Showing 6001 words to 9000 words out of 157517 words
yi alfahari da kai!”
A haka dai suka kawo ƙarshen meeting ɗin nasu ba tare da wata kafaffiyar matsaya wacce zata ɓulle musu ba. Daga nan kuma wannan duhu ya ƙara mamaye dajin, tsawon daƙiƙu biyar sai ga haske, waɗannan halittu kuma babu su babu alamunsa, they'll disappear.
_wannan kenan!_
*Oxford University of London*
Zaune yake a katafaren room ɗin shi kaɗai, babu abun da kake ji a ɗakin sai sauƙar ajiyar zuciya da yake sakewa lokaci zuwa lokaci kamar karamin yaron da ya gama shan kuka.
Saraki kenan!, yayi nisa cikin tunani wanda ya manta cewa a duniyar ma yake.
Cikin ransa babu Abun da yake tunani sai irin badaƙalar da ke cikin gidan nasu,gidan da ya zame masa tamkar baƙin kurkuku, gidan da yake jin ina ma bai kasance ɗaya daga ciki ba.
“Shin me yasa ƙaddara ta tazo da haka?, me yasa rayuwa ta ta kasance haka?, na gaji! Na gaji da wannan rayuwar, ina son samarwa Kai na cikakken ƴanci ko ma yaya ne! Ina so nima nayi rayuwa ba tare da wani ciwo ko nauyi a zuciya ta ba.”
Khalil da ke tsaye kansa ne ya jijjiga kansa cike da tausayawa ɗan'uwansa kuma amininsa, how he wish yana da yadda zai yi ya samar masa mafita, but babu!. Cike da kulawa ya durƙusa gabansa ya kamo hannayensa biyu ya haɗa da nasa. Cikin raunatacciyar murya ya ce
“Sadauki! Ya kamata a ce zuwa yanzu ka cire wasu damuwoyin cikin ranka, kowa da kake gani da yadda Ubangiji ke jarabtarsa, ka ƙara haƙuri, addu'a ita ce kawai makaminmu mu, ba kai kaɗai abun ya shafa ba Sadauki, mu ma nan duka family ya shafe mu, amma addu'ar da ake fadi kullum dole dai ita ɗin ce zamu riƙe, Allah ya kawo mana sauƙi cikin wannan rayuwa ya kuma sanya salama da nutsuwa cikin ahalinmu”
Runtse idanunsa da suka yi masa jajir kamar gauta yayi, zuciyarsa na wani irin tafasa, cikin rauni da kuma damuwa ya furta “Amin Dude, ina tsoron wata rana wani abun ne ya faru da tsofaffi da yaran da basu ji ba basu gani ba! Ina tsoron wani abu ya faru da su, Khalil in wani abu ya faru da su ba zan taɓa yafewa kaina ba, Ni ne sila Khalil! Mine sila!...” sai kuma ya dafe kansa da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya dafe ƙirjinsa da ke masa nauyi da zafi kamar an ɗaura masa karfen da ya shekara cikin razanannnen garwashi.
Da sauri Khalil ya miƙe, a zabure ya fara jijjiga shi sai dai attack ɗin da ya samu ɗin ya hana shi komawa daidai!, rungume shi Khalil yayi yana ƙara jijjiga shi, ya ma rasa me ya kamata yayi a daidai wannan lokaci. Hawaye ne suka fara zubo masa kamar ƙaramin yaro, har a lokacin kuma bai daina jijjiga Sadaukin ba wanda babu alamar numfashi ma a tattare da shi
“Don Allah Dude Ka tashi, ka tashi don Allah, kar ka bari baƙin cikinsu ya kashe ka su basu da asara, don Allah ka tashi ka tashi!”
Ganin dai Sadaukin ya ƙi yin ko da motsi yasa ya ƙara shiga wani matsanancin yanayin. Ya rasa ina zai sa kansa ciki ma, ƙarar shigowar saƙo yasa ya tuna da waya, da sauri ya sa hannunsa ya janyo wayar sannan ya shiga nemo numbern Doctor ɗin Sadauki da ke London. Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cikin harshe Larabci ya sanar da shi halin da suke ciki shi da patient ɗinsa. Bai tsaya bashi amsa ba ya katse ƙiran.
