Showing 54001 words to 57000 words out of 157517 words
ji horn ɗin da yake mata ba har ya kusa buge ta Allah ya bashi ikon taka brake, a fusace ya fito don ganin waye sai dai abun da ya gani Yasa ya ɗan zaro idanuwansa waje. Da sauri ya Sadauki ya isa gareta tare da ɗaga ta tsaye don lokacin ta riga ta saddaƙar shikenan ta mutu.
“From where are you Mabruka?, Ina za ki je da gudu haka?”
Bata ce masa uffan ba sai ma lafewa da tayi a jikinsa tana sakin wani irin kuka mai raunana zuciyar mai sauraron sa, bai yi ƙoƙarin janye ta daga jikinsa ba kuma bai hana ta kukan ba tsawon mintuna biyar kafin tayi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya. Hannunta ya ja bai tsaya ko ina ba sai front seat, ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga, bai tada motar ba sai da ya dube ta tsawon wasu sakanni yana nazartar ta, can kuma ya kau da kansa gefe yace
“Daga ina kike?”
Cikin rawar murya tace “Daga can nake..ehm hall ɗin da ake event ɗin.”
Kansa gefe yace “An gama ne?”
“A'a” ta bashi amsa tana jijjiga kanta
“Then why are you out, baki son bikin ne?”
Shiru tayi ba ta ce masa komai ba.
“Ki bani amsa”
Kai ta jijjiga masa alamar a'a
A ɗan hasale yace “Ba a min magana da ka”
Da sauri tace “I'm sorry”
Shiru yayi ba kuma shi da alamar tayar da motar ga shi maghrib ta kusa
“Then why are you out?”
Kuka ta fashe masa da shi tana jijjiga kai, bai san lokacin da ya janyo ta jikinsa yana tapping bayanta ba har ta Yi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.
Gently in his melodious voice yace
“Tell me, Ko Mommah ta je wurin ne?”
“A'a” ta bashi amsa
“Ok tell me why are so frightened kika fito ba ki jira an mayar da ke ba, sai kace ba amarya ba.”
Kokawar da take da zuciyarta akan ta sanar da shi ko akasin haka ta kawo karshe. Zuciyar ta ta bata goyon baya ɗari bisa ɗari kan ta faɗa masa, atleast he'll know something to do, probably he might confront the issue and resolve it, ko kuma a fasa auren gaba-daya.”
Nan ta buɗe baki ta sanar da shi abunda ya faru. Ɓacin ransa ya ɓoye don ya ma samfo waye ya aikata hakan, ba kowa bace face Mommah, kuma ko za ta mutu auren nan babu fashi.
Lallashin ta yayi cikin kalmomi marasa yawa, and he encouraged her to be brave, nothing bad will happen in Sha Allah. Daga haka ya ja motar, daidai bakin flat ɗin su yayi parking, sai da ya tabbatar ya gana shigar ta ya sauke wani gauron numfashi sannan ya ja motar.
Can wurin event lokaci ɗaya aka nemi amarya aka rasa, duk neman duniyar nan an yi ba ta wurin, hakan yasa aka ƙira gida aka sanar nan ake ce musu ai ta koma ba ta jin daɗi ne. Nan aka fara jigilar mayar da kowa gida.
*Mommah*
Cikin kwana ɗayan da ta yi a gidansu ta galabaita, ta saba kwana kan makeken gado ta juya yadda taso wai yau ita ce kan gayar tabarma, a can gidan mijinta ta kan manta da wata halitta ta sauro amma daren nan haka sauro suka hana ta rintsawa, da ta juya nan sai wannan ya mall mata. Da safe fuskar nan Tata ta kumbura suntum saboda rashin samun bacci, ko ina na jikinta ban da ciwo babu abun da yake yi, maimakon ta risina sai ma ƙara zafi da tayi, alwashin ta sha ma kanta tabbas aka yi auren nan sai ta hana su zaman auren nan.
Babbar magana, su Mommah an saba da samun ruwa ko yaushe sai da ta shiga wanka ta tarar ashe babu ruwa ko ɗiso, haka ta fito ranta ɓace, Hajja ta tarar a parlourn amma ko kallo ba ta samu ba, gaida ta tayi ta amsa kamar dai jiya daga haka ta ɗauke kanta. Cikin ta ne ya ba da sautin ƙulululuu, nan ta tuna rabin ta da abinci tun jiya da safe. Kamar za ta yi kuka ta ƙira sunan Hajja.
