Showing 147001 words to 150000 words out of 157517 words
zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*
Tsaye Abba ya miƙe jin Muryar uwargidansa Hajiya Baraka (Mamie) tare da dafe ƙirjinsa cike da tsoro, ɗaya hannunsa da ke tsaye ya ɗago yana pointing matan da ke kwance suna gurnani ya fara magana cikin rawar murya "Ba..ba..Bara...Baraka. mi...mi...mi kike..yi...a...a..nan?...me...me...kike ...Nu...nu...fi ...."
Everyone is shocked here, kowa kallon kowa yake duk da cewa ba su san me yake faruwa ba, Yaya sadauki ne yayi saurin miƙewa ya dafa Abba yana lallaminsa tare da ƙoƙarin zaunar da shi.
"Ka...ka..bari..."
"Ya isa Abba, calm down please, ka nutsu kada wani mummunan abu ya sameka" da ƙyar da siɗin goshi Abba ya zauna a mazauninsa.
Sheikh Imam ya dube su yace "Kun shafawa kan ku ruwan sanyi, muna sauraronku."
Duk abinda yake faruwa Yaya Sadauki yana recording a wayarsa in case for any legal purpose.
A tare su ukun suka miƙe, fuskarsu ta yi baƙi kamar sun shiga cikin buhun gawayi yayinda idanuwansu suka yi ja jawur kamar garwashi, fuskarsu gabaɗaya ta sauya ba a iya gane su waye ne. Har zuwa lokacin kuma babu alamar nadama a tattare da su sai ma masifar da ke cinsu.
Ɗaya daga cikinsu wacce ba ita tayi magana ɗazu ba ta fara magana cikin zafin rai da kaushin murya.
"Niii zan sanar da ku komai, amma ina kan bakata na babu gudu babu ja da baya!"
Wannan karen gabaɗayansu sai da suka miƙe jin Muryar da ta kasance musu kamar ruwa, zuciyar kowa ta cika da alhinin jin wannan abu, sai dai takamaimai ba su da masaniya kan abinda ke faruwa.
Gaban Yaya Sadauki na bugawa kamar zuciyarsa za ta fito yace "Ammie!" Cak maganarsa ta ƙafe ya fara bin kowa da kallo yayinda kowa ke kallonsa shima alamar suna buƙatar ƙarin bayani. Fahimtar hakan yasa Kawu Sadi faɗin "Muna sauraronku!"
Cikin kaushin murya Hajiya Saudatu (Ammie) ta fara magana.
*WAIWAYE ADON TAFIYA (Flash Back)*
Alhaji MOHAMMAD KABID ABATCHA (Alhaji Baba) mutum ne da Allah ya sanya albarka cikin nemansa, duk abinda zai saka hannayensa akai da izinin mahalicci sai ya yi albarka siyasa tun yana da ƙarancin shekaru ya yi suna sakamakon arziƙin da ya tara.
Matarsa ta farko, Karima (Hajjaty) sun yi aure ne irin na haɗin gida, suna zamansu kuma cike da so da ƙaunar juna. kafin aurensu ne harkar kasuwanci ta haɗa Alhaji Baba da wani bawan Allah mai suna Isiaq Babatunde, wanda Asalinsa bayerabe ne, kasuwancinsa ne ya kawo shi Abuja. Cikin ƙanƙanin lokaci sabo mai zafin gaske ya shiga tsakaninsu, Alhaji Baba yana jin zai iya sadaukar da dukiyarsa ga aminin nasa, sai dai a ɗaya ɓangaren Babatunde ba ya farin ciki da wannan abota tasu saboda samun da abokinsa yake yi a kere nasa.
Abunka da mugun mutum, ya ɓoye hakan ta yadda babu wanda zai fahimci cewa akwai wani abu a ɓoye a ransa ba, bai ƙara sanin cewa Alhaji Baba ya yi masa fintinkau ba sai lokacin da ya kai shi gidansa don su ci abinci tare. Tunda Babatunde ya ɗaura idanuwansa kan Hajjaty ya rasa sukunin rayuwa, kyakkyawar mace iya mace, cikin ransa yace "Shikenan, Ni komai nine a baya, Abatcha ya fi Ni kyau, ya fi Ni tarin dukiya, ya fi Ni mutane, ya kuma samu matar da ba zan samu irinta ba, ba zan jura bam"
Da wannan mummunan tunanin Babatunde ya koma nasa gidan wanda Alhaji Baba ne ya masa kyautarsa.
