Showing 99001 words to 102000 words out of 157517 words
kika kawo min ne?" ya ba ta amsa cike da son kawar da zancen, hakan da ya yi kuma ya sa ta ɗan ji hankalinta ya kwanta, hakan yasa ta fitar da abunda ya kawo ta tace
"Son, Salaha (sistern Mom) ta min waya tace kayan da ta haɗo sun iso, gobe za ta kawo da safe sai ka shigo ka duba idan da abun da za a ƙara."
Gabansa ne ya buga kamar an doka ganga, kansa ya ɗan langwaɓar yana son faɗin wani abu amma ya kasa, wani bushasshen yawu ya haɗiye maƙwat sai kuma ya ƙwaƙulo murmushin dole yace "Is alright Mom, zan shigo ɗin."
Murmusawa Mom tayi sannan ta shafa kansa kamar wani little baby tace "Ka je ka kwanta son, sweetest dreams."
"Same to you Sweetheart, bye" ya idasa tare da busa mata kiss ta iska.
Ajiyar zuciya Yaya Ishaq ya saki bayan fitar Mom, daga nan ya tashi ya nufi fridge nasa ya ɗauko kwalbar wine ya nufi bedroom nasa, tas ya kwankwaɗe ta kafin ya lodu kan bed ɗin yana lumshe idanunsa, ba jimawa kuma wani irin bacci ya kwashe shi.
*To jama'a, ga wata sabuwa ta ɓullo mana, Zahrah, Ya Ishaq me yake faruwa ne? Dama can yana Drug addict ne? If yes do you think this marriage will be possible? Just follow my ink to know all these answers.*
#A_babban_gida
#diamond_bhatool
[4/13, 10:11 PM] bhatooldiamond: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND*
*WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 4⃣6⃣
﷽
Tun da ya kwanta ba shi ya tashi ba sai around ƙarfe goma na safe. Miƙa yayi tare da yamutsa fuska kafin ya fara buɗe idanuwansa a hankali. Tar idanuwansa suka sauƙa a kan wall clock da ke manne a ɗakin, idanuwansa ya zaro ganin yadda lokaci ya tafi, tunawa da bai yi sallar la'asar bane yasa yayi yunƙurin miƙewa tsaye, cak ya tsayar kamar an sakawa mota birki sakamakon yadda yaji kansa ya masa nauyi , dalilin hakan yasa ya koma tare da lumshe idanuwansa yana mai tariyo abunda ya faru daren jiya, ɗan siririn tsaki yaja tare da ƙara miƙewa, kai tsaye toilet ya nufa ya wanke jikinsa tare da ɗauro alwala.
Yana fitowa yaji ana knocking ƙofa, hakan yasa ya dakatar da shimfiɗa sallayar da zai yi yana ajiyeta kan bed, ƙofar ya nufa ya murɗa handle, ganin Mom yasa ya ɗan saki fuska tare da murmusawa yace "Good Morning Mom"
Cike da nazari take dubansa, fahimtar hakan da yayi yasa ya ƙarasa buɗe ƙofar tare da hugging Mom ɗin by side, sai a lokacin da dawo hayyacinta. Sakinta yayi yana ɓata fuska kamar wani little baby sannan ya fara magana a shagwaɓe "Mom, tunanin me kike."
Murmushi kawai Mom tayi without minding his question tace "Morning Son, na ga alama dai ƙarfi da yaji so kake ka zama yaro, naga kamar alwala kayi, my son ba dai kula da sallar walaha ba."
Jin abunda Mom tace yasa ya ɗan sosa kansa tare da faɗin "Eh ai eh Mom ba walaha zan yi ba, subh ne ban yi ba sheɗan ya hana ni tashi." ya idasa yana mai sosa ƙeyarsa alamun rashin gaskiya.
Ɗan baya kaɗan Mom tayi tana zaro ido waje sai kuma tayi pointing ɗinsa da yatsa, lokaci guda kuma ta haɗe fuska. "Haba son, me kake son zama ne?, anya lafiyarka kuwa?"
