Showing 48001 words to 51000 words out of 157517 words

Chapter 17 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5158

ka san ba ni da hankali, bari ku ga haukar, tattara kuɗin ɗa na zanyi na yi idan ya so ku da kuka nace sai ya yi auren kwa haɗa masa lefen.” nan ta kai hannun ta kan akwatunan tana faɗin
“Habiba ku zo ku taya Ni mu kwashe”

Sai a lokacin su Ammie suka fito don da a maƙale suke.

“Wallahi Sughrah kika kuskura kika taɓa abu anan zan ɓata miki rai.”

Dariyar takaico tayi tana mai kallon Daddy da fuskarsa ke ɗaure
“Wane ɓacin rai ne ban gani ba a wurin ka tunda Gashi yanzu ina gani kai da iyayenka masu gadarar tsiya kuna shirin nuna min iyaka kan ɗana.”

A harzuƙe wannan karen ma Mommy Nasiba ta Yo kanta sai dai Daddy ya dakatar da ita. Murya a kausashe yace
“Sughrah ki koma ɓangaren ki”
Tsoro ta ji kawai sai ta juya tana burga ta bar parlourn, muƙarrabanta suka bi bayanta.

Nan dai aka tattara kaya aka shiga da su ɗakin Alhaji Baba, Hajjaty sai haƙuri take ba wa su Mommy Nasiba, su ma suna bata haƙuri don ko ba komai yau ƴar'uwarsu ta sa sun ji kunya kuma ta ɓata wayonta.

Duk abun da yake faruwa Yaya Sadauki bai sani ba saboda yana can kan aikin neman Mama. Wuraren Isha ya dawo. Har aka yi sallah ya wuce da su Alhaji Baba babu wanda ya ba shi labarin abun da ya faru yau. Bayan ya yi Dinner ya nufi part ɗin su don ya huta.

A parlour ya ci karo da Daddy bayan sun gaisa yana shirin Hayewa sama ya dakatar da shi. Tsawon wasu mintuna suka kwashe suna magana ƙasa-ƙasa can dai yaya Sadauki ya wuce DADDY kuma ya ciro wayarsa ya kira Ya Junaid Wanda ke Abu Dhabi da zama tare da matarsa. Shi ma sun jima suna waya kafin nan ya yanke, nan ya wuce Bedroom ɗin Mommahn.

Bai tsaya ɓata lokaci ba ya kira sunanta sai tayi kamar ba ta san da wanzuwarsa ba, sarai kuma ya san ta ji ɗin tunda idonta biyu. Bulb ya kunna ai kuwa ta Zabura ta miƙe daga kan Bed ɗin
“Mallam ya za ka kunna min haske ina bacci”

Murmushin takaici ya saki yace
“Ba wani dogon zance ko rigima nazo ba, ba kuma shawara ko suggestion na bayar ba, umarni nake baki da...”
Shewa tayi tace
“Dama ta Nan ka fi kauri ai, sai iya ba da umarni kamar kai ka haifi mutum, Ni zan kwanta, idan ka gama ka kashe min bulb.”

Zata haye Bed yace
“Na ba ki yau zuwa gobe ki tattara kayan ki na sawa ki bar min gida, ban yadda ki ɗauki komai ba bayan kayan sawar ki sai ki tafi tunda ba ki daraja kowa a gidan.”

Duk da cewa jikinta yayi sanyi amma da ta tuna karatun da ta sha sai tace
“To sai me in na tafin, ta fi nono fari ai. Kuma wallahi ku tabbatar kun dakatar da bikin da kuke shirin yi ba izini na.”

Bai tsaya jin me zata ce ba ya wuce Bedroom ɗinsa Rai a ɓace.

Washegari kuwa da sassafe Daddy da zai fita ya shiga ya ƙara nanata mata cewa Kada ya dawo ya tarar da ita. Bata damu ba ta fara tattara kayanta sannan ta yi shirin ficewa, ATM card ɗin ta tayi wa neman duniyar nan amma bata gani ba, haka keys ɗin motarta babu alamun su nan jikin ta ya bata cewa Daddy ne ya ɗauke.

