Showing 123001 words to 126000 words out of 157517 words

Chapter 42 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5174

ka jin magana da kyau"
Kansa ya tsinta da biye mata yace "Abi?"

Bakinta ta turo tana faɗin "Eh mana." A shagwaɓe ta ƙara da "Yaya zan wuce." Kamar bai ji ta ba can yace "za ki wuce ina?" Bakinta gaba tace "Gun Mamah zan je."
Ba tare da maida hankali ga abunda tace ba yace "Oh Yah! Serve your husband first, am starving." Ɗauke da mamaki take kallonsa ba tare da ta bari idonta ya shiga cikin nasa ba.
"Uhm, Hajiya na ga duk kin sauya, nace I'm starving, ko so kike na mutu."
A shagwaɓe tace "Ai ban faɗi ba, let's go."
Daga haka suka nufi dining area tana gaba yana biye da ita yayin da yake nazartar yadda ta sauya gabaɗaya kamar ba ita ba, ta cika ta zama full grown up lady ga kuma wani shagwaɓa da ta ƙaro. Tana gama serving nasa ta miƙe za ta wuce, muryarsa ce ta doki kunnuwanta
"Wait Ma'am..." Waiwayowa tayi tana kallonsa sai ta shagala da hakan, yadda yake cin abinci, the way he talks, the way he dresses, the way he do everything makes him to be unique, Na musamman ne don komai kyau yake masa, a nashi ɓangaren abincinsa kawai yake ci sai dai lokacin da yaji kaifin idanuwanta a kansa ya ɗan ɗago for some seconds ya kalleta tare da ɗage mata gira irin why all this staring?.

Kau da kanta gefe tayi tace "Ba ka ci da sauri Yaya." Ba tare da ya kula ta ba yaci gaba da cin abincinsa har ya kammala, tissue ya zaro ya goge bakinsa tare da ɗaukar drink ya kurɓa Sannan yayi hamada. Ganin ya kammala yasa ta mayar da hankalinta kwacakom gare shi yayin da shi kuma yake ƙara lura da yadda Lilynsa ta sauya don shi mamaki yake wai wannan itace Lilyn da ya bari wasu shekaru baya. Kamar ba zai yi magana ba dai can yace "Lily..." Kanta ta ɗago tana kallonsa, suna haɗa ido kuma ta janye kamar wata matsoraciya.
"Where's your phone?"
"Phone?" Ta maimaita after him
Gira ya ɗage mata for confirmation. Cikin kame-kame tace, ban san yadda yake ba Yaya."

Shirun da yayi bai ce komai ba yana tabbatar mata da cewa yana buƙatar ƙarin bayani ne daga gare ta. Nan ta faɗa masa cewa tun ranar da aka kai ta asibiti ba ta ƙara ganinta.
"Ok" ya furta can ƙasan maƙoshi "ina so mu yi magana ne zuwa anjima da dare, amma dai kafin nan in na fita zan taho miki da wani, ok?"
"Yea! Thank U so much Yaya." Ta ba shi amsa tana murmushi wanda ya ƙara haskaka fuskar ta, ba tare da Ya Sadauki ya kula ba ya tsare ta da ido yana ƙare mata kallo. Kukan shagwaɓarta ne ya dawo da shi kan hanya tare da fito da idanunsa waje.
"Wetin?" Ya tambaye ta
"To ba kai ne ba? Ni ka bar kallona."
Cike da wayancewa yace "Ni nake kallonki ko dai ke ce kika tsare Ni da kallo eh?" Kamar za ta yi kuka ta miƙe tare da barin wurin, murmusawa yayi har sai da haƙwarensa suka bayyana, a zahiri yace "She's damn cute, supercool and special..." Da haka ya miƙe ya bar part ɗin.

