Showing 21001 words to 24000 words out of 157517 words
ce “Dawo ki zauna ƴa ta gari, ga ƴan uwanki sun zo kuma shine zaki koma ciki”
Yaya Khalil who's tired of hearing ƴan uwanki ya ce “Hajjaty Ni ban ma gane Zahrahr taki ba, sai wani sunkuyar da kai take kamar mu ɗin sirkanta ne.”
Dariya suka yi baki dayansu, Ita dai Zahrah ta kosa ne amma haka ta dawo ta samu wuri a kasa ta zauna yayin da duk wani motsin ta yake kan idonsa.
Murmushi Hajjaty tayi sai kuma ta hade rai alamar she wanna say something important.
“Yanzu Halilu wai baka san Zahrah'u na ba kake nufi?, Dama shi wancan kam ba a magana” kai yaya Khalil ya gyada yana maida kallonsa ga Zahrah wacce ke zaune ƙasa.
“Da gaske Hajjaty ban san ta ba”
“Gaskiya ne, ba lallai ku san ta ba dama”
Ya Qasim ya faɗa yana kallon su duka biyun sai kuma ya ce
“To Hajjaty sai ki musu bayani amma ya kamata a ci tararsu.”
“Haba Yaya na Allah (kamar yadda suke kiransa su biyun) ka sa baki Hajjaty ta sassauta mana.”
Dariya Hajjaty tayi sannan ta ce “Ai babu sassauci tunda baku san shalelen jikanya ta ba, yau babu ku a girki na, kai wanda yayi muku ma ba zan baku ba, Qasim In ka tashi tafiya zan baka Gurasa ka wuce da ita.”
Da sauri kuwa yaya Qasim ya amsa da to.
Ba shiri Yaya Khalil ya sauko har kasa yana faɗin “Haba Hajjaty, ai babu wannan magana, ke Zahrah je ki jera mana gurasar a dining”
Mikewa Zahrah tayi tana nufin zuwa ta jera ta tsinkayi muryarsa da tun shigowar ta bata ji ya ce komai ba tun bayan cewa ta saka mishi zoɓon. Cikin ranta tana kara tabbatar da zancen Nasreen.
“Idan kin jera, ki ajiye sauran a kitchen anjima zan sa ki haɗa min shi” daga haka kuma ya make kamar ba shi yayi maganar ba, ita kam Zahrah kadan ne ma ya hana ta dariya saboda yadda taga yayi maganar yana wani shan kamshi kuma ya make kamar ba shi ba.
“He's damn amazing” ta faɗa cikin ranta.
Hajjaty ne ta dakatar da ita da faɗin “Koma Zahrah, ai hukunci na yanke musu” Zahrah sai ta koma ta zauna tare da daura kanta a cinyar Hajjatyn tana jiran ganin karshen wannan drama ta su Hajjaty.
Cikin ranta kuma tana yaba yadda suke mu'amalarsu da juna, abun ya matuƙar burge ta ya kuma kara karfafa mata guiwa kan ƙudirinta.
*React and comment please, yau fa In ba a gwangwaje Ni da reactions ba zan daina update gaba-daya sai kuma kun ji Ni, ah to , Ina matuƙar son ku my esteem fans da yawa da yawa din nan 💔🦋*
[12/24, 6:57 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
https://www.facebook.com/profile.php?id=61570606515077
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣0️⃣
_Not edited_
﷽
Hajjaty ta ce “Babu abun da ya shalle nikam, ba dai Wai ba ku San Zahrah'u na ba ku ka ce?” hmm” sai Kuma ta yi shiru.
Yaya Khalil da ya kosa da son sanin wace ce wannan Zahrahr ya sa ya ɗan kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce “To Hajjaty ki faɗa Mana please”
Sosai Zahrah ta so darawa sai da babu dama musamman yadda wannan sarkin izza ya haɗe girar sama da ƙasa dhi ala Dole bai son raini.
Gyara murya Alhaji Baba ya yi sannan ya ce “To ni bari na yi magana tunda ita ba faɗa muku za ta yi ba...”
Kafin ya ƙarasa Yaya Khalil ya katse shi da “Yauwa Tsoho Mai ran ƙarfe, Allah ya ja kwana.”
