Showing 129001 words to 132000 words out of 157517 words

Chapter 44 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5167

ya ƙarasa kusa da ita yace "Zaujaty" kamar ba ta ji ba tayi shiru, ba tare da ta sani ba kawai ya kai kansa saitin fuskarta da ta rufe idanunta gyam, ƙamshin da ta kiyo yasa ta tabbatar he's near her Amma ko kaɗan ba ta kawo komai a ranta ba, tunaninta dai may be zai tayar da ita ne, daidai chin nata ya sauƙe mata kiss, ai ba shiri ta miƙe zaune a zabure, murmushi yayi yace "Ashe baccin bai yi nisa ba." Kanta ƙasa tana tura baki tace "Shine za ka tashe Ni?" A ɗan shagwaɓe tayi maganar fatanta dai ya barta ta kwanta.
"Shine ba za mu yi salla mu godewa Allah ba?" Ya aika mata tambayar yana kokoyon yadda tayi Tata maganar.


*React and share fisabilillah.*

[28/04, 7:58 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:

*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 6️⃣1️⃣





*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*


Kwaɓe fuska tayi tana kai masa dukan wasa "Allah ba na so, ai zan yi" ta ƙarasa a shagwaɓe tana ƙara mamakin Yaya Sadauki, "is he that stubborn?" She asked herself.
Dariya mai sauti yayi wacce ta ƙara masa kyau, hakan yasa ta shagala da kallonsa.

"Dare ya yi, na san babu abinda kika ci yau, wurin dinner ɗin ma You refused to eat, o ya now sauƙo ki ci." Kamar za ta yi kuka tace "I'm satisfied Yaya" cikin kausasa murya yace "i said get down, don't let me repeat myself " turo bakinta tayi tare da fara ƙoƙarin tashi sai dai kafin ta tashin har ya miƙe ya ɗago ta a hannunsa kamar wata Little baby. Mutsuniya take tana son ƙwacewa sai duka take kai masa. Cikin ransa yace "She's damn stubborn." Duk yadda taso ya ajiye ta ƙi yayi, a daidai gin da ya aje kazar ya sauƙe ta sai harararsa ta ƙasan ido take tana tura baki. Slowly yace "Za ki yi bayani, Ni kike turawa baki ko Lily?" Ƙara tura bakin tayi don ya riga ya zama mata jiki ƙasaƙasa tace 'Ni ba da kai nake ba.'
Agogon bango ya duba without minding her yace "it's past 1, ba na son rigima, samu ki ci mu kwanta, I'm sleepy." Da haka ta fara cin kazar kamar ba ta so yayin da duk wani motsi nata kuma yake a idanunsa. Tana ci har ta ƙoshi sannan ya zuba mata youghurt a cup ya miƙa mata, amsa tayi ta sha daga nan ta furta "Alhamdulillah... Where's the kitchen? Bari na kai plate ɗin."
"No, Na hutar da amarya, just get in, I'll be coming." Gabanta ne ya faɗin jin yace he will be coming, a haka ta fara takawa har tana harɗewa shi kuma ya bi ta da kallo har ta shige. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya kwashe komai zuwa kitchen daga nan ya bi bayanta zuwa bedroom ɗin.

" O ya! Let's pray, ki yi alwala ina jiran ki" tsintar kanta tayi da tambayarsa "kai ɗin ka yi?"
Kai kawai ya gyaɗa mata, hakan yasa tace "Nima ai na yi" a gajarce yace "ki ƙara wata" sauƙowa daga bed ɗin tayi tare da nufar toilet. Alwala ta ɗauro ta fito lokacin har ya shimfiɗa musu abun sallah, tare suka jera sannan ya tayar da Sallah. Raka'a biyu ya ja su kamar yadda ma'aiki ya koyar, bayan sun sallame ya kama goshinta ya karanta

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ

Allahumma inni as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha ‘alayhi, wa a’udhu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha ‘alayhi.

Ma’ana: Ya Allah! Ina roƙonka alherinta da alherin abin da Ka halicce ta a kai. Kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin da Ka halicce ta a kai.

