Showing 39001 words to 42000 words out of 157517 words
don karatu kika gudu! Na riga na san dalili.” Yaya Sadauki ya faɗa don ya tsoratar da ita.
Idanuwa waje take kallonsa cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba da hatske ba ne. Zuciyarta tace “Da gaske ne tunda ya riga ya faɗa.”
Ai kawai sai Zahrah ta kwaɓe fuska sai ga hawaye shaaaa.
Tooo, tashin hankali wai ba a sa masa date.
Cike da mamaki yake kallonta yana tambayar kansa me ya same ta, ko ba ta da lafiya ne?”
“Look Lily!”
Ɗagowa tayi ta kalle shi da idanuwanta da suka fara ja
“Na duka ki ne?” ta jijjiga kai “Da kai kile ba Ni amsar?”
“A'a”
“Ok tell me, me aka miki”
“Nothing” ta ba shi amsa tana sunkuyar da kanta
“Lily” Ya kira sunanta, ta ba shi amsa da “Na'am”
“Look In to my eyes” gagara haɗa ido ta yi da shi don a tunanin ta yanzu kam ta gama ƙare mata tunda Yaya ya gano saboda ya ce mata zai yi aure ta gudu, a lokacin ne ma ƙwaƙwalwarta ta fara aiki daidai, “To meyasa ma zata ji haushi? ” ta tambayi kanta.
“Don't let me repeat myself Lily” ya faɗa a karo na biyu sounding so authoritative.
Babu yadda ta iya haka ta ɗago but she can't look straight into his eyes, who's she to do so?”
Ganin dai she's not stable yasa ya sauƙa ƙasa kusa da ita har yana iya jiyo sautin numfashin ta da ke fita da sauri da sauri.
Hannunta ya riƙo ya haɗa da nasa, cike da kulawa yace
“Lily tell my me ya same ki please, in ba ki faɗa min ba waye za ki faɗawa?” tabbas ya faɗi gaskiya ba ta da wanda a yanzu za ta ɗora kanta a kafaɗar sa tayi kuka, shi ɗin dai shi ne wanda zuciyarta ta saba da shi cikin ƙanƙanin lokaci, ta ya ma za ta buɗe baki ta faɗa masa yadda take ji. Nooo that's impossible.
Haka suka share kusan mintuna 15 suna fafatawa, shi ya ce ta faɗa masa damuwarta ita kuma ta nace kan babu abinda ke damunta, yadda ya nuna concern ɗinta a kanta ne yasa ta fara tausaya masa.
“Ba ki ɗauke ni yadda na ɗauke ki ba Lily shiyasa kike ganin ban kai na san damuwarki ba”
“Ya yi kyau” daga haka ya miƙe da nufin wucewa. Bata san lokacin da ta riƙe ƙafafuwan ba tana faɗin
“A'A Yaya, wallahi ka wuce kowa, Zauna zan faɗa maka.” murmushin gefen baki yayi kana ya koma mazauninsa tare da zuba mata shasshanyun idanuwansa.
“I'm All ears, tell me what's eating you inside!”
Kanta ta sunkuyar sannan tace
“Yaya dama batun Mama ne, ina tsananin kewar ta da tunanin ta.”
Nan ya sa ta gaba da lallashi kan Mamah ta kusa dawowa wajensu tayi hakuri, he's still working on it. Daga haka dai aka bar zancen nan aka koma hira cikin farin ciki. Laraba dai lokaci zuwa lokaci ta kan leƙo su ta koma tana dariya tana faɗin sun dace kuwa (ba ta san ba soyayya suke ba hala?)
Har lokacin azahar yayi suna tare, Zahrah sai zuba ake shi kuma ɗan Mulkin yana murmusawa. Ganin lokacin salla ya yi yace mata zai je Masjid ya dawo, saura ya tarar ta ƙara guduwa.
Dariya tayi tace “Ai ba zan ƙara ba tunda Yaya na baya so.”