Cikin ran sa ya amsa da Amin sannan ya ce “Idan ba ku mance ba akwai yarinyar mu Madina wacce ba zan ce ɗayanku ya San ta ba sabisa rasa ta da muka yi” sai ya ɗan ja numfashi ya ce “A taƙaitace dai wannan Zahrahr ɗiyarta ce, Amma ita a halin yanzu ba a San yadda ta ke ba”
Murmushi Yaya Khalil yayi yayin da Master Kuma ya dake kamar bai ji me ake magana a Kai ba Amma can ƙasan ransa ya tausayawa yarinyar ga Kuma su Hajjaty da ke tsananin kewar ɗiyarsu musamman da ta kasance tilon ya mace. Kallonsa ya Kai ga wurin da ta ke ita kuma lokacin ta sa hannu ta goge hawaye. Lokaci ɗaya tausayin yarinyar ya lulluɓe shi and he's eager to know how all these happened.
Ya na Shirin janye idanuwansa su ka haɗa ido sai Kuma kowa ya kasa janye nasa daga na ɗan'uwansa yayin da kowa ke saƙa wani abun cikin ransa. A ɓangaren Zahrah kwarjini sosai ya yi mata sai da ta gagara ɗauke idanuwanta, cikin ranta ta na ayyana irin kyan da Rabbi ya yi Masa. A nashi ɓangaren shi Kuma tsantsar tausayin yarinyar ya tsaya masa a rai and cikin idanuwanta Yana hango wasu exceptional abubuwa da bai jin ya taɓa gani tattare da wata halitta. Ko da ya dawo hankalinsa ganin kallonsa Zahrahr ma ke yi yasa ya ƙara haɗe fuskar Nan tare da zaro mata idanuwa, ai da sauri ta janye nata tana mai ƙara lafewa jikin hajjaty. Yaya Sadauki kuwa sai da ya murmusa ganin kallo ɗaya da yayi mata ya furgita ta.
Duk wannan zare idon hankalin Alhaji Baba Kansa yake lokaci ɗaya Kuma ya murmusa Tare da faɗin “Hajiya ki yi haƙuri ki sallami Sadauki don sai zarewa jikar ki ido yake saboda kin Hana ta haɗa Masa ɗa'ami”
Sosai kowa ya kwashe da dariya ban da Yaya Sadauki da ya ƙara haɗe fuska jin yadda Alhaji Baba ya ke Shirin yaga shi gaban yarinya, ita kuwa Zahrah sai da ta murmusa sannan ta ɗago tana Kai dubanta ga Hajjaty, fuska shagwaɓe ta ce
“Allah Hajjaty da gaske kin ga har haka yayi min” sai ta shata wuyanta da yatsa alamar yanka.
Tashin hankali Wai ba a sa Masa date, Yaya Sadauki kamar yayi Yaya saboda yadda yaji Sharrin da ta ƙulla Masa sai kuma ya murmusa cikin ransa yace “Atleast zan ci favorite bayan wani lokaci” yayin da a zahiri Kuma fuskarsa ke ɗaure ta ke sai ma Danna wayarsa da yake.
Sai a lokacin Hajjaty ta sa Zahrah ta haɗo Musu gurasar, ba Musu ta Wuce kitchen ta haɗo ta Kai dining. Ta gefen ido Yaya Sadauki yake kallonta har ta dawo ta zauna wurin zamanta ta ce “Na gama haɗawa”.
“Ki kawo Mana Nan!” ya faɗa in an authoritative way
Ba Musu ta koma ta kwaso ta kawo Musu Nan suka Fara ci. Ko da suka gama suka dawo ba su tarar da Zahrah a parlourn ba, hakan yasa kai tsaye suka nufi bangaren Hajiya Babba. A can suka zauna salla kawai ke fitar da su, abun mamaki kuma har zuwa lokacin Babu wani mahaluki da ya San da dawowarsu.
Bayan sallar isha suka koma part din Hajjaty kamar yadda ya saba dama wurin zaman sa ne.
Zahrah da kanta tayi warming gurasar sannan ta hada ta coz a yadda ta fahimta he too much like gurasa. Fahimtar cewa a nan din zai ci yasa ta jera a dining.
Tana fitowa ta wuce bedroom dinta jin alamar kiran salla, wanka tayi kana ta dauro alwala sannan ta gabatar da sallar ishar ta.