Kansa ya sunkuyar ba tare da ya ba ta amsa ba tace "Shiga kayi sallar, in ka fito meet me at the dining." cikin jin kunya Ya Ishaq yace "To Mom" kana ya juya cikin bedroom ɗinsa.
Wata irin ajiyar zuciya ya sauƙe yana jijjiga kansa wondering and asking himself why is he behaving so strange, ganin tsayuwar ba za ta kai shi ba ya sa ya nufi closet nasa, while jallabiya ya sanya kana ya shiga sallah, cikin sujjadarsa yana roƙon yafiyar ubangiji don ya rasa me ke damunsa kwana biyu kenan sallah tana yawan kuɓuce masa ga kuma baƙon yanayin da yake riskar kansa dangane da aurensa da matar da ya fi ƙauna a duniya, zaɓin mafi alkhairi yayi kana ya ɗago, bayan sallamewa ya karanta zikirorin bayan sallah kana ya miƙe don amsa ƙiran Mom zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri.
A dining area ya tarar da ita zaune tana shan kakkauran shayin da ta haɗa, ba tare da ta dubi inda yake ba ta ajiye cup ɗin daidai lokacin da ya isa dining ɗin, ba ta bari sun haɗa ido ba tayi serving ɗinsa kana ta zauna, duk da cewa ba shi da appetite haka yake ta famar turawa coz ba ya son Mom ta fahimci cewa yana cikin damuwa.
Sai da ya gama tukun Mom ta kai kallonta gare shi, ba tare da janye idanuwanta daga kallonsa ba ta ƙira sunansa. "Ishaq" a ɗan rikice ya amsa yana kallon Mom ɗin sai dai kwarjinin da ta masa yasa ya maida kansa ƙasa. "Akwai abunda ke damunka da kake hiding nasa away from us, what's that thing?"
Kasa ba ta amsa yayi hakan yasa ta maimaita tambayar in a serious tune "Me yake damunka kwanan nan?" A rarrabe ya amsa mata da "Ba...bu"
Murumshi irin nasu na manya tayi tace "I don't want to hear this babu anymore, ka ba ni amsa kafin ranka ya ɓaci." Ya buɗe bakinsa kenan zai ba ta amsa yaji maƙoshinsa ya bushe ga wani irin zafi da yake masa, dalilin hakan yasa ya fara tsiyaya ruwa a cup tare da kai wa bakinsa.
Haɗe fuska Mom ta ƙara yi ganin take-taken ya Ishaq, a ɗan zafafe wannan karon ta ƙara tambayarsa "Me yake damunka Ishaq?" Wani irin zafi da yaji a maƙoshinsa ya kere irin wadda yake ji da zarar an masa makamanciyar tambayar nan a baya tuni idanuwansa suka sauya launi zuwa ja jawur. Abun ya matuƙar ɗaurewa Mom kai amma sai ta tsinci kanta da faɗin
"Is ok tunda ba za ka faɗa min ba, in ta yi wari dai za mu ji." tana fadin haka yaji kamar ana saka mass ruwa masu sanyi a maƙoshinsa, tuni wannan zafi da yake ji yayi disappearing. Ajiyar zuciya ya sauƙe har lokacin kuma Mom na lura da ɗan nata. Ci gaba da magana tayi "A sanin da nayi a da game da ɗa na Ishaq, mutum ne mai fara'a da barkwanci ba mutum mai baƙar zuciya ba, ɗa na Ishaq mutum ne mai kula da ibadarsa ba mutum mai sake da addini ba, Ishaq! Ka ji tsoron Allah ka dawo kan hanya ko da kuwa ba za sanar da ni abunda ke damunka ba. Sannan ka sani, kowanne ƙunci yana tare da sauƙi, maganin ƙunci shine ka koma ga mahaliccinka ba wai ka saki hanya ba, sallar nan da ka koyi wasa da ita ka manta tana hana alfahasha? Ishaq ka ji tsoron Allah ka gyara, duk da ka ƙi sanar da ni damuwarka ba zan daina yi maka addu'ar sauƙi daga wurin ubangiji ba." sosai maganganun Mom suka sanyayawa Ya Ishaq jiki har yana jin bai kyauta mata ba, amma yaya zai yi? Yanayin da yake riskar kansa idan yaso hakan ya tuna hakan yasa ya jijjiga kansa. Gaskiya he can't endure the pain...daga haka ya furta "I'm sorry Mom" can ƙasan maƙoshi. "Won't repeat it again, i promise." ganin Mom ta ƙi faɗin komai yasa ya kama kunnuwansa cikin raunin murya yace "Da gaske Mom, ba zan ƙara ba kinji."