*React please, we're around an ending spot ooo*


[27/04, 7:31 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 5⃣8️⃣




Murmusawa tayi kafin ta tashi. Ɗakin Mamahn ta koma a karo na biyu ta ƙira Nasreen ɗin, daga nan ta koma nata bedroom ɗin. Ba a jima ba sai ga Nasreen ɗin ta zo.
Cike da tsokala tace "Amaryar Yaya Sadauki ya ne? Ko dai ta samu ne?"
Hararar wasa Zahrah ta wulla mata saying "Ki faɗa dai bakin ki, kin ga Ni ba wannan ba, har ma an barbaɗa miki ki ce?"
"A Toh, so kike a yi shiru da irin wannan abun alkhairin?"
Shiru Zahrah tayi can tace "To ya son ran ki? Ya kike gani Nasreen, kina ganin Yaya zai iya zama da Ni matsayin matarsa kuwa?"
Da sauri ta ba ta amsa da "Why not? Me kike tunani haka."
Shirun ta ƙara yi kafin tace "Kawai gani nake kamar ba zai zauna da Ni ba, ki duba fa, kyakkyawan mutum irin Yaya Sadauki mai ji da kuɗi da izza zai so Zahrahn Mamah kuwa?"
"Babu shakka, Kinga Zahrah, ki ma cire wani doubt ta kike da shi kan Yaya Sadauki, ke fa mace ce, macen ma wacce namiji ba zai iya ɗauke kai kanki ba, kina da duk wani abu da namiji yake so, ina tabbatar miki ba Yaya Sadauki ba ko Yaya waye zai so ki."
"Uhm, Allah yasa."
"Kin san me kuwa Nasreen?" Kai ta jijjiga Mata alamar a'a.
"Wallahi I'm dying for Yaya, ina son shi da ruhina da kuma zuciyata, na daɗe ina son shi, sai dai na fi so shi ya fara furta min kalmar soyayya kafin Ni, Nasreen in da a ce ban auri Yaya ba, wallahi ko wa na aura gangar jikina kawai zai samu ban da zuciyata because it's already meant for him, my heart only beats for him, Ni dama can wallahi kullum gani nake kamar zai dawo gare Ni, ashe dai Yaya kam ba mutuwa yayi ba."
"Eh wallahi Zahrah, ƴan baƙin ciki kuma sa mu tunda ya dawo, ke dai yanzu ya ake ciki, don yadda naji Hajiya Babba na faɗi next week za ki tare gidan Yaya Sadauki."
"What?" zahrah ta tambaya sounding so furious, kai kawai Nasreen ta jinjina mata sannan tace
"Ko ba kya so ne?"
"A'a fa..." Dariyar da Nasreen ke yi yasa Zahrah dasa aya
"Lafiyarki Nasreen?"

"Ragas ma kuwa?"
"Allah ya shirye ki to, Ni dai ba ma wannan ba ke, batun wannan maganar da nace mu tuntuɓi Ya Khalil, inaga yanzu kam tunda Yaya Sadauki ya dawo da shi za mu yi, amma dai not now, mu ɗan jinkirta."
"Mu jinkirta kuma Zahrah? Ain't U afraid of something bad to happen before that time? Da kunnena fa naji suna faɗin tarwatsa familyn mu." Ta Idasa cikin raunananniyar murya.
"Haka ne, anjima Yaya Sadauki ya ce zai kawo min waya, inaga akwai abunda yake son sanar da Ni, in Mun gama zan tuntuɓe shi da zancen."
"Da ya fi kam, don wallahi Ni yanzu kowa tsoro yake bani musamman da ba mu san su waye mugayen nan ba, Allah dai ya tsare mu."
"Amin Nasreen."

Ana kiraye-kirayen sallar maghrib Ya Sadauki ya aiko da sabuwar iPhone 16 pro max ma Zahrah, tare da miƙa mata sim cards nata na waccar wayar da ta fashe, cike da mamaki ta amsa tare da kunna wayar ganin har ya saita komai. Bayan ta yi sallah tana addu'o'in da ta saba wayar ta fara ringing. Da sauri ta ɗauko tare da dubawa, gani Yaya Sadauki yasa tayi picking da sauri tana mai yin sallama. As usual, cikin sassanyar muryarsa ya amsa mata, lumshe idanunta tayi saboda tsananin shaukin da muryarsa ta haifar mata.
"Are you there?"
Kamar tana gabansa ta fara ƙyakƙyafta idanuwanta "Yea, ina yini Yaya."
"Lafiya lau...ina jiran ki a garden." Bai jira amsar ta ba yayi ending call ɗin.