A lokacin da su Yaya Sadauki suka shigo ita da Hajjaty na parourn, nan fa aka baje a parourn ana hira. Yaya Kalil da bai da jimurin yunwa ya kwaye baki sai hamma yake saki.
Harararsa Yaya Sadauki yayi shi kuma sai ya kwashe da dariya.
“Haba Man, irin wannan kallo sai ka sa Sis Zahrah ta tsorata.”
Takaici kamar ya kashe Yaya Sadauki jin yana so ya kawo raini tsakanin su nan take ya tamke fuska.
“Sorry Man! Ka cewa Hajjaty yunwa nake ji please” ya fada kasa-kasa.
Hararar da ya balla masa wannan karon kamar idon zai cire, a daidai lokacin kuma Zahrah ta dago kanta sai aka yi rashin sa'a idonta ya sauka kansa. Kun san Zahrah da wata dabi'a tata na rashin iya kunshe dariya ai kuwa sai ta kece da dariya.
Nan da nan hankalin kowa ya dawo kanta including Yaya Sadauki wondering why is this girl laughing kamar mahaukaciya, on the other hand Yaya Kalil already ya gano kan me take dariyar coz a kan idonsa ya ga lokacin da Zahrarhr ta zaro idanuwa waje.
“Zahra'u lafiya?” Hajjaty ta tambaya.
Kafin ta tsayar da dariyar har ta yi tunanin bawa Hajjaty amsa tuni Yaya Kalil ya yi caraf ya CE “Wallahi Hajjaty ita da Man ne!”
AI Babu shiri Zahrah ta tsayar da dariyar tana kunshe baki sai zaro idanuwa take jin tereren bankadar da Dan'uwanta yayi Mata yayin da hanjin cikinta suka juya har cikin Na bada sautin kuuuuu.
“Wallahi ba haka bane!”ta fada a kidime.
Yaya Khalil da ya dago ta sai da ya murmusa kasa-kasa don yana so shirin sa yayi aiki a kansu.
Wani kallo Yaya Sadauki ya aika Mata tuni ta Kara shiga hankalin ta. Ganin yadda ta tare wuri guda yasa Alhaji Baba yin magana.
“Ya dai Zahra'u? Me kike wa dariyar ne?”
Cikin rawar murya ta ce
“Alhaji Baba Babu komai fa kawai Na tuna da Bibalon Aunty Amarya ne lokacin da suke duka na sai nake kwatanta Ina ma a ce yanzu ne da Na koya Mata hankalin.”
Ran Yaya Sadauki ne ya baci jin yarinyar na son raina masa wayo bayan kuma Dude dinsa ya sanar da shi cewa da shi take. Fuska daure ya maida kallonsa gare ta tare da zaro kwalakwalan idanuwansa waje sai dai Bai kai GA furta komai ba Alhaji Baba ya ce
“Rabu da ita Sadauki ba da kai take ba.”
Wai wai wai, tashin hankali ba a sa masa date, wai yau Yaya Sadauki aka rainawa wayo a gidan nan? The whole Sadaukin Abatcha? To ai ko manyanta ba za su masa irin haka ya share ba talkless of tiny her!, he must deal with her.
Abun ka da miskilin mutum sai ya waske ya ce “Okay” daga haka ya gimtse bakinsa.
Yaya Khalil dai dariya ya yi kasa-kasa yana kuma Kara jaddada wayon yarinyar cikin ransa and he feel good about her, ko ba komai yau ta harzuka Man din sa, he's always hoping for change, yana so ya koma ainihin Sadaukinsa.
A haka dai aka shashantar da zancen aka koma wani batun sai dai har lokacin zuciyar Zahrah bata daina tsalle ba GA firgicin da ya kasa barin fuskarta. Bangaren Yaya Sadauki kuma ya yi shiru ne kawai saboda baya son musu amma fa deep down his heart ya kudirikudiri aniyar saita yarinyar nan.
“Uhm jama'a ni fa hakuri Na ya riga da ya kare, tun dazu Na ji shiru, mai son Allah dai ya biyo mi dining mu ci kafin Na sume muku”
Jin batun nasa sai da kowa ya dara Banda Yaya Sadauki da ransa ya yi tsananin baci ganin dai da gaske Yaya Khalil raini yake son jawo musu, fisabilillahi gaban yarinya karama! Kai this is unfair of him, tirr.