A haka Ya Khalil ke jijjiga Sadaukin har tsawon mintuna goma. Ƙarar doorbell yasa ya zame shi daga jikinsa da sauri ya nufi ƙofar, yana buɗewa ko jiran ganin waye bai yi ba ya koma wurin ɗan'uwansa. Cike da tausayawa Dr. Arƙam wanda ya kasance balarabe ke kallon Ya Khalil ɗin ganin yadda duk ya firgice lokaci ɗaya, ɗaya ɓari na zuciyarsa kuma na ƙara jinjina ƙarfin so da kuma alaƙar jini da ke ɗawainiya da matasan biyu.
Murmushi kawai yayi shima yana mai tunawa da nasa ɓangaren rayuwar sai kuma ya shiga cikin ɗakin da sauri, First Aid kit nasa ya ajiye sannan ya nufi Sadauki da ke kwance kamar gawa. Shi kansa Dr. Arƙam ya gama sarewa da al'amarin patient ɗin nasa, zuciyarsa tayi rauni gani yake kamar zai rasa wannan patient ɗin da tunda ya fara aiki bai taɓa jin so da ƙaunar da yake yi masa ya taɓa bawa wani ba.
Da sauri ya fara fitar da kayan bada agajin gaggawa, CPR yayi ya kai sau biyar amma numfashin Sadauki bai dawo ba, nan shima zuciyarsa ta sare, hope ɗinsa kenan, tunanin me zai ƙara yi yayi amma ya kasa tunawa ga kuma Ya Khalil da ya tsare shi da ido yana jiran yaga ɗan'uwansa na numfashi. Haka dai Dr. Arƙam ya ci gaba da yi masa CPR ɗin amma shiru, tsoron da Dr. Ke ɓoyewa ne ya bayyana har hawaye na silalowa daga idanuwansa.
A tsorace ya Khalil ya riƙo hannun Dr. Arƙam cikin raunin murya yace “Dr. Ka faɗa min me ya faru da ɗan'uwa na? Ya mutu ko?, shikenan nima wallahi bin sa zanyi! Me zan yi a duniyar babu shi?, ka faɗa min Drrrrrrr.!” ya idasa yana jan ƙarshen sunan hawaye ba bin kuncinsa. Cike da ƙarfin hali Dr. Arƙam ya furta “Calm down Khalil, Umar is in need of your prayer now, so stop crying and pray for him, let's get him to hospital now, there's need for a thorough assessment and intervention, fatan mu Allah yasa ya tashi” ya idasa cikin kwaɓaɓɓiyar hausarsa.
Da sauri Dr. Arƙam yayi dialling emergency number, in three minutes time ambulance ta iso bakin apartment ɗin nasu, da taimakon Ambulance committee ɗin guda biyu suka ɗaga Yaya Sadauki wanda ke a halin rayuwa ko mutuwa sannan motar ta tashi cikin wani irin matsanancin sauri.
On the other hand Dr. Arƙam is wishing for life rather than death to his patient, yana fatan conclusion nasa na cewar he's dead ya zama ba haka ba, this time around so da kuma fata yake wani yayi prooving nasa wrong. A ɓangaren Ya Khalil shi baya ma cikin hankalinsa, surutai kawai yake yana faɗin “Wallahi Dude baka isa ka tafi ka bar Ni ba sai dai mu tafi tare, nima mutuwar zanyi wallahi, Ni Khalil ba komai bane in babu kai Sadauki! Shike nan sun ci galaba kan mu kenan idan da gaske zamu bar musu duniyar?, don Allah ka tashi Man!”
Sai kuma ya fashe da matsanancin kuka kamar wani jariri.
Cike da tausayawa suke kallon wannan bawan Allah, duk da cewa basu san me Ya Khalil ɗin ke faɗi ba don yayi maganar ne cikin harshen Hausa amma sun fahimci yana cikin matsananciyar firgici da kuma damuwa. A dai-dai nan suka iso gate ɗin hospital ɗin.