Murmushi yayi yana faɗin “That's good part of you!, Bye!” daga haka ya wuce masjid. Har ta yi hanyar shiga Bedroom ɗin ta kawai taji gwanda ta fara kwaso kayanta. Da haka ta wuce part ɗin Hajiya Babba, Thank God ba ta parlour iya Nasreen ce ke zaune tana aikin kallo tun safe, ba ta bi ta kanta ba ta wuce ciki, tana gama parking ta fito, har lokacin Nasreen ma kallonta hankali kwance. Ita kuwa Zahrah tana fitowa taci karo da Mami wacce da alama ɓangaren Hajjatyn ta nufa, suna haɗa ido gaban Zahrah ya bada wani irin sauti amma sai ta kauda kai sannan ta ƙarasa kusa da ita.
“Sannu Mami, Ina yini.”
Duk da cewa Mami ba kallon ƙurulla tayiwa Zahrah ba amma sai da gabanta ya buga, tsoronta Allah tsoronta kada kayan Zahrah ya ɗebi Sadauki yace da ita za a yi aure don tuna ranar da tagansu tare ranta ke ƙuna ganin yarinya ƙarama na shirin yi mata katanga da abun harinta.
“Mami” Zahrah ta faɗa a karo na biyu. Da yake wasu matan akwai iya ɓoye abu sai ta fara murmushi tana faɗin
“A'ah Zahrahn Hajjaty ne? Ina kika je haka?”
Zahrah ta bata amsa da “Na je ɗauko kaya ne daga ɓangaren Hajiya Babba.” sai kuma ta nuna mata kayan da ke hannunta.
Cike da son gulma tace
“Kayan na waye” Zahrah ta amsa mata da “Na Nasreen ne Hajjaty tace ta bani”
“Na gode Allah” ta faɗa a ranta a zahiri kuma tace
“Hala ba ki da kaya da yawa ne har sai sun baki?” duk da maganar ta ba ta haushi amma sai ta dake don tana buƙatar ƙara fahimtar matar. Dariya tayi tana faɗin
“E wallahi Hajjaty ta ce dai za ta sa a ɗinko min amma na karɓo waɗannan ɗin.”
An zo wajen, Mami ta murmusa tana faɗin
“Kin ga ki ɗauke Ni kamar Maman ki Zahrah, kina da buƙatar abu ba za ki samu Ni ba?” shaye da mamaki Zahrah ke kallonta tana kuma tunawa in dai ba mantawa ta yi ba first contact ɗin ta da matar nan a part ɗin Mommah kallon tsanatake mata amma da yake mata iyayen kaidi ne ji abinda take faɗi.
Zahrah na da wayo duk da ƙarancin shekarunta amma kuma in ta sa abu gaba sai ta yi. Saboda haka ita ma sai ta sunkuyar da kai kasa tana faɗin.
“Na gode Mami, Allah ya ƙara girma.”
Murmushin cin nasara Mami tayi tana amsawa Zahrah da “Amin”
Daidai lokacin kuma suka iso part ɗin Hajjatyn. Daga nan kuma Mani tayi shiru bata ƙara cewa komai ba.
Ko da suka shiga direct bedroom ɗin ta ta wuce ta ajiye kayan sannan ta fito don ganin sauran scene ɗin Mami.
Ganin Yaya Sadauki bai dawo ba yasa ta koma kusan Mami ta Zauna fuskarta sake.
Sai da Mami ta juya taga babu kowa tukun tace
“Saura kuma naga ba kya zuwa wurin nawa.”
Kan ta ƙasa ta amsa da “Zan zo In Sha Allah Mami.”
Daga haka hirar ta tsaya saboda fitowar Hajjaty.
Nan suka gaisa cike da girmamawa kamar ba Mami ba, Hajjaty dai mamakin ta bai ɓuya ba ganin abun da bata saba ba. Zahrah kuwa ƙimis tayi ta ƙi ba su wuri, tana so a yi kai gabanta, she wants to feel that she's one of them.
*Afwan My esteem people, Kuna ta jiran update ban yi ba sakamakon ayyuka da suka sha kaina. I'm sorry ga shi nan na yi muku, a taimaka a taya Ni sharing tare da reacting.*
*Na gode da ƙaunarku gare Ni and I appreciated it, thank you so much, love you irin sosai ɗin nan.*
[12/31/2024, 2:31 PM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣9️⃣
﷽
“Hajjaty dama na yi dahuwar kaji ne kuma na ga kina so shi ne nace bari na kawo miki.”
Mami ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da miƙewa Hajjaty food flask ɗin har da rusinawa kamar ta Allah.