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, Hajjaty ta samu cikinta na fari, zo ka ga murna wurin Alhaji Baba, har wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar liyafa ya haɗawa ƴan'uwa da abokan arziƙi, cikin waɗanda suka halarta kuwa har da Babatunde Aminin Alhaji Baba. Bayan taro ya watse ne Hajjaty ta fara wani matsanancin ciwon ciki, a tsorace Alhaji Baba ya miƙata asibiti mafi kusa sannan ya dawo ya ɗauki jug ya ɗebi Zamzam (dama can shi mutum ne mai amfani da shi, shi yasa yake yawan ajiyewa) addu'a ya tofa a ciki sannan ya koma asibitin, lokacin ne kuma likita ke sanar da shi su ba su ga wani abu da ke damunta ba, amma sun rubuta gwaje-gwajen da ya kamata a yi don gano ina matsalar take, daga nan Alhaji Baba ya shiga duba jikinnata, yanayin da ya ganta yasa ya tsorata da al'amarin, ganin ba ta cikin hayyacinta yasa ya shafa mata ruwan an fuskarta sannan ya bi lungu da saƙo na jikinta ya shafa, cikin ƙankanin lokaci ta fara zufa kamar tana cikin wuta, aniyar zuciya sauke sannan ya ɗaga kanta ya ɗura mata ruwan, tana haɗiyewa babu jimawa ta fara kwarara wani baƙin amai, sosai ta ligirta, iv fluids likita ya ɗaura mata don karin ƙarfin jikinta, ba a daɗe ba jiki ta ware kamar ba ita aka kawo magshiyyan ba, saboda haka ne ma yasa likita ba su sallama.
Tun daga wannan rana Alhaji Baba ya fara zargin cewa akwai wanda ba ya son ciggabansa amma bai zargi kowa ba tunda duk na kewaye da shi ya aminta da su. Daga nan ya fara kaffa-kaffa da iyalinsa, a haka har Hajjaty ta haife ɗanta na fari (Alhaji Babba). Babatunde wanda a yanzu Alhaji Baba ya nada a matsayin manager na companynsa (Abatcha Automobiles) shima ya zo ya yi Barka, har ya kawo tukuicin kaya masu kyau ga jaririn, Alhaji Baba da Hajjaty suka masa godiya, daga nan ya tafi.
Abunda babu wanda ya sani shine, asalin familynsu Babatunde, gungun matsafa ne na bugawa a jarida, ba su da imani ko kaɗan burinsu ko da yaushe bai wuce neman ɗaukaka da kuɗi ba ko da kuwa ta kan ko waye ta faɗo ba sa sararawa mutum. Babatunde shi kaɗai ne ba ya harkar tsafi a gidansu, amma dai mugun mutum ne mai baƙar zuciya. Haɗuwarsu da Alhaji Baba haɗuwace irin wacce ake cewa ƙaddara, wata rana Alhaji Baba ya fita zuwa taron Automobiles association of Nigeria wadda aka gudanar a ƙaramar hukumar Lade da ke jahar Kwara, bayan an tashi daga taro ya shiga motarsa don komawa gida, a kan hanyarsa ne motar ta lalace, ga shi kuma babu wani bil'adama a kusa ga yamma ta riga ta yi. Kwatsam sai Allah ya turo Babatunde wanda ya fito farauta, ganin mai kuɗi har da mota yasa ya masa magana cikin damammiyar hausarsa, a haka dai yace yazo du koma cikin gari, ya kwana a gidansa, idan ya so da safe sai su je da bakanike a gyara motar.
Ko da suka koma kamar yadda Babatunde ya faɗa, a gidansu Alhaji Baba ya sauƙa, cikin dare Baba Tunde ya Lale duk wani kuɗi da ke jikin Alhaji Baba, hatta Gold ring da ke hannunsa sai da ya cire. Ko da safiya tayi Alhaji Baba da bai ji abubuwansa ba hakan bai sa ya zargi Babatunde ba, nan suka fito don neman bakanike, ba su ɓata lokaci ba kuwa suka samu, cikin ƙanƙanin lokaci aka gyara motar. Alhaji Baba ya sallami bakanike da sauran kuɗin da ke cikin motarsa. Bayan ya tafi ya dubi Babatunde yace "Ɗan'uwa na gode da taimako, Allah ya saka da alkhairi ,ba ni da isassun kuɗin da zan ba ka a tare da Ni, amma wane irin aiki kake yi?"
