Showing 18001 words to 21000 words out of 157517 words
amma ina jin matuƙar tausayinsa Nasreen”
“Hmm Zahrah nima ina fatan kamar zuwan ki zai sauya abubuwa da dama da suka shige ma ahalinmu duhu”
Jiki sanyaye Zahrah tace “Wallahi tun yanzu naji ina son kasancewa hakan, kuma na saka raina In har na samu damar hakan zan yi yadda ya dace don kawo sauƙi ga radadin da ƴan uwa na suke ciki. Yanzu ki fada min please me ya faru?”
Dogon numfashi Nasreen taja kafin ta ce “Daf da zuwan ki ne abun ya faru _A babban gida_ wanda ya ɗaure kusan kwanyar kowa. A yadda na faɗa miki yaya Sadauki mutum ne da sha'anin mata baya gabansa, bazance gashi yadda abun ya faru ba amma dai naji zancen wai an kama shi ne da shirin raping Aunty Mabruka dai ta gidanmu, idan aka miki bayanin yadda abun ya kasance zaki san cewa shiri ne, don kuwa bayan tafiyarsa ne saboda ɓacin rai su Hajjaty suka farga da hakan, an tsara da gayya na farko don a raba tsakanin sa da Hajiya Babba, na biyu kuma akwai wani boyayyen al'amarin da nake kyautata zaton faruwar sa babu jimawa, Zahrah da ace ina da yadda zanyi ba shakka da tuni nayi don gano gaskiya, Yaya Sadauki don't deserve to be treated that way, duk irin yadda nake fada miki tsaurin sa amma fagen kyautatawa da mutunta na gaba babu ya shi Zahrah, kinga babu jituwa tsakanin Hajiya Babba da Mommah amma Yaya Sadauki baya duba hakan, duk gidan nan babu wadda yake mutuntawa sama da Ita cikin iyaye mata dake cikin ahalin nan, idan tafiya yayi zai dawo, tsaraba baya bambanta wani da wani....”
Kuka ne ya ci ƙarfin ta, cike da tausayawa Zahrah ta fara lallashinta wanda itama ƙarfin zuciya ne kawai. Bayan Nasreen ta dakatar da kukanta shiru ne ya wanzu na wani lokaci kafin Nasreen tayi ma Zahrah sallama.
Ko da Nasreen ta wuce sashen su, Zahrah tunani ne birjik cikin ranta na son samo maslaha ga wannan alhali. Ganin bacci yaƙi ɗaukar ta ya sa ta shiga toilet ta ɗauro alwala, nafila raka'a huɗu ta jera, sannan ta ƙara da witri. Daga nan ta roƙi Ubangiji kan ya kawo mata hasken da zai kasance jagora gare ta wajen saisaita komai cikin sauƙi. Daga nan kuma ta fara raira Alqur'ani, tana cikin yi ne bacci ya ɗauke ta kan sallayar.
Misalin ƙarfe 2:30am ta farka a firgice jikinta na ɓari, da ƙyar ta samu zarrar furta innalillahi wa inna ilaihi rajiuun. Ba komai tayi mafarki ba sai ɗaya daga cikin matan da tarar a parlourn su Nainarh (kamar yadda ƙwaƙwalwarta ta hasaso mata) tana bin ta da matsiyacin gudu hannunta kuma riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa wacce ke fidda tartsatsin wuta.
Bata kai ga cin mata ba sai ga wani haske mai ƙarfi gaske ya bayyana, tuni Zahrah ta samu nasarar shigewa cikin hasken wanda yayi daidai da isowar matar wajen sai dai ta tsaya tana haki a gaban hasken alamar ba zata iya tunkararsa ba.
Daga haka Zahrah ta farka, nan ta ɗauro alwala ta ƙara jera wasu four Raka'at ɗin sannan ta faɗawa Ubangiji damuwarta cikin sujjadarta. Daga nan ta fara karanta Alqur'ani har alfijir ya keto.
*London*
Tabbas ya Sadauki ya jima bai samu irin baccin da yake yi ba yau, hasali ma zai iya cewa tunda ya zo London bai taɓa yin baccin ba ma saboda tsantsar damuwar da ta cika kogin zuciyarsa, bashi da wani aiki sai tunani, idan daren ma yayi babu abun yi sai tunani, sai kuma in ya gaji ya ɗaura da ƙiyamullayli. Tunda ya rike wannan tsayuwa ta dare kuwa babu makawa Ubangiji zai tsaya masa, zai kuma kare shi daga sharrin makiya sannan zai tabbatar da samar masa da hanyoyin cigaba a rayuwa duk da wasu basu son hakan.
