Showing 63001 words to 66000 words out of 157517 words
ya bi family da su sannan kuma waje ma bai bar su ba. Ko da ya shiga kasuwar Kayan abinci wurin Alhaji Sammani ya wuce, dama can a wurinsa yake siya, duk da cewa farashin kayan ya hau kusan ninki uku zuwa huɗu bai fasa siya ba, yawan yadda yake siya hakan ya siya sannan yace a kai can Estate ɗin su gidan kakanninsa, shi kuma ya wuce, har zai wuce gida ya tsaya a wata plaza, ba tare da ya san me zai siya ba ya shiga, kamar an ce ya ɗaga kai yaga wani abokinsa da suka daɗe basu gamu ba a wani shago, shiga yayi da sallama bayan sun gaisa Yaya Sadauki ya tambaye shi ko me yake sayarwa?
Yace “Ai ga can ainihin shagon upstairs na wayoyi da laptops ɗin nan”
Fuska sake Yaya Sadauki yace “Amma jarin naka ya kai nawa?”
“5million ne”
Shiru yayi kamar mai nazari can yace “Ɗan bani account details naka” yana ba shi Ya masa transfer na 5million yace ka ƙara jari, Allah yasa albarka cikin kasuwancin ka, wallahi na ji daɗin ganinka mai sunan Daddy”
Alert ɗin da ya gani yasa ya zaro ido waje, tsabar mamaki ko addu'ar da ya masa bai bi ta kai ba yace
“5millions? Kai amma na gode sosai Ɗa na (kamar yadda yake kiransa da shi a da) Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, wallahi ba zan taɓa mantawa da alkhairin ka gare Ni ba, Ubangiji ya ƙara tsawon rai ya kare ka daga sharrin mutum da aljan”
Murmushi Yaya Sadauki yayi yace
“Ya Isa Daddy na, ai ka wuce haka a wuri na, mu je naga shagon ko da abun siya” sama suka hau nan kawai Yaya Sadauki yaji ya siyawa sisters nasa waya da laptop ɗin ai ko ba komai za su yi karatu da shi.
Kuɗin da ya ji sun ƙara shigowa na system 4 da phoned 4 da ya siya yasa Umar faɗin
“Haba Ɗa na, ai nima yayansu ne, zan mayar maka da kuɗin ka in Sha Allah”
“No need” ya ba shi amsa a taƙaice. Fdgd haka suka yi Musabaha, Yaya Sadauki ya wuce gida.
Bayan ya yi sallar maghrib ya kwaso phones da systems ɗin, sai a lokacin Aunty Mabruka ta gan su, bayan ta tambaye shi without thinking if anything yace “Na su Zahrah ne” gabanta ne ya ɗan faɗi don zuwa yanzu ba ƙaramin so take wa mijin nata ba, karo na farko da ta ji kishinsa a ranta da ta tuna scene ɗin da ya faru a bikinsu. Ganin kamar ta shiga wata duniyar yasa ya huta mata iskar bakinsa a idonta, a ɗan zabure tace
“Bye, sai ka dawo, ” daga haka ta juya da sauri ta nufi Bedroom nata tana sakin kuka.
Jim ya bi ta da kallo har ta shiga, bai ji daɗin yadda ta tafin ba duk da ya gano kamar kishinsa take amma ai ƙannensa ne, kuma ta sani sarai tun kafin su yi aure shi yake kula da al'amuran Zahrah, why daga faɗin sunanta za ta sauya fuska. Kafaɗarsa ya ɗage irin I don't care ɗin nan ya nufi motarsa da ke fake.
Yana shirin tayarwa wayarsa ta fara ringing, ganin Detective Musa yasa yayi connecting da Bluetooth tare da picking, gaisawa suka yi, Yaya Sadauki yayi shiru yana sauraran sa.
“Sir kana ji?”
Da “Eh” ya amsa sannan yayi shiru.
“Yauwah sir yanzu Baba Salahu ya ƙira Ni game da Issue na matar nan, ya ce wai ka ce mu je tare da shi ya nuna min gidan da take sannan....”
