Showing 108001 words to 111000 words out of 157517 words
furta komai bakinsa kuma sai rawa yake alamun yana son yin magana ne, ganin yanayin da Alhaji Baba ya shiga yasa su Daddy nufarsa suna rirriƙe shi tare da zaunar da shi don kuwa ba iya Alhaji ne cikin ruɗu ba, dukkansu sun shiga yanayin da ba zai misaltu ba. Kawu dai ɗan kallo ya zama haka Dad ma, duk da cewa ba su san fuskar ba amma jini hausawa suka ce ba wasa ba ne, tsananin kamar da mutumin yake yi yasa suka ɗarsawa zuciyarsu kaɗan daga labarin har ta yardar musu cewa shima jinin wannan ahalin ne.
Sai da ya gama goge fuskarsa da kuma hannunsa tukun ya maida handkerchief ɗin zuwa aljihunsa. Ba tare da wani tunani ba ya nufi Alhaji Baba da ke zaune yana karkarwa tare da rungume shi yana sakin wata irin nauyayyar ajiyar zuciya, sai a wannan lokaci Alhaji Baba ya iya furta "Sa..dau...dau...kiiiii" a rarrabe tare da jan ki ɗin ƙarshen sunan sai kuma ya fashe da kuka.
Bai yi yunƙurin amsawa ba bare kuma ya furta wata kalma sai dai shima zuwa yanzu zuciyarsa ta karaya har sai da ƙwalla ta fito daga ƙwayar idanunsa, a wannan yanayin da ya shiga idan yayi ƙoƙarin furta wani abu shima zai iya kukan hakan yasa ya fara shafa bayan Alhaji Baba da har wannan lokaci suke rungume da juna an kasa samun cikin su wanda zai fara sakin wani.
Tsawon wasu daƙiƙu masu tsayi kukan dattijon ya lufa, hakan yasa ya janye jikinsa daga na baƙon yana jan hanci. Sumar tsaye da su Alhaji Babba suka yi sai a lokacin suka farfaɗo tare da dawowa hankukansu duk da cewa har yanzu zukatansu da kuma ƙwaƙwalensu ba su gama gaskata musu abunda idanunsu suka gani ba, gani suke tamkar mafarki suke. Manyan baƙin da suke cikin masallaci suma sun farga da abunda ke faruwa, kowa kuma ya ƙi ya tafi don yana so ya ba wa idanunsa rabonsu su kalla.
"Ka yi magana Sadauki, say something, ka ce wani abun don Allah, ka faɗa mana cewa kai ne Sadaukin Abatcha...."
Alhaji Baba bai kai ga rufe bakinsa ba yaji muryarsa tana faɗin
"Ƙwarai kuwa, I'm Sadauki, your beloved grandson, nine gabanka ba wani ba, akwai abubuwa da yawa da nake son faɗi, amma kafin nan auren Zahrah da ba a ɗaura ba nake so a ɗaura da ni."
Murmusawa Alhaji Baba yayi tare da goge fuskarsa da tafukan hannunsa sannan ya kalli ƙibla yayi sujjada, kamar wasu jeloli suma su Daddy suka yi duk da cewa har yanzu tunaninsu mafarki suke.
"Alhamdulillah! Na san cewa Allah ba zai bari mu kunyata ba, Alhaji Haladu, ina mai ba ka haƙuri tare da sanar da kai cewa, ɗaurin aure da Shureim ba zai yiwu ba saboda ga Ɗan'uwan yarinyar ya buƙaci a ɗaura da shi, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi garesu baki ɗaya."
"Amin Ya Rabbi, babu komai ai." Dad ya faɗa a sanyaye yana mai baƙin cikin abunda Ishaq ya aikata musu.
Ba a ɓata lokaci ba aka ɗaura aure da Ya Sadauki wanda har yanzu iyayensa maza ba su amince da cewa shine a gabansu ba. Ana gama ɗaura aure kuma aka wuce wurin reception banda ya Sadauki da Alhaji Baba yasa Appa ya wuce da shi zuwa guest house ɗinsa ya kimtsa, sannan su je su yo siyayyar kayan sakawa bayan Ya Sadaukin ya sanar da Alhaji cewa ba shi da wasu kaya a tare da shi banda na jikinsa.
