Showing 114001 words to 117000 words out of 157517 words
da zai yi tare da wargaza auren, mun kuma yi mun gama amma wallahi ka ji na rantse ba za mu yi mata ci gaban aikin ba."
Har dai safiya ana abu ɗaya, sai da Azahar tukun aka samu ƙullin kan Ya Ishaq ya sace, duk wani siddabarun da ke tare da shi ya baje, daga nan kuma sai bacci.
A can gidan Mom kuma da yamma su Mommah da Aunty Madina, Aunty Salmah da kuma Aunty Na'ima suka dawo da lefen da aka kai musu amma Mom ta tubure tace ba za a karɓa ba. Da suka matsa ma cewa tayi "Gaskiya Ni ba zan karɓi kayan nan ba, ku yi haƙuri ku koma da su, mu ɗauki ƙaddara don Allah, ko babu wannan batun Ni mai iya ba wa Zahrah kwatankwacin su ne tunda yarinyar ba ta da laifi, ku ƙara ba da haƙuri a madadin Ishaq in sha Allahu za mu zo when everything is settled." Ba su yadda kuwa sun tafi da kayan ba sai da suka ƙira Hajjaty suka samar da ita tace babu komai su dawo da su, rabon Zahrahn ne.
*Ya Ishaq*
Sosai ya ware kamar ba shi ne Jiya aka fita da shi kamar gawa ba sai dai kuma akwai yanayi na damuwa akan fuskarsa. Bayan shawarwarin da Imam ya ba shi akan kula da azkar da kuma yadda da ƙaddara nan suka yi sallama Dad ya dawo gida da su. Tun da suka tunkaro gate ɗin giɗan yake jin faɗuwar gaba wacce bai san ta mece ce ba, bayan sun shiga ba su tarar da mom a parlourn ba ta shiga wanka. Dalilin nan yasa Dad ce masa shi ma yayi su wuce mosque, in sun dawo zai ga Mom ɗin nasa. Hakan ne ta faru sai da suka dawo daga masallaci ta fito lokacin har ta shirya itama tayi Tata sallar, kamar ba komai ta tarbe su musamman Ya Ishaq wanda kallo ɗaya in ya mata suka haɗa ido sai yaji kamar ya mata wani laifin. Kyakkyawar dinner ɗin da ta shirya musu da kanta tayi serving ɗinsu suna ci suna santi. Sai da suka gama suka koma parlour gaba dayansu suka zauna.
Ya Ishaq da ya gaji da danne abunda ke damunsa ne yace
"Mom, ban ji kina batun amarya ta ba, ko dai ba ku ɗaukota ba saboda ba Ni da lafiya?" Banza Mom ta masa, hakan bai sa ya ja bakinsa yayi shiru ba ya ƙara cewa "Mom kin yi shiru dai, Nikam gaskiya zan je na ɗauko kayata tunda ku ba ku buƙatarta, ai na riga na warke, U see Mom, I can drive." Ya faɗa yana miƙewa yana ƙara duba jikinsa, sosai tausayinsa ya kama zukatan iyayen nasa, sai dai ba su da wani ƴancin da ya wuce su bayyana masa gaskiya.
"Moooooom" ya faɗi sunan yana ja da ƙarfi "Dad kace Mom ta kula Ni, ko na mata wani abu ne ?"
Murmmushin yaƙe Daddy yayi yana faɗin "Ni ba zan shiga tsakaninka da sweetheart ɗinka ba a jima ku ba Ni kunya."
"Shikenan Dad, to ka ce ta min magana."
Dad yace "Mom wai ya ce ki masa magana."
Dariya dukkansu suka yi including Mom da ita kaɗai ta san me ke damunta, damuwarta ba ta wuce rashin sanin a wane irin ma'aunin Hankali Ishaq zai ɗauki al'amarin sanin yadda ya mutu kan ya auri Zahrahn.