**************************
_Readers! Nace my esteem fans! Da Ku dai nake kuna enjoying wannan labarin kuwa?, me kuke tunani game da rayuwar waɗannan matasa?, wace irin ƙaddara ce ke giftawa tsakaninsu da nasu ahalin? Kunji da wasu Devil Klans 👿! Nace su kuma su wanene?, kuna tunanin ƙudirinsu zai cika kuwa?, Su waye kuma waɗannan haske da ake faɗi?_
_Ku kasance da wannan alƙalami na lu'ulu'u (Diamond pen) don cigaba da samun wannan labari mai cike da tsantsar rikitarwa, zanen ƙaddara da kuma gwagwarmayar rayuwa._
_Mutanen channel ɗi na! Ina nufin my esteem Followers 💕 😘, ina ƙaunar ku da yawa da yawa, ina godiya da irin ƙaunar da kuke nuna min, tabbas yanzu na fara yadda cewa kuna a tare da Ni, zaku ci gaba da kasancewa da Ni saboda ƙaunar da ke tsakaninmu daga Allah ce!, i love you so much my esteem followers! Ina ji da Ku! Ku ɗin Ni ce, nima ku ne!._
_For more information, zaku iya tuntuɓa ta ta wannan number, WhatsApp only please: +234, 8143760764, ko kuma 07061707238/09027383866, phone call only._
*Remember that Diamond Bhatool 💎 Taku ce 💕 😘*
[16/10, 10:22 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎:
*Typing 📲*
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*
Wattpad: @diamond_bhatool
Arewabooks: @diamondbhatool
_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_
_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._
*PAGE* 0️⃣4️⃣
Ambulance na tsayawa ma'aikatan suka matso kusa, da sauri Dr. Arƙam ya furta “Wani ya taho da stretcher!” ana kawo stretcher aka ɗaura gangar jikin Ya Sadauki da ke sake, kallo ɗaya mai hankali zai yi ya tabbatar cewa babu numfashi a tattare da shi. Da sauri kuma aka tura stretcher ɗin zuwa cikin asibitin, directly A&E ward suka wuce da shi. Nan likitoci, Malaman jinya da sauran ma'aikatan da ke da ruwa da tsaki cikin kula da lafiyar majinyaci suka taru.
Abun ba'a cewa komai, Shi dai Ya khalil ya zama kamar wani mahaukaci, idanunsa duk faɗa kamar wanda yayi sati yana jinya, haka fuskarsa ta koma ja abunka da farin mutum. Dr. Arƙam kanshi baya cikin hayyacinsa Shiyasa ya yanke shawarar ƙin shiga room ɗin don a firgice yake da al'amarin patient ɗin nasa. Kafaɗar Ya Khalil ya dafa, cikin harshen turanci ya ce “Kayi haƙuri Khalil, muyi masa addu'a shine kawai, ka daina kukan haka ka ji?”
Kamar wani dolo haka ya gyaɗa kai, a reception ɗin suka zauna ganin tsayuwar ba yadda zata kai, cikin zuciyoyinsu kuma suna addu'ar Allah ya bawa Ya Sadaukin lafiya.
*NIGERIA*
*ABATCHA ESTATE*
*MORNING 🌅, 7:00 O'CLOCK*
Tun bayan sallar asuba Hajjaty ta saka Zahrah ta koma bacci wai ta huta da kyau. Ƙarar bedside clock ɗin da ta buga ƙarfe bakwai ya tayar da ita, ɗauke da addu'ar bacci a bakinta ta farka. Tsawon mintuna biyar kafin nan ta miƙe tana mai sauƙa daga kan bed ɗin. Toilet ta nufa tayi wanka, fitowar ta yayi dai-dai da shigowar Hajjaty wacce ta shigo da niyyar tayar da Zahran. Murmushi ɗauke a fuskarta take kallon jikar tata cike da so da kuma ƙauna. Ita ma Zahrah sai ta tsinci kanta da mayarwa Hajjaty martanin murmushin. Tsawon wasu daƙiƙu kamar wacce aka zabura Hajjaty ta nufe ta, ba tare da duba cewa daga wanka take ba ta rungume ta, wani bond ne ya kara ƙulluwa. Cike da farin ciki har haƙwarenta na fitowa ta furta “Barka da safiya kaka ta, fatan daren ki ya kasance mai daɗi” cikin sakin fuska Hajjaty ta amsa mata da “Eh jika ta, ya daren ki?” ta tambaya tana sakin Zahran. “Lafiya Lou Hajjaty, Hakan ta kasance ne da bacci a kusa da ke” wani irin murmushi Hajjaty tayi jin kalaman Zahrah.
