Showing 120001 words to 123000 words out of 157517 words
Allah. Sai da aka gama gaggaisawa tukun Alhaji Baba ya dubi shalelen jikan nasa yace "Sadauki Sadauki, Sadaukin Abatcha Sadaukin duniya, ai ba ka san wani abu ba mu nan har mun binne gawarka ashe ba kai ba ne, to ya aka yi bayan kuma an tabbatar da cewa kana cikin jirgin da yayi haɗarin?"
Kamar ba zai tanka ba yace "Allah ne mai yin yadda taso haƙiƙa, babu shakka ranar zan je Bauchi ne don cika muku muradinku game da ɗiyarku kuma Babata Mamah wacce na gano yadda take ta hanyar wani bawan Allah. Na so a ce ta hannuna ta dawo gare ku sai dai Allah shi ke yadda ya so, a ranar da muka tafi na yi sallama da matata tukun na wuce ba tare da wani ya san na tafi ba bayan ita. Ba zan ce ga abun da ya faru ba tunda a sararin samaniya ne sai dai zan iya tuna lokacin da jirgin mu ya kama da wuta tare da tarwatsewa gabadayansa. Ba zan iya tuna komai ba amma dai.." dakatawa yayi tare da miƙewa ya bude door ɗin hall ɗin, wani ɗan matashin da ba zai wuce Sa'an Yaya Sadaukin ba ya kalla tare da masa alamar ya shigo, wuri ya ba shi ya zauna tukun ya dubi su Alhaji Baba da suka yi tsit suna kallon su kana ya dubi mutumin yace "Wannan shine Junaidu, abokina ne a can kuma shine wanda ya taimaka min a lokacin da al'amarin ya faru, Aboki ko za ka iya ba mu labarin gabaɗayanmu."
Gyaran murya Junaidu yayi yana gyara zama, "To da farko dai alhamdulillah, kamar yadda ya faɗa Junaidu sunana, Ni mutumin garin Zubo ne, da ke jahar Bauchi, sai dai kuma Ni gidana yana bayan gari kusa da kogi saboda kasncewata masinci."
"Ranar wata juma'a da yamma na dawo gida daga cikin garinmu da yake in na yi su na kan kai cikin gari ne a saye, ina dawowa na sauya tufafi domin komawa nayi su, a lokacin da na kafa tulu na a cikin kogin sai na ji kamar na zunguri abu, a tunanina ma wani ƙaton kifi ne hakan yasa na fito na zara sangen da nake amfani da shi, abun mamaki kuma sai Na ci karo da wani ɓangare na abun hawa da ba zan iya fayyace menene ba, hakan ya sanya ruɗu da al'ajabi cikin raina. Hannuna na sa na janyo amma hankalina ya ƙi kwanciya da abun sai nake jin kamar akwai wata halitta tare da ɓangaren abun hawan, hakan ne yasa kawai na shiga kogin kamar mai wanka, ba tare da na zata ba na ci karo da abu, abun ka da ƙwararre na jawo abun take muka yo sama, ga mamaki na me zan gani? Mutum, mutum ne gwarzo a siffa kuma kyakkyawa, a lokacin na san cewa ba ƙaramin mutum bane, kalar fatarsa yasa nayi tunanin ko dai ba ɗan ƙasar bane? Da haka na ciro shi kusa da tutu na na shimfiɗe shi tare da matse ruwan da ke cikinsa, cikin ikon Allah ashe akwai sauran numfashi a tattare da shi. Sosai na godewa Allah, saboda yadda na fahimci akwai jigata a tattare da shi yasa na saɓa shi a baya na muka shiga cikin gidana, ɗaya ɗakin da muke ajiye kayan abinci na nufa da shi, da yake lokacin abincin ya ja baya kawai sai na gyara ɗakin tare da kwantar da shi bisa tabarmar kabar da uwarɗaki na ta kawo min."