Babatunde yace "Ina tara ƙarafuna ina sayarwa, amma talauci ya min yawa, watarana ko ƙwayar abinci ba na ci."
Cike da tausayawa Alhaji Baba yace "Na ji daɗin taimakon da ka min, saboda haka in ba za ka damu ba ka taho mu tafi can Abuja tare, ina da companyn sayar da kayayyakin safara kama daga motoci, mashina, zuwa kekuna"
Jin maganar kuɗi yasa Babatunde amincewa nan take ya biyo Alhaji Baba don su yi business tare.
Tun zuwan Babatunde Alhaji Baba yake rasa abubuwansa, amma ba ya magana saboda ya yarda da shi, a hankali kuma Babatunde ya fara ƙoƙarin ganin sai ya wuce Alhaji Baba a kowanne fage na rayuwa wannan shine mafarin komawarsa ganinsu da zimmar hutu, ashe ba hutu yaje ba, gidansu yaje wurin yan'uwansa don karɓar nasa gadon na tsafi, ba shi ya dawo ba sai da ya zama matsafi shima, ya kuma koyi duk wata dabara ta tsafi cikin ƙanƙanin lokaci yayinda ɗan imanin da yake da shi duk ya gusa gefe, ya koma ƙatoton mushriki kuma arne.
Haihuwar Alhaji Babba itace silar razana shi, don ya ga rabon ƴaƴa maza tsakanin masoyiyarsa da kuma amininsa wanda a zuci ba shi da wani maƙiyi da ya wuce shi, don Allon tsafinsu ya nuna cewa in dai yaran suka tashi Alhaji Baba zai ɗaukaka, za a sanshi sosai kuma dukiyarsa za ta bunƙasa, hakan yasa ya ƙudiri aniyar sadaukar da duk wani ɗa da Alhaji Baba zai samu. Wannan kayan da ya kawo a sakawa Jaririn akwai wani sirrin tsafi a jikinsu, matuƙar an sakawa yaron to babu makawa jininsa gabaɗaya zai tsotse ta yadda babu wanda zai zargi kowa a kan mutuwarsa sai ma a aje mutuwar a matsayin ƙarar kwana.
Ranar da Hajjaty tayi niyyar saka masa kayan, bayan ta gama wankansa ashe ba ta fita da bahon da ta wanke shi ba, babu zato kawai kayan suka faɗa cikin ruwan wankan....zuuuuu ta fara ji, tana waigawa taga ruwan yana tafasa tare da fitar da wani hayaƙi yayinda kayan ke sauyawa daga ainihin kalarsu zuwa baƙaƙen launi. Hajjaty da jikinta ke ɓaru saboda Abunda ta gani yasa ta ɗauki jaririnta ta rungume shi tana karanto addu'o'in da suka zo bakinta yayinda ta matse a angle na ɗakin, bayan wani lokaci da taji shiru ta sauƙe ajiyar zuciya ta ajiye Jaririn kan gado tana furta Bismillah, leƙa bahon tayi taga babu komai a wurin, bahon babu shi bare ruwan da ke ciki ko wani abu makamancinsa. A ranar ta ga tashin hankali babu shiri ta aika mai wankin motar Alhaji Baba gidansu ya ƙira Yayanta ta sanar da shi komai. Bai ɓata lokaci ba yazo, abunka da mutum mai ilimi nan ya fahimci cewa yaron ake so hallakawa hakan yasa ya tambaye ta wa ya kawo kayan, da ta faɗa masa yace zai sanar da Alhaji Baba tace A'a, ko ya sanar da shi ba zai yadda ba saboda akwai yarda tsakaninsu, ta dai roƙi ya rufe sirrin nan, za ta kula sosai, da zai tafi ta bashi sauran set biyar ɗin da ya kawo, daga nan ya wuce, tun daga ranar kullum yakan zo, ya ba ta wasu addu'o'in tsari tukun ya wuce.
