Showing 96001 words to 99000 words out of 157517 words

Chapter 33 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5161

free ki faɗa min meye damuwarki kin ga ba ki da wacce ta kai ni, in ba ki fada min ba wa za ki faɗawa?"

Tabbas gaskiya Hajiyarta ke faɗi amma sam ba ta jin cewa za ta iya sanar da Hajiyar tata damuwarta, duniyar tunanin da t lula ya ƙara tabbatarwa Hajiya Babba cewa yarinyarta is in pain. With so much care ta ƙara dafa kafaɗar Nasreen ɗin tana faɗin "Idan har ba ki faɗa min ba Nasreen wa ya cancanci ya san damuwarki? Please tell me what's actually wrong with you if not i'll also be affected with it." murmushi Nasreen ta ƙirƙiro tana faɗin "Hajiya Babu komai fa, wata classmate namu ce ta rasu and abun tausayi kullum tana cewa za ta musulunta Allah bai yi ba. Yanzu shikenan ta mutu kafura ko Hajiya?" ta faɗa tana ƙara kwaɓe fuska cikin ranta tana ayyana yadda ta iya zaro wannan zancen. A ɓangaren Hajiya Babba kuma sai lokacin ta sauƙe ajiyar zuciya.
"Ba kuka ai za ki yi ba Nasreen, kowanne mai rai mamaci ne, so addu'a kawai za ki mata, Allah ya duba niyyarta yasa ta rabauta dalilin kyakkyawar niyyarta. Kinji?" kai ta gyaɗa kamar wata ƙaramar yarinya.
"Yauwah good girl, Allah ya sa ta huta."
Da "Amin Nasreen ta amsa mata.
"Good, don't cry again kin ji ko?"
"Uhm" ta ba Hajiya Babba amsa a taƙaice.

Ganin Hajiya Babba ta miƙe za ta fice yasa Nasreen sakin ajiyar zuciya, bayan ta ji alamar rufuwar ƙofa ta koma t kwanta wasu hawayen na ƙara silalowa daga idanuwanta zuciyarta na mata zafi ga wani banzan tunani da zuciyarta ta fara, ganin shaidan zai yi galaba kanta yasa ta miƙe da sauri ta janyo wayarta ta kunna ƙira'ar Muhammad Ayyubi, nan ta ji zuciyarta na sanyaya, ba ta ankare ba bacci ya kwashe ta.

*ZAHRAHS' POV*

Bayan su Zahrah sun idar da sallah kai tsaye bedroom ɗinta suka koma, ganin Nasreen ba ta nan babu wadda ya tanka, sai da suka yi Lunch tukun suka wuce ɓangarorinsu banda Nainarh. Bayan tafiyar su Nainarh ta dubi Zahrah tace "Sis Zahrah nifa i smell something, ko ke ba ki fahimci wani abu dangane da Nasreen ba?"
"Wallahi Nasreen gabaɗaya ba na jin daɗin yanayin da nake ganin Nasreen, akwai abunda take ɓoye mana."
Ƴar dariya Nainarh tayi tace "Ba na faɗa muku ba? Sis Nasreen is in love, sai wani ɓoye mana take, kin ga tashi ma muje wallahi sai ta faɗa mana, ya ma za a yi ace ƴar'uwar mu na cikin damuwa mu kuma muna zaune, zo mu je wurinta."
Da to Zahrah ta amsa tare miƙewa, ko da suka isa part ɗin Hajiya Babba kai tsaye bedroom ɗin Nasreen suka wuce.

A kwance suka tarar da ita, har suka zauna bakin bed ɗin ba ta san da zuwansu ba sai da Nainarh tace "Sister!" a ɗan zabure ta ɗago tana kallonsu. Yadda idanuwanta suka yi ja ne yasa Zahrah jin ba daɗi, a hankali Nasreen ta juya kamar ba ta so.
"Sis Nasreen ki juyo please, magana za mu yi."
Ba tare da ta juyo ba tace "Ina jin ku ai"
Kallon kallo suka yi tsakanin Zahrah da Nainarh. Zahrah ce ta ɗaure fuskarta tace "Wallahi Sister ki tashi kuma ki juyo ki kallemu mu yi magana in kuma ba haka ba wallahi zan faɗawa Mamah, hala ita in ta miki magana za ki ji."
Da sauri Nasreen ta miƙe tana kallonsu ba tare da ta ce komai ba.
Cikin ƙarfin hali Zahrah tace "Sister me yake damunki, kwanan nan gabaɗaya kin sauya always behaving odd, ki fada mana damuwarki ko za mu iya magance miki ita."
"Babu komai fa sisters" ta ba su amsa a raunane, a irin yanayin da ta yi maganar ko kurma ya ji zai fahimci akwai damuwa gareta.
"Kada ki maida mu shashashu mana Sis Nasreen, we know u more than everyone, kin tunanin ba mu damu da ke bane? Look, kawai ki faɗa mana damuwarki."