“To madallah, sannu da ƙoƙari Baraka, Allah ya saka.”
Mami ta amsa da “Amin”.
Hajjaty na shirin ficewa Mami ta dakatar da ita “A'a Hajjaty wurin ki fa nazo.”
“To bari na kai abun nan kitchen.”
“Hajjaty ai ga Zahrah ki ba ta kawai, ke Zahrah karɓi ki kai, Babba ba ya aiki in da yaro kusa kin ji?”
Kai Zahrah ta ɗaga daga nan ta wuce kitchen kamar yadda Mami ta so. Tana ajiyewa ta juyo da sauri. Isowar ta ya yi daidai da lokacin da Hajjaty ta yi magana.
“Ban gane ba Baraka”
Ƙasa-ƙasa Mami ta Yi maganar ya yadda Zahrah ba ta iya jin komai. Kamar za ta fasa ihu haka ta koma Bedroom ɗin ta tana cije baki.
Shigowarsa kenan ya ci karo da fuskar Mami a tare da Hajjaty kuma, nan ya fara tambayar kansa ko me ya kawo ta? Har ya yi nufin juyawa wata zuciyar ta hana shi, gyaran murya ya yi wacce ta yi indicating presence na shi.
Kama wata tsohuwar munafuka Mami ta fara zaro idanuwa.
“A'a Aliyu ne?” ta faɗa tana washe baki. Ba tare da ya kalle ta ba yace “Good afternoon”
Bai jira amsawarta ba ya wuce zuwa Bedroom ɗin Hajjaty tunda abokin hirar tasa ba ya nan. Cikin ransa har yanzu ganin matar nan ya buge shi, ko wanne munafurcin take ƙullawa oho mata.
Da hararar Zahrah ta raka Mami da za ta fita daga nan kuma ta ƙarasa wurin Hajjaty tana faɗin
“Hajjaty dama Mamin su Ya Faruq tana shigowa nan? Ko gaisuwa ban taɓa ganin ta shigo ta miki ba”
Murmushi irin na manya Hajjaty ta yi kana ta ce
“Zahra'u ashe kema kin iya sa ido ban sani ba?,”
A shagwaɓe Zahrah tace
“Ba wani nan Hajjaty, ai dole na sa ido kan duk wani mai zuwa tun da dai noma I belonged to the place.”
“Za ki yi bayani ai, kin ga shiga ciki ki kira Yayanku ya zo ya yi lunch.”
“Yaya kuma? Ya shigo ne?”
“Ban sani ba, kar ki cika Ni da surutu, wuce ki je”
Daga haka Zahrah ta wuce tana tura baki wai Hajjaty ta nata faɗa, lokacin da ta shiga ba ta yi sallama ba ganin yana kwance kamar bacci yake, murmushi tayi tare da juyawa, taku ɗaya biyu ya dakatar da ita
Juyowa tayi tana kame kame
“Dama ba bacci kake ba Yaya? E Hajjaty ce tace ka fito ka ci abinci”
“Ok wait for me”
Tare suka yi lunch ɗin su daga nan ya mata sallar zai wuce office ɗinsa.
Tun bayan tafiyarsa Zahrah ke tariyowa abun da ya faru da ita a daren jiya, gani take kamar mafarki tayi amma tunawa da alwashin matar da ta kira kanta da Black-devil yasa ta ƙara tabbatarwa kanta a zahiri abun ya faru.
Tunaninta a yanzu ya ta'allaka ne ga don gano wacece wannan Black Devil Kuma meme ne ƙudirin ta ga ahalin nan, amma me? She need someone that'll support her.
A da ta yi tunanin Nasreen sai kuma ta fasa, haka ta yi ta ɗaura mutanen da ta
sani kan mizanin amma babu wadda ta ga ya cancanci wannan matsayi na sa rayuwarsa a kasada musamman da ta gano abun Black-devil na da alaƙa da Cultism.
“No!” ta faɗa a zahiri “I won't put any one's life in danger, I'll support myself ko da zan mutu sai na gano wace ce ita!”
“Amma ai a'a buƙatar wani ya san al'amarin nan, amma za a gaskata Ni kuwa? If yes waye zai yadda da Ni?”