*THE BRIDES*
Tunda aka sanar da su cewa aure ya ɗauru suka fashe da kuka kamar an aiko da saƙon mutuwa. Sosai suka ba wa Aunty Na'ima, Aunty Madina da kuma Aunty Salma dariya, musamman yadda suka haƙiƙance kamar ba su ke ɗaukin auren ba uwa uba kuma yanayin da aka fitar da Zahrah yasa hankulansu mummunan tashi.
Aunty Salma da ke aikin rarrashi tun shigowarsu Aunty Madina ta kalla tace "ke ma kika biye su, ba su bane suke ɗaukin auren? Rabu da su."
Sautin kukansu suka ƙara jin batun Aunty Madina, hatta Nasreen da ba ta cikin amaren kuka take, damuwarta ɗaya, they'll all leave her alone. Ficewa Aunty Madina da Aunty Salma suka yi, dama kaya suka zo ɗaukarwa Zahrah.
Baba Dumba ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Ayyiriri yiriri ayyiriri amare ku kuka ce, kuka ce, ku kuka ce kuna so, da ba ku ce, ba kuce, da ba ku ce kuna so ba da ba a ba, ba a ba da ba a baku su ba, ayyiriyiriyiriyiri." cak ta tsaya da guɗar da take tana binsu da kallo musamman yadda suka dare baki suna kuka, dariya ta kece da ita tana faɗin
"E lallai, ka ji min yaran zamani, ina ce dai ku kuka ce kuna so?"
Dakatar da kukan suka yi suna cillawa Baba Dumba harara.
"To ina ruwan ki da mu?" Nainarh ta faɗa
"Eh lallai Nainai (kamar yadda take ƙiranta da shi), dole ki harare ni ai, ƴan banzan yara kawai, ku mana shiru a nan, in kuma ba kwa so na ƙira kakanku nace mazajen su aiko muku takaddar saki, shikenan ai."
"Ke tsohuwar nan wallahi...hmm"
"Ƙarasa mana Zakiya'u."
"Ita wannan sai ta ɓata sunan kowa ne?" Zahrah ta tambayi Nainarh. A take Baba Dumba mai abun ban mamaki tace "Kun ci uwaku, nace kun ci uwaku" ta faɗa tana jefa musu daƙuwa "Yo an sa muku sunayen aljanu ai dole mutum ya kasa faɗi."
"Mu dai to ki tafi cikin ƙawayenki su Hajja tsofi, kin wani shigo cikinmu kin zauna." Nainarh ta faɗa tana tura baki gaba.
Daƙuwa da aiko mata tare da cewa "ungo nan, dan uwaki ba zan tafi ba, a nan cikinku zan zauna kuma ni zan kai ku ɗakunan ku, washegari in je gashi."
Tsit kake ji babu wanda ya ƙara magana jin Baba Dumba na shirin musu tijara, jin sun yi shiru yasa ta ja ƙafarta ta fice sai mita take.
Tana fita Aunty Na'ima tace "Wannan tsohuwa ba dai iya magana ba kam? Ga shi ta dakatar da kukan cikin mintuna kaɗan, kai Allah mata albarka."
Ke kam Aunty Na'ima ai an daina kunyarki, wayoyinsu suka ɗauko tare da kunnawa, kamar haɗin baki kowacce mijinta ya turo mata da heartfelt congratulation message, stating deeply how happiest they are today banda Zahrah da ke can kwance gadon asibiti ba ta san wainar da ake toyawa ba.
*React and Share*
Diamond💎Bhatool🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣2⃣
﷽
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*
*ZAHRAH*
Da ƙyar likitoci suka iya ceto rayuwar Zahrah daga mummunan haɗarin da ta shiga, saboda haka ba su ba wa kowa damar ganinta ba sai kayanta da Nurse Ramlat ta amsa ta shiga da su ciki. Bayan likitocin sun fito Aunty Madina da Aunty Salma suka tare su da faɗin
"Dr. Eh Dr. Ya jikinta? Hope ba wata matsala, Dr..."
Hannu ya ɗaga tare da faɗin "Follow me to my office." ba musu suka bi bayan Dr ɗin har zuwa office ɗinsa, bayan sun zauna Dr. Ya sauƙe numfashi ya fara magana.
"Ku ne relatives ɗin Patient ɗin can Zahrah who? Ehm Zahrah Abdulkarim?"
A tare suka ce "Eh mu ne Dr."
