Showing 72001 words to 75000 words out of 157517 words

Chapter 25 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5145

shiga ki yi wanka kafin a sanarwa Alhaji Baba da zuwanki ko?"
"Ke Zahrah kai ta bedroom 'dina,ba'kin kuma ki kai su naki kafin Laraba ta gyara musu wurin kwanansu" Kallon ba'kin tayi tace "Ku samu ku watsa ruwa sai ku ci abinci, Allah yasa dai ba da azumin kuka zo ba"

Murmushi Inna tayi tana kallo Hajjaty tana kuma yaba kirki da sau'kin kan Hajjaty tace "A'a ai da yake tafiyar mai tsayi ce shiyasa bamu 'dau azumin ba"
"Masha Allah, ku bi Zahrah ta 'karasa daku ko?" Hajjaty ta fa'da tana 'kwala kiran Laraba, ko da ta zo ta fa'da mata dalilin kiran sai ta wuce dining don taga me ya rage tunda ba a yi girki da su ba, an sha ruwa kuma in ta ce laraba tayi ita ma ta san ta gaji.

*MOMMAH*

Sosai wasu 'dabi'unta suka sauya sakamakon yadda rashin 'danta ya ta'ba ta, wannan hali na izza da kuma nuna isa duk babu shi, babu wannan rashin girmama manyan...haka dai duk ta koma ga ubangijinta, Sallah take tana addu'a babu dare ba rana ko Allah zai sa Daddy ya mayar da ita gidanta don nadama kam ta riga ta yi ta. A yau kuma ta kuduri aniyar tabbatar da maganar Hajjanta game da 'kawayenta wa'danda suka juya mata baya lokaci guda, kayan takaicin shine duk cikinsu babu waccetaga wulgwarta a rasuwar Yaya Sadauki, ta kuma 'kullace su za ta ji dalilinsu na 'kin ko da yi mata ta'aziyya ne.

Wannan kenan!

*React and Share please*
*For those who share, jazakumullahu khairan, Allah bar ni da ku masu 'kamshin humra.*


[1/23, 3:05 PM] Diamond Bhatool:








*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 3️⃣3️⃣




Tabbas cikin wannan family babu wanda suke having good time fiye da Ammie, amma wai ace har a mata rasuwa ba za ta iya kira ko a waya ta mata ta'aziyya ba? Meye amfanin abotar. A matu'kar raunane ta wuce part 'dinta na da tana share 'kwalla tare da fatan Allah yasa wata rana tana da rabon sake rayuwa ciki. A haka har ta iso part 'din Ammie. Da sallama ta shiga ciki amma bakinta kusan biyar tukun Ammie ta amsa, sarai ta gane muryar Mommah amma ta share, sai da ta shafe kusan mintuna biyar tukun ta aiko Afifa ta shigo da ita.

A dadda'kile suka gaisa don kuwa nunawa tayi kamar ba ta san Mommah ba, tarin mamaki da al'ajabi suka cika Mommah duk takaicin kanta ya kama ta. A da idan ta zo wurinta takan ka'da yaran 'dakunan su tukun ta fuskanci Mommah, amma a yau sai ta ha'de girar sama da 'kasa ta 'daura 'kafarta 'daya kan 'daya. Gauron numfashi Mommah ta sau'ke kana ta fara magana.

"Hajiya Saudatu wurinki nazo"
Fuska yatsine Ammie tace
"Ina sauraronki ai, kika zo me?"
Murmushin takaici Mommah tayi tace
"Hajiya Saudatu dama na zo neman wani taimako ne a wurinki, don Allah ina so ki ara min ku'di ne zan biya ki da zarar Junaid ya zo"
Wani malalacin kallo Ammie ta jefa mata tace
"Ku'di har nawa Sughrah?"
Mommah ta maimaita Sughrah cikin ranta, wai Hajiya Saudatu yau ita take ambaton sunanta gatsare babu wani girmamawa kamar ba ta fi ta ba? Kawar da tunanin tayi tace

"Million 'daya nace miki, in Allah ya yarda zan biya ki"
wata irin shewa Ammie ta saka tana dariya har da dafe ciki, sai da tayi mai isarta ta dakata tana ha'de fuska.
"Ke yanzu in na ara miki million 'dayar a ina zaki samu ki biya?"
"Na riga ma fa'da miki Hajiya Saudatu, Junaid zai zo bikin abokinsa nan da wata biyu, da zarar ya dawo zan baki ku'dinki"
"Hahahaha! Lallai kuwa! Wai zai zo biki, don yana 'kasar waje sai aka ce miki ni mahaukaciya ce zan 'dau ku'di na na baki, tab!"

