, hannunsa Yaya Khalil ya riƙe yace
"Haba man, daga fadan gaskiya? To shikenan na mayar da kalmomina, ya amaryar?"
"Alhamdulillah, tana lafiya"
"Haka ake so....a dai bi a hankali don Allah kar a lahanta min ƙanwa da gwauronci..." Daga haka ya saki hannun Yaya Sadauki yana sakin dariyar shaƙiyyanci. Smile ne yayi escaping kan fuskarsa daga nan ya yi kwana.
Yana shiga ya ajiye abincin a Parlour sannan ya shige ciki, ganin har lokacin bacci take yasa yayi murmushi. Durƙusawa yayi daidai saitin fuskarta yayi Kissing forehead ɗinta tare da hura mata iska a kunnenta. A hankali yace "Sleeping bae...wake up and pray"
Miƙa tayi tana tura bakinta. A hankali ta buɗe idanuwanta a kansa, suna haɗa ido ta turo bakinta tare da mayar da idonta ta rufe.
"Please ki daure ki tashi ki yi sallah"
"Then ka fita ai zan tashi"
"Na fita naje ina?"
"Ni dai Allah ka fita" ta faɗa tana sakin kukan shagwaɓa.
"Is ok, zan fita ki tashi kema." Daga haka ya fice, sai da ta tabbatar ya fita tukun ta miƙe da kyar, a hankali ta taka har ta isa toilet, gasa jikinta ta kuma yi tukun ta watsa ruwa tayi alwala, tana fitowa ta tayar da Sallah.
Bayan ta idar Yaya Sadauki ya shigo ɗakin, wuri ya samu jikin praying mat ɗin ya zauna sannan ya kalleta yace "My precious...za ki iya fitowa ki ci abinci ko na kawo miki nan?"
Precious? Sabon sunan da yayi mata kenan wanda ya rage kaso hamsin na haushinsa da take ji. Zan fitom" ta faɗa ba tare da ta ɗago ba, hakan yasa ya sauƙw ajiyar zuciya yana faɗin "My stubborn BAE" cikin ransa. Ba tare da ta cire Hijab ɗin ba ta mayar da praying mat bigirenta sannan ta fara yunƙurin ficewa, kallonta kawai yake ba tare da yace uffan ba hakan kuma yasa ta ji ta a takure don da ya san yadda take ji in yana kallonta da zai ɗan sarara mata. Ba tayi aune ba taji ya ɗaga ta kamar baby, ba ta yi ƙoƙarin dakatar da shi ba saboda ba wani ƙarfi gare ta ba. A dining ya direta sannan yayi serving nasu a Plate ɗaya.
Bakinta ta tura ganin ya zuba a iya plate ɗaya, ga mamakinta sai ga shi ya ɗauki plate ɗin ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna ta yadda zai iya fuskantar ta, abincin ya ɗebo tare da kai mata bakinta, kafaɗa ta maƙe tana tura baki, "God! Please eat..."
"Ni da kaina zan ci"
"I said eat, in kina Min musu fa zan gyara miki zama" da sauri ta amsa ta fara cin abincin har sai da ta ƙoshi tukun ya ƙyaleta sannan shima yaci. Maganinta ya ɗauko ya ba ta amma sai da aka yi drama kafin tasha. Da ba don jan wuya bane yau kam da ta haukata Yaya Sadauki. Da kansa ya tattare kwanukan ita dai kallonsa kawai take yi tana mamakin yadda yake yi da ita, dama ya iya aiki ne can?" Ta tambayi kanta. Da kansa ya ɗauketa ya mayar da ita bedroom, kan bed ya dire ta tare da kissing chin ɗinta.
"Rest my precious " Duk yadda yake ƙoƙarin ganin sun haɗa ido abun ya faskara don muguwar kunyarsa take ji.
Tunawa da kyaututtukan da yayi mata daren Jiya yasa ta kwashe da dariya.
Shaye da mamaki ya kalleta yace "are you ok?"
Kai ta gyaɗa masa tare da gimtse dariyar da take yi.