Dad da ya lura da hakan ne ya fara ba su labaran nishaɗi suna dariya, ya yi hakan ne kuma don ya kawar da tunaninsu, shi dai dama a son ransa baya so baragurbin ƙwannan ya fashe musu da dare don ya san cewa akwai tashin hankali. Hira sosai suka yi har wajajen 10:30pm na dare, shi dai Ya Ishaq dannewa kawai yake amma zuwa yanzu ya riga ya fahimci cewa something fishy happened or is gonna happen shiyasa iyayen nasa suke wani beating around the bush.
Cike da ƙosawa yace "Mom, Please joke apart." Ya faɗa sounding more serious
"Jikina yana ba Ni cewa I've done something bad, na yi tunanin na ƙara amma ba na iya tuna komai, don Allah ki faɗa min laifin da na miki, na san cewa ba haka kike ba."
A gajarce tace "Ba komai Son"
"This is not my Mom gaskiya" ya faɗa yana jinjina kai
"Ba haka Mom ɗina take ba, Please feel free ki sanar da bugun zuciyar ki laifin da ya miki kike fushi da shi."
Cikin rashin son magana tace "Did I tell U so? Na ce maka ina fushi da kai ne?"
"Yes!!! Nooo, you didn't but your face shown that, kinga help me and stop beating around the bush, ki faɗa min."
Murmmushin yaƙe Mom tayi tana kallon Dad da ya naɗe hannunsa a ƙirji
"Seriously my baby didn't offended me, ko ya yi ma na yafe."
Side hug ya ba wa Mom tare da faɗin "Yauwah Sweetheart, to yanzu ki faɗa min ina kika ajiye min matata, na san an kawo miki ita, tana bedroom ɗinki?"
Da kai ta ba shi amsa, "To ina kika kai ta? Dad kace ta fito min da matata" ya faɗa yana kwaɓe fuska.
"To Daddy's boy, Mom ki fito masa da matarsa."
"Yauwah Dad, I love U, Mom kin ji me Dad ya faɗa ai."
"Na ji, shiyasa zan faɗa maka gaskiya."
Gabansa ne ya ba da sautin dumm, hakan yasa ya nutsu don jin me Mom za ta ce sai dai wa'azin da ta fara masa yasa ya ce "Mom..." Fuska a shagwaɓe.
Ba ta saurare shi ba sai da ta gama nasiharta, Dad ma ya ɗaura da ta sa. Daga nan Mom tace
"Duk abunda kaga baka samu ba, to Allah bai rubuta cewa rabon ka bane, sau tari za ka ga muna son abun, amma sai Allah ya hana mu abun saboda sharri ne abun gare mu, abunda muka ga ba ma so Ubangiji ya ba mu mu yarda kawai cewa alkhairi ne garemu."
Ajiyar zuciya ya sauke yana duban Mom ɗin "Na fahimce ki Mom, amma ban san ina zancen ki ya dosa ba ke da Dad, akwai abunda kuke son faɗa min, kawai ku faɗa min kun ji."
Shiru suka yi na wani lokaci kafin Dad ya fara magana
"Kamar yadda ka buƙaci sani...yanzu ai daga gidan Imam Nasir ka ga muke ko?" Nodding kansa Ya Ishaq yayi shi kuma Dad ya ci gaba "Toh Dad's boy kai ne ba ka da lafiya, akwai wani al'amari da ya faru da kai...." Nan ya kwashe komai tas ya sanar da shi, kafin ya ƙarasa tuni jikin Ya Ishaq ya jiƙe da zufa ya rasa ina zai sa kansa yaji daɗi. Sai da Dad ya gama faɗin abunda zai ce tukun Ya Ishaq ya fara magana cikin karyayyar muryarsa da ke tsananin bayyana karayarsa
"Shikenan Mom?, Dad? Na rasa Zahrah kenan forever? Ba zan rayu babu ita ba, ko ma waye ya aure ta dole ya sake min ita domin ita ɗin tawa ce Ni kaɗai."