"Da gaske nake muku sisters, kawai zuciya na ne ba ya mun daɗi, bht believe me, nothing is wrong with me."
"U're lying Nasreen, nace ƙarya kike." Nainarh ta faɗa a kausashe alamun ta gaji da wannan wasan da Nasreen ke yi. Ganin haka yasa Zahrah sauƙe ajiyar zuciya kana tace
"Sister tunda ba mu kai mu ji me ke damunki ba, ba ki ɗauke mu matsayin da muka ɗauke ki ba shikenan, bari mu tafi, mun gode." shirin miƙewar da Zahrah ke yi yasa Nasreen ɗan riƙe ta. Harara Nainarh ta cillawa Nasreen ɗin tace "Wallahi Nasreen you're in love! An fada miki ba zan fahimci yanayinki ba?, wallahi ko ki fada min ko na sanar da Yaya Khalil!"

Idanu zare Nasreen tace "Rufa min asiri sister" nan take yanayinta ya koma na damuwa.
"Yes! I'm in love, amma wanda nake so bai sani ba kuma ma akwai wadda yake so, the only thing i need from you is du'ah, ku min addua Allah ya cire min son shi a zuciyana." tana gama faɗin haka ta fashe da kuka. Tapping bayanta Nainarh tayi tana faɗin "Who's that guy da zai sa ƴar'uwarmu kuka? Just relax and tell me ko waye sai ya so ki."
Gaban Zahrah ne ya buga, sai kuma ta ɗan kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka tace
"Ki faɗa mana, we will fight for u sister!"

Dakatawa da kukan tayi tana sakin murmushi wanda ke nuna ba ku san meye bane sai kuma tace
"Na faɗa muku addu'a kawai nake so, ba zai yiwu ba abunda kuke tunani."
Ganin ta kafe yasa suka ce to, amma dai za su gano ko waye.
Daga nan Zahrah ta wuce ta bar Nainarh a tare da Nasreen ɗin.

Bayan La'asar Yaya Ishaq yazo, duk da cewa Zahrah ba ta ɗaukin fitar da za su yi saboda damuwar Nasreen hakan bai hana ta cire wanka ba, sosai tayi kyau Ya Ishaq sai santin adon yake har ya sa tana jin kunya. Wurare daban-daban suka je sannan suka dawo, nan ya sanar mata cewa yau Daddynsa zai ƙaraso gida. Daga haka suka yi sallama ba don ya gajj da sarauniyar tasa ba. Haka ya juya yana mai ƙara godewa Allahn da ya ba shi ita yana kuma addu'ar Allah ya mallaka masa ita.
Kamar yadda ya faɗa mata kuwa tana shiga taga sai haɗa abinci ake iri-iri ko da ta tambaya da harara kawai Mamah ta bi ta. Hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke.
Bayan sallar Isha aka kai abincin sashen baƙin Alhaji Baba, Suna dawowa daga masallaci ƴaƴansa maza suka hallara saboda ya sanar da su akwai baƙin da za su zo.
Ba a jima ba kuwa Dad ɗin Ya Ishaq da kuma baffaninsa biyu suka iso. Sai da aka gabatar musu da kayan ciye-ciye suka ci suka yi hani'an kafin a kai ga fara magana. Daga ƙarshe dai suka yi concluding cewa an ba shi Zahrah, amma ba za su yanke ranar biki ba har sai sauran mata da matasan da ke cikin familyn sun gabatar da masoyansu, daga haka Dad yayi godiya suka wuce.