Da misalin 4:20am ya farka ɗauke da addu'ar bacci a bakinsa. Bai miƙe ba yana kwance har bayan wasu daƙiƙu. Ba komai ya ke yi ba sai ƙoƙarin tuna mafarkin da yayi da kuma mamakin ta ya aka yi har bacci ya ɗauke shi bayan tun ba yau ba ya guje masa.
Lumshe idanuwansa yayi, a lokacin kuma komai ya fara dawo masa. Ajiyar zuciya ya sauƙe wondering who's that light? Wane haske ne ya tunkaro shi!? Kuma wace murya ce take wannan amo da yaji?
“Ya Allah” ya furta tare da sakin wani gauron numfashi sannan ya miƙe tare da shiga toilet ba tare da ya tashi ya Khalil da ya taya shi kwana ba.
Sai da ya gabatar da raka'atanil fajri sannan ya zauna kan praying mat ɗin yana ambaton Ubangiji. Ganin kamar lokacin salla yayi yasa ya gabatar da tasa, sannan ya karanta azkar ɗinsa kafin ya tashi Yaya Khalil Wanda da ƙyar ya tashi.
Kayansa ya fara haɗawa cikin trolley don ji yake kamar garin ba zai gama wayewa ba, ya ƙosa ya koma gidan da yayiwa rani. Allah Allah yake ya koma domin fara sabon shirinsa, tabbas shine ƙarfin guiwar kansa da ma ahalinsa, sannan kuma ƙarfin guiwar partner ɗinsa da ya gani tana taimaka masa cikin mafarki.
Har yaya Khalil yayi sallarsa bai daina mamakin wannan sauyin na ba zata da aka samu ba. Sauyin da ya matuƙar bashi mamaki tare da alerting nasa cewa something fishy is happening right now.
Cike da mamakin da ya kasa dannewa yace..
“Man! What a sudden change! Allah dai yasa wannan annashuwar da na gani tattare da kai ta dauwama da kai.” sai kuma yayi shiru. Yaya Sadauki bai tanka masa ba sai ma cigaba da haɗa kayansa da yake yi.
“Wai duk zumuɗin na meye?, Mu da zamu bi Flight ɗin 10 shine tun yanzu kake haɗa kaya”
“I'm eager to be home coz finally my strength is home!”
A zabure Yaya Khalil ke dubansa yana son ƙara tabbatarwa kansa cewa shi din ne yayi maganar ko kuma dai wani daban?. Bai tsinke da mamaki ba yaji ya ƙara faɗin.
“With my strength! In Allah's name zamu gano komai and dude!” sai kuma ya dakata
“I swear by almighty God! Duk wanda muka gano responsible for that wallahi ba zai sha ba” ya idasa in a bitter voice.
Kai Yaya Khalil ya jijjiga yana ƙara jaddada ikon Allah, tare da fatan Alkhairi ma abokinsa, amininsa kuma ɗan uwansa.
“Ehm man za mu faɗawa Alhaji Baba batun dawowarmu ne ko kuwa!?”
Cike da isa da taƙama yace
“Don't worry dude!, I'll handle that.”
Shi ma Yaya Khalil shiru yayi don ya san ko ya ja maganar yaya Sadauki ba barinta zai yi tayi tsawo ba. Daga haka ya naɗe praying mat ɗin tare da komawa kan bed ya bar mallam zumuɗiyo sai ha abubuwa yake yi.
*Akwai baƙin al'amura da ke Kunno Kai zuwa rayuwar Zahrah A Babban gida! Fatan mu su zo da Alkhairi*
*Ga kuma su yaya Sadauki kan hanyarsu ta dawowa? Ko me zasu tarar a babban Gida? Meye kuma zasu kawo babban Gida?*
*Kuyi share tare da react in har kuna so na ci gaba da update!*
*Group members a taimake Ni a gwangwaje Ni da comments don Allah, hakan ne kaɗai zai sa naji ƙarfin guiwar yi muku update gobe.*
*I love You my esteem people.*
# diamond_bhatool
# Yayasadauki
# Zahrah
# a_babban_gida
[12/8, 8:04 AM] Diamond Bhatool: https://chat.whatsapp.com/Fw6rJSk0GuxKd8IGqbsf35
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
*PAGE* 0️⃣9️⃣
﷽
Yana gama haɗa kayansa ya zauna bakin gadon yana maida numfashi. It has been long time since he have such beautiful and awesome night ga kuma bright morning da yake hasashen samu. Murmushi yayi a karo na farko wanda ya ƙawata kyakkyawar fuskarsa, (Ni Bhatool sai naji kamar kar ya daina😳) da sauri ya janyo wayarsa yana duba time. Ganin 6:29am yasa ya ɗan ja karamin tsaki, gaba-daya agogon kansa baya masa gudu. Gani yake kamar garin ba zai waye ba.
