Showing 156001 words to 157517 words out of 157517 words

Chapter 53 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5164

ci sunan Hajjaty, suna kiranta da Imaan, sai kuma ɗiyar Nasreen Mai sunan Zahrah ce, da kuma Zahrahn suke kiranta.

*Bayan wani lokaci*

Ammie ita kaɗai ke rayuwa a prison ɗin, ɗakinta ma ita ɗaya ce saboda ƙurajenta masu zubar da ruwa mai jahilin ɗoyi, daga ƙarshe itama daina cin abinci tayi, yunwa da tayi yunwa ta kashe ta, haka dai mutuwar wulaƙanci dukkansu suka yi.

Allah ya kyauta yasa mu fi ƙarfun zukatan mu.

*THREE YEARS AFTER*

Zahrah ce da Yaya sadauki suke sauƙowa daga matakalar jirgi yayinda wata charming little girl ke biye da su, sai da suka sauƙo na lura da cewa Angel ce ta girma. Cikin shigar su irin ta alfarma da ke bayyana zallar cigaban da suka samu na eayuwa tare da sauye-sauye a tattare da su, sun sauya sun ƙara kyau abunsu kamar ka ɗauke.

Yaya Khalil ne ya fara hango su, da sauri ya ɗago hannunsa yana faɗin "Hey man!" Yaya sadauki ne ya juya, gani amininsa yasa ya saki hannun Zahrah yayi hugging ɗinsa yana faɗin "Buddy..." Cak ya dakata da magana ganin Nainarh da ke riƙe da hannun Baby Zuhrah wacce ba ta fi tsarar Angel a tsaye ba. Naonarh ce ta gaida shi tana murmushi shima ya amsa fuskarsa sake yana riƙo hannun Zuhrah wacce ke kallonsa kamar ta ga sabuwar halitta. Murmusawa yayi yana ɗan jan kuncinta yace "Baby ba ki iya gaisuwa ba?"
Bakinta yarinyar ta tura tace "Good morning" amsawa yayi yana faɗin "Morning...kin girma abunki sai school ko?" Magananniyar yarinyar ta amsa tana faɗin "Ai an caka Ni Uncle, kai ɗin waye?"
Kuncinta yana yana faɗin "I'm your uncle, kin fiye surutu, just like your parents"
Da sauri yarinyar tace "Daddy, Mommy wai kune magana?" Dariya dukkansu suka yi.

Karasowar Angel da Umminta yasa Nainarh tahowa da gudu kamar za ta faɗi tayi hugging Zahrah yayinda dukkansu suke cikin farin ciki kowa na expressing how much he missed his half. Ganin suna bata time yasa yaya Sadauki faɗin "Oh ya, let's go!" Da haka suka wuce, ita dai Angel shiru ko uffan ba ta ce ba har suka isa.
Kafin ka ce me kowa ya ji labarin dawowar su. Sosai aka cika su da kayan abinci yayinda Zahrah da Yaya Sadauki suka mance da kowa suka fara cin abincinsu sai zuba soyayya suke Hajjaty da bakinta ba ya shiru sai mita take.
Zahrah da ba ta ga Mamah ba tace "Hajjaty jan ga Mamah ba"
"Kaji yar bantan uba, zama za ta yi tana jiranki ai ke kina ɗakin mijinki"
"Kai hajjaty, tambaya fa kawai nayi."
"To, Tafiyarku da sati biyu aka ɗaura mata sure da Alhaji Bashar, ɗan ƙawatace tun ta yarinta kuma ba ku ga yadda yake kula da ita ba, kin san shi bai taɓa haihuwa ba kuma matarsa Allah ya mata rasuwa..." Katseta Yaya Sadauki yayi yana faɗin "is ok Hajjaty, daga tambaya ɗaya kin ba da amsar da ta kai cikin randa"
"Ungo nan!" "Dan gidanku ba dai tambar tayi ba shine a ka shiga zancen mu no da jikata?"

Shigowar Alhaji Baba yasa aka mayar da akalar hirar zuwa gaida shi, nan aka fara hirar yaushe gamo, shekara uku cur da tafiyarsu sai dai a waya, amma alhamdulillah tunda Yaya Sadauki ya gama course ɗin da yaje yi ɗin.
Angel wacce ke maƙale jikin Abie ɗinta ta ki zama bare ta ci abincin. Alhaji Baba ne ya hango ta yace "Wannan ce mai sunan mai rasuwar?" "Eh Alhaji itace, ka ganta nan tunda suka shigo ta ƙi barin jikin uban ta bi ta name masa kamar cingan." Lokaci guda Angel ta saki dariya tace "Cingan, Abie wai cingan?"
Kai ya gyaɗa mata yace "Rabu da Hajjaty, ba ta iya faɗa ba" nan hajjaty ta fara faɗa wai yarinyar ta yi baƙin rai irin na ubanta.
Ba su suka wuce part ɗinsu ba sai yamma, washe gari kuma suka nufi gidan Mamah, a hanyarsu suka haɗu da wata mai Bara gurguwa kan kekenta sai kuma wata tsohuwa itama kan keken, kamar ta sansu haka Zahrah taji, tsayar da drivern da ke jansu tayi da suka iso wurin matan. A hankali ta sauƙa, shima Yaya Sadauki ya fito riƙe da hannun angel.