“Yauwa Zahrah ga can kaya na sa Ruƙayya ta duba miki cikin kayayyakin Nasreen, anjima bayan kinyi breakfast akwai family meeting da Alhaji Baba yayi magana a kai jiya, yanzu ki shirya ki fito ki karya”
“To Hajjaty na gode” ta bata amsa tana ƙarasa zuwa wurin Ghana must go nata. Alhamdulillah ta furta bayan ta zuge ganin wata doguwar rigar Bibalo da ta taho da ita. Cike da kuzari ta shirya zuciyarta tas kamar farin wata.
Tana gama shiryawa ta fito ta tarar da su Hajjaty Zaune kan dining ɗin, da ido ta bisu don ganin su waye, Alhaji Baba ne, sai Hajjaty sai kuma Ya Auwab, ta gane fuskarsa sosai, a hankali ta fara takawa zuwa dining area ɗin, da sallama a bakinta ta ƙarasa tana sunkuyar da kai ƙasa. “Barka da safiya Alhaji Baba ” fuska sake ya amsa mata da “Barka Zahra'u, kin tashi kenan” murmushi kawai Zahrah ke saki har lokacin kanta ƙasa “Ya kuma kwanan baƙunta?” “Alhamdulillah” “Masha Allahu haka ake so, matso kusa da kujera ta ki zauna tunda jiya Hajjatyn ki ta ɗauke ki, matso nan” Alhaji Baba ya faɗa yana nuna mata kujerar da ke gefenta.
“A'ah Alhaji Baba yaushe kuma zata zauna kusa da tsoho, kin ga Ƙanwata zo kusa da ɗan'uwanki” Ya Auwab da ke kallon Zahrah yana murmushi ya faɗa “A sit for you sister”
Hajjaty Kam kasa magana tayi ganin ikon Allah. Danƙwalon sa Alhaji Baba yayi yana gyara zaman farin gilashin sa wanda ke ƙarawa idonsa ƙarfi kafin ya ce “Ungo nan! Nace ungo Nan Muhammadu! Kai Auwabu ina nuna wa jikata wurin zama shine zaka nuna mata wani daban?”
Kwaɓe fuskarsa yayi kamar zai yi kuka har sai da ya kusa sa Zahrah dariya.
“Kai Alhaji Baba don kawai na nunawa ƴar'uwata wurin zama shine, to in ban nuna mata ba wa zai nuna mata?”
“Usmanu ne! Nace Usmanu ne zai nuna mata!, kai Auwabu ka fita ido na na rufe fa!”
Dariya ya Auwab ɗin yayi yana faɗin “Calm down my only grandpa”
Hararar sa Alhaji Baba yayi yana faɗin “Zaka yi bayani ne, bari dai dodonku ya dawo ko na huta da zuwan ku nan kuna caja min kai”
Ita dai Zahrah kamar Status haka ta tsaya kallonsu, sun matuƙar burgeta, musamman yadda Ya Auwab ɗin ke tsokalo Alhaji Baba ga kuma yadda yake ƙoƙarin jan ta a jiki, Muryar Hajjaty da ta dafa ta ne yasa ta dawo daga duniyar tunnin.
“Kin ga Zahra'u kada ki biye surutun waɗannan don sai kan ki yayi ciwo, samu ki karya ki je ki shiryo, zuwa takwas da rabi kowa zai hallara.
Murmushi tayi cike da jin kunya ta zauna a gefen Alhaji Baba. Ɗago Ido Alhaji Baba yayi yana duban side ɗin Auwab sai aka ci Sa'a ya ɗago suka haɗa ido, fuska kwaɓe ya Auwab ke kallon Alhaji Baba Shi kuma Alhaji Baba sai ya ɗan zaro idanuwansa alamar ya ka ga Ni?
“Hajjaty kin gan shi ko?, Allah wannan mijin naki Ni ya takura min”
Murmushi kawai Hajjaty tayi tana serving Alhaji Baba sai kuma ta ɗago ta dubi Auwab ɗin da in Ka kalle shi zaka ce ƙaramin yaro ne, yadda yayi da fuskarsa zai matuƙar baka dariya.
“Ku kuka fi kusa, anjima kaɗan zaku haɗe kai” ta karasa tana turawa Ya Auwab ɗin plate.