Kishingiɗa yayi ya kwanta, nan bacci ya kwashe shi unknowingly. A zabure ya miƙe kamar wadda aka tayar. Dage kansa yayi lokaci guda yana tunanin meye matsalar? Da sauri ya ɗauki wayarsa da saƙo ya shigo cikinta a lokacin.
Tsaki ya ja bayan ya karanta saƙon. Kamar koyaushe Rumana ce sending him morning sms, ita ta San ma me take yi coz har yau ko number ta Bata samu arziƙin saving ba, to in zai yi saving bai san waye ɗaya daga cikin ƴan matan gidan ba da suka kasance marasa aji (kamar yadda yake faɗi.)
Ganin 8:10am yasa ya shiga call log nashi, babu wasu important calls, mostly Kiran Mommah ce wanda yawanci ma missed calls ne, scrolling yayi amma bai ga number da yake nema ba.
“Shit!” ya furta tunawa da yayi blocking number kwanakin baya. Da sauri ya danna unblock tare da dialling number. Bayan an ɗaga ya gaida Alhaji Baba cike da mutuntawa
Alhaji Baba ya amsa fuskarsa sake kamar yana ganinsa, farin ciki sosai ya rufe shi ganin yau jikan nasa ya neme shi. Bai tsinke da mamaki ba sai da yaji muryarsa na faɗin.
“I'm on my way Alhaji, but don't let anyone know! Iya Hajjaty zaka sanarwa and ka ce mata ta yi min gurasar Nan da take yi mai daɗi. I'll be landing soon.”
Cike da farin ciki Alhaji Baba ya amsa da “Ok babu damuwa sai kun dawo”
Nan ya jera nasa addu'o'in a sauƙa lafiya daga nan suka katse kiran.
Duka ya kaiwa Yaya Khalil Wanda ya tashi a zabure. Kamar ba shi yayi dukan ba kuma sai ya make
A harzuƙe Yaya Khalil yace “Why such drum! Kaji zafi kuwa! Gaskiya man Bana son tashi da duka, kayi min magna kaga In ban tashi ba”
Kafada ya dage tare da faɗin “Mallam ka samu ka shirya don Ni ba jiranka zanyi ba” daga haka ya shige toilet ba tare da ya ƙara kallon yaya Khalil ɗin ba.
Baki sake Yaya Khalil yake kallon Yaya Sadaukin har ya banko ƙofar toilet ɗin.
Wane sashe na zuciyarsa kuma na farin ciki da sauyin da ɗan'uwan nasa ya samu cikin ƙanƙanin lokaci.
************************************
*Nigeria, FCT, Abatcha estate*
Tun bayan kammala wayar da Alhaji Baba yayi da yaya Sadauki, kai tsaye ya sanar da Hajjaty cewa Allah ya amsa addu'ar ta, jikallenta na hanya. Zo ka ga murna wurin Hajjaty kamar ta taka rawa.
Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa ta shiga kitchen da kanta ta duba meye da meye zata bukata!, Sai da ta tabbatar komai da zata yi amfani da shi akwai shi tukun ta shiga Bedroom ɗin Zahrah wacce ke ta kwasar baccinta hankali kwance..
“Zahra'u Zahra'u”
“Uhmmm”
“Baki tashi ba dama?, Kinga ba sai kun tashi ba dama zan ce miki anjima zaki tays Ni yiwa Yayanku abinci ne, suna kan hanyar dawowa.”
Duk da cewa baccin bai gama sakin Zahrah ba amma kalmar Yayanku da Hajjaty ta ambata yasa taji gabanta ya faɗi sai ta tsinci kanta da tashi zumbur har sai da Hajjaty da ke shirin juyawa ta dara.
“lafiyarki kuwa?”
Cikin Muryar bacci ta furta
“Kince yaya na zai dawo?”