Kallonta kawai Mommah tayi tace
"Haba Hajiya Saudatu, cikin gidan nan in baki bani ba waye to zai bani? Ki duba abotar da ke tsakanin mu ki kuma dubi tsananin bu'kata ta da ku'din ki bani, wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi"
"Toooo lallai Sughrah kin zo da bidi'a, har da wani wa'azi? To ki je masallaci ki hau mimbari sai ki yi musu, ke bari in fa'da miki mutum to mutum, ba zan bayar da bashin ba kuma ki tashi ki bani waje don kuwa babu wata ala'ka da ta rage tsakani na da ke, kada ki kuskura ki 'kara zuwa min gida, kin je kin kashe aurenki saboda son zuciya yanzu kuma za ki zo ki taya ni na kashe nawa? Wallahi ba ki isa ba, maza tashi ki bani waje, out!" Ta 'karasa a zafafe tana nuna wa Mommah 'kofa.

Jiki babu 'kwari Mommah ta mi'ke ta fara takawa Ammie na bin bayanta, sai da ta kai bakin 'kofa tace
"Kin ci amanar abota Hajiya Saudatu, na gode, sai kuma gani na gaba"
Harararta Ammie tayi tace "Eh maza dai fice ki bani wuri, dama can saboda tunanin za ki ha'da auren marigayin attajirin 'danki da Rumana ne, amma da na fahimci take-taken ki yasa na ja baya, can dama ni ba son ki nake ba, ku'din ki da na iyalanki nake so, yanzu tunda babu ko 'daya sai na kama gaba na, dalla can malama fice min a gida zan rufe." Ta idasa tana dakawa Mommah tsawa.

Murmushi Mommah tayi hawaye na zubo mata ta juya za ta wuce suka ci karo da Papa wanda da alama ya jima tsaye za ma a iya cewa ya ji kusan koma da suka yi, gaida Shi Mommah tayi for the first time, hakan yasa yaji banbara'kwai sai ya mayar mata da gaisuwar a maimakon ya amsa, daga Haka Mommah ta ra'bi gini ta fice abunta ta bar Papa da al'ajabin halin matar tasa yana tunanin dama can haka 'dabi'unta suke ne ko kuma dai a sama ta yafawa kanta. Da haka shima ya shiga ciki yana jinjina kansa.

Ko da Mommah ta bar sashen Ammie sashen Mamie ta nufa, a can dai ba a wula'kanta ta can ba amma an kashe mata warning na kar ta kuskura ko a hanya ta nuna ta san Mamie 'din daga 'karshe ta ba ta dubu biyar tace ga iya abunda za ta iya ara mata, tsabar takaici ko ku'din ba ta 'dauka ba ta nufi part 'din Hajiya Babba. Sosai ta samu kyakkyawar tarba daga Hajiya Babba ba tare da nuna mata wata 'kyama ba duk irin tsiyar kuwa da ta shuka mata a baya, bayan sun gaisa Mommah take tambayar Ina Aunty Mabruka. Nan Hajiya Babba ta gyara zama tace
"Ai Mabruka tun rasuwar mijinta shikenan ta'ki lafiya, kullum cikin razana take, da dare kuwa ta rin'ka gane-ganen abubuwa suna kawo mata farmaki, gaba 'daya dai ta koma kamar mahaukaciya tsawon satin nan."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una, ubangiji ya ba ta lafiya, ko zan iya shiga na duba jikinta?"
Hajiya Babba ta ba ta amsa da "Eh mana, muje na kai ki"
Bayan ta gaida Aunty Mabruka wacce ba kowa take ganewa ba ta dan'ka mata Atm card nata da ba ta ta'ba amfani da shi ba ta sa mata albarka tukun ta dawo parlourn. A nan ta tarar da Hajiya Babban, nan ta fa'da mata dalilin zuwanta. Fuskarta babu yabo babu fallasa tace "Babu komai Hajiya Sughrah, ki ba da account details 'din ba kuma sai kin biya ni ba, kyauta zan baki."