Cike da nutsuwa tare da bismillah suka fara cin abincin hankalinsu kwance, Baka jin komai sai ƙarar spoons da ke colliding da plate. Tsawon wasu daƙiƙu har suka gama ci, kamar yada taga Ya Auwab ya goge bakin sa ita ma ta goge nata da tissue sannan ta furta Alhamdulillah.
Bayan an gama breakfast babu Wanda ya tashi ciki, sai ma wata ƴar hira da suka tayar. Ita dai Zahrah murmushi ne nata idan anyi abun da ya burge ta, idan kuma abun dariya ne ai ta sunkuyar da kanta ƙasa tana rufe bakinta.
Da misalin ƙarfe 7:40 suka miƙe, kowa yayi nasa sashen don fara shirin zuwa Family Hall saboda Taron da za'a yi na family. Duk wani ɗa da ke da alaƙa da gidan kowa ya san da meeting ɗin saboda daren jiya Ya Auwab da Ya Taj sun yi magana a WhatsApp group na family. Nan fa group ya ɓarke da hira ca-ca-ca kawai kake ji, kowa so yake yaji taƙamaimai dalilin wannan unexpected meeting da za'a yi because it's unusual ayi meeting irin haka a family babu wani abu da ya faru.
*****************
*BAUCHI*
A ɓangaren Bibalo jiki ya yi sauƙi sai dai muce Alhamdulillah, lafiya ta samu, surutan da take yi duk ta daina su, hakan yayi wa Baba Amarya daɗi sosai, sai dai babbar damuwarta shine rashin ganin Zahrah a gidan. Duk yadda tayi tunanin a nan iyayen Uwarta suke ta rasa don bata san wacce jaha suke ba. Tun tana neman a hankali har ranta ya fara ɓaci, ta kuma ƙudiri aniyar nemo Zahrah duk yadda take. Alwashin ta darr yake, ba zata taɓa bari Zahrah tayi rayuwa mai kyau ba, kamar yadda uwarta tayi wulaƙantacciyar rayuwa (a nata tunanin) ita ma Zahrah ita zata ɗanɗana. Bata ko tunanin illar hakan duk irin yadda Bibalo ta wahalta gashi kuma babu biyan buƙata.
Kawu ma dai nasa ɓangaren babu sauƙi, cikin kwana biyun nan mugayen mafarkai yake yi da Mama, mostly Kuma yana faɗawa mawuyacin hali ne tana taimaka masa, ya rasa ina wannan mafarki ya dosa, gashi kuma yanzu wata ƙaunarta ke kama shi, ya rasa yaya zai yi cikin kwana biyun nan, a halin yanzu babu abinda ya tsana sama da Baba Amarya, ko da ya shiga gidan ɗakin Mama ya fara nufa. To his suprise sai yaga ƙura alamar dai babu mai rayuwa ciki ga kuma yadda aka barwatsa komai na cikinsa.
Zuciyarsa ce ta buga, cikin ƙarfin hali ya nufi ɗakin Baba Amarya, a tare da Bibalo ya tarar da su suna cin taliyar murji da manja da kuma yaji, Baba Amarya na ganinsa ta miƙe da sauri ta zo gare shi. Kallon da ya jefe ta da shi yasa ta ɗan dakata. “Ina Madina ne?”
Sai da ta ɗan yi jim don har ga Allah ba zata ce tana iya tuna wace Madina ba har sai da ya tambaye ta a karo na biyu “Ina Madina ne?”
Cikin kame-kame ganin wannan sauyi tattare da Kawun yasa ta ce “Eh ah eh dama haka ne, eh ita da ƴar ta dama dama can sun shirya ne sai suka gudu don cin duniyarsu da tsinke....!”
Dakatar da Ita kawu yayi, shi kansa mamakin dalilin jin wannan zafi yake , a da shi kansa cin kashin da yake mata ko kare ba zai shinshina ba, amma yanzu duk wanda yaji zai faɗi magana kan ta, yana dai-dai ne da dakatar da shi ko ma waye. Juyawa yayi ya fice abunsa tare da barin gidan.
Cike da takaici Baba Amarya ta koma kusa da Bibalo ranta ɓace tace “In dai boka da Malam na nan, cikin su babu wanda ya dakatar da aikinsa, to nima ba zan gaji akan ƙudiri na ba. “Dole ka kasance a tafin Hannayena Idrisu.” ta furta a zahiri tana