Murmushi Hajjaty tayi ta bata amsa kai tsaye
“eh, baccin ya isa ki tashi ki samu ki kimtsa jikinki sai mu samu mu gama da wuri, zaki raka Qasim dauko shi daga airport ai?”
Jiki mace ta tsinci kanta da faɗin “Eh”
Bayan Hajjaty ta fita Zahrah ta sheƙa wankanta sannan ta sanya ɗaya daga cikin kayayyakin da Nasreen ta kawo mata, daga nan ta nufi dining. Sai da tayi breakfast kafin ta nufi kitchen ɗin, ganin Hajjaty bata nan yasa ta nufi Bedroom ɗin ta don ta tambaye ta me zata fara kafin ta zo.
Ko da Hajjaty ta sanar da ita abubuwan da za'a yi sai ta juya zuwa kitchen. Cikin ƙanƙanin lokaci Zahrah ta gasa gurasar, ƙamshinta kuwa har Bedroom ɗin Hajjaty.
Ganin yanayin zafi da ake yi lokacin yasa ta fara haramar dama abun sha, duk da cewa bata san wane yayan nata ne zai dawo ba sai ta ji kamar ta fasa yi ganin akwai drinks iri-iri a gidan ta yadda ba lallai ma abun da ta haɗa ya zama ya samu ko da kallo ne daga garesu ba.
Wata zuciyar ce ta ce mata a'a ki yi, ki da basu sha ba ai kinyi, and zasu ga kin mutunta su. Da wannan shawarar ta samu ta haɗa zoɓo mai kyau wanda ƙamshin sa kaɗai mutum ya ji sai ya so da kuma fatan harshen da ya dandana.
Bayan ta gama ta koma ta watsa ruwa sannan sanya wasu kayan.
Tana gamawa ta nufi Bedroom ɗin Hajjaty don sanar da ita cewa ta kammala, sosai Hajjaty ta nuna jin daɗinta sai albarka take saka ma Zahrah.
*Nnamdi Azikwe international airport, FCT*
Ƙarfe sha ɗaya daidai jirgin yayi landing a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, tsawon wasu daƙiƙu bayan daidaita tsayuwa da yayi passengers suka fara fitowa.
Sanye yake cikin fatan riga kirar Armani, sai kuma p-cap da ya sanya da alamar dai baya son a gane shi ne. Garin three quarter ya saka sai wani farin takalmi say ciki.
Fuskar nan ɗaure ya sauko daga matakalar Benin, biye da shi kuma ya Khalil ne wanda sabanin ya Sadauki shi fuskar sa a sake take.
Wayar shi ya fitar sannan ya kara a kunne alamar dai kira yayi, can kuma ya sauke tare da kallon gefensa. Tun kafin ya ƙaraso Alhaji Baba da ke tsaye ya ƙarasa gare shi tare da rungume shi.
“Nayi kewarka sosai”
Ya faɗa can kasan maƙoshi.
Sake shi Alhaji Baba yayi jin Muryar ya Khalil yana faɗin.
“Tare da Ni fa muke tafe.”
Shi wallahi tsabagen farin cikin ganin Sadaukin sa yasa ya manta ma da cewa tare da Khalil suke. Murmushi irin na manya yayi yana faɗin “mu samu mu wuce gida ku huta ko?”
Kai suka gyada, nan ya Qasim da ke tsaye yana kallon su gwanin ban sha'awa ya wuce zuwa wurin da motar su tayi parking, nan yaya Khalil ya shiga front seat, su kuma Alhaji Baba da Sadauki sa suka zauna gidan baya.
Kai tsaye estste ɗin su suka nufa, bisa umarnin Alhaji Baba suka tsaya a ɓangaren su. Bayan sun daidaita parking suka dunguma baki dayansu.
Babu kowa a parlourn hakan yasa duka baje kan kujerun da ke parlourn yaya Khalil na korafin wai ya gaji Alhaji Baba da ya Qasim sai dariya suke masa. Hayaniyarsu yasa Hajjaty fitowa da sauri don tabbatarwa kanta cewa su din ne.
