Showing 144001 words to 147000 words out of 157517 words
Yaya Sadauki da ba su saba ba. Around 8pm suka iso Abuja, kai tsaye ABATCHA ESTATE suka nufa, a part ɗin Hajjaty suka sauƙa dukkansu, Yaya Sadauki da kansa ya raka Kasu Sadi guest house Na Alhaji Baba, daga nan yayi masa list ɗin abubuwan da zai siyo masa, kafin ya fito aka fara shigowa kawu Sadi da Abinciccika kusan kala huɗu. Shi kuma yaya Sadauki ya fito ya cewa Zahrah ta zauna a nan yana dawowa, tare da Detective suka wuce nearest Islamic store, Tas ya siyo komai ban da Zamzam tunda dama can suna da shi da yawa a gidan, a bakin gate Yaya Sadauki ya sauƙa, Detective Musa ya wuce Office Quaters nasu.
Lokacin da ya koma kan abinci ya sauƙa don ba ƙaramar yunwa yake ji ba, yana gamawa ya wuce gidanshi ya watsa ruwa sannan ya ɗebo ma Zahrah duk abinda za ta buƙata.
Lokacin da su Daddy suka shigo gaida Alhaji Baba bai yi yunƙurin sanar da su komai ba, sai dai yana so ya ba su mamaki duk da cewa shima a tsorace yake, zuciyarsa bugawa take cike da fargaba, bai san su waye za a ce responsible for such bad act ba, don kuwa babu wadda ya cire cikin sirikan gidan, gani yake ko da Mommahnsa aka gano ba zai Musa ba tunda ba a gane mugu a fuska, amma fatansa ta kasance ba ta cikin waɗannan miyagu da suka cutar da rayukan jama'a cikin familyn suka dasa rashin fahimta tsakanin wasu.
Ta waya suke communicating da Kawu Sadi, ba jimawa kira ya shigo wayarsa, ganin Sheikh Imam Nasir yasa ya ɗaga da sauri, few minutes ya katse kiran tare da miƙewa a sukwane. Da kansa ya shigo da shi har ɗakin da Kawu Sadi ya sauƙa. Suna shiga Kawu Sadi yace "Nasir?" Yana bin Sheikh da kallo, da Sauri Sheikh Imam Nasir ya ƙaraso kusa da Kawu Sadi tare da riƙe hannunsa yace "Sheikh Sadi? Kana nan? Kana duniyar, da rabon zan ƙara ganinka?"
Nan dai suka manta da kashin Yaya Sadauki suka shiga gaisawa, ashe dai tare suka yi karatun Allo da kuma karatun gaba da secondary a A.D Rufa'i da ke garin Misau.
Bayan sun gaisa sosai aka dawo kan batun da ya haɗa su aiki, nan suka tattauna kan yadda komai zai kasance. Bayan sun gama Yaya Sadauki yayi insisting Sheikh da ya taho akai shi ɗakinsa yace a'a, ga shi ga ɗan'uwansa nan ya bari kawai, da haka ya koma part ɗin Hajjaty ya ba wa Zahrah saƙon su Sheikh kan kada ta kwanta bacci yau.
Har 12:30 am idonta biyu, tana jin baccin amma babu damar yi saboda Abunda ke gabanta ya sha baccin. Takun tafiyar da ta ji yasa ta ɗan zabura ta tashi ta zauna, ajiyar zuciya ta sauƙe ganin Yaya Sadauki ne, sai da ya ƙaraso daf da ita, a saitin kunnenta ya furta mata "Za ki iya fitowa ko kina tsoro"
"Zan iya" ta ba shi amsa a taƙaice.
"Saka hijabinki ki zo mu tafi." Hijabi ta saka sannan ta riƙe hannunsa suka fita a tare.
"Za ki iya gane wurin da kika taɓa gani suna meeting ɗin ina?" Kai ta gyaɗa, yace "Ok, ga su Sheikh na jiranmu kada ki ji tsoro, mu kula da takunmu."
Kai ta gyaɗa masa again suka fara takawa har zuwa daidai wurin da suka yi artabu da waɗannan shaiɗanun mutane.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da goge fuskarta da tafukan hannayenta. A hank dubi Kawu Sadi tace "A nan ne".