"Bayan nan na sa ta tafasa ruwa masu zafi, Ni na taimaki bawan Allahn nan yayi wanka, sannan na ɗauko suturata na ba shi ɗaya, bai ji ƙyanƙyami ba kawai naga ya amsa ya saka. Ganin hakan yasa na koma wurin su ɗi na bayan izinin daga wurinsa da na karɓa, ina komawa ban kama wasu kifaye masu yawa ba na dawo na ba wa uwargidan ta yi abinci da shi. Nan ta tsare Ni da tambaya, ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita, abun ku da mace tuni tausayinsa ya kama ta itama. Bayan ya ci abincin bai wani jima ba ya kwanta sai bacci."
"Washegari tare muka karya, bayan mun karya nake tambayarsa daga ina yake, amma sai yayi shiru da alamun dai ba ya cikin hankalinsa hakan yasa na haƙura na tambayi sunansa, abun mamaki a take ya amsa min da Sadauki. Mamaki sosai na shiga ganin ya iya Hausa, sai dai tsawon kwanaki uku in na tambaye shi daga ina yake ba ya cewa komai duk da za mu zauna mu ɗan taba taɗi da shi, daga haka na fahimci cewa ya manta abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa. A ranar ne kuma na je cikin gari naji ana zancen haɗarin jirgin sama da aka yi daga wurin jama'ar gari, wanda su ma labarin ya Riske su ne ta hanyar sauraran rediyo."
"A haka muka ci gaba da zama, sannu a hankali shima ya koyi su har ma ya fi Ni iyawa, cikin ƙanƙanin lokaci sai ya kama kifayen da a rana iya adadin su nake iya kamawa. Nan da kasuwa ta ta bunƙasa, har aka fara zuwa daga wasu ƙauyukan kusa da mu ana sarin kifi wurin mu. Daga baya ma dai sai muka fara fita har wasu wuraren muna kai kifi, ganin ƙwarewa irin tasa yasa na nemi shawarar uwargidan nawa Ni da shi muke tafiya jama'are yin su ɗin, ai kuwa mun samu alkhairi ba kaɗan ba, tuni arziƙina ya bunƙasa sai dai damuwata ɗaya har yau wannan bawan Allah bai tuna wani abu ba daga rayuwarsa."
"Mun shafe shekaru biyu zuwa uku da shi a wannan halin, kwatsam sati biyu da suka wuce mun je jama'are a Babban titin garin wata jibgegiyar mota ta zo wucewa, nan fa Sadauki ya ƙi biyoni muje su wai shi wannan baron yake so yake kalla, ganin tuburan dai ba zai biyo NI ba yasa muka tsaya gindin wat bishiya muna kallon motocin ɗaya bayan ɗaya har yamma. Hakan yasa na fara lallaminsa yazo mu koma amma ya ƙi, ƙarshe dai cewa yayi na tafi, shi motarsa zai hau ya tafi."
"Jin kalamansa yasa na fahimci cewa akwai wani abu da ya fara tunawa da ganin motocin, hakan yasa na zauna tare da shi, can wajajen ƙarfe biyar na Yamma naga ya zabura ya miƙe tsaye, sai kuma ya faɗo ƙasa sumamme. Hankali tashe na ɗauke shi nayi haramar sama mana abun hawa, muna samu kuwa muka wuce gida kai tsaye. "
"Lokacin da ya farfaɗo na sha mamaki ƙwarai jin yana furta wasu maganganu kamar haka _A'a Mubaraka ki bar Ni haka da rashin jin ki, dole yau zan taho da Mamah._" can kuma yace _Zahrah, ki taya Ni da addu'a, ina tabbatar miki da cewa Yayanki will not disappoint you, in sha Allahu yau zuwa gobe in muna da rai za ki yi farin ciki sosai._ _Mommah na ita ce matsalata a rayuwa, na gaji da hulɗa da mutanen banzan nan da take, Mommah wallahi ba son ki suke ba, don Allah ki fita hidimarsu._
"Zantuka makamantan waɗannan yake yi yayin da kuma idanuwansa ke rufe. Kalmar shahadar da ya rangaɗa yasa na tsorata a tunanina ma ko mutuwa zai yi, sai dai lokaci guda kuma ya miƙe ya zauna yana bin ko'ina da kallo. Can dai na dubeshi nace, Mallam Sadauki ka tashi? Sannu. Kallona kawai yake yi daga bisani yace Malam lafiya? Ina ne nan? Me nake yi a nan? WHERE'S my wife and family? Da kyar na lallaɓa shi sannan nace masa yayi haƙuri jikinsa yayi ƙarfi kafin ya koma gida amma ya tubure shi fa dole ya taho, da ƙyar dai ya yadda ya zauna, bayan sati ɗaya da kwanaki shida kuma yace zai tafi, nan dai muka yanke shawara da maiɗaki na akan na raka shi har zuwa ga ahalinsa tunda ya riga ya dawo daidai. Shine muka taho, zuwan mu na yi mamakin ganin ashe shi ɗan babban gida ne irin wannan, taron da muka ga yasa muka yi tunanin ko mutuwa aka yi ashe aure ake ɗaurawa."