Dakatar da shi yayi sanin halin Sarkin zance
“Eh Ni ne”
“Ok sir, sai na kira ka” ya faɗa cike da girmamawa.
Daga haka ya katse kiran tare da jan motar, bai tsaya ko ina ba sai ɓangaren Hajjaty.
*React and share please*
[1/18, 2:25 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣9️⃣
Bayan sun gaisa da Hajjaty nan yake tambayar Zahrah, bai rufe baki ba ta fito daga Bedroom nata don ɗaukar snacks da drink ta sa a bakinta saboda karatun da tayi ya sa duk glucose nata ya ƙone.
Turus tayi ganin Yaya Sadauki a parlourn, da sauri ta ƙarasa wurin da yake tana washe baki.
“Oyoyo Yaya Ango, an yini lafiya?”
Ba tare da ya kalle ta ba yace
“Lafiya lau Lily na, ya karatun, ana maida hankali dai ko?”
Fuskarta ɗauke da murmushi tace
“Alhamdulillah Yaya ana yi sosai.”
Ɗagowa yayi ya dube ta sannan yace
“Ma sha Allah, ban da biye samari dai.”
Ƙasa tayi da kanta ba tare da ta ce komai ba, Hajjaty kuma tayi karaf tace
“Tooo! Ji min wani zance, In ba ta kula su ba ta ya za ta samu mijin?”
Kunya ce ta kama Zahrah jin zancen Hajjaty, ba ta san lokacin da ta ruga da gudu ta koma Bedroom nata ba. Kallonsa ya mayar kan Hajjaty yace
“A'a Hajjaty, Lily na ta yi yarinya da kula samari yanzu, In lokacin ta yayi ma already na mata miji”
Baki sake Hajjaty ke kallon sa kana tayi dariya irin tasu ta manya tace “Lallai ne Ishyaku.”
Shima dariyar yayi yace “Yanzu ga shi kin sa ta ji kunya ta tafi, kuma ban faɗa mata saƙo na ba”
“In na fahimce ka so kake yanzu naje na kira maka ita?”
“Ni ban ce ba Hajjaty, zan je na faɗa mata da kaina ma”
Harararsa Hajjaty tayi tace “Ɗan baɗo kawai, ya Mabruka?”
“Lafiya” kawai yace daga haka ya nufi Bedroom ɗin Zahrah.
Littafan da ya gani gabanta yasa ya murmusa sannan yace.
“Put on your Hijab and follow me Lily”
Kamar yadda ya faɗa tana saka Hijab ta bi bayansa. Ɗan gefe ta tsaya ganin ya buɗe motarsa.
“Come closer” ya faɗa a hankali. Pointing mata jerarrun laptops ɗin yayi yace
“Choose one”
PINKY....ai kuwa tana hango pink ta nuna masa, Phones ɗin da yake iri ɗaya ne sai ya miƙa mata su yace, pick yours sauran ki ba ma sisters naki”
Kasa magana tayi tsabar farin ciki sai jujjuyo Phones ɗin take, wai iPhone dai da take gani yau ita Yaya ya mallakawa. Ganin ta tsaya yasa ya ɗan kalle ta yace
“Lily?”
Sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunanin, fuskarta na nuna zallar farin ciki tace
“Thank You so much Yaya na, Allah ya ƙara maka buɗi yasa ka fi haka, mun gode”
Without minding at her appreciation yace
“Mu je na taimaka miki ki shiga da su” daga haka yayi gaba tana biye da shi, ta ma rasa ina za ta sa kanta saboda tsantsar farin ciki.
Bayan ya kai mata har Bedroom nata ya miƙa mata wasu kuɗaɗe yace
“Ban samu siya muku Sim cards ba, gobe In kun dawo daga school sai driver ya Kai ku ku siyo, banda waya da samari Lilyn Yaya, karatu na siya muku ku yi da su.”
Cike da ladabi tace “In sha Allah Yaya, mun gode sosai, mu kwana lafiya”
Daga haka ya wuce abunsa.
Kai tsaye gida ya koma, sosai Aunty Mabruka ta tada masa rigima don ya siya ma su Zahrah waya da system, shi mamaki ma ta bashi, sai kace bai ƙannenta ba, share batun ta yayi ganin tana so ta kawo masa wargi da ta gaji da kanta ta sauƙo.