Alhaji Baba ne ya fara tashi fuska sake sai kuma sauran ma su ka Mike ban da Yaya Sadauki da ya hade girar sama da kasa alamar ma ba ya son wargi. Bayan sun zauna Zahrah ta yi serving kowa sannan ta zuba ma kanta, har ta kai spoon din farko bakinta ta tuna da shi, sai ta tsinci kanta da karewa dining din kallo, ganin ba ya nan yasa ta ji wani iri. Hakan Sam bai Mata dadi ba sai take ganin kamar laifin ta ne, ba ta ci wani mai yawa ba ta Mike tare da nufar flask din da ta hada gurasar tare da daukar ta, ta juya zata nufi kitchen Hajjaty ta dakatar da ita da fadin
“Ina za ki je ne Zahra'u?”
Wuri-wuri ta yi da ido tayi kana ta sunkuyar da kai sai shafa flask din take da hannunta. Ganin ba ta da abun fadi yasa Hajjaty ta ce
“Maza dawo ki zauna Ina gani ba ki ci Na kirki ba.”
“A'a Hajjaty ki bar ta, hala kunya ta take ji, in Na tashi probably ta dawp ta ci” cikin ransa yana addu'ar Allah yasa dai kar su Hajjaty su ce a'a coz ya riga ya dago jirginta don dama can Yaya Khalil ba dai sa ido ba. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Zahrah ta San ko ba komai Yaya Khalil ya cece ta har tana tunanin tsaftace aika-aikar da ta yi.
Jin Hajjaty ba ta ce komai ba ya sa Yaya Khalil murmusawa sannan ya mayar da duban sa ga Zahrah wacce har lokacin kanta ke kasa yace
“Je abun ki sister, anjima zan tashi sai ki dawo ki ci tunda kunya ta kike ji.”
Jikinta har rawa yake ta nufi kitchen, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya a bayyans ta furta
“Allah na gode maka da ka tseratar da ni.”
Basket ta dauka ta hada komai da zai bukata a ciki kana ta ajiye sai ta fice ta backdoor ta zagayo zuwa parlourn dauke da sallama a bakinta yayin da ya amsa kasan makoshin sa ba tare da ya kalli inda sallamar ta fito ba sai ma maida hankalinsa da ya yi kan phone dinsa da yake latsawa.
Jikinta sanyaye ta karasa cikin can kasan ranta kuma tana addu'ar Allah ya bata nasarar wanke laifin ta, sai a lokacin ita ma take nadamar abun da ta yi, deep down her heart she's apologizing and hoping that her apology will be put in to consideration.
*Mommah's Pov*
Gabadaya Mommah ta fara zabgewa saboda damuwar rashin nagartaccen danta tana Kara tabbatar da zancen su da Hajiya Baraka da kuma Hajiya Saudatu. Babu shakka Hajiya Babba tana cutar da su amma Babu komai zata San matakin dauka.
“Amma batun shawarar Hajiya Baraka fa?”
Lokaci guda tayi na'am tare da gyara zamanta kan sofa, amma kuma sai ta tuna da dabi'un Kausar din nan take ta jijjiga kai, ba zata yi wa danta fatan samun mace irin sa ba, amma dai zata yi mai yiwuwa ta ga ya auri wata ko da kuwa a wajen Ahalin ne.
*Na rage tsayin update yau saboda Na tabbatarwa kai Na cewa kuma tare da ni, hakan zai faru ne idan Na GA reactions din kuitanen kirki. ILYSM*
_Be with my pen to know what will happen next, shin plan din Kawayen Mommah zai yi aiki?, me zai faru tsakanim Zahrah da Yaya Sadauki? Idan kun yi reacting sosai da safe zan yi update._
[12/25, 11:36 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©️Diamond Bhatool*
https://www.facebook.com/profile.php?id=61570606515077
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣1️⃣
_Not edited_
﷽
Shi fa har ga Allah bai ma San da zamanta ba sai da ta ɗan bige ƙafarsa garin zuba gurasar a plate tukun ya San da mutum kusa da shi, a hankali ya mayar da dubansa ga wurin da ƙafarsa take, mamaki fal cikin ransa ganin mutum, mutum ɗin ma yarinyar da ta gama raina sa, a fuska ɗaure ya kalleta sai dai ita ba ta san da hakan ba sakamakon yadda ta maida hankalin ta ga zoɓon da take zuba masa.