Daga haka Junaidu masinci yayi shiru can yace "wannan shine abun da ya faru." Mamaki da al'ajabi sun cika kowa yayin da shi kuma hankalinsa yanzu gabaɗaya yana ga matarsa da ya bari tsawon shekaru, ko ta yi aure bayan takaba? Oho.
Sosai su Alhaji Baba suka yi ta jajanta abun, Mommah sai kuka take tana jin kamar ta janyo shi ta rungume shi, nan suka yi wa Junaidu godiya bisa taimakon da yayi wa Yaya Sadaukin, daga nan Alhaji ya ba shi labarin lokacin da aka gano yayi hatsari har da gawar da suka je aka ɗauko aka yi jana'izarta. Sosai yayi mamaki tare da godewa mahallicinsa. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan yace "What about her?"
Yaya Khalil da ke bayansa yace "Who?"
"I mean she, my wife, Mabruka"
Rasa mai faɗa masa aka yi can dai Mamah ta ba shi labarin rasuwarta tas, ƙwalla kawai ya share tare da mata addu'ar neman rahama, cikin ransa kuma yana alhinin rashi mace ta gari irin Barr. Mabruka. Shiru ne ya wanzu a cikin ɗakin can dai little ya cilla ihu ya fara zillewa daga hannun Zahrah. Sai lokacin hankulansu ya dawo ga Little Sadaukin da ba su sanar da mahaifinsa batunsa ba, kuma ba sa tunanin ya san da samuwarsa.
*React and share*
[27/04, 7:28 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣7️⃣
﷽
Gabansa ne ya faɗi lokacin da suka haɗa ido da yaron ganin irin kamar da yake, wani tsoro ne ya ɗarsu a zuciyarsa sai kuma ya miƙo hannunsa ga yaron ganin yadda ya Zubo idanuwansa cikin nasa. Zillewa Little yayi Cikin tafiyarsa ya taka ƙwas ƙwas sai wurin Ya Sadauki. Mamaki ne ya kama mutanen da ke hall ɗin, wato dai gaskiyar bahaushe cewa jini ya fi ruwa. Don tun lokacin da Ya Sadauki ya ɗauki Little yaron yayi shiru tare da lafewa jikinsa, can kuma ya fara masa gwalatu kamar dai ya san shi..
Idon kowa a kan su yake banda Zahrah da kanta ke ƙasa,
Murmusawa Alhaji Baba yayi yace "Ashe ba mu sanar da kai batun Little ba, wannan ɗin jininka ne, yaron da Mabruka ta haifa ta rasu bayan kwanakin suna, an sanya masa sunanka amma muna kiransa da Little Sadauki, Zahrah'u ita ce ta kasance tamkar uwa a wurinsa...." Nan Alhaji Baba ya ba shi labarin yadda komai ya faru bayan rasuwar Aunty Mabruka.
Murmusawa Yaya Sadaukin yayi tare da kai dubansa ga inda take sai dai wayam babu ita, dariya abun yaso ba shi tunawa da halinta na rashin son disgi. A hankali ya furta "Allah ya saka mata da alkhairi."
"Amin" dukkansu suka amsa, ita dai Mommah sai mamaki take musamman yadda al'amarin ya kasance, tabbas da a ce ba a ɗaura auren Zahrahn da wani ba da babu shakka a yau za ta sa Yaya Sadaukin ya aureta coz ta cancanci haka, ita kaɗai ta cancanci maye gurbin marigayiya Mabruka, amma Allah ya riga yayi babu aure tsakaninsu.