"To" sai kuma ya sauƙe numfashi. "Meye alaƙarku da ita?"
Aunty Madina ce ta ba shi amsa a wannan lokacin da faɗin "Ni cousin sister ɗinta ce, wannan kuma in-law ɗinmu ce."
"Is ok, amma garin yaya kuka bari yarinya ƙarama ta shiga irin wannan halin? Kun kuwa san illar da hakan zai haifar da ba don kun kawo ta da gaggawa ba?"
Diri diri suka yi tunda duk cikinsu babu wanda ya san silar faruwar hakan.
Nan likita ya nuna musu illar hakan tare da sanar da su condition ɗin da take ciki, sosai hankalinsu ya tashi, fahimtar hakan yasa likitan kwantar musu da hankali har ya sanar da su cewa zuwa gobe za a iya discharging ɗinta.
*At the estate*
Can estate babu wanda ya san da faruwar wannan al'amari saboda gargaɗin da Aunty Madina tayi na cewa kada su sanar da manyan gidan, a ci gaba da hidima su za su kula da ita. Hajjaty ce ta shigo cikin ɗakin don shaida musu cewa Alhaji Baba yana buƙatar ganinsu a parlournsa. Ita kanta ba ta san wani al'amari ya faru ba bare ta san cewa ba da Ya Ishaq aka ɗaurawa Zahrah aure ba saboda babu wanda ya samu lokacin sanar da ita cikinsu. Lura da babu Zahrah yasa tace
"Ku samu ku zo mana, su Jiddah duka suna can, ina Zahrah ne?"
Kallon kallo suka fara aikawa juna, da ƙyar Nasreen ta ƙarasa kusa da Hajjatyn tace "Hajjaty..." nan ta labarta mata abunda ya faru da Zahrah, a matuƙar ruɗe tace "Shine ba za ku faɗa ba kuma?"
"A'a Hajjay su Aunty Madina na tare da ita, sun ce kada a faɗa muku ne kada hankalinku ya tashi."
Ɗan nazari tayi na wani lokaci kana tace "Ku ɗin ku taho." nan suka wuce zuwa parlourn Alhaji tare da zubewa ƙasa suna sunkuyar da kai.
Nasiha sosai aka musu ba tare da fahimtar cewa one of them is missing ba, haka suka koma suna ta famar share ƙwalla.
Sai da suka fice tukun Hajjaty ta sanar da su batun Zahrah, ba kaɗan ba su ma hankalinsu ya tashi tunawa da suka yi da al'amarin da ya faru a masallaci. Allah sarki poor girl.
Misalin ƙarfe huɗu daidai Alhaji Baba yasa aka shirya amaren don wucewa da su gidajensu da ke cikin estate ɗin. Su kansu ba su yarda da hakan ba har sai da suka ga haiƙan ficewa da su za a yi, nan fa suka ce kuka assalamu alaikum. Cikin alkyabba aka fito da su zuwa parlourn Hajjaty. Nan ma dai nasiha iyaye matan suka musu, nan aka fice da amaren zuwa gidajensu. Sai bayan an fice da su iyayen suka lura babu Zahrah, ko da suka tambaya Hajjaty ce musu tayi ai tana can wurin Alhaji ita ɗin. Nan aka kawar da zancen.
*YA ISHAQ*
Tun lokacin da Dad ya sake shi ya fice a masallacin tare da jan motarsa kai tsaye sai gida. Bayan mai gadi ya buɗe masa ya shiga yayi packing. Kamar dai basu san me ya faru ba, don ga alama, gidan cike yake da ƴan'uwa da abokan arziƙi sai kai da komawa suke yi. Kasancewar ba ya cikin hayyacinsa ga wani irin ciwo da kansa ke masa yasa bai duba dandazon matan da ke kai kawo ba ya kutsa kansu cikinsu. Waɗanda suka sanshi dai abun ya ɗaure kansu amma sai suka yi shiru, waɗanda basu sanshi ba sai Allah wadai da jahilcin wasu mazan suke kan don me zai shigo cikinsu babu excuse.
Haka ta kasance har zai bi ta main parlour ya fasa ya bi da ƙofar baya ta bedroom ɗinsa, da kyar ya iya shiga saboda yadda kansa ke tsanin ciwo ga kuma wani juyawa da yake kamar an ɗaura shi kam fanka mai gudu. Yana idasa shigewa kuma ya faɗi kwance ƙasan carpet.