Lokacin da Babatunde ke jiran jin mutuwar jaririn ya ji shiru, ganin haka yasa ta tambayi ubangidan nasa kuma amininsa, ba tare da ya fahimci komai ba yace masa ai Abubakar Sadiq na lafiya da ƙyar ya iya binne yadda yake ji a ransa, bayan sun rabu ya koma gidansa, cikin dare ya fito farauta, wurin miskinai yaje kai tsaye, suna ta sharar baccinsu a ɓigiren da suke zama, ya lallaɓa ya sati yara biyu, daga nan ya wuce da su matsafarsu. A can ya sadaukar da su, tun daga wannan rana ya samu ɗaukaka a duniyar mutane da ta matsafa. Daga nan samunsa ya linka na da sau babu adadi, cikin ƙanƙanin lokaci yayi dukiya ta ban mamaki, ya kuma shahara ya sanu a bakin mutane, ko ina ka wuce za ka ji ana zancen Attajirin nan, multimillionaire Babatunde.
*React and share fisabilillah.*
[10/05, 7:11 AM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 7️⃣1️⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*
Wannan suna da kuma dukiya da ya ga ya tara yasa ya fara jin kansa wani, nan ya buɗe kamfaninsa shima Babatunde Automobiles saboda ya kawar da zargi a kansa ya haɗa guiwa da Abatcha Automobiles. Shi dai Alhaji Baba ba shi da matsala da Babatunde ko kaɗan, sai dai shi kullum cikin tunani yadda zai ƙwace Hajjaty daga gareshi yake. Ana cikin hakan Allah ya ƙara azurta Alhaji Baba da haihuwar Daddy, ganin hakan yasa Babatunde ƙara faɗaɗa tsafinsa ta hanyar sadaukar da jinin yara ƙanana da manya, kai har da tsofaffi waɗanda ba su ji ba basu gani ba, sai dai sadaukar da iyalan Alhaji Baba ba abune mai sauƙi ba, ba sa wasa da ibada da addu'a, babu wani mahaluki da ya isa cutar da su sai da izininn Allah.
A lokacin da ya fara ƙoƙarin kawar da Daddy wanda ya gano cewa shi ne zai gani mahaifinsa ya rasa abubuwa da yawa, tuni kadarorinsa suka fara lalacewa ya fara samun karayar arziƙi amma saboda baƙar zuciya irin tasa yasa ya ƙi ja da baya har sai da ta kai cewa komai nasa ya salwanta, dalilin haka yasa ya ƙara tsanar Alhaji Baba, ya kuma tsani jininsa, ya yi alƙawarin ko zai yi yawo tsirara sai ya dakatar da ƙaddarar ahalinsa ko da kuwa sun hayayyafa sun zama Babban Gida kamar yadda ya gani a allon tsafinsa.
Alhaji Baba wanda kullum cikin tausaya abokin nasa da karayar arziƙi ta samu yake, duk wata riba da zai samu a Companynsa zai raba biyu ya ba wa Babatunde amma fa hakan bai sa ya sauƙo ba, watarana Alhaji Baba suna taɗi da Babatunde ya kawo masa batun aure, da ƙyar da siɗin goshi yace zai yi tunda Alhaji Baba ya nace, kuma ya ɗauki nauyin duk wani abu da za a kashe a bikin. Babu daɗewa Hajjaty ta haifi Papa, hakan yasa aka haɗa bikin sunan da bikin Babatunde wanda Alhaji Baba ya nema masa aurenta.
Bayan auren da shekara biyu mata ba ta haihu ba, hakan yasa Babatunde sadaukar da ita ga dodon tsafinsu, wannan sadaukarwa ita tasa aka ƙara masa matsayi cikin DEVIL'S KLANS 😈, babu ɓata lokaci dukiyar da ya rasa ta dawo, sunansa da ya dishe ya farfaɗo, cikin lokaci ƙalilan mata masu son zuciya suka fara kawo masa farmaki, ba ya ƙi sai dai yakan more rayuwarsa da su daga baya ya sadaukar da su ga dodon tsafinsu. Yadda ya shahara a Duniyar matsafa ne a wani taro da aka yi a ƙasar Germany na matsafa ya haɗu da Gabriella, ɗiyar wani mashahurin matsafi wacce itama kanta ta shahara a fagen, nan yaji yana sonta, ko ba komai ikonsa zai ƙaru, ta yadda zai ruguza Alhaji Baba da ahalinsa saboda yana so yayi maintaining suna da dukiyar da yayi gudun kada in sun hayayyafa su shafe tarihinsa.