“Hajja” kallo ɗaya Hajja ta mata ta ɗauke kanta
“Ina abinci na?”
Wani kallo da Hajja ta aika mata sai da ƴaƴan hanjin cikinta suka motsa
“Dama nauyin ciyar da ke a wuya na yake Sughrah?, Ba dai ke kin isa da kan ki ba? Sai ki yi zaman gidan idan daɗi ne da shi aka ce miki, ga fili ga mai doki.”
Daga haka Hajja ta miƙe ta bar parlourn ranta na ƙuna.
Baki sake Mommah ke kallon ta, “ko meye na ɗaukan zafin rai?” Ta tambayi kanta. Daga haka ta kyaɓe baki ta wuce zuwa ɓangaren Yaya Kabir, bayan sun gaisa da Aunty Rahina sai ta rasa mai zata ce mata, ga shi yunwa take ji ga kuma izza ta hana ta faɗin abun da ya kawo ta, sarai ita ma Aunty Rahina ta fahimta amma sai ta kafse ta ci gaba da wankin kayan yaran da take yi.
“Don Allah nace ba” Mommah ta faɗa ranta na ƙuna tare da kawar da kanta gefe.
“Idan akwai abinci ki bani”
“Babu” shi ne kaɗai amsar da ta samu daga gareta. Daga haka Aunty Rahina ta ci gaba da wankin ta. Ran Mommah ina ya yi dubu to yau ya ɓaci, haka ta fice a hasale, ta shiga ƙofar Yaya Sa'ad, gwanda Aunty Rahina ta amsa mata, Aunty Maryama ko kallonta bata yi ba har ya gaji da tsayuwa ta fito don kanta.
Part ɗin ƙaninta Sadiq ta shiga, amaryarsa tace ita ma gaskiya ba isanta zai yi ba bare ta ba wani. Rai ɓace Mommah ta dawo Bedroom ɗin da aka bata, wayar ta ta ciro tana doka wa Sadauki kira amma har yau numbern ba ta shiga, hankalinta ne ya tashi amma sai ta tuna ba iya shi ta haifa ba, hakan ya sa ta ƙira ɗan'uwansa sai dai shi ma bai yi picking ba.
Ta ma rasa ta ina za ta fara ga yunwar da ta sako ta gaba, can ta yanke shawarar sayar da wayarta idan ya so ta siyo abubuwan buƙata da kuɗin kafin ta samu su yi magana da Junaid. Da wannan shawara Mommah ta fice, cikin samarin unguwar ta samu wani Ɗahiru ta bashi wayar ya sayar mata, bayan ya dawo ya bashi 3k sannan ta je ta yi siyayyar abun da za ta buƙata, indomie, macaroni, da sauran abubuwan amfani. Yara ne suka shigo mata da su har ɗakin da aka bata, ƴar katifar ta irin ta ƴan boarding school ɗin nan ta ajiye, sannan ta ƙara fitowa ta samu wasu yara suka siyo mata petrol ta tayar da generator tukun ta samu ruwan amfani.
*My readers! How did you see Mommah's life now? Shin ta cancanci hakan? Anya kuwa an kyauta mata?*
*Ina team Zahrah ne? Kun haƙura da Yaya Sadauki kenan? Muje zuwa*
[1/14, 9:06 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎* _Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣5️⃣
﷽
*BAUCHIN YAKUBU, ƘARAMAR HUKUMAR TAFAWAƁALEWA*
Malam Sufi ne zaune da mai ɗakinsa Baba Laure wacce ke dama masa ruwan shayi, tana gamawa ta miƙa masa. Kurɓa ɗaya yayi ya juyo gare ta.
“Uwar yara yau ina so na kammala da aikin Goggo Balki, ki taimakawa maras lafiyar ku zo a kammala.” miƙewa Baba Laure tayi ta nufi cikin gidan, ɗakin da aka sauƙi Inna da maras lafiyarta sai kuma Asma'u da Balkisu ta shiga.