Tashin hankali Wai ba a sa masa date! Zahrah ba mugun ƙoƙari ta yi ba, bayan ta kammala sai ta ja gefe tare da tsugunnawa gabansa sai Kuma ta kama kunnuwanta biyu.
“I'm sorry Yaya, ka yafe min, I don't meant to hurt you, please ka Yi haƙuri ba zan maimaita ba.”
Ko ɗagowa yayi ya kalle ta bata samu ba talkless of ta sa ran zai amsa, hakan ya sa guiwarta yin sanyi.
“Yaya ga gurasar I prepare it to you myself, don Allah ka ci kada ka kwana da yunwa, I won't forgive myself if you didn't eat, don Allah Yaya.....”
Hannu ya ɗaga mata alamar ya isa sannan ya nuna mata ƙofa da hannunsa.
“Out of my sight!”
Ai da sauri har tana harɗewa ta bar parlourn sai bedroom ɗinta. Duk Wannan ban haƙuri da take bashi yana jinta, and temper da ya hau ya sauƙo musamman yadda ta iya lanƙwasa harshe ta bashi haƙuri. Shi a da yana da wani stereotype game da mata that Suna da girman Kai but karo na farko kenan da yayi proving kan shi wrong.
Abun da ya fu burge shi da yarinyar bai Wuce yadda yadda nuna concern ɗinta kansa ba, he really appreciated it Amma cikin ransa fa, ganin tunanin babu yadda zai Kai shi yasa ya ja tsaki tare da furta Bismillah sannan ya fara cin gurasar yana lumshe idanuwa, cikin ransa ya furta “This sister is unique”
Bai Kai ga kammala ci ba yaji muryar su Hajjaty, idanuwa ya zaro sai Kuma ya gyara Zama ya ci gaba da cin gurasar sa hankali kwance. Ko da suka dawo babu Wanda yayi wa ɗan'uwansa magana sai Yaya Khalil da ɗan banza tsokalarsa ya ce
“Man wa ya kawo maka gurasa kuma?”
Ya ƙarasa yana ƙura Masa ido, gogan naka bai ce komai ba ya ci gaba da Kora zoɓo abun sa. Sauran jama'a babu wadda yace uffan game da hakan.
Alhaji Baba ne ya miƙe don ya Wuce ɗakinsa ya kwanta, Sallama ya Musu sannan ya nufi bedroom ɗinsa, Nan Yaya Sadauki ya bi bayansa ya rage iya Hajjaty ce Sai Yaya Khalil.
Hajjaty ta kalli Yaya Khalil ɗin tace
“Ni Halilu wa ya kawowa Sadauki abinci Nan?”
“Ina ga Zahrah ce fa”
“Zahrah kuma?”
“E Hajjaty, ni fa akwai abun da nake hasasowa and Ina fatan ya tabbata, you people will be Happy with it.”
“To Allah ya tabbatar da alkhairi.”
“Amin” ya and.
A ɓangaren Yaya Sadauki da Kansa ya kaɗewa Alhaji Baba shimfiɗa kana ya taimaka Masa ya zauna bakin gadon Shi kuma ya Nemi waje ya zauna kan carpet din dake shimfiɗe a bedroom ɗin.
Ganin hakan yasa Alhahi Baba fahimtar cewa da abun da yake so.
“Ya dai Sadaukin Abatcha? Akwai damuwa ne?”
“A'ah Alhaji Baba, it's all about that case.” ya faɗa cikin ƙunar rai.
“I believe in you Sadauki, bayan tafiyar ka na Yi bincike and it's found that akwai wadda ya haɗa wannan Abu, a matsayinka na jami'in tsaro da bincike ina roƙon ka da ka faɗaɗa binciken don na ƙosa da ire-iren abubuwan nan.”
Tun da Alhaji Baba ya fara bayani zuciyar Yaya Sadauki tayi sanyi ƙalau, tsoro da fargaban da yake ji all disappeared. Cikin ransa yana