Da sauri ta shirya sanin bai son jira, turaruka ta fesa sannan ta fice, a parlour ta ci karo da su Hajjaty da Aunty Salmah. Bayan sun gaisa Aunty Salmah tace "Amarya ina zuwa ne? Ko dai angon ke kira ne?" Cike da jin kunya Zahrah ta juya ta fice da sauri ba tare da ta amsa kiran ba. Har ta isa inda yake bai san ta iso ba sakamakon duniyar tunani da ya faɗa, ƙamshin da ya cika ƙofofin hancinsa ya tabbatar masa da isowarta, gyaran Muryar da tayi yasa ya ɗan zabura yana gyara zamansa. Kujerar da ke facing nashi ta zauna tana ajiye phone nata kan table ɗin da ke gabanta.

Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanuwansa, lokaci guda wata irin nutsuwar zuciya ta samu wuri a ƙirjinsa yayin da yake jin wani irin farin ciki maras misaltuwa. Tsawon mintuna biyu suna zaune shiru bayan sallama, Zahrah da ke jinta cikin yanayi na jin daɗi da walwala yasa ta lumshe idanunta tana ƙara yaba gayu irin na Yaya Sadauki, duk irin turarukan da ta shafa lokaci kaɗan ƙamshin daddaɗan turarensa ya danne nata. Har ta cire ran zai magantu ta tsinkaye shi yana faɗin
"Kina lafiya Lily?"
"Eh lafiya na lau, and my Yaya?"
Duk da ba yau ne karo na farko da ta ƙira shi da nata ba sai dai na yau ɗin ya tsaya masa a rai, yadda ta faɗi sunan yasa ya murmusa tare da faɗin
"Alhamdulillah, same here."
A hankali ta furta "na ga saƙo Yaya, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara..." Yatsantsa ƴar manuniya ya ɗaura kan cute Lips nasa, hakan yasa tayi shiru itama.

Gyaran murya yayi tare da gyara zamansa, yadda facial expression nasa ya nuna seriousness yasa ta nutsu tare da sunkuyar da kanta ƙasa lokaci guda kuma jin nauyinsa ya mamaye ruhinta.
"Lilyyy " ya ƙira sunanta a sanyaye, giving him her total attention ta amsa da "Yaya...."
"Magana nake son yi da ke, and ina son ki faɗa min gaskiya kada ki ɓoye min komai, ki faɗa min zallar gaskiyar ki ko ya take I'll accept it, ok?" Kai ta gyaɗa tana ƙara mayar da hankalinta gare shi.
"Kin san bawa ba ya taɓa gujewa ƙaddarar da mahalicci ya tsara masa haka ne?"
"To, kamar dai hakan, da Ni da kuma ke har ma da iyayenmu babu wanda ya taɓa tunanin aure zai ƙullu tsakaninmu."

Dim! Gaban Zahrah ya buga, fatanta dai kar Yace ba ya son ta.
"Cikin ikon Ubangiji sai kuma ga shi Allah ya sallaɗa hakan, before I go deep, lemme extend my heartfelt thanks to you Zahrah for everything, kin kula da Little tun yana shan nono, kin ɗauki risk kin sa ma rayuwarki just to see my own seed grew, Allah ya saka miki da alkhairi."
"Amin Yaya, amma dai godiyar ta isa, what I've done is something compulsory on me, ka ɗauke shi kawai Matsayin hakan, matsayinka a wurina ya wuce hakan, ba zan taɓa barin ko da bishiyar da ka shuka ta mutu ba don ka gusa, Allah ya raya mana Little."
A takure ta ƙarasa maganar saboda yadda idanuwansa ke yawo kanta, sosai ta ƙara sace masa zuciya da kalamanta masu hikima, cikin ransa yana ƙara godewa mahallicinsa da ya azurta shi da Ƴar'uwa kuma mata ta gari.