Haka yinin ranar ya kasance, motsi kaɗan za ta yi yace "me kike so, me ya faru, Are You ok?" Sallah ce kadai ke fitar da shi, fitarsa sallar maghrib ta miƙe tayi Tata, jin zafin ciwon ya ragu yasa taji sha'awar dafa wani abun, kitchen ta nufa kai tsaye ta fara duba meye da meye suke da shi, ba tare da wani tunani ba ta ƙudurta yin spaghetti with egg sauce. A gaggauce ta samu ta haɗa, tana gamawa ta fito ta jera, ganin har lokacin bai shigo ba yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Sallar Isha' tayi ta faɗa toilet tayi wanka, tana gama shirya wa taji sallamarsa, amsa masa tayi tana tura baki don har yanzu da sauran haushinsa a ranta. Murmushi kawai yayi yace
"Kin ji sauƙi kenan tunda har girki kika yi?"
Fuskarta ta kwaɓe tana mayar da idanunta kan yatsun hannunta da suka sha lalle.
Lura da hakan yasa ya riƙe hannayen nata yayi kissing sannan yace "It's damn beautiful, ina son shi, ki dinga yi min kin ji?"
Kai ta gyaɗa masa daga haka yace
"Kamar kin san ina jin yunwa, me kika dafa mana?"
"White spaghetti with egg sauce." Lumshe idanunsa yayi tare da lashe lips ɗinsa
"Yummy..can't wait in yi tasting girkinki a gida na, amma tunda kin warke yau ma za a yi ko?"
"Is he that naughty?" Ta tambayi kanta.
"Yauwah my precious, tunda kika yi shiru na san kin yadda"
Da sauri ta ce "Ni dai a'a wallahi, har yanzu fa da ciwo."
"Ina ne yake ciwon?" Ya tambaya
Fuska kwaɓe tace "Ni dai Allah ban yadda ba"
"To ai ban ce dama kin yadda ba, i just ask, ina ne ke ciwon?" Banza ta masa hakan yasa yace
"Tunda babu yau ma dai za a yi"
Kuka ta fashe masa da shi don ta san shi kaɗai ne zai tseratar da ita daga tarkon Yaya Sadaukin.
"Is ok, ba zan yi ba, I was only joking " ya faɗa cikin sigar lallashi
"Yanzu dai ina son cin abinci kafin nayi wanka, can you help me?"
Ba tare da ta amsa masa ba ta fara takawa a hankali yana biye da ita. Shi yayi serving nasu sannan yayi feeding nata kamar ɗazu kafin yaci. Suna gamawa yayi wanka ya sauya zuwa kayan shan iska yayinda ƙamshinsa ya zagaye ko ina na ɗakin, Zahrah kam yau ba ta yi amfani da turaren wurin Aunty Na'ima ba a cewar ta shi ya sa Yaya Sadaukin yi mata mugunta.
Laptop ɗinsa ya ɗauko tare da zama bakin bed ɗin ya kunnata saboda akwai aikin da yake so yayi a yau. Kwanciyarta ita kam tayi don bacci ma take ji, hakan kuma na da nasaba da maganin da take sha. Tsawon wasu mintoti da ba za su haura rabin sa'a ba ya kammala abinda zai yi, kashe laptop ɗin yayi ya rufe tare da ajiye ta kan bedside drawer, haske ya kashe musu sannan ya karanto addu'o'in bacci ya shafa, itama ya shafa mata. Janyo ta yayi jikinsa, tuni ta tsorata zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri yayinda shi kuma ya lumshe idanuwansa, so da ƙaunarta na ƙara ratsa ɓargo da jijiyarsa.
Cikin raɗa yace "precious I'm very grateful, jazakillahu Khairan, Na ji daɗin yadda kika zo min da mutuncinki, ina alfahari da kasancewata mutum na farko da ya sameki ina kuma roƙonsa da ya bar mu tare...Allah ya yi miki albarka."
A hankali tace "Amin" yayinda daɗi ya gama cika ta kamar ta tashi ta tsalla, tunawa da cewa ita kaɗai ke sonsa yasa tace "Amma ai yaya ba ka so na ko?"
Yatsarsa yasa kan lips ɗinta Yana faɗin "Shhhh"
"Waye yace miki mijinki ba ya son ki?"
Cikin sigar sagwaɓa tace "To ai ba ka taɓa faɗa ba, kuma ban taɓa ji wani ya faɗa ba."
"Ai kuwa dai Precious ke ta musamman ce a wurina, ba sai na furta da bakina ko wani ya faɗa ba za ki san ina son ki, ina son ki ne da dukkan zuciyata, ina sonki Zahrah, so irin wanda ba a taɓa yi wa wata mace kwatankwacinsa ba. Kin san me?"