Babu shakka, Bibalon Aunty Amarya ce, cike da maɗaukakin mamaki tace "Bibalo?" Gurguwar tace "Hajiya, har kin ji sunana bakin Inna?"
"Ba ki gane Ni ba Bibalo, Zahrah ce, Zahrah dai ta wajen Baba idrisu" ido waje Aunty amarya da kunya ta lulluɓeta ta kalli zahrah sannan ta sauƙe kai, "Zahrah ki yi haƙuri, ina mamanki, wallahi sharrin shaiɗan yasa na mata kurciya ta ɓata, Allah ga shi haƙƙin ku na bibiyar mu, Allah yasa dai ba ta mutu ba, zahrah ki yi haƙuri "
Haka suka haɗa baki sai haƙuri suke ba wa Zahrah
Murmusawa tayi ganin yadda Allah ya mayar da su Aunty Amarya lokaci guda, tsayuwar ta ta gyara tace "Babu komai, mun yafe muku, wannan mijina ne, wannan kuma ɗiyata ce, mun haɗu da dangin Mamah, sannan mamah ta dawo har ta auri wani hamshaƙin mai kuɗi, kwanaki Kawu ya zo, shima gidansa yanzu a nan yake, kamar ku shima ya rasa ƙafafunsa biyu, haka Allah ke yadda ya so, mun yafe muku Allah ya yafe mana baki ɗaya."

Mota ta koma tana share ƙwalla sannan ta ɗauko cheque ta rubuta musu na 5millions ta ba su
"Ga wannan ku je ku gyara kanku don Allah, ku kama sana'a ku bar Bara, ga wannan, katin address ɗina ne, in kun samu lokacin sai ku zo mu gaisa." Godiya sosai suke mata amma ta wuce mota abunta tana share ƙwalla, a haka Angel da Abie ɗinta suka shigo.

*React and share*
[10/05, 12:52 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 7️⃣5️⃣ *The final episode*






*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2348102851740*

"Ummie, who are they? Ki yi shilu jan lama miki, Abie ba jai balsu ba"
"Haka ne Angel, Abie ba zai bar su ba tunda suka taɓa Ummin Angel, haka ne?"
Kai ta gyaɗa tare da hugging Zahrahn. A haka suka iso gidan Mamah. Lallai sun jinjinawa Allah da buwayarsa, duk wanda yayi haƙuri shi ke da Riva a rayuwa, yanzu Mamah ce a wannan tamfatsetsen gidan? Bayan sun shiga mamah ta tarbe su hannu biyu, har Daddy Bashir ya dawo shima ya nuna farin cikin ganinsu, zahrah ta ba ta labarin haɗuwarsu da su Bibalo, murmushi kawai mamah tayi tace "Allah mai yin yadda ya so ne, shi yasa ake so mutum yayi ƙoƙari ya yaƙi zuciyarsa ya zamana shi yake juya zuciyarsa ba ita ke juya shi ba, dama kuma an ce Mugun abu jakada (na Aysha Angel) ga shi kuwa ya koma musu ai, nan suka aje zancen gefe Mamah na tambayar Yaya Sadauki ya karatun fatan an samu Abunda ake so, ya amsa mata da Alhamdulillah, nan ta musu fatan alheri da samun dacewa duniya da lahira, sosai Angel ta sake da shi da Mamah, sai da suka zo tafiya tace ba za ta zauna ba bayan kuma ita tace da ba za ta kola gidan hajjaty ba, duka take, ta duka Yayanta ma. Bayan Mamah ta musu goma sha tara ta arziƙi haka Daddy Bashir ma, daga nan suka koma.

Bayan sati da dawowarsu hukumar bincike ta ƙasar Turai ta karrama shi tare da ba shi offer na aiki a tare da su saboda hazaƙarsa, sai dai bai karɓa ba saboda ƙasarsa ta haihuwa ta fi buƙatarsa akan can, a yanzu kuwa babu wadda bai san NIC ba da kuma founder ɗinta AU Abatcha. Bisa wannan cigaba da aka samu ma'aikatan NIC suka haɗa musu party mai ƙayatarwa tare da presenting masa gifts, a shekarar kuma Zahrah ta ƙara samun juna, same year political party Na APC suka buƙaci da ya shigo cikinsu yayi contesting a matsayin president, alkhairinsa a cikin ƙasar yasa ɗiban fari ya ci wannan kujera, nan fa su Zahrah aka zama first lady.

*ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH*
*Nan na kawo ƙarshen wannan littafin nawa *A BABBAN GIDA* wanda ya kasace aiki na ƙirkira, ina fatan kun nishaɗantu kuma kun fadakantu da wanan Labarin, ina roƙonku da duk wani abu na amfanarwa da kuka gani cikin littafin ku yi amfani da shi, na san akwai kura-kurai da yawa a ciki, ina fatan za ku min uzuri kasancewar Nima ajiza ce kamar kowa, sannan kuma na gode ƙwarai da kasancewarku tare da Ni, Allah ya bar ƙauna. Sai mun haɗu kuma a sabon littafaina na wannan shekarar AYA DA TSAKUWA (Diversity from shared humanity) da kuma TUMUN DARE wanda zan saki kwanan nan.*

*Ina matukar godiya gare ku*
_Diamond Bhatool Reading Club_
_A babban gida Reading club_
_Jameelah K Mashi Novels fans_
_Imara's corner_

*Ban manta da ku ba*
_Maryam Muhammad_
_Sholyn Abba_
_Sa'adatu Abdullahi._
_Maman Aslam_
_Esha_
_Meelerh Danganerh_
_Ummee_
*Ina roƙon Allah ya bar ƙauna tsakaninmu*

وبالتوفيق ، السلام عليكم ورحمة الله وبركاته

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login