Fuska sake tace
“Goggo Malam yace ko Amina za ta zo a ƙarasa aikin nata”
“Ah ai dole, taimaka mata ku je tare, ko Asma'u da Balkisu ku taya ta in ba za ta iya ba.”
“Dama kuwa taraddadin yadda za mu tafin nake, Takwarar Goggo ku taya Ni mu tayar da ita.”
Da haka suka taya Baba Laure suka ɗaga Baba Amina suka nufi Ɗakin da Malam ke aiki, ko da suka kai ta fitowa suka yi Mallam yace Inna ta Zo Ayi gabanta.
Tabbas Alqur'ani waraka ne, a yau dai Malam ya samu damar warware sihirin da ke jikin baiwar Allahr ta hanyar ladabta shaiɗanin da aka wakilta don juya mata tunani. Nan ta baje kuma sai bacci.
Ba ita ta tashi ba sai wuraren la'asar, a hankali ta fara buɗe idanuwanta da suka yi nauyi cikin ranta tana ayyana wane irin nauyayyan bacci haka ta yi? Bismillah t furta tare da ƙoƙarin tashi ta zauna wanda yayi daidai da shigowar Baba Laure.
Cike da farin ciki ta ce
“Ah! Baiwar Allah kin tashi? Goggo, Goggo!”
Kiran da take ƙwala musu yasa Inna fitowa da gudu ta shigo ɗakin kamar ba ƴar tsohuwar nan ba.
Saboda rashin ƙarfin jiki har ta kusa gama tashi ta koma yaraf ta kwanta. Rintse idanuwanta tayi tana ambaton sunan Allah.
Da sauri Inna ta Zauna kusa da ita ta taimaka mata ta miƙe zaune. Idanuwanta da ta kasa buɗewa ta ƙara ƙoƙarin buɗe wa, alhandulillah kuma sun buɗu, ɗakin ta bi da kallo ba tare da ta furta komai ba, can ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata last moment da ta yi aiki. A zabure ta furta “Zahrah!”
“Ma sha Allah” Inna ta furta tana faɗin
“Baiwar Allah tashi ki watsa ruwan zafi ko kya ji daɗin jikin ki.”
Sai a lokacin ta Kai dubanta ga Inna wacce ke washe mata baki. Ganin ba ta santa ba yasa ta fara kokonto kan me ya same ta
“Wace ce wannan?” ta tambayi kanta
Ganin shirun ya yi yawa yasa Inna ƙwala ƙiran Asma'u da Balkisu. Suna zuwa Inna ta basu umarnin su taimaka mata ta je ta watsa ruwa wanda tuni Baba Laure ta haɗa shi a bayi.
Ƙoƙarin gocewa matar take tana faɗin
“Ina kika je ne Zahrah?”
Cikin sigar lallashi Inna tace “Yi haƙuri baiwar Allah ki watsa ruwa kin ga jikin ki ba ƙarfi, In kin sa abu a cikin ki kin yi salla sai a yi magana ko?”
Cikin ruɗanin zuciya matar ta gyaɗa kai. Nan su Asma'u suka kai ta har bayin kafin su fito, nan suka baro ta tayi wankan suna jiranta a ɗan nesa kaɗan da bayin.
Tsantsar farin cikin da fuskarsu ta nuna zai tabbatar da irin yanayin da suke ciki.
Ta jima sosai a bayin saboda yanayin tariya da ƙwaƙwalwarta ta faɗa, can dai ta watsa ruwan ta fito, da sauri su Asma'u suka zo suka taimaka mata zuwa ɗakin da aka ba su tun farko. Kayan Baba Laure da yake ba ta cika ƙiba ba aka ba ta ta saka. Nan aka baje mata tsiren da Inna ta sa a siyo takanas don ita. Duk da bakinta babu daɗi a haka ta daure ta saka tsiren ciki, da ƙyar ta iya cin yanka biyar ta sha ruwa sannan ta jinginar da kanta jikin gini. Damuwarta ɗaya ina ƴarta take? Me take a nan kuma su waye waɗannan?”
Cikin ƙarfin hali ganin ba ta ra'ayin magana Inna tace
“Baiwar Allah kin tashi lafiya” sai lokacin ta mayar da kallonta ga Inna.