Hararar wasa ta cilla masa tare da faɗin "Is ok, Allah ya ƙara shirya ka Son."
"Amin My beloved Mom, i'm so much proud of you, ina ƙara godewa Allah da ya azurta ni da mahaifiya ta ƙwarai ba tare da na biya shi ko asi ba, Allah ya ƙara miki lafiya da Imani My Sweetheart."
Murmushi kwance a fuskarta ta amsa da "Amin Yaron kirki...Now ina muka kwana ne? Ko dan ma, yanzu ka jira mun yi waya da Salaha tana kan hanya. Ka ƙara duba lefen gobe juma'a za mu kai, in kuma da abunda za a sauya ka ga sai mu sauya kafin nan."
Fara'ar da ke kan fuskar Ya Ishaq tuni ta ɗauke kamar walƙiya, duk abunda ke faruwa kuma Mom na lura da hakan amma ta waske tana faɗin. "Wa ya ga su Son Ango? Can't imagine how happily he'll be." shiru yayi bai ce uffan ba kuma yanayin fuskar kan iya bayyanawa mai kallonsa halin da yake ciki musamman yadda yayi kici-kicin da ransa.
"You can go, in ta zo i'll let you know." bai ce komai ba ya wuce tare da barin Mom tana gyaɗa kanta tare da faɗin "Allah yasa dai lafiya, i have to find out coz na fahimci cewa something fishy is happening, daga haka itama ta miƙe zuwa bedroom ɗinta.
Lokacin da Mommy Salaha ta zo Mom da kanta ta ƙira Ya Ishaq, ba don yana so ba sai famar harhaɗa fuska yake haka ya fito Momny Salaha na zolayarsa ango ango amma ko uffan bai ce ba sai ma kau da kansa gefe da yayi. A haka dai aka buɗe komai shi dai hankalinsa ma ba kan lefen yake ba ya tafi can wani wuri. Muryar Mommy Salaha da yaji yasa ya dawo duniyarmu.
"Me za a sauya Ishaq, me da meye ba su yi ba?"
Yana ƙiƙƙifta ido tare da sosa ƙeya yace "Komai ya yi, a bar shi haka." without minding on kakkaucewar da yake ba suka fara mayar da komai muhallinsa shi kuma ya koma bedroom nasa.
Nan Mom ke ba wa Mommy Salaha labarin sudden change na Ya Ishaq ta kuma roƙi alfarmar in sun kai lefen ta san yadda tayi ta samu damar keɓewa da Zahrah ta tambaye ta ko akwai matsala. Daga nan suka koma hirarsu ta duniya har dangin Mom da Dad suka fara zuwa musamman waɗanda ke ganin lokacin cin banza ya zo tuni suka taro zuwa gidan.