Daga haka ya mata wasu tambayoyi game da addini and she responded to her best, Bai wani yi mamaki ba sanin dama tana kula da Addini sosai. Daga haka suka ɗan yi shiru, can yace "Ki je ki kwanta Lily, naga sai lumshe ido kike" ba tare da ta ba shi amsa ba ta tashi ta nufi bed ɗin ta kwanta can ƙarshe, praying mat ya naɗe tare da kai dubansa gare ta, smile ne yayi escaping kan lips nasa, cikin ransa yace "ba za ta girma ba, I'm doing nothing for her." Yana ajiye praying mat ɗin ya nufi bed ɗin shima ya haye. Tana jin ya hau ta ƙara takurewa wuri guda hakan ya so sa shi ya dara, da ƙyar dai ya riƙe dariyar tasa. Addu'o'in bacci ya karanta ya shafa jikinsa sannan ya shafa mata itama. Ajiyar zuciya ta sauƙe lokaci guda tare da lumshe idanunta tana ayyana kasantuwar wannan dare a rayuwarta, jin ya janyota yana ƙoƙarin raba ta da Hijabinta yasa ta fara mutsuniya, a hankali ya furta "I'm doing nothing to you, just wannan hijab ɗin zan cire miki, it's hot."
"Hot?" Ta maimaita cikin ranta, duk wannan sanyin ACn yake kira da zafi?"

Ba ta ankara ba taji ya cire mata hijab ɗin, Yaya za ta yi? Tuƙunƙunewa wuri ɗaya ta ƙara saboda night wear ɗin da ta sanya ba su cika girma ba kuma suna showing sosai. Wani irin yawu ya haɗiye tare da kau da kansa gefe sannan ya janyota tana ƙwacewa har ya mannata a jikinsa ta yadda sukan iya jiyo sautin numfashi da bugun zuciyar junansu, lafewa Zahrah tayi a jikinsa tare da shaƙar daddaɗan ƙamshi da ke fita daga jikinsa tana mai lumshe idanunta, a nashi ɓangaren shima wani irin yanayi ya shiga mai wuyar fassara sai dai alƙawarin da yayi na cewa ba zai mata komai ba yasa yayi ƙoƙarin danne komai, cikin kunnenta ya raɗa mata "Sweetest Dreams Zaujaty, make sure kin yi mafarkina coz da safe zan miki tambaya." Ya ƙarasa in a cooler voice, daga haka ya ƙara mannata da jikinsa tare da amfani da ɗaya hannunsa ya kashe bedside lamp, a haka bacci ya ɗauke su cikin so da shaukin juna.

(Sweetest dreams amarya da ango)


*DEVIL 😈 KLANS*

"A haƙikanin gaskiya muna gaɓar barazana, muna gab da rasa ikon mu, ku tashi shaiɗanu...ku tashi tsaye mu dawo da martabar mu." Ɗaya daga cikin membobin kungiyar ya faɗa, "idan har ba mu tare abinda ke faruwa ba a yanzu, ina ji a jiki na abokan gaba za su iya galaba kan mu..."
Bai ƙarasa ba uwargijiya ta dakatar da shi "Gutsurito forbid, ka daina jawo mana bala'i Nwanna, DEVILS KLANS will never fall, dole mu yi sadaukarwa ta musamman matsawar muna buƙatar martabar mu ta dawo, kowa ya shirya, daren gobe mu gabatar da ibada, ki shirya."
"Gaskiya kam, ba zai yiwu ace ko buri ɗaya ban cika ba cikin wannan tafiya, dole mu zamo masu power fiye da tunani, fansarki, fansata duk sai mu ɗauka mun kuma ɗaukaka a duniyar matsafa."
"Da izinin Gutsurito dodon tsafi."
Madubin tsafi uwargijiya ta kawo gabanta sannan ta fara karanto wasu dalasimai, cikin ƙanƙanin lokaci wasu dunƙulallun haske guda biyu suka bayyana, a tsorace ta miƙe tana dafe ƙirjinta, hakan yasa sauran members ɗinsu buɗe nasu maduban a gabansu, Abunda suka ga suma sun tsorata. Sai dai ta sarara tukun ta ƙara zama tare da ƙara karanto dalasimai sai dai abu ɗaya, a matuƙar fusace tace "Sai na sadaukar da waɗannan haske biyu da suke kawo min cikas, dole na san su waye su, ba zan juri rasa muƙami da matsayin ƙingiyarmu a duniyar tsafi ba." A haka dai har aka tashi a meeting ba su gano waɗannan haske ba, hakan yasa suka watse a hasale.