“Alhamdulillah, yau kusan kimanin shekaru biyu zuwa uku kenan kina kwance sai yau Allah yayi kika dawo daidai, na godewa Allahn da ke warkar da marasa lafiya, ya kuma azurta su da lafiya a karo na gaba.
“Ina yarinya ta Zahrah?”
Murmushi irin na manya Inna tayi tace
“Ke kaɗai muka tsinta Ni da ƴan jikoki na, amma Alhandulillah ki huta zuwa jimawa Mallam zai zo sai mu ji daga bakinsa.
*ABATCHA ESTATE*
A yau juma'a Ya Junaid ya diro ƙasarsa ta haihuwa don shaida auren ɗan'uwansa shi da iyalinsa. Abokinsa Jamal shi ya ɗauko su, kai tsaye Abatcha estate aka wuce da su. Saboda rashin gyara gidansa sakamakon a bagatatan ya zo yasa ya sauƙa Part ɗin su, surprisingly Mommah was nowhere to be found. Daga parlour suka yada trolleys nasu, matar shi Aunty Na'eema ta baje a ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin shi kuma ya zaga kowanne room Amma ba kowa, fitowa waje yayi niyyar yi suka ci karo da Nainarh wacce ta shigo ɗaukar hand bag nata da zata yi amfani da shi yau.
Da gudu tayi hugging nasa tana faɗin
“Oyoyo big Bro, yaushe ka zo? Kai ɗaya ne? Ina baby Arya” lokaci guda ta jera masa tambayoyi tare da sakin sa tana jiran jin amsoshinta.
Fuska sake ya ja kuncinta yace
“My rigima Sis, waɗannan tambayoyin naki ai sai su sa na ɗimauce, wanne kike so na fara da shi?”
Fuska shagwaɓe tace “Duk nake so ka amsa min, shine kazo babu sanarwa ko?”
Murmushi yayi yace “I'm sorry, ai ban san da zancen bikin ba sai jiya da dare, I've to book flight for us mu zo a yi da mu”
Ta buɗe baki za ta ce wani abu yaja kuncinta “Allow me to rest, Ina Mommah? I've been calling her number but not reachable.”
Shiru tayi ba ta ce komai ba saboda ba ta so a ji mutuwar sarki a bakin ta sai ta ce
“Ai Mommah ba ta nan, ta yi tafiya tun shekaranjiya, but we're expecting her return today or tomorrow”
“Good! Ki shiga ki kai kayan In-law ɗinki ciki sai ki sa masu aiki su gyara mata one of the bedrooms. Ok?”
Cike da zumuɗi tace “Har da Aunty Na'eema aka Zo?” ba ta jira amsarsa ba ta shige da gudu tana hugging in-law ɗin ta tana mata sannu da zuwa. Sai lokacin kallon ta ya kai ga Baby Aryan, her soul, da sauri ta ɗaga shi tana cilla shi sama tana mai wasa, shi kuwa sai ƙyaƙyatawa yake. Aunty Na'eema ce tace “Kin ga Nainarh shiga da Ni ciki, ina so na gasa jiki na”
“Sorry Aunty na” Nainarh ta faɗa “Mu je ciki” nan ta kai ta Bedroom ɗin ta sannan ta wuce kitchen ta sa Saratu ta shiga da kayan sannan ta gyara musu ɗakin.
Komawa ɗakin tayi ta ɗauko handbag ɗin sannan ta fice ganin Aunty Na'eema ba ta fito ba.
Ko da ta koma Zahrah ce ta fara kallon ta, ganin kyakkyawan baby yasa ta furta “Ma sha Allah, Sis Nainarh Ina kika samo wannan baby Mai kama da ke?”
Sai lokacin sauran ma hankalin su ya kai ga Baby Aryan da ke hannun Nainarh.
“Yaron Big Bro na ne, yanzu suka zo daga Egygt, meet my son Aryan”
Zahrah tace “Wow! Nice name” kuncinsa ta taɓa nan yaro ya miƙo mata hannu.
Dariya dukkansu suka yi, nan yaro ya dawo hannun Zahrah.
Ko da Aunty Na'eema ta fito bata tarar da Nainarh ba murmushi tayi ta nufi part ɗin Hajjaty don ta san ba za ta wuce nan ba.