Ɓangaren Yaya Ishaq tun da ya koma bedroom ɗinsa yaji kansa na wani irin juyawa, kai tsaye kan makeken bed ɗinsa ya kwanta yana jujjuyawa, ringing ɗin da ya jiyo na wayarsa yasa ya saki tsaki ya san ba zai wuce wannan jarababbiyar bace amma wani sashe na zuciyarsa ya ba shi shawara da "Pick it, it's not gonna be easy...just let her know the truth" Da haka ya janyo wayar yana mai kara ta a kunnensa. Da niyyar masifa ya ɗaga tunda ko sunan mai ƙiran bai duba ba ya ɗaga ƙiran. Muryar da yaji yasa ya sauƙe ajiyar zuciya. Tsawon wani lokaci tukun mai ƙiran ya ba shi damar magana hakan yasa yace "Ok, ok send me your location." ba wani jima ba ya ajiye wayar tare da miƙewa. Toilet ya shiga ya tsalo wanka ya shirya cikin wata black dakakkiyar shadda wacce ta haska shi, bai ɗau lokaci yana shirin ba ya sanya hula da takalminsa baƙaƙe kana ya feshe jikinsa da turare nan da nan ya fito a matsayin sa na ango. Ta ƙofar baya ya fita coz ba ya so Mom ta san da ficewarsa, gabaɗaya ma ba ya son wannan zancen ango ango ɗin da Mommy Salaha ke yi.
Kai tsaye motarsa ya shiga ya ja ta da gudu tare da ficewa daga gidan ya harba kan titi. Cike da mamaki yake kallon location ɗin, "anya kuwa daidai ne?" Ya tambayi kansa, ƙara dubawa yayi a karo na biyu ganin dai nan ɗin ne yasa ya dasawa zuciyarsa shakku kan wannan babe ɗin da yake jin kwanciyar hankali da zarar ya ji sautin muryarta. A iya saninsa dai ba Zahrah bace, yarinyar da ya mutu a son ta a da wacce a halin yanzu ba ya jin akwai halittar da bai jin nutsuwa a tare da ita kamar ita. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana lumshe idanunsa.
Numbernta da babu suna jiki ya duba tare da danna mata ƙira, bugu ɗaya ta ɗaga.
"Hello my own, na ji bugun zuciyata ya sauya, hakan na tabbatar min da kusanci na da kai."
Murmushi ya saki har jerarrun haƙwarensa na bayyana, lokaci guda ya tsinci kansa da faɗin "Ki hanzarta ki fito please, ina so ya zama kusanci na da ke babu shamaki don samun nutsuwar zuciyata." murmushi ta saki tare da ending call ɗin.
*ba zan gaji da farantawa fans ɗina ba duk da ba sa nuna soyayyarsu gare ni, amma al'amarin da abun dubawa, don Allah fans ku soni ko da rabin yadda nake son ku ne, ku faranta min ta hanyar reacting*
*Comment, share and react fisabilillah.*
[4/14, 8:04 PM] bhatooldiamond: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND*
*WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 4⃣7⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
Ya tsorata da al'amarin wannan baiwar Allah da ke bibiyar rayuwarsa musamman da bai ga ta ina ta fito ba sai dai jin muryarta kusa da shi da yayi. Ɓoye tsoron da yaji yayi saboda yadda kusancinsa da ita ke haifar masa da wata matsananciyar kwanciyar hankali fiye da yadda muryarta ke haifar masa cikin waya, ji yake a halin yanzu babu wata halittar ubangiji da ke jin daɗi kamar yadda yake ji. Duk iya ƙoƙarin Ya Ishaq na ganin ya nazarci fuskar abun ya farskara don yadda idanunta ke ƙara kaifi gare shi ga kuma wani irin kwarjini da take masa. Ya share awannin da ba zai iya faɗi ba kafin ya juya zai tafi, babu yadda ya iya haka ya koma duk da tsoro da fargaban da ke ƙara matsowa gareshi bayan kowacce tazara da zai ƙara daga gare ta.
*ZAHRAH'S POV*
Zaune suke gabaɗayansu a ɗakinsu sai surutu suke, sallamar Baby Ayman ne ta katsar da su, kai tsaye wurin Zahrah ya nufa wacce ta buɗe masa hannayenta.