*MORNING*

Sosai suka sha baccinsu, lokacin da bedside clock ya buga alarm hannu kawai yasa ya kashe sannan suka ci gaba da baccinsu. Ba su suka tashi ba sai wuraren seven, shima hasken ranar da ya ɗan hasko ta wurin da aka janye labule ne. A hankali ta fara buɗe idanuwanta har ta buɗe su tas akan wall clock, zaro idanuwanta tayi ganin seven har ta gota, jinta a jikinsa yasa ta ɗan lumshe ido tare da fara ƙokarin zamewa ta miƙe sai dai kuma ya riga yayi crossing bayanta da hannunsa, babu yadda ta iya ta san sai ya tashi tunda a manne suke sosai. Hannunta tayi ƙoƙarin jawowa, jinsa manne a ƙirjinsa yasa ta zaro ido waje tare da buɗe baki. "Ya Ilahy" ta furta a hankali. A ƙoƙarinta na raba hannunta da jikinsa yasa ya buɗe kyawawan idanuwansa a kanta, saukar da kanta ƙasa tayi ganin hakan, murmusawa yayi ya ƙara mayar da idanuwansa ya lumshe.
"Yaya...rana fa tayi, ka tashi shine ka koma?" Ta faɗa tana turo bakinta gaba. Bai kula ta ba sai da tace "we didn't pray and lokaci ya wuce, Please..."

Ba ta kai ga ƙarasawa ba ya buɗe idanuwansa yana mai ƙoƙarin janye hannayensa daga bayanta, sarai ta lura da shi ko kunyar hakan ma bai ji ba, kanta ta kawar gefe jin ya sake ta, tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙo hannunta.
"Ba za ki jira Ni ba ne?" Kwaɓe fuska tayi shi kuma bai sake ta ba har sai da ya miƙe shima. Sauƙa tayi shima ya sauƙa, toilet ta nufa jin footsteps nasa yasa ta juyo tana kwaɓe fuska tace "ina ne za ka?" Sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Toilet mana?"
"To ai na riga ka kuma" ta faɗa a shagwaɓe
Amsa ya ba ta da "ba ki ga lokacin sallah ya wuce ba, mu je mana."
Baki ta ɓare tare da sakin kukan shagwaɓa wanda yayi sanadiyyar jefa shi cikin wani yanayi, numfashi ya sauƙe tare da juyawa ya fice don ya ba ta wuri ta yi alwalar shima ya tafi yi a ɗaya bedroom ɗin.