"Na fara sonki ne tun haɗuwarmu ta farko, kin tuna ranar da kika yi min dariya?" Kai ta gyaɗa masa yace
"To tun ranar nan nake jin wani baƙon al'amari a tattare da ke sai dai ban san menene ba sai a daren Jiya, a duk lokacin da za mu kasance kusa da juna nakan ji bugun zuciyata ya sauya, kin san saboda me?"
"Duk saboda ƙaunarki ne Lily. Ina son ki, ina sonki, zan kuma ci gaba da son ki har ƙarshen numfashina, alfarmar da zan roƙa ɗaya ce....kema ki so Ni Lily, ki so Ni ko da kaɗan ne ba sai yawan yadda nake son ki ba, ki kula da Ni da rayuwata, ki kula da gudan jinina kuma ki kula da duk wani wanda nake so ko da Bayan raina ne...."
Yatsarta ta ɗaura kan lips ɗinsa "Shhh, ya isa haka Yaya, duk abubuwan da ka lissafo zan yi su ko da ba ka roƙi alfarma a kansu ba, kana faɗin bayan ranka Yaya? Ba na fatan hakan...ba na fatan a ce yau na wayi gari babu kai a tare da Ni, do you think it's possible?" Amsa ta ba sa kanta da "No...ina fatan idan mutuwa za ta zo ta tafi damu a lokaci guda don na san ba zan Iya surviving babu kai ba, ka san me?" Da kai ya amsa mata da "a'a"
Tace "ko a lokacin da muka yi imani da cewa ba ka doron duniya ka san irin matsananciyar damuwar da na shiga saboda haka? Ka sani kuwa? Tabbas kowa ya ji a jikinsa amma nawa feelings ɗin sun haura na kowa, ban koma hyyaci na ba har ka dawo gareni a rayayye don Ni dama can jiki da zuciyata sun kasa gaskata gushewarka, kullum cikin mafarkinka nake kana faɗin za ka dawo...a ranar da na fara ganinka na shiga matsanancin farin ciki yayin da ɓarin zuciyata kuma ke baƙin cikin rasa ka a matsayin miji tunda an riga an ɗaura aurena. Lokacin da na Riski bayanin cewa kai ne mijin ka san irin Yadda naji kuwa? Ji nayi kamar an ba Ni aljanna a duniya, kwatankwacin hakan ne saboda kai ɗin aljannata ne da Ubangiji ya min tukuicin ta a rayuwar duniya...Ina sonka Nima Yaya..i love You with every beat of my heart, I'm wishing to be with U till my final breath."
Cikin shauki da ƙaunar junansu da suka bayyanar yasa kowa yake jinsa tamkar ya sauke wani nauyi, they hug each other tightly as if someone is taking one from the other, sun shafe wasu mintoti suna shaƙar daddaɗan ƙamshin junansu and hoping to stay like that forever. Ajiyar zuciya Yaya Sadauki ya sauƙe tare da faɗin
"Ina so nayi miki tukuici Precious, tukuici for your virginity...irin tukuicin da Babu wata mace da ta taɓa samun irin shi, something precious as you are."
*Share and react fisabilillah.*
[30/04, 7:17 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 6️⃣5️⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
"Choose anything you want, matuƙar akwai abun kuma bai fi ƙarfi na ba I'll make sure that Na mallaka miki shi, me kike so precious?"
Tunanin me za ta faɗa masa take, can tace "Ka ga dare ya yi yanzu, ka bari da safe sai na faɗa maka."
"Is ok, amma kina jin abun da nake ji kuwa?"
"What?" Ta tambaya
"Ji nake kamar mu dauwama a wannan yanayin, kusancina da ke ya sa ina ji na kamar wani Basarake."
"Ka cire kamar ɗin, you're beyond that Yaya, Allah ya ƙarawa rayuwarka albarka."
"Amin" ya amsa mata a gajarce, shiru ne ya wanzu a tsakanin yayinda sautin numfashinsu kawai ake iya jiyowa.
"Are U asleep?" She asked
"No Precious,but I'm about to."
"Ok..sweetest dreams" ta faɗa tana ƙara lafewa a jikinsa.