"Kyakkyawana me ka kawo min ne?"
Cikin muryarsa mai daɗin sauraro yace "Aunty Jahla wai Ya Auwab yace ki zo parlourn iya jilanki." fuska ɗauke da mamaki tace "Ya Auwab kuma?" kansa ya gyaɗa alamar eh.
Haɓarsa ta ɗago ta yadda idanuwansa suka sauƙa cikin nata.
"My Baby ba Aunty Rumaysa yace maka ba?"
Kansa ya jijjiga yana faɗin "A'a Aunty Jahla yace kuma ya ce ki yi cauli."
Kai Zahrah ta ɗaga tana kai dubanta ga Rumaysa sannan ta ɗage mata gira "Madam, ina jin Babe ɗinki na kusa yana jiranki parlour." ta idasa tana sauƙe Baby Ayman ta nufi toilet.
Rumaysa da aka yi komai gabanta dialling numbern Ya Auwab tayi, luckily ta ga ya katse ƙiran sai kuma ga nasa, after gaisuwar da suka yi ta jefa masa tambayar "Waye kake nema ne soulmate?"
"Zahrah, ki ce tayi sauri please, ina da abubuwan yi."
"Ok" ta ba shi amsa tare da datse kiran wanda yayi daidai da fitowar Zahrah daga toilet tana goge fuskarta da wani farin hand towel. Kallonta Rumaysa tayi tace "Zahrah it's you Ya Auwab yake nema, ya ce ki yi sauri please." yadda tayi sounding serious yasa Zahrah saka hijab tare da ficewa zuciyarta na bugawa da rashin sanin me yasa Ya Auwab ke nemanta.
A parlourn kuwa tarar da shi yana zaune, gaida shi tayi bayan ya amsa yace "Kinga ina sauri ne, just want to ask you."
"Ok Yaya, Allah yasa na sani."
Wayarsa ya miƙo mata yana faɗin "Kin san wannan?"
Idonta ta tsura kan kyakkyawar fuskarshi cikin shigar bakar shadda fuskarsa ɗauke da murmushi. Gabanta ne ya faɗi ganin Ya Ishaq, hakan yasa ta lula izuwa duniyar tunani. Gyaran murya Yaya Auwab Yayi wadda yasa Zahrah ɗan zabura kaɗan "Kin yi shiru, ko ba ki san shi ba."
Cikin rawar murya tace " Eh na san shi, Yaya Ishaq ne, mijin da zan aura."
Ba tare da ya ƙara faɗin uffan ba ya miƙe fuskarsa ɗaure ya raɓa Zahrah ya wuce, hakan da yayi ya jefa zuciyarta ga ruɗani da kuma fargaba, da ƙyar ta iya jan ƙafarta ta kai ta ɗakinsu. Ko bayan maghrib sai da Zahrah ta ƙara ƙiran Ya Isaq amma still bai yi picking ba, hakan bai sa ta gaji ba ta tura mishi saƙo duk da cewa baya tura mata amsa ko da ya gani, sai ta yi niyyar share shi kuma sai ta tuna may be ko aiki ya masa yawa ne ko ta bata masa rai, in tayi tunani kuma ba ta tuna ko abu ɗaya da tayi da zai bata ransa, a yau ta fara jin shakku kan alaƙarta da shi, why the sudden change, 2weeks to biki ango sai ya watsar da amarya? Me hakan yake nufi?.
Ta ɗau aniyar daga yau itama ba za ta ƙara nemansa ba ko da kuwa a yanayin nan za a ɗaura musu aure, she's tired of suffering from his pain saboda haka ta tura mishi last message ta kashe wayarta tare da cilla ta ƙasan wardrobe nata.
*WASHEGARI*
Tun da safe ake ta hidimar snacks da kuma abincin da za a sauƙi bakin da za su kawo lefen Zahrah.