Zuciyarta ta na ta amsa da “Yaya Sadauki”
Idanuwa ta zaro kamar dai tana gabansa ta maimaita sunansa da zuciyarta ta ambata. Cike da karfafa mata guiwa zuciyarta tace
“Yes Zahrah! Yaya Sadauki ne kaɗai zai iya yadda da ke ka ya zamo garkuwarki har ki cimma nasara a muradun ki, ina tabbatar miki he'll be there for you kamar yadda yake faɗa.”
Safe kanta ta yi jin shawarar da zuciyarta ke ba ta, kan ta ta gyaɗa alamar na'am sai kuma ta fesar da wata zazzafar iska.
“Feel free Zahrah! Calm and relax”
Nan ta ja numfashi ta fesar.
“Yes! Zan mishi magana” ta faɗa a bayyane. Ganin dai tunanin nan ba barinta zai yi na ga shi kuma ƙwaƙwalwarta na shirin fashewa saboda tunani yasa ta miƙe ta nufi parlour tare da kunna kallo, this is her first time to sit in the parlourn da niyyar kallo. Ko da ta kunna na ba fahimtar komai take ba coz her mind was taken away.
Da yamma Alhaji Baba ya dawo dama ya je wurin makoki mara abokinsa da ya rasu yau ɗin. Ko da ya huta ya a Hajjaty a ƙara yawan dinner without telling her the exact reason.
*BAUCHIN YAKUBU, ƘARAMAR HUKUMAR TORO*
Alhamdulillah za a ce, sauƙi ya fara samuwa ga matar da Inna ke kula da ita tare da ƴan jikokin ta. Yau ma kamar kullum zaune suke su uku, Asma'u, Inna sai kuma Maras lafiyar da ke bin su da ido suna hira, yanayin yadda yake kallon su zai tabbatar maka da cewa ba abinda take fahimta a ciki sai dai kuma suna sanya ta cikin hirar saboda ita a yadda Inna fahimci ciwon Amina (Sunan da suka laƙana mata.) Bai wuce gushewar tunanin ta da kuma hankali ba wanda ke da alaƙa da sihiri ko sammu.
Balkisu tace
“Inna har yau dai Malam Sufin bai zo ba, ina tausayawa Baba Amina wallahi, gaskiya Inna me zai hana mu ku ta can ɗin la'alla shi ba shi da lokacin zuwa, ko ya kika ce Asma'u?”
“E wallahi Inna, gobe mu shirya kawai muje can ɗin.” kalaman su sun taɓa zuciyar Inna, hakn ya sa ta yanke shawarar zuwa ganin Malam Sufin ɗin tare da Amina.
Washegari kuwa suka niƙi hanya sai Tafawaɓalewa don kai Amina wurin Mallam Sufi ko Allah zai sa a dace kamar kowa ita ma ta rayu cikin farin cikin.
*GRA, BAUCHI*
Cikin jerin gwanon gidajen da suka amsa sunan gida motar ta fito, bayan fitar ta free man ya rufe ƙatoton gare ɗin hakan ya sa ban samu damar kutsa kai cikin ba sai na bi motar don ganin ina za ta.
Unguwar Zango ta nufa kai tsaye, dai-dai wani gida wanda in ban manta ba gidan Idrisu ne!
Wane ne wannan kuma? Kafafuwansa ya ziro don fitowa, kamar wani basarake haka yake taku yayin da fuskar sa ke sanye da face mask Amma tsaro da yanayin jikinsa uwa uba kuma yanayin dressing ɗinsa zai tabbatar wa mai karatu da cikar izzarsa, da gani ka matashin ba zai wuce shekara 29-30 ba.
Takawa ya ci gaba da yi har isa daidai kofar gidan da ke sanye da kwaɗo. Tsaki ya ja tare da ƙara nazartar kwaɗon wadda alamun an jima da maƙala sa ta bayyana saboda yadda yake cijewa ga kuma tsatsar da ke jiki.
“Ya Allah!” ya furta yana dafe kansa tare da addu'ar Allah yasa dai ba tashi suka yi ba. Nan ya ga wani mutumin da sauri ya ƙarasa gunsa yana faɗin
“Am sannu da rana Malam.”
“Yauwa sannu ɗan saurayi”
“Baba don Allah tambaya nake” ɗan tsohon ya amsa da “Allah ya sa na sani.”
Gyara tsayuwar sa yayi sannan ya nuna masa gidan da ke kallonsu.