Baki sake Mommah ke kallon Hajiya Babba tare da jin wata irn kunyarta ta sau'ka mata lokaci guda, hawaye ne suka fara zarya daga idanun Mommah.
"Ya haka kuma Hajiya Sughrah?, meye na kukan kuma eh? Don Allah ki yi shiru kada yara su shigo suga kina kuka, zuciya 'daya na baki ku'din nan ba da wata manufa ba, ki 'dauke ni kamar 'yar uwarki Nasiba, don Allah ki bar kuka."

Ba tare da ta daina kukan ba ta dubi Mommah tace
"Dole zan yi kuka Hajiya Babba, kuka yanzu na fara shi tunda ba ni da hankali, na 'dau yadda ta ta duniya na dam'ka musu ashe ba 'kaunata suke ba, sun sa na bar gidan aure na ashe duk shiri suka min, ke da nake wa kallon abar 'ki yau ke kika yi min abunda wanda nake wa kallon masoya suka kasa, na yi asara ni Sughrah...."
Yatsarta Hajiya Babba ta 'daura kan bakin Mommah tukun tayi shiru.
"Ya isa haka Sughrah, kuka ba naki bane yanzu, ki godewa Allah da ya sa kika gane kuskurenki da wuri, yanzu sai ki san matakin 'dauka. Ki tattaro kuma ki dawo 'dakinki, dama saboda auren Sadauki ne kika tafi, yanzu sai ki dawo tunda babu shi, ki gyara abubuwan da kika 'bata."

Murmushin da yafi kuka ciwo Mommah ta saki kana tace
"Ba wannan bane Hajiya Babba, Daddynsu ya 'ki amincewa na dawo in na kira wayarsa ba ya 'dagawa, in na same shi a office nashi ba ya ko kallo na, Yaya zan yi ni Sughrah"
Hajiya Babba tace
"Kwantar da hankalinki in sha Allah za ki dawo 'dakin ki kwanan nan, ki dage da addu'a sannan kuma ki yi magana da Hajja, nima zan yi wa Alhaji Babba magana, da izinin Allah za ki dawo 'dakinki." Hawaye na zubowa Mommah tace
"Na gode sosai Hajiya Babba, don Allah ki yafe min duk rashin albarkar da na miki tsawon wasu shekaru masu yawa..


"Ya isa haka, komai ya wuce Allah ya yafe mana baki 'dayanmu" da "Amin" Mommah ta amsa. Daga haka ta fara shirin tafiya bayan Hajiya Babba ta mata al'kawarin gobe Ya Khalil zai je har gidan Hajja ya kai ta a bu'de mata sabon account sai a saka mata ku'din daga nan kuma tayi wa Hajiya Babba sallama ta fice zuciyarta wasai tana kuma 'kara yabon halin dattaku irin na Hajiya Babba.

Tana fita sai taji ya kamata tayi wa Hajjaty Sannu da shan ruwa duk da ba ta zo da komai ba, bayan sun gaisa da Hajjatyn fuska sake Hajjatyn ke bata labarin ai yau 'diyarta Madina ma ta dawo, yanzu za ta fito daga wanka ta jira su gaisa don Allah. A matu'kar 'kagare Mommah ta zauna don itama ta ji tana son ganin Madina don rabonta da ita tun marigayin 'danta yana yaro, Allah sarki ashe tana raye.

Few minutes da zaman Mommah sai ga Mamah ta fito daga bedroom 'din Hajjaty. A matu'kar zabure Mamah tace "Hajiya Sughrah!" Ita ma Mommah tace "Maman Zahrah! Ke ce Madina kuma? Ya akai ban gane ki ba a wancan lokacin?"
Mamah tayi murmushi tace
"Ke ma a nan kike aure kenan? Ki sanni can damah?"