A lokacin da Dad ya dawo ya Ishaq ba kunya ya tare shi da zancen don kuwa abunda ya tsayar da shi kenan bai shiga part ɗinsa ba, Harararsa Dad yayi yace
"Matsa ka ban waje, sai da safe tukun." kamar zai yi kuka haka ya wuce part ɗinsa saboda sanin ba faɗa masa Dad ɗin zai yi ba tunda ya faɗa don ko Mom ɗinsa ya san Dad ba zai faɗawa ba.

*Daddy and Mommah*

Daddy da kansa yaje gidan Hajja ya ɗauko Mommah wacce farin ciki ya gama cikata bayan jan hankali da kuma addu'ar da Hajja ta musu. Ko da suka iso Abatcha Estate sai da suka je wurin wurin Hajjaty da kuma Alhaji Baba, suma dai addu'ar suka musu sannan suka yi sallama. Wannan dare dai ya kasance na musamma ga waɗannan iyaye, ko ba komai zai kasance mafarin shimfiɗa kyakkyawar rayuwa a tsakaninsu.

Haka nan ɓangaren Nasreen da ƙyar bacci ya sace ta tana tunanin makomarta.

A cikin wannan daren ne kuma miyagun nan na ƙungiyar Devil's Klans suke ƙaddamar da meeting wanda a yanzu Uwargijiya ta sako jininta cikin ƙungiyar wacce yanzu tauraronta ya fara haskawa, wannan dai sai mu ce Allah ya hallaka mana irinsu saboda irin baƙar zuciyar da take da. A cikin abubuwan da aka tattauna akan ƙudirinta akwai shirin rusa alaƙar da ke tsakanin wasu masoya da ba su ambaci suna ba, amma haƙiƙa kalamanta sun nuna a cikin estate ɗin ne. Ta kuma yi alwashin tarwatsa wannan alaƙa da ke tsakanin masoyan.

*A GURGUJE*

Washegari Alhaji Baba yasa duk jikokinsa da ke garin a gaba sannan yace idan akwai waɗanda suka haɗa kansu sai su yi magana, sauran ma duk ya ba su lokaci su gabatar da waɗanda za su aura. A day after Alhaji Babba yayi maganar Nainarh da ya Khalil, Zakiyya da Ya Taj, Rumaysa da Ya Auwab, sai kuma Nasreen wacce tace ita sai ta kammala karatu saboda wanda ke son ta shima karatun yake. Ba wanda ya tsauwala mata da hakan, Jiddah, Hibba, duk sun kawo mazajen da suke so, Rumana ma Alhaji Baba ya yi mata magana duk da cewa ita mahaifiyarta ce ƴar'uwar Mamie. Daga nan tace ita ma za ta turo nata, nan aka tsayar da ranar biki nan da watanni biyu cur.
Cikin lokacin nan kuma dukka masoyan nan sun ƙara shaƙuwa, musamman 4babes din nan, Zahrah da Ya Ishaq ɗinta wanda kullum soyayyarsu ƙara gaba take, Ya Khalil da Sweet Nainarhnshi, Yaya Taj da Zakiyyarsa, ga kuma iyayen jan aji Ya Auwab da Rumaysa.

*we're around the corner, yanzu mun shiga tsilim, ku dai ku taya ni sharing don Allah.*
*React please*
[4/12, 4:20 PM] bhatooldiamond: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*








*💎💍ELITE DIAMOND*
*WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_













_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 4⃣5⃣




Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau daɗi gobe akasanin haka, an samu sauyi sosai a cikin estate ɗin, rayuwar gidan Daddy ta sauya yadda suke gudanar da rayuwarsu gwanin ban sha'awa, su Ya Haidar da Ya Junaid sun dawo estate ɗin tare da matayensu, sosai al:amuran familyn ya sauya. A lokacin da su Mamie da Ammie suka ji labarin dawowar Mommah saboda su ba su da kunya sai suka lallaɓo don su ɗinke, Mommah tace inaaa ai na yi hankali, a yanzu ba ta da aminan da suka wuce Hajiya Babba da Mamah, a haka har Ammin Badi'a ta kawo ma Mamah Ziyara, lokacin kuma Zahrah ta ci karo da aminiyarta ba ƙaramin farin ciki tayi ba haka kuma sisters ɗinta su ma sun taya ta, nan duka suka haɗe kamar wasu ƴan'uwa, da Ammie ta tashi tafiya sai ta bar Badi'a ta zauna tare da Zahrah na tsawon sati tukun ta koma tunda itama an sa mata rana da cousin brothern ta, abun mamaki ashe Prince Bello cousin ɗinta ne. Cike da kewar juna Badi'a ta koma Bauchin Yakubu.