Wayarta ta ɗaga ta kira Number su Mamie cewa tana son ganinsu, ba jimawa kuwa ta suka zo, nan ta labarta musu halin da take ciki, sa yake su ƴan duniya ne suka ƙara ɗaura ta layin kada ta kuskura ta bari ayi auren nan tun da yanzu ya ce ta bar masa gida. Da wannan shawara suka wuce, Mommah kuma tayi amanna da ita.
Ba tare da ta damu ba kuwa ta haɗa ta fice, ko ta kan auta Ra'ees bata bi ba ta fice, daidaita ta hau bata tsaya ko ina ba sai gidansu.

Nan ta biya mai a daidaita kudinsa da sauran cash ɗin da ya rage mata. A bakin gate ta tsaya tana ƙarewa gidan kallo, babu laifi gida ne mai kyau sai dai kana gani za ka fahimci cewa masu gidan tsoffin masu kuɗi ne. Ko a mafarki ba ta jin za ta iya zaman gidan amma a haka ta daure ta jefa ƙafarta ciki.

*Ina buƙatar reactions ɗinku sosai my esteem people, don girman Allah na ci albarkacin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama a yi min share zuwa wasu groups ɗin. Thanks You so much, Diamond Bhatool taku ce🦋💞!*

[1/13, 9:42 AM] Diamond Bhatool:

https://vm.tiktok.com/ZMkaSGVu8/

*Please follow my Tiktok handle*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 2️⃣3️⃣



                                  ﷽

Mahaifin Mommah ya daɗe da rasuwa, mahaifiyarta ce kawai a gidan sai kuma yayyenta maza uku da matansu tare da yaransu da suke zaune gidan.

Tun daga hanyar da zata sada ka da mai flt ɗin ta ci karo da ruwa kwalale a ƙasa, ɗage rigarta tayi tana yamutsa fuska kamar ta taka kashi. A main parlourn ta tarar da mahaifiyarta Hajja wacce ke zaune tana kallon SunnahTV. Sallama tayi ciki-ciki Hajja ta amsa tana aika mata wani mummunan kallo na za ki sani don tuni su Mommy Nasiba suka sanar da ita abun da ya faru.

Da yake ma can ba zuwa take ba tunda taga mijinta mai hali ne dama kuma can akwai ji da kai su Hajiya Sughrah sai ta janye ƙafafunta, sai ta share shekara bata ziyarci mahaifiyarta ba, amma su Yaya Sadauki suna zuwa duk juma'a su gaida Hajja.

Gaida Hajja Mommah tayi, ba tare da Hajja ta ɗago ba ta amsa daga haka bata ce komai ba sai da aka gama karatun tukun ta kashe TV ta juyo ta fuskanci Mommah fuska ɗaure.
“Ba dai zaman gidan kika zaɓa ba Sughrah? Madalla da ke! Ga can ɗaki sai ki zo ki gyara ki zauna tunda ba za ki taɓa yin hankali ba. Ai Umar ya kyauta ma da ya dawo dake, shashasha kawai.”

Kamar Mommah za ta saka kuka haka ta tashi ta nufi ɗakin da Hajja ta nuna mata, subhanallah! Sai da ta dafe ƙirji ganin yanayin ɗakin, ƙura ce cike da ɗakin ga kuma yana kamar an shekara goma ba a buɗe ba, abun da ya fi ɗaga mata hankali ko labule babu ga shi ko fanka babu a ɗakin. Kamar za ta yi kuka haka ta naɗe gyalenta ta ɗaure saman rigarta da kwalinta sannan ta fara shara, tsabar an dade ba a haɗu ba sai da idonta ya raina fata har shaƙewa numfashin ta yake. Da ƙyar ta gama ta nufi toilet ɗin ta fara share ƙurar da ke ciki. Ko da ta kunna ruwa tap ɗin ba ya zuwa, kamar za ta yi kuka ta fito ta tambayi Hajja. Amsar da Hajja ta bata ne ta sa gabanta bugawa.