Towel guda biyu ta gani sabbi hakan yasa ta fara yin wanka, brush tayi sannan ta ɗauro alwalarta. Ɗaure da towel ɗin ta fito wanda ba zai wuce iya guiwarta ba, fitowar ta yayi daidai da shigowar Yaya Sadauki, ba shiri tayi diri-diri kamar za ta yi kuka ta juya masa baya. Duk da cewa ta sanya shi cikin wani yanayi hakan bai hana shi darawa da yadda tayi reacting ba. Ba tare da ya kula ta ba kawai ya shimfiɗa praying mat ya tada sallah, kabbararsa tasa tayi saurin ƙarasawa jikin closet, wani ɗan ƙaramin switch ta danna, take ya buɗe, kaya ta gani jere hakan yasa ta murmusa, da sauri ta fara duba wanne za ta saka, tsawon mintuna tana tsaye tana duba wanne kayan za ta saka, ta ma manta cewa ba ta yi salla ba, har ya idar tana tsaye tana duba kaya, daga ƙarshe dai ta janyo wata atamfa super mai milk da coffee brown, so take ta ɗauki undies sai dai ba ta ga ta ina suke ba, ta buɗe closet ɗin ɗaya bayan ɗaya amma ba ta gani ba ga shi kuma Allah Allah take ta ɗauko kafin ya idar sallar ta saka. Hannunsa ta gani ya kai can saman closet ɗin, me za ta ga ya ɗauko? Pants ne da bras, vest da kuma undie skirt. Idanuwanta ta zaro tana mamakin ta ya aka yi yasan yadda suke? Kamar ya san me take saƙawa a ranta yace "Ni na jera kayan, ki shirya lokaci yana ƙurewa."
Da "Toh" ta amsa tana mai sunkuyar da kanta ƙasa, juyowa tayi amma ba ta bari sun haɗa ido ba ta amshi abinda ya miƙo mata, yunƙurin komawa toilet tayi don ta saka kayan ya dakatar da ita da faɗin "Where do you think you are going? Lokacin Sallah yana wucewa."
Kame kame ta fara "ehmn e Dama eh zan je toilet..."
"Ki je ki yi me?, ki saka a nan ina jiran ki"
Yadda yayi maganar in an authoritative way yasa ta sha jinin jikinta, ƙwalla ce ta fara Zubo mata yayin da ta fara ware kayan za ta saka.

Kan Stool ɗin dressing mirror ya zauna tare da juya mata baya, ganin hakan yasa ta fara ƙoƙarin saka undies ɗin a gaggauce cikin Sa'a har ta saka bai juyo ba. Half bubu ne ɗinkin sai straight skirt, sosai ya amshi jikinta kamar a jikinta aka ɗinka. Tana gamawa ta janyo hijab ɗinta na Jiya ta saka sannan ta hau kan abun sallar, har ta tayar bai kalleta ba, numfashi ya sauƙe tare da ficewa waje ya bar ta tana sallar.


*Share and comment fisabilillah.*

[29/04, 3:36 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋: *Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 6️⃣2️⃣





_Gabaɗays shafin sadaukarwa ne gare ki Sa'adatu Abdullahi.... alkhairin Ubangiji ya kai gare ki._
*Ga waɗanda ke buƙatar book 1, book 2 zuwa yadda muka tsaya, kindly follow my whatsapp channel ko ku tuntuɓe ni ta wannan layin: +2349136050040*

Har ta idar da sallar bai dawo ba, hakan yasa ta naɗe praying mat ɗin ta ajiye daga nan kuma ta koma ta sakawa ƙofar lock, gadon da suka kwanta ta fara gyarawa sannan ta fara ƙoƙarin cire kayan da ta saka. Tas ta cire su don ita ba ta ji daɗin yadda ta saka ba tunda ba haka ta saba ba, mayukan da ke jere kan mirror ɗin ta shafa sannan ta mulke jikinta da man turare, daga nan ta mayar da kayanta. Sumarta ta gyara tare da shafa mai, sannan ta fesa turaren kai, kwali ta ɗauko tayi simple ɗaurin da ta iya na A'isha Buhari, tana gama ɗaurawa ta ta ɗauko turaruka ta feshe jikinta da shi take ɗakin ya cika da ƙamshinta.

Ƙoƙarin barin gaban dressing mirror ɗin take taji knocking ɗin ƙofar, da sauri ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, turus tayi tana kallonsa haka shima dai kallon nata yake kowa da abinda ke ransa. Duk irin ƙamdhin da take wanzuwar sa ta sa nasa ya kwantar da nata ƙamshin. Lumshe idanunsa yayi yayin da ya janyo ta jikinsa yana shaƙar daddaɗan scent ɗin jikinta, ba tare da itama ta sani ba tayi hugging nasa, tsawon wasu sakanni suka kasance a hakan kafin ya sake ta har lokacin kuma idanuwansa na kanta, ita dai kunya ce ta lulluɓe ta, tana ƙoƙarin juyawa taji ya riƙo hannunta
"You look so adorable Zaujaty..."
Ba tare da ta juyo ba ta amsa mai "You're looking more handsome Yaya, ka yi kyau kamar na ɓoye ka."