*MORNING...*
Shi ya fara tashi da asuba, a hankali ya zame jikinsa daga nata daga nan ya nufi toilet, few minutes ya fito ya zura jallabiyarsa fara tas sannan ya fara ƙoƙarin tayar da ita, sai da ya tabbatar ta tashi tukun ya wuce masjid.
Bayan Zahrah ta yi sallah ta yi azkar ɗinta na safe, tana gamawa ta fara da gyaran ɗakin, zuwa parlour sannan ta saka turaren ɗaki mai sanyin ƙamshi, kitchen ta wuce directly ta fara ƙoƙari haɗa musu breakfast. Ganin potatoes yasa ta fere daidai yadda zai ishesu, chips ta soya sannan ta yi dying Egg sauce ɗinta wacce ke famar ƙamshi. Tea ta tafasa sannan ta zuba a thermoflask. Zuwa tayi ta jera komai sannan ta wuce bedroom nata, toilet ta wanke kafin ta fara rage kayan jikinta. Yau ma sai da ta ƙara gasa jikinta tukun tayi wanka, tana fitowa ta shirya tsaf cikin wani lace ɗinta wanda aka zubawa ɗinki, sosai tayi kyau abunta maganar ƙamshi kuwa a ajiye ta gefe don mutum yana doso ƙofar bedroom ɗin zai jiyo shi kamar an yi wanka da turare.
Wayar ta ta ɗauko ganin bai dawo ba ta ƙira numbern Hajjaty, bugu ɗaya kuwa ta ɗaga tana sallama, amsa mata sallamar Zahrah tayi tare da miƙa gaisuwarta.
"Lafiya ƙalau Zahrah'u, ya baƙunta?"
"A ɗan shagwaɓe tace "Alhamdulillah, kin ma manta da Ni Hajjaty ko kira na ba kiyi ba bare ki duba lafiya ta, Ni na ma yi fushi."
"A'a ƴar nan, ban manta da ke ba, kin ganta nan, Madina ce ta hana kiranki tana ba Ni wani uzuri da Ni bai ma yi min ba"
"To hajjaty me yasa ba ki watsar da uzurin nata kin kirani ba?"
"Ungo nan!" Ta aiko mata daƙuwa kamar tana ganinta.
"Uwar taki ko?"
"To hajjaty duk kun manta da Ni ke da ita kuma kewarku ma nake."
"To shikenan Zahrah'u ki yi haƙuri zan sa Sadaukin ya kawo min ke ai." Cike da farin ciki tace "Allah ya kai mu, na gode ƴar tsohuwar mu"
Sallama ta musu ta kashe wayar don Mama ƙin amsa tayi daga wurin Hajjaty.
Juyowar da za ta yi taga mutum gabanta sai Binta yake da kallo, cike da kunya tace "Good morning Yaya"
"Ban karɓa ba" ya amsa mata cikin kasalalliyar muryarsa da kallonta ya haddasa masa. "Haka aka ce miki mata ke gaida miji? Tsaya ki ga"
Kusa da ita ya matso yayi hugging nata by one side sannan ya aje mata peck a chin ɗinta.
"Haka za ki ke yi min in za ki gaida Ni, in ba haka ba ba zan ke amsawa ba kin ji ko? Kai ta gyaɗa masa yace "How's your night?"
"Alhamdulillah...and yours?"
"Alhamdulillah, perfect one ever because I slept with no burden in my mind but with your love."
"Za ka yi wanka na sani, bari na haɗa maka, ka jira Ni a nan"
"Ok Zaujaty, thank you" tana gama haɗa masa ya shige yayi wanka, bayan ya shirya suka yi breakfast. A Parlour suka zauna kan 3seater, shi yana zaune ita kuma kanta na kan lap ɗinshi yana wasa da gashin kanta.
"Zaujaty na tuna, safiya ta yi, i want to hear what you want from me as a your virginity gift"
"Yaya Sai ka yi alƙawarin za ka kasance a tare da Ni, za ka goya min baya tukun na faɗa maka" ba tare da wani tunani ba yace "Na yi"
Miƙewa tayi ta zauna tana dubansa tare da riƙe yatsunsa cikin nata.
"Yaya...it's something strange and dangerous nake so mu yi handling, idan har ka taimaka aka magance shi wallahi ka gama min komai..."
"Stop beating around the bush my angel, just go straight, I'll be there for you."
"Allah yasa dai ka aminta da Ni, don na