Ba tare da waninsu ya ce komai ba suka samu wuri suka fake jikin busassun ciyayin da suka bushe. Sun shafe kusan mintuna talatin babu wani baƙon al'amari da ya bayyana garesu.
Kamar ƙiftawa da Bismillah wani duhu ya gauraye wajen, yanayayin duhun ya fita a misali, ko hasken hakware ba a iya gani, hakan yasa Sheikh Imam Nasir ya umarce su da karanta addu'o'in tsari, Babu abinda zahrah ke maimaitawa sai "la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"
A haka suka kwashe kusan mintuna goma ba tare da ganin wani haske ba, kamar ƙiftawa da Bismillah kuma yanayin ya koma tamkar yadda yake a baya. Duk da haka Kawu Sadi insisting nasu yayi da su ci gaba da karanta addu'o'in tsari.
*THE KLANS 😈*
Kai tsaye suka fara gudanar da tattaunawarsu. Yau da alama a fusace kowa yake, siyasa abu kaɗan za a yi sai hayaniya. Fahimtar hakan yasa Kawu Sadi da Sheikh Imam suka matsa kusa da mutanen a hankali tare da mannewa jikin wasu bishiyoyin tsamiya biyu da ke jere.
Cikin fusata uwargijiya tace "Gutsurito na gaji! Gutsurito me kake so na sadaukar maka don cikar buri na, na gaji, ina buƙatar ɗaukar fansar da ta kawo mu cikin ahalin nan kafin a samu wasu su dakatar da Ni, Gutsurito na yi rauni, raunin da na gagara sanin dalili. Ga kuma ƴan'uwana da muke shayar da kai da jini tare da su, suna buƙatar ƙarfin da za su iya gamawa da duk wata damuwa da ta Kunno musu! Ka faɗi me kake so mu cika maka, a daren yau muke so mu tarwatsa komai, ina so na mayar da wannan gidan kamar mahauta, jini ya malale ko ina ta yadda za ka sha yadda zai maka!"
Wata tsawa aka sake wacce ta razana kowanne mahaluki da ke cikin farfajiyar wurin yayin da ƙasar wurin ta fara girgizawa kamar za ta dare na zaune zu lume ciki. Zahrah, Yaya Sadauki, they're all afraid, ƙanƙame juna suka yi yayin da suke furta duk wata addu'a da ta zo bakinsu. A ɓangaren DEVILS KLANS 😈 duk cikin su babu wadda bai tsorata da al'amarin ba, tunda suke tattaunawa ba su taɓa ji Dodon tsafi ya yi magana ba, kaico! Yau tsawa ma yayi, kowa ya tsorata ya gama saddaƙarwa. Lokacin da rawar ƙasar ta sarara Muryar dodon tsafi ta daki kunnuwansu.
"Uwargijiya! Ke uwargijiya, ki duba madubinki za ki ga me yake shirin faruwa da ku! A daren yau ku ba Ni jinin da zan tsotsa, ku bani wadatacce wanda zai ishe Ni har na dakatar da Abunda ke tunkaro ku! Maza ki duba!" Ya ƙarasa faɗin haka cikin wata razananniyar murya.
*React and share fisabilillah.*
[09/05, 7:30 AM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 6️⃣9️⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*
Jiki na rawa uwargijiya ta shafa iska, nan madubin tsafinta ya bayyana, baƙin mayafin da aka lulluɓe madubin ta janyo tare da buɗewa, Abunda ta gani yasa ta saki wani razanannen ihu!
Wasu dalasimai ta fara karantawa, daga bisani ta ƙara kallon madubin sai dai abun da ta gani bai sauya ba.
Magajiyar uwargijiya ce ta fito a zafafe tace "Ya isa haka Dodo! Ka dakatar da komai, kada ka bari mu rasa ikon mu, da kai muka dogara ka sani. Ka dakatar da komai, akwai masu leƙen asiri a kusa, saboda haka jininsu za mu mallaka maka ba tare da ɓata wani lokaci ba."
Daga haka ta buɗe tafukan hannayenta kamar mai tattara wani abu, jujjuya hannunta tayi can fasa wani irin mahajkavin ihu tana faɗin
"Ko su waye ba zan yafe muku ba, ku zo jininku dole Dodo ya sha don dawowar martabarmu."