Cike da girmamawa suka gaisa da Hajjaty, nan take sanar da ita ba su san da batun bikin ba. Hajjaty tace mata ai abun ya zo babu zato ne, amma Alhandulillah tunda sun zo. Daga nan ta tambayi Hajjatyn ko ina Nainarh, Bedroom ɗin Zahrah ta nuna mata, ko da ta je don ta amshi Aryan su shiga sauran sassan gidan ne yaro Yace a'a, ga uwarsa amma ya maƙale wa Zahrah, haka Aunty Na'eema ta fice ita da Nainarh don ta raka ta. A hanya take tambayarta ko wace ce wacce Aryan ke hannunta?, Nan Nainarh ta fere mata zancen tas.
Aunty Na'eema ƴa ce ga Mommy Nasiba, mace ce wayayya shiyasa tun auren su ba a taɓa jin ta da wani ko wata ba. Shiyasa kuma kowa ke mutunta ta don In ta zo kamar a jefa ta ciki haka ake. Part ɗin Hajiya Babba ta yada zango wurin amarya, shirye-shiryen duk sai ya dawo hannunta.
Da yamma aka gabatar da rantsattiya kuma hamshaƙiyar walima wacce ta tashi kan duk wanda ya halarta musamman ɗan waje da ahalin. Kowa ya koma da kayan kwatance, daga nan aka watse. Aunty Na'eema dai na ɓangaren amarya.
*Yaya Ishaq's POV*
Kamar yadda ya mayar da abun tamkar ibada, yau juma'a sai da yaje can gidansu Zahrah, amma jiya i yau babu wani sauyi.
Rai babu daɗi haka ya dawo gida yana kewar abar ƙaunarsa.
*TAFAWAƁALEWA L.G.A*
Bayan shigowar Mallam mai ɗakinsa ta sanar da shi cewa maras lafiyar ta warke. Sai da suka ci abincin dare ya aika kiransu gabaɗayansu don jin bayani daga gare shi.
Bayan sun zo Mallam Sufi yayi gyaran murya yace
“Assalamu Alaikum Warahmatullahi wabarakatuhu, bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci ina so na miƙa godiya ta ga Ubangiji, tabbas godiya ta tabbata ga Allah mai rayawa da kashewa, mai juya al'amuran duniya, Ubangijin da ya halicci cuta ya kuna tanadar da maganinta. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon tsira, shugabanmu kuma jagoran mu, cikamakin annabawa Sallahu alaihi Wasallama tare da iyalinsa, sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa i zuwa ranar ƙarshe.”
“Ina mai farin cikin samun lafiyar wannan baiwar Allah, Goggo Balki Ubangiji ya biya ki, tabbas samun mutane irin ku masu zuciyar tausayawa abu ne mai wahala. Ba tare da ɓata lokaci ba muna son jin taƙaitaccen tarihinki baiwar Allah don mu samu mayar da ke ga ahalinki.”
Gabanta ne ya bada sautin dimm, amma sai tace “Suna na Madina, ina da ɗiya ɗaya ƙwal a duniyar nan, Zahrah. Muna zaune ne a garin Bauchi.”
“Ma sha Allah” malam ya faɗa
“Madina sannu, za ki iya tuna unguwar da kike ai?” kai ta gyaɗa masa, yayi murmushi.
“Ma sha Allah, kamar yadda kika ga wannan, wato Goggo Balki” ya nuna Inna da yatsa
“Ita ce ta tsince ki kwance a hanyar ta na dawowa daga gaida wata aminiyarta ta yarinta tare da jikokin ta a wani kango, har sun wuce ta sa jikokin ta gaba su koma baya su ga kamar mutum ta gani, ai kuwa ta tarar da ke kwance alamar ba ki san yadda kike ba ma. Da yake mutuniyar kirki ce kuma zuciyarta akwai hasken imani haka ta sa jikokin ta suka nemo mai adaidata sahu ita kuma ta tsaya tare da ke, nan ta kai ki gidanta tana baki magungunan gargajiya sai dai babu wani cigaba. Ba ki taɓa yin magana ba tsawon lokacin sai dai a tayar a kwantar, abinci kuwa iya kunu kike iya sha, duk wannan ɗawainiyar ita da ƴan mata biyun nan suka yi, watannin baya Goggo ta min magana game da ke, da yake nima ina da sabgogi sai na manta. Yau sati