Hausawa suka ce rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya taji kunya, yau ya kama saura sati biyu ayi wannan gagarumin biki da za a yi a Abatcha Estate. Shirye-shirye ake ba kama hannun yaro, iyaye sun zage suna gyara yaransu wanda aka bar fannin gyaran a hannun Aunty Na'ima.

Kamar kullum Zahrah ce zaune ita da sisters ɗinta ana musu gyaran jiki, duk da cewa Nasreen ba ta cikin amaren amma har da ita ake gyarawa, dukkanin su sunyi kyau kamar ba su ba musamman Zahrah amma kuma yanayinta duk ya sauya ga kuma ƴar ramar da tayi. Hayaniyarsu ce ta cika ɗakin ganin Aunty Na'ima ta fita, wannan na faɗin ai wance kaza, cike da sanyin jiki Zahrah ta miƙe ta nufi ƙofa, Bedroom ɗinta ta shiga tare da zama bakin bed tana dafe saitin zuciyarta a hankali ta furta "Ya Allah!, me ke shirin faruwa da ni ne?" kyawawan idanuwanta ta lumshe tana mai ƙara buɗesu, secreen ɗin wayarta ta kalla tana sauƙe ajiyar zuciya. Take wayar tayi unlocking saboda haka ta shiga call logs nata, Husband to be, shine sunan da ta taɓa, tuni ƙiran ya tafi sai dai kamar yadda ta zata hakan ne ta kasance, bai ɗaga ba har kiran ya yanke, kamar za ta yi kuka haka yanayin fuskarta. Iska ta fesar daga bakinta sannan ta shiga gallery nata, private folder ɗinta ta shiga tare da saka password ɗin. (Ido waje nake kallonta ganin abunda ta danna ɗin.) Ko da ta buɗe hotuna ne suka zubo, a kan ɗaya daga ciki ta tsaya tare da zuba idanunta kai. Ta share wasu daƙiƙu kafin ta saki ajiyar zuciya ta fita kana ta ajiye wayar kan bed ɗin. Ƙara janyo wayar tayi tana ƙara zubawa picture ɗinsa ido don ji take kamar zai dawo gareta ne shiyasa wannan al'amarin yake faruwa, how she wished ace ya dawo gareta, amma it's impossible, ya riga ya tafi wurin da ba zai dawo gare ta ba, da wannan tunanin ta sauƙe ajiyar zuciya tana share ƙwallar da ta zubo mata kan kyakkyawar fuskarta.

"Ya Allah ka sa alkhairi ne ke tunkaro ni, ina jin bugun zuciyata ya sauya ga Ya Ishaq ya ƙi picking call na tun jiya nake kiransa, Allah ka sa dai lafiya."
Tsaye ta miƙe ta koma bedroom ɗin da aka zamar da shi nasu yanzu, abunda ya zamo ruwan shan su ta sha sannan ta koma kusa da Nainarh ta kwanta tana mai ɗaura kanta a cinyar Nainarhn.
"Ya dai malama?"
Nainarh ta faɗa tana jifan Zahrah da wani kallo, ba iya Zahrah kallon ya ba wa dariya ba sai da dukkansu suka dara. Marairaice fuska Zahrah tayi tana faɗin "Kai sister me ya faru."
Kan Zahrah Nainarh ta zame daga cinyarta tana harararta.
"Don kin raina ni ko Ya Khalil bai hau cinyata ba sai ke?"
Ido dukkansu suka zaro suna sunkuyar da kai ƙasa yayinda hamshaƙiya Nainarh ke famar janye kan Zahrah ita kuma ta ƙi ba ta dama.
"Lallai Nainarh, Sannu da aiki." muryar Mommah ta doki kunnuwanta, tuni wata irin kunya ta lulluɓe ta, kan ta ta sunkuyar tana matse idanuwanta gam. Aunty Na'ima da ke murmushi ƙasa-ƙasa tace "kuma da an taɓa ta ta nuna ta fi kowa kunya ba."
Dariyar da suke riƙewa ne ta ƙwace musu ƙya-ƙya sai Mommah ta riƙe baki tana kallonsu cike da mamaki, kanta ta jijjiga kawai ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta ajiye musu fruits ɗin saman centre table ɗin da ke dakin daga nan ta fice tana murmusawa ita ma.