Yana Zaune yana aiki a system nasa wayarsa tayi ringing. Ganin Detective Musa yasa yayi picking a hanzace.
“Hello Sir, ga Ni ga Baba a gidan da matar take, kafin ka iso za ka iya hawa Whatsapp kuyi magana da ita.”
Bai tsaya ƙarasa jin zancen ba ya datse kiran ya hau Whatsapp. Video call ya Danna direct, lokacin da suka zama connected Detective Musa ya miƙawa Mama da ke zaune kusa da inna, da yake akwai adequate light a gidan a kan fuskarta idanuwansa suka sauƙa, ko ba a faɗa masa ba ya tabbatar ita ɗin ce, ba tare da ya ce uffan ba ya katse kiran, ɓangaren Mamah ma kusan abun da ya faru kenan, tana kallonsa fuskar ɗan'uwanta ta zanu a zuciyarta har sai da gabanta ya faɗi.
Ko da yayi ending call ɗin bai tsaya ɓata lokaci ba yayi booking flightpip duk da cewa yau za a tashi da azumi gobe ne. Ganin yadda yake zakwaɗi yasa Aunty Mabruka faɗin
“Kwana nawa za ka yi ne Yaya?”
“Ai sai kun ganni kawai.”
Kamar za ta yi kuka tace
“Ya batun zuwa gaida Mommah?.”
“Kar ki wani damu da wannan, In ba na Nan ma Khalil Yana nan, zai iya kai ki. Daga haka ba ta ƙara cewa komai ba ganin dai alamun har yanzu fushi yake da ita.
*Washegari*
Bayan sun shirya a part ɗin Hajjaty suka haɗu bayan sun gaisa Zahrah ta dube su cike da zumuɗi tace
“Guess what?” a tare suka ce
“What?”
Murmushi Zahrah tayi tace
“Tukuicin me zan samu?”
Nainarh tace “Na baki Yaya na”
Sauran ma duk irin amsar da suka bayar. Ɗauko musu system ɗin ta fara yi, kowaccen su ta zaɓa cike da zumuɗi
“A ina kika samo waɗannan kuma?” murmushi tayi tace
“Ku ba kwa cin ribar zance, to Yaya ne jiya ya siya mana bayan kun tafi, bari ku ga”
Kwalayen wayoyin ta fitar ɗaya bayan ɗaya, ihun murna suka saki suna faɗin
“Wayyo mun more wallahi, kai Zahrah Allah ya bar ki da Yayan mu”.
Ganin za su makara yasa ta fara fita saying
“In Kun gama kwa zo mu tafi ai” da sauri suka ajiye suka bi bayanta.
Suna ficewa Yaya Sadauki ya shigo, da yake kayan da ya siya duk sun iso hakan yasa ya ɗebo masu aikin rabon, kowanne Part aka ba su nasu sai addu'a suke zabga masa, sauran kuma kai tsaye yace a wuce da su masallatai a rabawa mabuƙata kafin ya dawo. Bayan sun gaisa da Hajjaty ya mata sallamar cewa zai tafi Bauchi, addu'a sosai ta masa haka Alhaji Baba ma, bayan sun gaisa da Daddy ma ya faɗa masa, shi ma dai addu'ar ya masa daga nan Yaya Khalil yazo ya miƙa shi airport.
Haka kawai Aunty Mabruka take jin gabanta na faɗuwa, da ta ga hakan ya yawaita sai ta kira Ya Khalil tace yazo ya Kaita za ta gaida Mommah.
Bayan ya Kaita har ciki ya raka ta lokacin iya Hajja ce a parlourn tana kallon maimaicin wani tafseeer a AfrikaTV3.
Cike da girmamawa suka gaisa, Yaya Khalil ya gabatar da Aunty Mabruka matsayin matar Yaya Sadauki, nan Hajja ta ƙara sakewa da ita suna hira. Daga nan Yaya Khalil yayi musu sallama yace In ta gama ta kira shi.