Kamar daga sama Muryar Kawu Sadi ta bayyana yana faɗin "ke shaiɗaniya, jininmu ya fi ƙarfi mushrikai irinku, a yau ba gobe ba zan nuna muku cewa Allah ne ya halicce ku, kuma shi Yakamata ku bautawa..!"
"Ya isa haka munafiki!" Uwargijiya ta dakatar da shi.
"Ka jira ka ga in ka tsira daga hannunmu sai ka fara faɗin Allah, mun san Allahn muma, idan har kun fita a nan zan gani."
"Authubillah minasshaiɗanir Rajeem!"
Kawu Sadi ya ambata.
Mahaukaciyar dariya uwargijiya tayi, sai da tayi kusan mintuna uku tukun ta dakata ta pointing iska da yatsa "Kafin Allahn da kake gadara ya ceceka da kai da wasu mutanen da ban san su waye ba! Ka tabbatar mun shanye jininku, Allahn ku ba ya amsa roƙonku nan take kamar yadda Gutsurito yake amsa namu! Ni da ku."
Kai Sheikh Imam Nasir ya jijjiga, cike da jimami yace "wanda ya halaka ya halaka! Wanda yayi nisa ba ya jin ƙira, amma yau ko ku su waye sai mun karya alkadarin tsafinku."
A matukar fusace magajiyar uwargijiya ta fara magana tana amfani da hannunta cike da siddabaru
"Kai! Kun kawo kanku ga fadar Gutsurito, ku tabbatar yau kashinku ya bushe!"
Nan fa abu ya fara cin tura, Su Shaikh Imam na famar karanto ayoyin Ubangiji yayin da devil's klans ke auna fasahar tsafinsu. Kowa yi yake cike da ƙwarewa, Zahrah da Yaya Sadauki dai suna ƙanƙame da juna suna karanto nasu addu'o'in.
Mintuna uku da fara wannan muƙabala fannin DEVIL'S KLANS 😈 suka fara raunana, ayoyin Ubangiji babu wasa a cikinsu, tuni dukkansu suka haɗu, su wajen kimanin 30 suna haɗa ƙarfi da ƙarfe, sai dai tun ba a je ko'ina ba suka ligirta, ƙananun cikinsu tuni suka faɗi ƙasa. Manyan shaiɗanun cikin kuma sai haki suke suna ƙara ƙaimi wurin aikinsu na siddabaru. Ganin Ayoyin Ubangiji suna ci gaba da raunana su yasa uwargijiya ta ɓace ɓat kamar ba a halicce ta a wurin ba. Wannan dalilin ne yasa magajiyarta yin rauni, sai dai raunin bai hanata ci gaba da fafatawa ba.
Sheikh Imam Nasir da Kawu Sadi ba su tsaya da karanta Alqur'ani ba, babu tsammani uwargijiya ta bayyana a filin dagar.
"Ya isa haka! Ku dakata nace!" Ba tare da sun saurareta ba suka ci gaba da karatunsu
A raunane tace "Ya Isa haka Nasir! Sadi ya Isa haka!"
A zafafe Kawu Sadi yace "Ke da kika ce Ubangijin mu ba ya ba mu promft assistance? Mu zuba mu gani"
Da sauri tace "Ka dakata, mu sulhunta Nasir! Kowa ya riƙe nasa, ka bar mana rayuwarmu mu huta muna, ba mu yi maka komai ba, ka fita sha'anin mu."
Dariya Kawu Sadi yayi yace "Ba ku yi mana komai ba kuka ce? Ku kuka tayar da rikincin don haka a yau za mu magance komai, kowa ya huta da cutarwar ɗan'uwansa."
"A'a Sadi, a'a, a'a, nace a'a, ka yi haƙuri ku tafi, ku fita daga al'amarin da bai shafeku ba. Na faɗa muku. Ku bari na ƙarasa aikin da na fara kada ku min haka."
"Ya ishe ki! Abu ɗaya da zan iya muku sai kun bayyana kanku, ku kuma sanar mana ƙudirinku ga mutanen da ba su ji ba basu gani ba. Shine kawai abun da zai iya sa mu yafe muku, in ba haka ba...kun san sauran."