Daddy ne ya dubi yaron nasa cike da kulawa da ɗauki yace "To Son, Sai batun amaryar taka, ka fara shirye-shirye don ba za mu bar ta ta ci gaba da zama haka ba, ka samu ka kammala shirye-shiryen ka ka ɗauki abarka."
Ƴar kunya ce ta kama shi sanin babu wanda yasan da zancen, sosa kansa yayi tare da faɗin "Toh eh dama to Daddy, in sha Allahu, amma..."
Ɗauke da ayar Tambaya a fuskokinsu Mommah, Hajiya Babba, da kuma Hajjaty suka ce "Amarya kuma?"
Murmmushi Alhaji Baba yayi tare da faɗin "Eh fa, kun san ranar da yaron nan Ishaq ya fasa auren Zahrah ana shirin ɗaurawa da Ɗan ɗan'uwan uban yaron sai ga Sadauki ya bayyana garemu, shi da kansa kuma ya buƙaci a ɗaura auren da shi."
Ba waɗanda suka yi addu'a kaɗai maganganun Alhaji Baba suka doka ba ita kanta Zahrahn sai da ta miƙe daga tsugunnon da tayi tana dafe ƙirji tare da ƙwalalo idanuwanta waje. Yadda ta yi yasa kowa darawa sai ta tsinci kanta da sunkuyar da kai. Murmusawa Yaya Yayi tare da gyara zaman Little kan cinyarsa, ɓangaren Mommah kam wata hamdala ta sauƙe tana faɗin "Haɗi ya yi, Allah sanya alkhairi." Hajjaty da Mamah suka amsa da "Amin."
Zahrah kam maƙalewa tayi a baya tana babbaza idanuwa, ganin sun fara ficewa daga ɗakin yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Shirun da ta ji yasa ta yi tunanin kowa ya fice hakan yasa ta ɗago kanta tare da miƙewa tsaye tana dafe saitin heart ɗinta. Cike da sassarfa itama ta fara ƙoƙarin ficewa daga hall ɗin sai dai ta tsaya cak jin an riƙe hannunta. Ba tare da ta juyo ba ta zaro idanuwanta waje sai dai kuma ƙamshin turarensa shi ya tona asirinsa. Little Sadauki da ke hannunsa ya sauƙe jin yana "Ammi Ammi.." sai kuma ya fara gwalatu.
Cikin sassanyar muryarsa da tayi kewa tsawon shekaru yace "Ba za ki jira mijinki bane?" Sai a lokacin ta fara kiciniyar ƙwace hannunta daga riƙon da yayi mata. Ganin ta gagara yasa ta shagwaɓe fuska tace "Please ba na so.."
Yadda tayi maganar ya kashe masa jiki amma ya dake yace "meye ba kya so ɗin Lily?"
Bakinta gaba tace "Ni ka sake Ni na wuce abu na kar wani ya ganmu."
"To meye idan an ganmu, ba dai da mijinki kike tare ba, ko ba kya so na ne, ba ki yi farin ciki da dawowa ta ba ko?"
"Uhm uhm" ta ba shi amsa tare da ɗago Little da ke famar ɗale ta yana ƙiran "Ammi Ammi ba".
Jin ta yi shiru yasa yace "ok let's go." Babu yadda ta iya haka suka fito tana riƙe da little shi kuma yana riƙe da hannunta. Fitowar su ta yi daidai da wucewar Rumana wace ke kai wa da komawa a bakin hall ɗin tun lokacin da ta fahimci cewa ba fatalwarsa ba ce. A zafafe ta ƙaraso yadda yake tsaye tace "Yaya Kai ne dai? Ina yini" ko kallo bai ishe ta ba hakan yasa ranta ya ɓaci da ganinsa da tayi tare da Zahrah. Idonsa Zahrah ta fara ta yi mata gwalo, ai kuwa a hasale ta yo kan Zahrah za ta kai mata bugu, da sauri Zahrah ta ɓoye a bayansa sai kuma tace "Amma dai ke kam ba ki da hankali, mutum na tare da mijinsa kice za ki dake shi.?"