"Ameen Lily, As I said ina son ki faɗa min gaskiya, kada ki sa komai ran ki ko meye ki faɗa min, za ki iya zama da Yayanki a matsayin mijin aure ko kuma kina son komawa ga masoyinki da yanzu ya dawo hayyacinsa?"
Yanayin yadda ya ƙare tare da kai aya yasa jikinta yin sanyi lokaci guda kuma zuciyarta ta fara saƙa mata furta eh ko a'a saboda ta tsira da ajinta. Opportunity comes at ones, hakan yasa ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya.

Nazartarta Yaya Sadauki yake a natse sannan yace "Lily.." diri-diri tayi tana famar tattaɓa wayar ta da yatsarta.
"Just feel free, zan fahimce ki, ko kaɗan ba na son damuwarki... I want you to have a better life just like Little."
A sanyaye tace "Yaya how on earth kake tunanin I'll say no to you? U deserved to be loved, mata nawa ke jiran samun kwatankwaciyar damar da na samu? Why zan yi denying rahamar Allah, ko ba don kasancewar ka ɗan'uwa mafi soyuwa gare Ni ba, yadda kayi kokarin ɗaga mutuncin iyayenmu ma ya kai na zauna da kai, ballantana kai ɗin fa majingina kuma garkuwar Zahrah ne! I'm ready to live with you Yaya."

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da hadiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi, shafa kwantaccen sajensa yayi har ya kai kai sumarsa da ta sha gyara, can ƙasan maƙoshi ya furta "Alhamdulillah, thank you Zahrah, ina roƙon Allah ya tabbatar mana da alkhairi cikin rayuwarmu."
"Aamin"

"Now tunda na san ra'ayin ki, sai a fara shirye-shiryen biki ko in ce tarewa, Daddy yace kada ya wuce next week. Kiyi list na abubuwan buƙatarki gobe sai ki faɗa min, as for the matter of lefe, Mommy Salima suna haɗawa."
Ba tare da tunani ba tace "waɗancan na wurin Yaya Ishaq ɗin fa? Ai su ma sun isa ba sai ka ƙara wasu ba."
Hankali kwance ta faɗa ba tare da kawo wani tunanin ba. Fuskarsa ya haɗe yana faɗin
"You still love him Abi?"
Rau-rau zahrah tayi da ido ta ma kasa furta komai sai jijjiga kai take.
"Then yane in ba haka ba?"
Jin ta samu dama yasa tace "I don't mean anything bad Yaya, kawai dai sai naga kamar zai zama almobazzaranci ne."
"Ni nayi wancan ɗin?" Jijjiga masa kai tayi shi kuma yace
"Kuma kike cewa almobazzaranci?"
"I'm sorry Yaya" ta ba shi amsa da sauri.

Numfashi ya sauƙe kana yace "Is ok, ba ma za ki yi amfani da waɗancan ɗin ba, You better know that, za a kyautar da waɗancan."
"Duk yawansu?" Ta tambayi kanta.
"An fara kiran sallah, mu je ki koma ciki sai na wuce masallaci, and don't hesitate to tell me anything you want, I'm now husband not only brother ok?"
Kai ta gyaɗa masa tare da faɗin "thanks Yaya." Daga nan suka jera har part ɗin Hajjaty, sai da ta shige kafin ya juya yana sakin wani murmushi, a haka ya wuce mosque.

Bayan ta yi sallah ta yi dinner sai da ta watsa ruwa, ta watsawa Little da ya kafe yau a gunta zai kwana,, kayan bacci ta sanya masa ita ma ta saka, sai da ta musu addu'a tukun ta ja bargo duk kuwa irin zafin da ake sheƙawa. Ƙarar wayar ta ne ya hana ta ƙarasa rufa musu blanket ɗin. Ganin Yaya yasa ta murmusa tare da picking call ɗin.
Hira sosai suka yi da daren sannan suka yi sallama, kowa ya kwanta da tunanin ɗan'uwansa.