*An hour later*
Awa guda da shigowarsa Dad ya dawo gidan ransa ɓace. Mamaki kowa yake ganin uban ango shi kaɗai kuma a wannan lokacin da ya kamata ace yana part ɗinsa yana karɓan baƙi masu taya shi murna. Ƙanwar Mom Dad ya sanarwa ta yi masa magana da Mom ɗin daga haka ya juya zuwa part ɗinsa..
Bayan ta sanar da Mom ba ta tsaya wani jira ba ta nufi wurin mai Gidan nata cike da tunani da mamakin me yake a gida a wannan lokaci da take tsaka da hidimar biki. Taba shiga ta tarar da Daddy tsaye gaban Bed ya juya baya, tun daga wannan yanayi da ta ganshi ta fahimci cewa ba lafiya. Cikin sassanyar muryarta tace "Zaujiy?" Bai amsa Mata ba sai dai kuma ya juyo yana dubanta. Ƙirjinta ta dafe da hannunta ɗaya ganin yadda idanunsa suka sauya zuwa launin ja ga kuma tsantsar masifa da take gani a cikin idanun nasa.
A hankali ta matsa kusa da shi tana riƙe hannunsa, jiki a sanyaye tace
"Dad Ishaq..." bai bari ta ida faɗin abun da take da niyyar faɗi ba ya ɗaga ɗayan hannunsa yana dakatar da ita
"Stop calling me his Dad...ni ba mahaifinsa bane."
Sakaka Mom tayi tana kallon Dad, anya kuwa lafiyarsa? Ta tambayi kanta.
Fahimtar a cikin fushi yake yasa ta ja hannunsa ba musu kuma ya bita, zaunar da shi kan bed tayi tare da nufar fridge ɗin da ke ɗakin ta ɗauko favourite drink ɗinsa _Fearless_ sannan ta buɗe tare da miƙa masa. Babu musu Dad ya amsa ya kafa kai, ba shi ya aje ba sai da ya kwankwaɗe tas sannan ya saki goran ƙasa.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da nunawa Mom gefensa, babu musu kuma ta zauna. Kamar ba yanzu ya gama shan abu mai sanyi ba amma maƙoshinsa wani irin raɗaɗi yake kamar zai tsage saboda ɓacin rai, gauron numfashi Dad ya sauƙe tukun yace.
"Ina yaronki?"
"Zaujiy yarona kuma?" mom ta tambaya a ɗan rikice
Cikin ƙunar rai Dad yace "Eh shi dai! Ko sunansa ba na da buƙatar faɗi, amma saƙona ki tabbatar kin isar masa shi, Babu ni babu shi, na riga na cire cewa na haifi wani ɗa mai kama da shi..."
"Ban gane ba Zaujiy, ka sa ni cikin duhu, don Allah me yake faruwa."
Nan Dad ya sanar da ita komai da ya faru a wurin ɗaurin auren da kuma ɗaura auren da aka yi da wani ba ɗanta ba."
Idanuwanta waje sakamakon fargaba da tsoron da suka dira a ranta, ta ma rasa me za ta ce saboda gaba ɗaya kalaman da ke bakinta kafewa suka yi.
"Kin ji abinda ɗanki ya yi? Shin ya cancanta na ci gaba da bearing sunan mahaifi gare shi? Bai saurare ni ba, ya zubar min da mutuncina idon duniya, a lokacin da na nuna na isa da shi ya nuna Ni ba kowa bane gare shi, ga shi wautarsa ta kai shi ga rasa mace nagartacciya. Shikenan!"
Dafa kafaɗarsa Mom tayi tare da shafa bayansa, cikin sigar rarrashi ta fara furta sanyayan kalamanta amma sam Dad ba ya jin zai iya jurar abunda ɗan nasa ya aikata masa. Ganin hakan yasa Mom faɗin "Aba Ishaq, ba na jin cewa ɗanmu yana lafiya tunda naji hukuncin da ya yanke, ba zan goyi bayansa ba, amma tabbas Akwai wani ɓoyayyen al'amari Dangane da hakan, ka tuna yadda yaronmu ya mutu akan son yarinyar, ka tuna har zuciyarsa sai da ta shiga haɗari sanadiyyar soyayyarta, kana tunanin abu ne mai sauƙi a ce ya rabu da ita haka kawai ba."