Ganin da gaske su ɗin ne yasa ta ƙarasa wurin nasu tana sakin kukan farin ciki na ganin shalelen jikanta. Da sauri duka suka juyo suna kallon ta. Cike da zolaya yaya Khalil ya ce “Ya da kuka kuka Hajjaty, gaskiya zan sa ɗan'uwa na gaba mu koma tunda baki farin ciki da zuwan mu”
Dariya dukkansu suka yi banda Hajjaty dake hararar Ya Khalil ɗin sannan ta ƙaraso gefensa ta zauna tana faɗin “To ja'iri ku koma mana”
Yaya Khalil ya ce “Ai don ina tausayin halin da zaki shiga ne In na ɗauke miki shi da kin ga aiki da cikawa ”
Ya idasa yana mata gwalo.
Danƙwalon sa tayi tana faɗin “ kaga Ni ban Don kai na fito ba” sai kuma ta mayar da kallonta ga ɓangaren da Yaya Sadauki ke zaune fuska babu yabo babu fallasa
“Ga don wanda na fito ”.
Nan suka kwashe da dariya bako dayansu , daga nan kuma aka fara gaisawa. Sai a lokacin Hajjaty ta tuna da Zahrah da ke kunshe can a Bedroom dinta.
“Zahra'u Zahra'u” dim dim zuciyarsa ta buga jin bakon sunan da Hajjaty ta ambata sai kuma ya waske yana tunanin ko sabuwar mai aiki ce.
Ɓangaren Zahrah ta ji shigowar su har ta mike zata fito sai kuma ta gargadi kanta ta koma yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Ko da Hajjaty taji karar rufe kofar sai kawai tace “Ki kawo ma su Yayanku abun sha ko?”
Ta gefen ido yake kallon mai fitowa daga wannan dakin, haka kawai yaji gabansa na faduwa da fitowar ta sai kuma yake ji a ranar yana biɗar kallon wannan sabuwar mai aiki. Tunanin sa ya katse nr jin kalaman Hajjaty na Yayanku, sai kuma zuciyarsa ta fara raya masa ko dai cikin ƴan matan gidan ne.
Tunanin sa ya katse ne yayin da sallamarta wurin ta rike dodon kunnuwansu. Zuciyarsa ne ta bada Wani sauyi Na daban sai dai a zahiri ba zaka fahimci hakan ba saboda hankalinsa kwacakom ya mika shi ga wayar da yake dannawa.
A ɓangaren yaya Khalil shi ma abun da ya faru kenan, sallamarta yasa yayi saurin ɗagowa don ganin wacece, shi dai iya tsawon rayuwarsa bai taɓa jin makamanciyar wannan Muryar ba a fadin estste ɗin su.
Kan ta ƙasa ta ƙaraso tana ajiye babban jug ɗin da ta zuba zoɓon da ta yi dazu. A sanyaye ta furta
“Sannun ku da hanya, ina yini”
Baki sake yaya Khalil ke kallonta yayin da zuciyarsa ke tunanin wacece wannan, sai dai kamarta da ya gani ya sa ya tabbatarwa kansa cewa jininsu ce. Ɓangaren yaya Sadauki ma haka abun take, sai dai shi babu wanda zai san cewa kallonta yake yi.
Yaya Khalil ne yayi ƙarfin halin amsa mata da “Yauwa sannu, lafiya kalau.”
Without minding his response ta fara zuba zoɓon a cups Tana Mika musu. Sai da ta sakawa kowa har su Hajjaty da Alhaji Baba kafin tayi yunkurin zuba nasa taji Muryar yaya Khalil yana fadin
“Ki ɗaukowa man drink coz ba lallai ya iya shan wannan ba.”
Da “To” ta amsa tare da ajiye cup din hannunta tana kokarin juyawa muryarsa ta daki kunnenta “No bar shi, serve me wannan ɗin.”
Ba iya Zahrah ba Kowa na parlourn kallon mamaki yake masa don iya saninsu dai baya son home made drinks shi kuwa ganin haka yasa ya kara maida hankalinsa ga wayarsa sai dai shi ma he's eager to know who is this lady don ya tabbatarwa kansa cewa ba mai aiki bace ganin yadda take zubi da famoly members don musamman Hajjaty, zai iya cewa photocopyn ta ne.
Kai kasa Zahrah ta juyo sannan ta dauki cup ta zuba tare da mika masa, tsawon wasu daƙiƙu tana shirin kara ce masa ga shi ya miƙo kyakkyawan hannunsa ya amshi cup din. Tana shirin komawa Hajjaty ta dakatar da ita
“Ina kuma zaki je Zahrah?”
“Zan koma ne ina karatu ne” ta bata amsa kai tsaye.
Alhaji Baba ya ɗago ya kalli Zahrah kafin ya