“Ki tambayi su Rahina la'alla su ba ki, idan babu kuma sai ki fita waje ki ɗebo. Babu yadda ta iya haka ta nufi sashen babban yayansu Alhaji Kabir. Kallon arziƙi bata samu ba saboda dama sun tanadi wulaƙancin da za su mata musamman da ya kasance umarnin Hajja ne. Kamar wacce lakar ta ta saki ta ƙaraso. Ba tare da ta gaishe da Aunty Rahina ba tace
“Ki ɗan san min ruwa zan wanke bayi”
Hararar ta Aunty Rahina tayi tace
“ki ɗauki plastic ɗaya daga haka kar ki dawo saboda wuta ta ɓaci ba lallai mu samu ruwan ba.”

Babu yadda ta iya ta buɗe randar ta fara zuba ruwan a plastic ɗin sai dai kafin ta gama tuni ta gaji saboda a gidan ta iyakaci ba da umarni ne. Ƙasa ɗaukar ruwan tayi ta juyo tana kallon Aunty Rahina.
“Don Allah ki taimaka ki miƙa min wallahi na kasa”

Abun mamaki wai yau Sughrah ce ke haɗa ta da Allah? Kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka mata ta kai mata. Mommah tace “Na gode”
Daga haka ta wanke bayin sai yamutsa fuska take..

Bayan ta gama ta shimfida tabarma a sabon ɗakinta ta zauna, nan ta jera kaya sannan ta kira Ammie take sanar da ita ta iso, bayan ta gama mata karatu ta fara laluɓen Numbern Yaya Sadauki coz akwai abubuwan da za ta buƙata amma Numbern ba ya shiga. Duk abun da Mommah take yi a kan idon Hajjja ne, jijjiga kai kawai ta yi tana mata fatan shiriya.

*Yaya Sadauki*

Aka ce biki ya yi biki, zaune yake shi da Ya Khalil sai kuma wasu friends ɗin su da Ya Khalil ɗin ya gayyato waɗanda suka iso safiyar yau. Ban da tsokanarsa babu abun da suke shi kuma mutumin ya tsuke fuska kamar a filin daga. Kamar wanda aka tsikara ya ciro wayarsa, Mommah ce ta fara faɗo masa a rai amma sai ya sauya fuska yana yamutsa ta, Numbern Hajjaty ya lalaɓo ya dannawa Kira, cikin Sa'a kuwa wayar na hannunta. Suna gaisawa ya miƙe zai fice sai tsiya suke masa ba tare da sun san wane irin ware zai yi ba. Tambayar Hajjatyn yayi ko Zahrah na nan, tace “Gaskiya to bari dai na duba,sun dai ce za su karɓo ɗinkin su ita da su Nasreen” jim yayi kafin yace
“Don Allah ki duba min ita Hajjaty.”
Katse kiran Hajjaty tayi taje dubo Zahrah.

Yana zaune ba tare da ya ce da su komai ba wayarsa ta yi ringing.
“A'a ta ƙira fa! Wannan kuwa za ta bar mu da abokin?” Ya Salim ya faɗa yana ɗage masa gira. Ba tare da ya ɗaga kiran ba har ya katse ya dubi Ya Salim yayi murmushin takaici kana ya miƙe, kiran Hajjaty ya bi, bayan ta ɗaga tace masa “Ga Zahra'un”

Jin shiru ba a yi magana ba yasa Zahrah faɗin
“Hi! Who's on the line?”
Gyaran murya yayi, lokacin ta fahimci waye ne.
“Ah Yaya Kai ne?” ba tare da ta jira amsarsa ba tace
“Hajjaty tace za ka yi magana da Ni ”

“Eh Lilyn Yaya, idan ban takura ki ba please lazy creatures ɗin nan su taimaka miki ku yi mana girki Ni da baƙi na.”
Amsa ta bashi da “To Yaya, In an gama zan sanar da Hajjaty cewa ta ƙira ka, Bye Ango..”

Maganarta ta ƙarshe ta so ta bugi zuciyarsa wai ango? Da gaske wai angon zai zama? Ya tambayi kansa.
Murmushin takaici yayi yana mai ƙara tausayawa ƙanwarsa Mabruka, kamar wanda aka zare masa laka ya fara laluɓen Numbern da jiya ta ƙira shi tana masa magiyar ya ce ya fasa auren don Allah.
Bai ɓata lokaci wurin shawara da zuciyarsa ba ya danna mata kira, ringing ɗin farko ta ɗaga kiran.
Shiru yayi sai da ta yi sallama ya amsa mata. Shirun ne ya ƙara kasancewa tsakanin su kafin tace
“Yaya Sadauki ina jin ka”
Ƙuƙƙifta ido ya fara yi kamar wani maras gaskiya yace
“Akwai abun da kuke buƙata na hidimar biki, kuyi listing sai ki tura min ko?”
Amsa ta bashi da “To Yaya, na gode” daga haka ta cire wayar a kunnen ta tana mai fashewa da kuka.