Lokacin da ya sanar da Alhaji Baba cewa zai yi aure, zo ku ga murna kamar shi aka ba wa matar, duk da cewa dukiyarsu ba za ta kwatantu ba, tuni Babatunde ya sha kwana amma Alhaji Baba ne yayi ruwa yayi tsaki har aka kawo Gabriella wacce ta sauya suna zuwa Sheima don badda kama. Bayan zuwanta kuwa suka haɗe baki da mijinta don son ganin bayan mutanen da ba su ji ba basu gani ba.
Shekara guda da auren Babatunde Hajjaty ta haifi ɗanta Aliyu, wanda hakan yasa Babatunde ƙara hasala, nan yace ko Ni ko ku! Ana tsaka da wannan al'amari matarsa ta samu ciki sai dai an riga an sadaukar da yaron tun yana ciki, ba a jima ba kuma Alhaji Baba ya ƙars auren Khadijatu, wacce ta kasance mace mai addini sosai, ba ta wasa da addini shi yasa yaran suka dawo kamar ƙawayenta, tare suke komai, da safe sai ta tabbatar sun yi azkar duke fita school.
Bayan wani lokaci, cikin ikon Ubangiji da sahalewarsa, Iyalan Alhaji Baba suka ƙaru yayinda aka yi mummunan rashin ɗaya daga cikin matan gidan. Tun daga wannan lokaci matsaloli suka fara Kunno Kai cikin gidan, yau a tsoratar da wane, gida dai ya koma kamar matattarar aljanu, kana zaune za a yi ta kwala maka ƙira, abun da ya fara isan Mai gidan ya nemo almajirai ya ciyar da su da abinci mai kyau suka sauƙe Alqur'ani tare da tawassuli da shi don neman kariya ga ahalin. Wannan ne yasa abubuwa suka fara lafawa.
*WATARANA*
Alhaji Baba ya kai wa amininsa ziyarar ba zata saboda ya bar gidan da yake ya koma Kaduna kwacakom da zama tare da ƴarsa Baraka da kuma ƴar ɗan'uwansa Saudatu, wadanda a zahiri ne kawai suke maintaining sunan, amma a ainihin gaskiya Amaka ne da Joy. A ranar da yaje mai gadin ya sanar da shi cewa weekends Alajinsa a gidan hutunsa yake zama ba nan ba, nan ya buƙaci da ya kwatanta masa gidan hutun Babatunde. Bayan ya kwatanta masa Alhaji Baba ya wuce. Da yake babu mai gadi a can ɗin, kawai shiga yayi, sai da ya ƙeyare gate huɗu kafin ya ci karo da mai ginin gidan wanda aka kashe dukiya wurin yinsa kamar ba za a mutu ba. Abunda ya ba shi tsoro bai wuce paint ɗin gidan ba, launin ja, sai kuma zanen kayuwa mutane, mace da namiji, sai skull (ƙoƙon kai) da Cross a kai. Tun daga wannan gaɓar Alhaji Baba yaji wata rashin yadda da aminin nasa ta ɗarsu a ransa. Bai gama shan mamaki ba sai da iska ta buso, wani mahaukacin ƙarnin da ya buge shi bai san lokacin da ya toshe hancinsa ba yana jijjiga kai, saboda dakiya irin tasa yasa yace sai ya ga me ake a nan, yayinda wani sashe na zuciyarsa ke ƙaryata masa abinda yake tunani.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da goge gumin da ya jika fuskarsa cikin ƙanƙanin lokaci, ƙofar ginin da ya gani a buɗe yasa ya fara ƙoƙarin danna kansa ciki. Yana shiga wani jahilin ƙarni da ya kusa saka shi amai ya buge shi, handkerchief ɗinsa yasa ya rufe hancinsa tare da fara kalle kalle, tashin hankali wai ba a sa masa date! Abunda ya gani sai da ya kusa sanya numfashinsa barin gangar jikinsa! Daga kunkumin mace ne zuwa cinyarta aka lanƙaya a jikin wata igiya an banƙaro da gabanta gaba kau da kai Alhaji Baba yayi yayinda zuciyarsa ke ƙara tashi yana jin ƙaƙarin amai.