Murmushi Mommah tayi tana fa'din
"'Kwarai a nan nake aure kin manta matar 'dan'uwanki Umar? Maman Junaid da Aliyu?"
Da kallon Mamaki Mamah ke bin Mommah sai a lokacin 'kwa'kwalawarta ta tuna da hakan
"Dama ke ce?, a lokacin da na fara ganinki a gidan Maman Badi'a na yi tunanin na sanki, amma iyakar tunani na na kasa tuna a ina, ashe dai matar 'dan'uwa na ne, Allah sarki duniya."
Murmushi Mommah tayi tace
"Nima da naga fuskarki a lokacin na fa'dawa 'yar'uwata cewa kamar na san ki, tace ai sai dai mai kama da ke saboda lokacin ne karo na farko da na fara zuwa Bauchi."
"Ikon Allah, ashe dai da rabon za a 'kara gamo" sai kuma suka rungume Juna tunisuka manta da Hajjaty.

Saia lokacin itama ta farfa'dodaga sumar zaune da tayi tace
"Sughrah? kin ta'ba ha'duwa da Madina ne bayan rasa ta da aka yi?"
Zama Mommah tayi tace
"'Kwarai kuwa Hajjaty, kin san 'yar'uwata Kubra dake Bauchi, a can naga Madina, nima iyakar 'ko'kari na na ganin na gano fuskar na kasa, ashe haka ita ma a nata 'bangaren, Allah sarki"
Hajjaty tace "Ikon Allah, Allaj mun gode maka."

Sallama Mommah ta musu ta wuce, sai bayan tafiyarta Mamah ke tambayar Hajjaty Mommahn ta bar gidan ne? Nan tace mata ai dogon labari ne, in ta gama hutawa za ta bata labarin komai da ya faru a gidan. Da haka Mamah tayi shiru da batun bawan Allahn da aka ce ya rasu zuwa gobe ta yi tambayar. Daga nan Hajjaty ta kai ta wurin Alhaji Baba, sosai aka 'kara bu'de wani shabon shafi na kukan farin ciki daga nan kowa ya nemi makwancinsa.


*WASHEGARI*

Sai da aka idar da sallar maghrib Alhaji Baba yakawo musu zancen dawowar Mamah, a lokacin dukkansu suka 'dunguma wai za su je su ganta sai kace wasu yariya, murmushi irin na manya Alhaji Baba yayi yace
"Kul! Ban ji ba ban yadda ba, kwa bari gari ya waye dai ko?" Kansu 'kasa suna murmushi suka ce to shikenan.
Da misalin 'karfe 7:00am sai ga Daddy ya zo, idan baku mance ba Daddy na matu'kar 'kaunar 'yar'uwar tasa sai dai zuwansa har su Hajjaty babu wanda ya tashi, hakan yasa ya wuce office nasa ba tare da sun ha'dun ba, sosai yake jin da'di da bayyanarta, kuma ta bayyana a lokacin da ake bu'katarta ne, suna cikin jimamin rashin Yaya Sadauki kuma sai ga ta, Allah ya 'dauke ya kawo kenan.

Haka sauran 'yan'uwan nata duk suka fice wuraren ayyukansu ba tare da sun sa ta a idanuwansu ba. Ba su kuwa suka tashi ba sai wuraren 10am coz babu laifi sun sha gajiyar hanya, abuja to bauchi a cikin mota ai dole a jijjiga. Bayan an gaisa da juna, Zahrah ta ja Asma'u da Balkisu cikin sauran 'yan'uwanta su ma suka ja gefe suna hira, tun ba sa magana har suka saki baki suka fara.

Su Mamah ma hirarsu suke yi da Inna da kuma Hajjaty, Yaya Khalil ne ya shigo gaisuwar safe, yana 'karasowayaci karo da Mamah, shaye da mamaki yake kallonta, can dai yace "Ina yini Mommy Madina"
"Lafiya lau" ta amsa masa fuska sake.
Hajjaty ce ta 'dan ha'de rai tace
"Ban gane ba Halilu, yau saboda ka ga uwarka shine ka manta da zamana har sai da ka gaishe ta? A hakan ma mu da alama ba za ka gaishe mu ba"
kunya ce ta kama Yaya Khalil yace
"Haba Hajjaty kya tsaya dai in gama da sabon hannu, ke kam ai....."