*Washegari*

Tare da Nasreen da Aunty Salmah da suka shigo gaida Hajjaty ita da Aunty Na'ima suka tsara komai, list suka yi daga nan suka damƙa mata duk da cewa ita ba wata bidi'a da take so a yi a tarewar a nata son ran da tarewar kawai aka yi, amma naci da son hidima irin na su Aunty Salmah yasa suka ce sai an yi musu ƙasaitacciyar walima da dinner. Bayan sun tafi ya kirata, sun daɗe suna hirarsu tukun ya buƙaci list ɗin, ba su jima ba daga nan suka yanke kiran. Cikin ƙanƙanin lokaci ga shi sabo ya ɗinku tsakaninsu fiye da wadda suke da shi a baya.

*React and share fisabilillah*

[28/04, 8:51 AM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 5⃣9️⃣





*RUMANA...*

Cikin ƴan kwanaki duk ta bi ta rame saboda jarabar da ta saka gaba, babu kunya uwar goyonta kuma sai famar naniƙewa Mommah take, tun ranar da suka fahimci cewa akwai aure tsakanin Zahrah da kuma Yaya Sadauki suke ƙoƙarin ganin sun lalata komai sai dai Kuma Allah ya fi su, duk ta yadda suka ɓullo sai sun samu matsala, hakan yasa Rumana ƙara tsanar Zahrah, ta kuma yi munanan alwashi kan Zahrahn.

Kwanci tashi asarar mai rai, in ji Malam bahaushe. Yau ta kama talata, gidan Ya cika maƙil da jama'a kamar dai yau ake ɗaurin auren, a yau ne kuma devil KLANS 😈 ke shirin tarwatsa auren, yau suke so auren ya tsinke don sun gano cewa aka yi wannan aure ba ƙaramin faɗuwa darajar ƙungiyarsu za ta yi ba, uwa uba kuma ƙarfinsu da tasirinsu duk zai ragu, cikar burinsu kuma zai hau keken ɓera. Hakan yasa tun kafin Tariyar suke son lalata komai.

Yaya Sadauki kuwa Allah Allah yake asabar tayi akai masa matarsa ɗakinsa, matar da bai taɓa tunanin zai mallaka ba, matar da bai san yaushe ya fara sonta ba amma daidai lokacin nan yana jin zai iya ba da rayuwarsa a kanta. Around 11:06am Na safe ya ƙirata suka sha hirarsu, daga nan kuma suka rabu cike da kewar juna.

A yau na ga tasirin azkar ɗin safiya da marece, in taƙaice muku daren yau duk yadda suka so ganin sun lalata komai abun ya faskara, hakan ba ƙaramin fusata magajiyar Uwargijiya yayi ba, ta yi wa dodo alƙawarin in dai ya tarwatsa wannan tariya za ta sadaukar da mahaifarta gareshi. Cike da zullumi suka ƙare meeting ɗin wanda kowa ya tafi zuciyarsa babu daɗi. Haka dai ranar Laraba ma suka yi amma tasirin azkar dai ya hana su cimma matsaya.

Ranar Alhamis aka kawo lefen Zahrah wanda suka linka wancan kyau, yawa kai har ma da tsada, haka dai jama'a sai yabawa suke, ƴan baƙin ciki irin su oo kuma sai tura baki ake ana ɗage ɗaurin kwali. Bayan maghrib Yaya Sadauki ya zo wajenta, kayan da ya karɓo direct daga wurin ɗinki ya miƙa mata nata jakan wacce ke ɗauke da kayan da za ta yi amfani da su a bikin, godiya ta masa daga nan suka yi sallama. Ganin ta shiga yasa ya juyo zai wuce can gidan da za su tare yaga ko masu aikin sun kammala komai, motarsa ya faɗa ya ja ta, ya yi nisa can ya kai bayan buildings nasu, wurin da babu kowa, yana shirin yin cornern da zai sada shi da gate ɗin nasu mansion ɗin na jikoki wata akuya mai ciki ta bayyana gabansa, bai iya take burki ba kawai ya bugi akuyar,
"Subhanallah" ya furta yana cin birki tare da mamakin ta ina akuya ta shigo estate ɗin don a iya saninsa gidan gonarsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login