*YAYA ISHAQ*

Kwance yake kan makeken gadonsa sai juyi yake, a jima kaɗan ya juya nan daga gani za ka fahimci cewa ba lafiya ba. Ya shafe tsawon lokaci yana juye juye can dai ya ɗago kansa tare da janyo pillow ya rungume, ya ƙara shafe wasu daƙiƙun kafin ya miƙe ya zauna, idanuwansa ya buɗe wanda launinsu ya koma jawur kamar ana hura wuta ciki.
Gabaɗaya ya rasa me yake masa daɗi a zuciyarsa, ina ma zai sa ransa yaji sanyi yake nema amma duk position ɗin da yayi assuming sai yaji shi uncomfortable hakan yasa ya miƙe ya nufi toilet tare da banko ƙofar. Can kuma sai ga shi ya fito yana goge jikinsa alamar wanka yayi.

Har abun tausayi haka Yaya Ishaq yake strange abubuwa kamar ba wannan mutumi mai fara'a da son mutane ba, ga shi duk ya bi ya rame kamar ba wannan giant and handsome guy ɗin nan ba. Hannunsa ya kai kan wayarsa tare da buɗe ta, bai bi ta kan tarin missed calls ɗin da aka masa ba bare yayi calling back. Tsaki ya ja kawai ya cilla wayar gefe sannan ya fice parlourn sa, kallo ya kunna ko Allah zai sa ya ji relief game da abunda ke damunsa amma ina kamar wanda ake ƙarawa damuwar, ganin hakan na shirin zame masa matsala yasa ya miƙe ya tsiyaya ruwa cikin glass cup ɗin da ke kan centre table sannan ya kai bakinsa. Sau ɗaya yayi sipping daga nan ya ajiye. Ransa ne ya ƙara jin yana tafasa, ba tare da wata-wata ba ya zube kan sofa yana dafe kansa da ke tsananin yi masa ciwo.

Motsin buɗe door ɗin da ya ji yasa ya lumshe idanuwansa tare da buɗesu, sanin cewa ba zai wuce Mom ɗinsa bane yasa ya ƙara lumshe idanuwansa.
"Son, Son!" jin shiru yasa Mom tunanin ko yana bedroom nasa sai dai ba ta kai ga shigar ba ta jiyo muryarsa yana ƙiranta a kasalance. "Mom"
Yanayin Yadda taji muryar tasa kamar ɗan maye yasa ta juyo a tsorace tana nufowa yadda yake.
"Son, Sweetheart, mene ne?"
Jin shiru bai amsa mata ba yasa ta ƙarasa tare da ɗaura hannunta a wuyansa try to feel the degree of hotness/coldness of his body, a rikice tace "Ba ka da lafiya ne? Me yake damunka? Lemme call Dr..." Ba ta Kai ga ƙarasawa ba ya katsar da ita cikin kasalalliyar murya yace "Nooo Mom, no...no need of calling any Dr. I'm alright just just..." sai kuma yayi shiru yana miƙewa zaune.

A matuƙar gigice Mom ɗinsa tace "No Son, i've to call the Dr. Ba lafiyarka ba, ka sha wani abu ne?"
"No Mom" ya ba ta amsa a gajarce
Kanta take jijjigawa cike da rashin gamsuwa da amsar tasa tace "Ka fara shan ƙwaya ne Son?" cike da ƙosawa ya ba ta amsa da "Damn it! Ba abunda na sha, i just..."
Tun tana a tsorace har lamarin ya fara ba ta mamaki thinking of why the sudden change from her son amma babu mai ba ta amsar, hakan yasa tace "Is alright, na ji son, lafiyarka ƙalau, amma me ya hana ka bacci?"
"Mom babu komai fa, me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login