A nasa ɓangaren katse kiran yayi yana mai ƙara kallon sararin samaniya na tsawon daƙiƙu kafin ya koma cikin ƙawayen nasu.

Can ɓangaren Zahrah tuni ta tattaro Aminanta suka nufi kitchen don cika umarni mai martaba sarkin da ke mulkar zuciyarta. Nan kuma suka hau aiki.

*GRA, Bauchin Yakubu*

“Yanzu shi ke nan Mom, na rasa Zahrah! Na rasa ta kenan har abada?”
Ya Ishaq ya faɗa yana share ƙwalla. Kan sa Mom ta kwantar bisa cinyarta tana share masa hawayen da ke zuba, bangare guda zuciyarta na tsananta bugun yadda tilon ɗan ta ke wahaltuwa kan soyayya.
Lallashin sa ta fara tana ƙara kwantar masa da hankali.
“Is ok son, ya isa kukan haka, jarumi kamar ka bai kyautu a ce yana kuka ba idan matsala ta tunkare shi, ina so ka ƙara samun ƙarfin zuciya, In Sha Allah in dai Zahrah rabon ka ce za ka same ta duk daren daɗewa.”

Idanuwansa da suka gama yin ja ya buɗe a hankali kana yace
“Mom In babu ita ba zan rayu ba! Ban san ta ina zan fara neman ta ba, ko da numfashi na ƙarshe zai kasance to ina so ya kasance na haɗu da Zahrah, na so angel da zuciya ta da kuma gangar jiki na, ta ya za a ce na rasa ta? Nooo ba zai yiwu ba Mom, Idan ban same ta mutuwa zan yi” sai kuma ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.

Tapping bayansa Mom ke yi tana faɗin
“Ya isa son, be brave man Mana, na maka alƙawarin zan taya ka neman ta only on one condition”
Kamar ba shi bane mai kuka ba nan take yayi shiru tare da miƙewa zaune yana mai zubawa Mom ɗin ido.
“Ina jin ki Mom, ai ko meye sharaɗin na yadda da shi”
Kamar za ta yi dariya ganin yadda ya sauya lokaci ɗaya, hakan yasa ta ƙuduri taimakon sa wurin dawo masa da farin cikin da ya rasa tsawon wasu shekaru dalilinsu ita da mahaifinsa tana kuma tirr da hakan.

“Kana ji ko Son?” Kai ya gyada kamar wani ƙaramin yaro
“In har kana so na taya ka neman Zahrah to dole za ka zama mai ƙarfin zuciya, wannan kukan da kake kamar wani baby boy duk za ka daina shi, be strong and pray, Allah zai ji ƙan ka ya tausaya maka sannan ya samar maka da mafita, ok?”
Kai ya gyaɗa yana murmusawa amma kallo ɗaya mai karatu zai masa ya san cewa murmushin nan ne da ake kira Yaƙe.
“Oya now, tashi ka ci wani abun, zama da tunda ba na jarumin ɗa na bane!” babu yadda ya iya haka ya miƙe gudun kada ta samfo har yanzu fa damuwar ba raguwa tayi ba.

*ABATCHA ESTATE*

Aunty Mabruka ce tare da wasu ƙawayen ta guda biyu sun sa ta tsakiya sai rarrashinta suke akan ta cire damuwar komai ta fuskanci zahirin.
Ma'eesha ta ƙara dafa kafaɗarta tana faɗin
“Haƙuri za ki yi Barrister Mabruka, kowa da yadda ƙaddararsa take zuwa masa, karɓanta hannu bibbiyu sai kiga Ubangiji ya dube ki ya musanya miki da mafi alkhairin ta. So calm down.”