A hanyar waje suka ci karo da Mommah, da ya gaida ta ta amsa kamar koyaushe tana kawar da kanta gefe. Da ta shigo kai tsaye ɗakinta ta wuce ba tare da ta dubi mutanen da ke parlourn ba bare su samu ran za ta kula su. Murmushin takaici Hajja tayi sannan ta miƙe tace
“Ina zuwa” ganin gun Mommah Hajjan za ta je yasa ta ce
“Ehm Hajja, ki koma ki zauna, zan je ai ba sai ta fito ba”
Ba tare da Hajja ta Musa ta ba ta dawo ta zauna tana ƙara yaba kyan hali irin na Aunty Mabruka.
Da sallama ta shiga ɗakin, ƙasa-ƙasa Mommah ta amsa saboda wajibcin hakan bayan ta yi tozali da halittar da take zargin ta jaza mata shiga halin da take ciki. A kan tabarma Aunty Mabruka ta Zauna tana wasa da ƴan yatsunta.
“Ina yini Mommah”
“Lafiya” ta amsa murya a kausashe. Tsawon mintuna arba'in babu wanda yayi magana a cikinsu, hakan yasa Aunty Mabruka ta ƙira Yaya Khalil tace mishi ta gama.
Cike da tsoro duk da cewa ta ga alamar buƙatar taimako da Mommah take ga shi ta fige tace “Ehm Mommah ki bani account Numbern ki don Allah”
Ai da sauri jin zancen kuɗi Mommah ta juyo ta dubi Aunty Mabruka. Fitar da tayi neman bashi taje amma bata samu ba, jikinta ne yayi sanyi tana shirin magana Aunty Mabruka tace
“Mommah don Allah ba don na raina ki ba ne kawai ina so na kyautata miki ne, Please....”
Abun da ta gama yi tana roƙon a ba ta bashi aka ƙi ga shi yanzu abun da ta raina yana roƙon ta da ta amince ta amshi kyautarsa.
Cikin wata raunananniyar murya kamar ba Mommah ba tace “Ai yanzu ba Ni da wata account already Daddynsu ya yi deactivating nasa”
Cike da tausayawa Aunty Mabruka ta fitar da nata ATM card ɗin ta miƙa wa Mommah. A hankali tace
“Pin ɗin 1990, ki riƙe shi a wurin ki don Allah, duk lokacin da kike da uzurin amfani ki cira a ciki, kada ki ce a'a Mommah”
Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Mommah, Aunty Mabruka ta share mata tana faɗin
“Please Mommah ki daina kuka, na tabbsta In Yaya ya Gani ba zai yi farin ciki ba.”
“Dole nayi hawaye Mabruka, na yi wasa da dama ta, meyasa bani da tunani? Yau abun da naje nema bashi aka hana ni sai ga shi na samu daga wurin mutanen da nafi ƙyamata a rayuwata ba tare da sun min laifin komai ba, na yi hasara a rayuwata Ni Sughrah”
Kuka ne ya ci karfin ta, Aunty Mabruka ji tayi kamar Hajiyar ta ke kukan hakan yasa ta matsa kusa da ita, ba ta san time ɗin da tayi hugging nata ba.
“Ya isa haka Mommah, don Allah ki yi shiru kada ki yi saɓo, ki ɗauka hakan a rubuce take zai faru, don Allah ki yi haƙuri, na san kina fushi da yaya amma ki yafe masa, kullum cikin zancenki yake sai dai yana tsoron tunkararki ne.”
Hawayen ta ta share tana faɗin
“Na gode Mabruka, Allah ya miki albarka ke da mijinki, ya sa albarka cikin rayuwar auren ku, sai na zo muku”
“Amin Mommah, sai kin zo”
Bayan fitarsu Mommah ta ƙara ɗaga ATM card ɗin da Aunty Mabruka ta bar mata, wasu irin zafafan hawaye na baƙin ciki da nadama ta share kana ta fito zuwa wurin Hajja. Bayan ta ba wa Hajja labarin komai murmushi kawai irin na manya tayi tace
“Ke ce kika kasa fahimta Sughrah, tun ba yau ba nake nuna miki hanya, ba a ƙyamatar Mutum saboda zuciya na ƙinsa, Rukayya tun ba yau ba na san cewa mutuniyar ƙwarai ce duba da irin yadda kike mata son ranki ba ta taɓa yi min wani kallo na rashin ɗa'a ba bare kuma zagi. Yanzu ya rage naki ki san me Yakamata kiyi.”