"Miji?" Rumana ta maimaita kalmar sau uku kafin ta farga sun yi gaba har sun kai bakin sashen Hajjaty. Takaici sosai ya cika ta ganin wannan yarinyar tana mata shigar sauri amma ta yi alƙawarin saitata.
Da sauri ta koma part ɗinsu lokacin Ammi na zaune a Parlour. Yanayin da ta ga Rumana yasa ta jefa mata tambayar "A'a ke lafiya?"
"Ammi ba lafiya ba" ta ba ta amsa "in dai har ba ku aura min shi ba wannan karan Babu wanda zan ƙyale, ya dawo gareni ne dama, shi kuma wancan dustbin ɗin Ishaq ɗin yace ya ƙarata, amma fa wannan kam dole na mallake shi."
Bayanta Ammi ta shafa tana faɗin "Ki dai taka a sannu Rumana, kin ga yanzu ba yi nake da uwarsa ba, amma dai inags sai dai kawai a yi mai kankat kowa ya huta."
"Gaskiya kam don Ni ba zan juri ganinsa da wannan figaggiyar Zahrahn ba, da alama soyayya suke har wani ƙiranta da matarsa yake."
"Mata kuma?" Ammi ta tambaya.
Fuska haɗe Rumana tace "E Ammi, shine abunda ya ɓata min raina ai, I can't hold it anymore, sati mai zuwa dolensa ya aure Ni"
"Dolensa!" Ammi ta maimaita cike da ƙwarin guiwa.
Few minutes Sai ga ƙira daga Mamie, labarin haɗa auren Ya Sadauki da Zahrah ta sanar da su, a hasale Ammi ta gimtse wayar tana faɗin "Wallahi ba zai yiwu ba, Sadauki mijin Rumana ne ko ba a so." Tsabar yadda masifa ke cin Rumana kasa naga tayi sai nuna bango take da yatsa, can dai tace "Ai kuwa dole a san abun yi, idan ba haka ba babu mai zama lafiya." Haka dai Ammi tayi ta ƙarfafa mata guiwa kan hakan.
Shigar su part ɗin Hajjaty suka tarar da Hajjaty da kuma Mamah zaune, a ɗan kunyance Zahrah ta ja gefe tana shirin wucewa bedroom nata, muryarsa ce ta dakatar da ita ta tsaya "Na yi missing girkin ki Lily, ko za ki iya haɗa min lunch?" Ba tare da ta juyo ba tace "ok" Sai kuma ta ajiye Little tana faɗin "Ka je wurin Mamah Little." Daga nan ta wuce kitchen directly tana mita wai daga zuwanshi zai ce abincinta yake so, da haka ta hanzarta tare da yi masa simple girki tunda Azahar tuni ya yi. Lokacin da ta fito ganin ba ya nan yasa ta jera abincin tare da wucewa bedroom nata tayi sallah, sallah tayi wacce ba ta taɓa yin kamarta ba, sosai ta yi wa Ubangiji godiya bisa tseratar mata da abun ƙaunarta da yayi, praying mat ta naɗe tare da rage kayan jikinta sannan ta faɗa wanka. Tana fitowa ta shirya a gaggauce tare da sanya kaya marasa nauyi saboda yanayi na zafi da ake.
Fitowa tayi don ta kira Nasreen da wayar Mamah sai dai cikin rashin Sa'a ba ta tarar da su Mamahn a parlour ba, fuska ta yatsina kamar ta ga kashi yayin da ta tunkari bedroom ɗinta gadan-gadan, karon da ta ci da mutum yasa ta ɗago da sauri.
"I'm sorry Yaya, ban kula kana zuwa ba ne."
Smile ne yayi escaping kan fuskarsa sannan yace "Kin gama girkin ne?"
Bakinta ta ɗan turo tana faɗin "Ni na gama mana"
Idonsa kan cute Lips nata yace "You know I'm not good in repeating words ko Lilyn Yaya?"
Kamar za ta yi kuka tace "Eh fa nace, Yaya da alama yanzu kam ba