Kanta kawai ta jijjiga tana mai goge ƙwallar da ta zubo mata.
“Ba za ku taɓa gane raɗaɗin da nake ji a zuciya ta ba, ba wai ban karɓi ƙaddara ta bane ko wani abun makamancin haka, ina so ku fahimci matsaya ta ne, ina da wanda nake so, amma saboda wani dalili an katange Ni da shi.”

Galala su Raudha suka yi suna kallon ta, ko yaushe rai ta fara kula samarin bare har ta ce akwai wanda take so, dey play.

“To ke Mabruka ina ce dai ko samarin dama ba ki kulawa, ƙarewarta ɗan'uwa na dake mutuwar ƙaunarki ma haka fir kika ƙi saboda wani ra'ayin ki, yanzu ga shi Allah ya baki namiji son kowa ƙin wanda ya rasa amma kina neman butulce masa.” Raudha ta faɗa tana hararar Mabruka.

“Rabu da ita Raudha, wai ma uban waye take cewa tana so ɗin, ina ce duk cikin masu son nata ma iya Captain Hisham ne ya samu arziƙin kallo, shi kuwa har yau ba ta amsa soyayyar sa ba, and see her wai akwai wanda take so, na rantse da Allah Mabruka in kika yi sake mijin nan ya kuɓuce miki ba za ki samu ya shi ba.”

Caraf Raudha tace “Wallahi ko Ni aka haɗa da guy ɗin nan da gudu zan yadda, wallahi maza irin su wuya suke Mabruka, kin sani ko cikin ƴan matan familyn ku ba za a rasa waɗanda ke son shi ba, in za ki kama abun ki ki riƙe Tom, In ba Haka ba za ki ji ana labari.”

Ba ta ce komai ba saboda ta san duk abun da suka faɗa gaskiya ne, ya za a yi su fahimci cewa mahaifiyarsa ba ta son ta bare kuma auren? Meye makomar auren bayan duk su biyun ba su son juna? Ga shi kuma ƴar'uwarta uwa ɗaya uba ɗaya ta mace a son mijin? Da a ce tana da wata dama da ba shakka za ta yi wa ƴar'uwarta wannan ƙoƙarin ko don yadda ta kasance mai iya ɓoye damuwarta. Da haka dai suka ci nasarar shawo kanta har ta saki ana hira, zuwan wasu gang ɗin friends ɗinta yasa ta sake kamar ba komai, fatan ta Allah ya sa zaɓin ya zama alkhairi.

*Zahrah's POV*

Ba su daɗe ba suka kammala haɗa girkin ko don suna da yawa ne oho, sai da ta tabbatar ta jera komai cikin basket kafin ta sanar da Hajjaty. Daga nan suka koma Bedroom ɗin Zahrah suka ci gaba da gwada ɗinkin da suka karɓo, su saka wannan su cire su saka wancan gashi duk ba wanka suka yi ba.

Rumaysa da ke gefe tana kallon su tace
“ku ci gaba da saka kayan ba wanka idan kula gumama su da tsami kwa yi bayani ai” ta idasa tana hararar su
Nainarh tace “Kut! Rumaysa mu ne za mu gumama kayan da wari? Me kike nufi?”
“Abun da kika fahimta” ta bata amsa a taƙaice.

Zahrah tace “kin dai san ba mu kai matakin gumama kaya da wari ba don mun shiga kitchen tun da duk cikin mu kin fi kowa kitse, look at you, wata tiƙeƙiya da ke” ta idasa tana aikawa Rumaysar gwalo.

A hasale Rumaysa ta miƙe ta yo kan Zahrah, ai ba shiri Zahrah ta daka tsalle ta haye Bed, Nasreen sai dariyar mugunta take
“Tab! Yau Zahrah sai ɗan buzun ki”

“Na rantse da Allah kika taɓa Ni sai na faɗawa Hajjaty, kawai daga faɗan gaskiya! Naga kema kin gasa mana maganar mun ƙyale ki.” Zahrah ta faɗa tana sauƙe ajiyar zuciya, daidai nan Hajjaty ta shigo da wayarta tana faɗin
“Ungo Yayan ku zai yi magana da ke”
Amsa tayi ta kara a kunnenta tana faɗin
“Assalamu Alaikum”

*React please, sannan a taimaki baiwar Allah a taya ta sharing.*

[1/13, 8:15 PM] Diamond Bhatool:











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login