Hannun da ta mi'ko kamar za ta kwa'de shi ne yasa yaja baya yana dariya, gaba'dayansu suka saki dariyar suma, gaishe da Hajjaty da Inna yayi kana ya wuce corridorn da zai sada shi da 'bangaren tsoho mai ran 'karfe. Bayan sun gaisa da Alhaji Baba haka ya sako shi gaba wai sai ya fito sun yi hira da 'yarsa don ga can Hajjaty ta ma'kale ta kamar ita ka'dai ta haife ta, sosai Alhaji ya dara jin shiriritar Yaya Khalil, daga nan suka fito tare, Yaya Khalil yayi wa Mamah Sallama daga nan ya wuce office shima.

*React and Share Lillah, for those who share, Alkhairin ubangiji ya kai ku.*

[1/27, 5:41 PM] Diamond Bhatool:











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 3️⃣4️⃣




Bayan Alhaji Babba ya fito suka 'kara gaisawa da Mamah, tare suka ci gaba da hirarsu, a nan ne ma Mamah take ba su labarin wadda suka yi waya ranar da shi kan zai zo su taho ranar da aka 'dauki azumi amma shiru har ta zo da kanta.

Hajjaty tace
"Dama cikin gidan nan akwai wanda yasan yadda kike ne?"
gyara Zama Mamah tayi tace
"Akwai dai wanda yake aikin bincike a jikokin gidan don ya yi kama sosai da Yaya Umar..."
Hajjaty ta dakatar da ita da fa'din
"Wai kina nufin marigayi Sadauki ya san yadda kike?"
"Ban gane marigayi ba kuma Hajjaty, nace miki ana gobe za a 'dau azumi mun yi waya da shi kan cewa zai zo mu tafi tare washegari, to dai shiru da shi da wani shima jami'in duk ban 'kara jin 'duriyarsu ba."
Hawaye Hajjaty ta share tace
"Allah sarki, shi 'din ne dai...Sadauki ne, ashe dalilinki ya tafi Bauchin ma, Allah ya masa rasuwa ne a ranar amma ta taho."

A 'dan zabure Mamah ta kalli Hajjaty, Hajjaty tace "Kwantar da hankalinki...." nan ta ba ta labarin komai daga tafiyarsa ba tare da kowa ya san dalilin tafiyar ba, zuwa riskar labarin rasuwarsada tashin hankalin da suka shiga."
Allah sarki Mamah a lokacin taji 'kaunar marigayin ta kama ta, nan ta sha kukanta ita ma ta share tare da yi masa addu'a. Ba a jima ba kuma Drivern Hajjaty da su Inna suka hau hanyar Bauchi bayan goma sha tara ta arzi'ki da aka ha'da su da shi, suna godiya tare da ba'kin cikin rabuwa da Mamah suka wuce. (Safe trip Inna da jikokinta)

A 'bangaren Aunty Mabruka babu laifi zuwa yanzu ta fauwalawa ubangiji komai, ta koma ga Allah tana mi'ka al'amuran ta gaba'daya gare shi, tana kuma addu'ar Allah yayi wa mijinta rahama. Ko da ta riski labarin zuwan Mamah a wurin Hajiya Babba tace itama za ta je yau su gaisa tunda ba ta ta'ba ganinta. Hajiya Babba ba ta hana ta ba amma ta sa Humairah ta raka ta har part 'din Hajjatyn wacce a yanzu duk ta risina ita ma.

Ko da Aunty Mabruka taje sosai sabo ya samu a tsakaninsu kamar sun san juna da da'dewa, a 'bangaren Mamah tunani ne fal a ranta musamman da aka ce mata ita ce matar marigayin. Ba Aunty Mabruka bace ta tafi sai wuraren la'asar, bayan ta yi wa Mamah Sallama ta wuce tana fa'din za ta dawo in an sha ruwa. Sosai Mamah taji da'di da wannan sakewa da Aunty Mabruka tayi da ita Zahrah kuwa duk takaici ya cika ta saboda rashin samun time 'din Mamah,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login