Kawu Sadi na rufe baki gabaɗaya suka ɓace ɓat kamar wasu iskoki.
Ajiyar zuciya suka sauƙe tare da fitowa daga maɓoyarsu, fara duba su Yaya Sadauki suka yi, ganinsu wuri guda yasa Sheikh Imam Nasir kau da kai tare da yin gyaran murya, ɗan razana suka yi sannan suka waiwayo a ɗan tsorace, Ganin dai su Sheikh Imam ne yasa suka sauƙe tagwayen ajiyar zuciya tare da fara ƙoƙarin miƙewa, luuu zahrah ta yi baya za ta faɗi, yayi saurin riƙeta tare da ɗaukarta kamar wata baby ya tunkaro wurin su Kawu Sadi, kan su suka kawar gefe sannan suka fara takawa a hankali. Muhallin su ya raka su, Kawu Sadi yace "Yauwah Sadauki, yanzu ka Kaita ta huta, in sha Allahu da safe za mu kammala tunda yanzu alkadarin tsafinsu ya raunana mun riga mun ga abinda suke. Ka zauna kusa da ita na ga alamar a tsorace take." Sunkuyar da kai Yaya Sadauki yayi tare da jinjina kai alamar ya ji.
Kai tsaye part ɗin Hajjaty suka shiga rufe ko'ina yayi kafin suka nufi bedroom ɗin Zahrahn. Kan bed ya ajiye ta yana zama shima, hannunsa ya kai kan fuskarta, idanunta a zazzare kamar ta ga mutuwa tace "Heartbeat za su dawo su kama Ni ko?"
Murmushi yayi cike da son gamsar da ita yace "Babu wadda zai zo, I'm here with you, sleeping by your side, Babu wadda zai taɓa ki jikin jaruminki, haka ne?" Kamar wata yarinya ta ɗaga masa kai.
"Za ki watsa ruwa?" Kai tayi saurin jijjigawa har ta so ba shi dariya.
"Is ok, mu kwanta ko?" Ya faɗa tare da kwantawa kan gadon yana gyara kwanciyarsa, kamar kullum jikinsa ta shige tare da ƙanƙamesa, addu'ar bacci ya karanta musu ya shafa musu, cikin ƙanƙanin lokaci suka fara sauƙe numfarfashi. Safiya ta gari.
Ƙarar wall clock Na ɗakin ne yasa ya fara buɗe idanuwansa da suka yi masa nauyi saboda rashin isasshen bacci. Addu'ar tashi daga bacci ya karanta sannan ya fara ƙoƙarin raba jikinsa da nata, War! Ta buɗe idanunta tana bin sa da kallo kamar yau ta fara ganinsa, Gira ya ɗage mata alamar wetin? Murmusawa tayi tare da sakinsa ya miƙe tsaye, da ido ta bi shi har ya shiga toilet sannan ta lumshe idanunta tare da buɗesu. Jin ya fito yasa Zahrah sauƙowa tare da ɗauro alwala, ko da ta fito ba ta tarar da shi ba kawai ta tada sallarta, da ta idar ta roki Allah da ya yaye musu damuwoyin su. A kan sallayar bacci ya sake kwasheta.
Ko da gari ya waye bayan an yi breakfast aka kaiwa guest nasu, Zahrah Yaya Sadauki they all feed a part ɗin Hajjaty. Mamah da Hajjaty sun fuskanci cewa Zahrah is not ok, hakan yasa suka fara jera mata tambayar ko lafiya, Yaya Sadauki ya amsa musu da lafiya. Hajjaty ta dube shi tace "Kai na tambaya ne malam?" Murmusawa yayi tare da ajiye spoon ɗin da ke hannunsa yace "In kin ce ita ai Ni kika ce"
"Ka ce me?" Hajjaty ta tambaya tana riƙe baki, gira ya ɗaga mata tare da goge bakinsa da tissue, nan ya miƙe yana koƙarin fita lokacin da ya ga Mamah, don shi har ga Allah ya manta da tana wurin,da kallo Zahrah ta bi shi tana ƙara godewa Allah da ya mallaka mata shi a matsayin mijinta.