Ƴar ƙaramar dariya yayi yana ƙoƙarin turning nata ta kalle shi.
"Really?"
"Uhm" kawai tace
"O ya turn your head, look directly in to my eyes ki faɗa min, in kin faɗa min zan yadda ki ɓoye Ni as you sai"
Da sauri tace "da gaske?"
Shiru ya mata tare da sakin ta, wucewa tayi zuwa bakin bed ta zauna shima ya ƙarasa wurinta.
"Ina za ki je kuma kika dawo?"
"Ina son naje kitchen ne, I want to prepare something for you."
Hanjinta ya ja yace
"Kada ki damu, Hajiya Babba ta ce za a kawo ai, Ni kin ma gaida Ni kuwa Lily?"
Rau-rau tayi da ido tana kame-kame
"To ..to ba kai ne baka zauna ba?"
Cike da kokoyon muryarta yace "To to shine ba za ki gaida Ni ba?"
Fuskarta ta kwaɓe tana shirin kuka, zama yayi gefenta yace "Sorry Lilyn Yaya, saboda mun kwana wuri guda shine kika samu damar raina Ni ko?" Ya yi maganar sounding so intensed. A ɗan shagwaɓe tace
"I'm sorry Yaya, ba haka bane, ina kwana?"
"Ban gan shi ba"

"Good morning."
"Morning..." Doorbell da aka taɓa yasa ya miƙe da sauri, can bayan fitarsa ya dawo hannun shi ɗauke da basket ɗin abinci. Bai koma bedroom ɗin ba ya jera abincin a dining sannan ya kirawota, ita tayi serving ɗinsu a plate ɗaya sannan yace mata spoon ɗinma they should share one. Bayan sun karya ne tace mishi za ta duba gidan, bai hana ta ba sai ma wucewa ciki da yayi don ya shirya saboda kiran da Yaya Khalil ya masa.

Sai da ta ga ya shige ta fara kallon ko ina na ɗakin, tun daga ginin, paint zuwa kayayyakin da aka zuba a Parlourn ya tabbatar mata da an kashe kuɗi, ƙwalla ta share a fili tace "Allah sarki Yayana, na san wannan duk aikinka ne, Allah ya yi maka albarka."
Haka ta rinƙa bin komai da kallo tana dubawa, tana gamawa da parlourn ta wuce kitchen ɗin da ke parlourn....sosai nan ma ta yaba shi saboda irin kayayyakin zamani masu tsada da aka zuba ta. Gajiyar da tayi yasa ta fara ƙoƙarin komawa ciki, karo suka ci da shi yana amsa kira, hakan yasa ta ja baya a hankali.
"Ok, I say just wait for me outside ba sai kun shigo ba "
Me aka ce oho ya amsa da "Kai fa Khalil...Hmm. ga Ni dai zuwa." Daga haka ya yi ending call ɗin. Kallonta yayi yace
"Sorry Zaujaty, suna waje suna jirana, ki kula min da kanki, sai na dawo.."
Cikin sanyin jiki tace "To Yayana, Allah ya kiyaye, ya dawo da kai lafiya."
"Amin" ya amsa mata, har zai wuce ya dawo yayi kissing forehead ɗinta tukun ya bar gidan.

Tafiyarsa ke da wuya su Aunty Salmah da Aunty Na'ima suka zo, babu jimawa sai ga Nasreen ma. Ba a jima ba mutane suka fara zuwa yayin da wasu ke tafiya. Ba su Aunty Salmah ne suka tafi ba sai around 1pm bayan sun yi ma Zahrah sabuwar lecture tunda suka fahimci har yanzu akwai duhun kai tattare da ita, wasu turaruka Aunty Na'ima ta ba wa Zahrah irin nasu sannan tayi mata bayanin yadda za ta yi amfani da su, daga nan suka mata sallama suka wuce.

Bayan wucewar su Nasreen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login