Cikin wata irin murya da ke nuna zallar nadama tace
“Ki yi haƙuri Hajja, kada ki ƙara bari na da hali na, ki yi wa Ubangiji ki yafe min, na bi ki na bi mijina, na bi Allah.”
Sai da Hajja taso yin dariya amma ta make tace
“Kin ga Habibah da Saudatu da kuke wa kallon masu son ki? Wallahi da za su samu dama su za su fara ruguza rayuwarki. Yanzu zan baki wani aiki, daga nan za ki tabbatar da me nake faɗa miki.”
“Abun da nake so da ke shine, ki kai musu ziyara har ita Ruƙayya ɗin, ki nuna musu buƙatar ki ta taimako, idan suka nuna a'a ki ce su ba ki bashi to....ina tabbatar miki kan kuɗi halin kowacce su zai bayyana gare ki, sai ki yi taka tsantsan da rayuwarki.”
Da wannan shawara suka rufe wannan babin, nan Hajja ta sake mata fuska karo na farko tun zuwan ta, sosai suka yi hira kamar ba su ba.
*Aunty Mabruka*
Bayan ta koma haka tayi ta al'ajabin yadda rayuwa ta mayar da Mommah, tabbas duniya ba abar tinƙaho bace ba kuma wurin zama ba, idan yau kai ne to gobe ba komai bane, sosai jikinta yayi sanyi.
*React and share fisabilillah!!!🙏🙏🙏😍😍😍, Much love my fans.*
[1/21, 10:03 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 3️⃣0️⃣
﷽
*ZAHRAH'S POV*
Bayan sun dawo daga school basu 'bata lokaci ba saboda zumu'din wayar da suke, duk da cewa tana jin wani iri a jikinta kamar wani ba'kon al'amari na tunkararta amma ta dake, suna dawowa babu wadda yayi lunch wanka kawai suka yi suka fita don tsabar mazari, gani suke kamar in ba su je yanzu ba abubuwan za su 'kare ne.
Cikin shigar Abaya da suka yi rolling veil akai suka fito, Zahrah wacce ke ri'ke da handbag nata da sauri ta juya ciki, ku'din ta kwaso daga nan kuma driver ya ja motar. Sosai suka hidimtawa sabbin wayoyinsu bayan sun sayi Sim cards sun yi register, daga nan kai tsaye suka koma gida suna 'dan banzan mazari.
Ganin har dawowarta ba ta ga 'kiran Yaya Sadauki ba yasa ta 'dauko wayarta ta lalumo numbernsa tayi dialling, five times tana 'kira amma shiru ba ya tafiya, ta ala'kanta hakan ne da ko baya bu'katar distraction but her mind did'nt believe with that statement, gabanta ne ke bugawa da sauri-sauri.
"He should have let us know ya isa lafiya Allah yasa all is ok"
ta fada cikin ranta. Girkin da ta tashi za ta yi ma fasa shi tayi saboda yadda gabanta ke fa'duwa.
A can 'bangaren su Hajjaty ma sun 'kira wayarsa amma dai amsar 'daya ce, not reachable, Yaya Khalil ya 'kira ya 'kara shima abun ya fara 'daure kansa, ba tare da ya sanar da kowa ba coz shima bai san specifically abun da Yaya Sadaukin zai yi a Bauchi ba tunda iya saninsu dai ba su da wasu ahalin a can sai dai in aiki ne ya kai shi.
*Ya Ishaq's POV*
Alhamdulillah, there's a little bit progress regarding his condition kuma yana coping yadda ya kamata sai dai deep down his heart is suffering, how he wish ko da sau 'daya ne ya kamata a ce ya 'kara kallonta, even once, amma tun da 'kaddara tai masa yankan 'kauna da ita ya amshi hakan tare da fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi saboda