Da misalin ƙarfe 10:00pm, Sheikh Imam, Kawu Sadi da Yaya Sadauki suka fito da manya manyan jarakunan Zamzam ɗin da aka tofa ayoyin Ubangiji ciki, a tare suka fara bi ɓangare-ɓangare suna watsa ruwan a kowanne apartment, sai da suka bi kowanne gini da ke cikin estate ɗin suka watsa ruwan, hatta filin da ake gabatar da meeting ba su bari ba tukun suka dawo guest house ɗin.
A tare suke zaune Kawu Sadi da Sheikh Imam Nasir na ta aikin addu'o'in da karatun Alqur'ani.
Sun shafe awanni biyu Cir suna yi tukun suka fara jin ihu a hankali daga nesa, ba tare da sun lura ba suka ga shigowar wasu mata guda uku a hargitse suna ta ihu kamar mahaukata, shigowarsu suka zube kan carpet ɗin ɗakin suna masu ci gaba da ihun da suke yi, ihunsu kuma bai hana su Sheikh Imam Nasir karatunsu ba.
Sai da suka kai ayar ƙarshe a cikin suratul jinn, tukun suka dakata kowanensu ɗauke da murmushi kan fuskarsa yayin da matan suka fara sauƙe ajiyar zuciya. Me? Shi dai Yaya Sadauki kallon matan yake yana ƙoƙarin gano su waye ne, amma ya gagara ga kuma murmushin da ya gani kan fuskar su Kawu Sadi wanda yayi dalilin sanya shi cikin ruɗani. Cikin abinda bai wuce mintuna goma ba sai ga su Daddy, Alhaji Baba, da sauran ƴan'uwansu suna baza manyan riguna, ko waye ya sanar da su oho? Shi dai Yaya Sadauki an tara masa luguden tambayoyi ga shi babu mai ba shi amsa, ido kawai ya zura musu yana ganin mai zai faru.
Lokacin da Kawu Sadi da Sheikh Imam suka haɗa ido, a take suka fara karanto suratul mulk, wanda hakan yasa waɗannan mata ukun sakin razanannen ihu suna gurnani, ci gaba suka yi da karatun amma har lokacin matan suna a rub da ciki, babu ta yadda za a iya gano su waye.
Ayar ƙarshe da suka kai suka dakata, hakan yasa Sheikh Imam murmusawa ba tare da ya kalli su Alhaji Baba ba ya ce "Na ga alama ba ku ji jiki ba, har yanzu kuna ganin cewa tsafinku zai tseratar da ku." Kai suka fara jijjigawa ba tare da sun ɗago ba.
"Da a ce kun ji jiki da za ku magantu, tunda har ba za ku magantu ba, Sheikh Sadi, mu ci gaba da nuna musu ƙarfin ikon Ubangijinmu..."
Ci gaba suka yi da karatun, amma saboda taurin kai irin na matan sun ƙi yin magana amma dai suna jijjiga kansu alamar dai a bari, amma Kawu Sadi da Sheikh Imam suka yi kamar ba su gani ba.
Du Alhaji Baba kuwa kowa a tsorace yake da wannan al'amari yayinda zuciyar kowanensu ke cike da fargabar Abunda idanuwansu ke gani, kowa kuma zuciyarsa ta cika da son sanin me yake faruwa, su waye waɗannan mata? Me kuma ake miye dalilin kukansu idan ana karanta ayar Allah, "to ko dai shaiɗanu ne?" Suka tambayi kanunsu.
Yadda jikkunansu ke musu wani irin zafi kamar an ɗaura su a saman wuta amma sun gwammace su shanye kowacce irin azaba ne, babu gudu babu ja da baya sai dai komai ya faru, the more Ayar Allah ta shiga kunnuwansu the more ƙarin tiririn da ke shiga jikinsu. Tun suna ita jurewa har dai biyu daga ciki suka yi rauni. Ɗaya daga cikinsu tace
"Ku dakata haka, mun gaji, mun ji za mu faɗa muku komai, amma kuma ba ku isa ku ku dakar da mu daga Abunda muka girma da shi ba..."
*React and share fisabilillah.*
[09/05, 7:02 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 7️⃣0️⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2