“Baba don Allah masu gidan nan ko sun yi ƙaura ne?”
Tsohon yace “E to ba zan ce kamai ba amma dai kwanaki na ji mai ɗaki na tana faɗin ko matar gidan ce aka sace ko meye, amaryar gidan kuma kamar dai sun sayar gidan ita da ƴar ta sunyi gaba.”
Zuciyar matashin ne ya tsananta Bugu sakamakon zancen da yake ji daga wurin tsoho. Tattara jarunta da ke shirin barin gangar jikinsa ya yi sannan yace
“To Baba, shi Mai gidan fa?”
“Ai yaro bari in gajarta maka zancen nan, shima Mai gidan babu wanda yasan ina yake.”
“Shikenan ba gode Baba, ga wannan”
Ya faɗa yana miƙo masa kuɗin da ke jikinsa, nan tsoho ya fara godiya, ba tare da ta saurari godiyar ba ya masa sallama tare da nufar motarsa fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali da damuwa, a haka ta figi motar, bai tsaya ko ina ba dai gidansu. Ko da ya Yi parking sai ga Guards ɗin sa sun kewaye shi to see if he's alright saboda taka tsan-tsan da suke da aikin su. Uban gidansu ya musu warning kan shalelen ɗansa, saboda haka ko da ya ce ba zai fita da su ba zaman addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya suke yi.
Wannan kenan!
*ABATCHA ESTATE*
*Yayan Lily*
Bayan sallar maghrib ya dawo, kai tsaye part ɗin su ya wuce, sai da yayi wanka tukun ya fito, lokacin kuma Mommah na zaune parlourn ta caɓa uban ado ga kuma yadda ta make fuska babu annuri. Tana ganin fitowar sa ta nufi inda yake.
“Aliyu!” ya dakata jin ta ambaci sunansa sai kuma ya waiwayo yana smiling
“Sannu da gida Mommah”
Ba tare da ta amsa masa ba sai ma cakushe fuska da ta ƙara yi tace
“Aliyu sau nawa zan faɗa maka cewa ka cire zancen auren wannan ƴar iskar a ranka? Me yasa ba ka jin magana ta? Remember Ni Mahaifiyarka ce K kumaum ina da ikon hana wannan auren. Wallahi tun muna shaida juna da arziƙi ka ce musu ka janye!”
Lumshe idanuwansa ya yi ya buɗe waɗanda lokaci guda kuma suka yi jawur, ya gaji da irin wannan hali na mahaifiyarsa, ƙoƙarin controlling temper ɗinsa yayi sannan ya kwantar da Murya
“Mommah Please, ah beg you ki daina batun janye aure, Sanin kan ki ne fa Alhaji Baba da kansa ya yi wannan hukuncin kuma babu wanda ya isa ya ja da shi kin sani, so Please Mommah ki kwantar da hankalin ki kawai ki rungumi ƙaddara.”
A hasale tace
“Na kwantar da hankali na fa kace Aliyu! Ka san kuwa me kake faɗi?”
Ganin ta hau da yawa yasa ya ja hannunta ya zaunar da ita kan ɗaya daga cikin kujerun da ke parlourn sannan ya ɗauki cup da ke kan Centre table ya tsiyaya mata ruwa yana miƙa mata.
“Have this” ganin tana bukatar ruwa yasa ta amsa ta kafa kai, tas ta shanye sannan ta miƙa masa cup ɗin. Ajiyewa yayi shima sai ya zauna gefenta tare da riƙo hannunta, motherhood bond is different, tuni ta fashe da kuka tana faɗin.
“Ni yanzu shikenan so kake na kashe kaina kafin ka haƙura da auren?” ta faɗa sounding so serious.
“Ba Haka ba nee Mommah, get one thing please, cewa sai an fasa aure kin san ba mai yiwuwa ba ne tunda Alhaji da.....”
Katse shi tayi tana ɗaga masa hannu
“Ya isa haka Aliyu! Na gaji da jin fasawa ba zai yiwu ba, na gaji! sai cewa kake Alhaji Baba ne ya yanke hukunci ba zai yiwu ba nace shi Alhaji Baban Allah ne In ya yi hukunci dole a bi? Nace shi ya haifa min haifa min kai ne da zai ke nuna ikonsa a kanka, let him show his power only on