"Kema bayansa kike goyo ko?" Dad ya tambaya a ƙufule.
Cikin sanyin murya Mom tace "A'a Aba Ishaq, ina dai faɗa maka abunda yake faruwa ne, na san Zahrah, yarinyar kirki ce wanda babu shakka ba wai wani ɓoyayyen abu game da ita ne yasa shi fasa aurenta ba, sai dai..."
"Sai dai me? Kina kare shi ne still ko?"
"A'a Aba Ishaq, a cikin makonni biyu ga lokacin bikin, ina lura da yaronmu, Aba Ishaq kada ka yanke hukunci cikin fushi, mu fara tarar al'amarin yaronmu mu san dalilin faruwar haka. Ina maka rantsuwa da Sarkin da ke bisa numfashi, wallahi akwai wasu strange abubuwa tattare da Ishaq, kuma haƙƙinmu ne nema masa lafiya kafin mu yanke hukunci." Jikin Dad sanyi yayi da maganganun Mom, hakan yasa ya ba ta umarnin nemo Ishaq ɗin tunda ya ga motarsa a packing lot.
Ba musu ta fito daga part ɗin Dad don yin abunda zai fisshe ta yayin da ta baro Dad cikin fargaba da tsananin tsoron abunda zai faru ɗin lokaci guda kuma jikinsa yayi sanyi.
*ZAHRAH'S POV*
A hankali ta fara buɗe Brow eyes ɗinta yayin da take bin kowanne lungu da saƙo na ɗakin da kallo lokaci guda kuma tana son tunano abunda ya faru da ita. Wasu zafafan hawaye ne suka fara rige-rigen sauƙa daga idanunta tun lokacin da ƙwaƙwalwarta ta fara tunano abu na ƙarshe da ta yi. A hankali ta fara shafa gadon ba tare da ta kai dubanta ga inda take shafawar ba.
Buɗe ƙofar room ɗin da Dr. Yayi yasa ta mayar da kallonta gare shi. Cikin shaƙaƙƙiyar muryarta ta furta "Where is my phone? I can't hold it anymore, Sai na sanar da Alhaji Baba..."
"Sorry Zahrah, kina asibiti ne, you're in danger, please ki kwantar da hankalinki, everything will be normal ok?"
Dr. Ɗin ta faɗa tana riƙe hannun Zahrah tare da ɗage mata gira alamar tambayar ko ta fahimta. Kai kawai Zahrah ta gyaɗa daga nan Dr. Ta fita waje, nan ta sanar da Aunty Madina da Aunty Salmah cewa Zahrahn ta tashi, har karo suke ci da juna saboda su samu kallon Zahrahn.
Bayan sun shiga sosai suka nuna mata kulawa, Aunty Salmah ta taimaka mata tayi wanka, Aunty Madina ta shigo da kayayyakin abincin da Nasreen ta koma ta taho da shi, a tare da Nasreen ɗin suka shigo, sai da suka tabbatar ta ci tukun su ma suka samu damar taɓawa ba su tare da sun kawo mata batun kwanciyar Tata ba, hakan kuma umarnin Hajjaty ne bayan Nasreen ta sanar da su komai...
Hirar da suke jefawa yasa Zahrah ɗan sakin jiki. Bayan su Aunty Madina sun yi waya da su Hajjaty, ba su jima ba sai ga mutanen gida tuta tuta suna zuwa duba jikinta hakan ne yasa ta so manta cewa tana da wata damuwa a duniyar ta.
Bayan Dr ta dawo ta ƙara yin wasu gwaje-gwaje, ganin komai ya koma kusan daidai yasa ta rubuta musu sallama, a daren kuma dukkansu suka ɗunguma zuwa estate ɗin. Hajjaty kafewa tayi kan lallai abar ɗiyarta ta kwana tare da ita. Bayan an watse ya rage iya Mamah da Hajjaty, Aunty Madina da Aunty Salmah, Hajiya Babba sai Mommah a parlourn Hajjatyn. A lokacin ne kuma Hajjaty ke tambayar Zahrah me ta sa a ranta haka damuwa ke shirin illata ta?
Hawaye na tsiyaya a idanunta ta buɗe baki ta fara magana "Hajjaty dama..." Kasa furta