"Ka manta abunda na faɗa maka cewa kai da kanka ka ƙi aure? A gaban iyayenta ka ce kai ba ka buƙata su kai gaba, to a lokacin da wa Shureim zan karɓawa auren sai ɗan'uwanta ya karɓa. Saboda haka kawai ka rungumi ƙaddara, who ever is behind separating you from your choice God will not leave him for granted, ka yi haƙuri Son, be courageous please, ka yi imani cewa Ubangiji bai ƙaddara cewa matarka ba ce ita ɗin, rabon wancan ɗan'uwanta ɗin ne."
Hawayen da ya kasa tsayarwa daga sintiri daga cikin idanuwansa ya goge tare da haɗiyar wani abu mai ɗaci da ya tsaya masa a maƙoshi, magana yake son yi amma ba shi da ƙwarin guiwar yin hakan.....
*React and share please*
Diamond 💎 Bhatool 🦋
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 5⃣5️⃣
﷽
Aikin rarrashi su Mom ke yi da ƙyar dai ya iya shiru amma sam ba ya jin ƙarfin jikinsa ko kaɗan, ji yake kamar an zare duk wani ƙarfi da ƙwarin guiwar da yake da. Cikin sarƙaƙaƙƙiyar muryarsa yace "Na haƙura da Zahrah tunda yanzu ta kasance mallakin wani, amma tabbas an cutar da Ni duk da cewa haka Allah ya tsara, haka nan ya zama dole na je har gidansu na sanar da su abunda ke faruwa, ya zama wajibi su san cewa ba Ni da laifi." Ya idasa cikin ɗaga murya. Tapping bayansa Mom take tare da faɗin "Kada ka damu, gobe in sha Allahu za mu je gidan, ɗazu dama sun kawo lefen da aka kai, amma nace su koma da shi ai ba a yi haka ba." Jinjina kai Dad yayi tare da faɗin "ƙwarai kuwa, yanzu dai Son ka kwantar da hankalinka, ka kwanta ka yi baccinka ka ga ba isasshiyar lafiya gare ka ba, gobe in Allah ya kai mu sai a warware musu komai, Allah ya maka albarka ya musanya maka da mafificiyar Zahrah."
"AMIN" Shi da Mom suka amsa, daga nan ya musu sai da safe ya wuce nasa ɓangaren tare da kwantawa sai dai bacci yace bai san wannan Magana ba, saboda haka ya tashi ya ɗauro alwala ya fara nafilfilu.
*WHERE'S THE RETURNED YAYA SADAUKI?*
Tun daga wurin ɗaurin aure suka wuce tare da Appa saboda alfarmar da ya roƙa na kada a sanar da kowa batun dawowarsa, yana so ya ba wa waɗansu mutane mamaki, dalilin hakan ne yasa Appa tafiya tare da shi wai fa duk gudun kada ya ƙara guduwa musu ne. Sai da suka tsaya suka yi shopping kama daga kayayyakin sawa, turaruka zuwa kayayyakin amfani daga nan suka nufin gidan Appan amma Ya Sadauki ya roƙi alfarmar ya kai shi gidan Mommy Salima coz yana buƙatar wasu mutanen a tare da shi.
Ko da suka je sosai Mommy Salima ta razana musamman da ta ga dai shi ɗin ne wanda ya mutu kuma da idanunta taga gawarsa, hakan yasa da ƙyar Appa ya shawo kanta yace mata "Ai ba mutuwa yayi ba, dogon labari ne,." Kawai yana son hutawa ne, idan tana son sanin me ya faru akwai family meeting in the next five days. Da haka ya baro Ya Sadauki a can.
Ko da Appa ya koma ya sanar da Alhaji Baba yadda suka yi da Ya Sadaukin bai ce komai ba.
*ABATCHA ESTATE*
Misalin ƙarfe biyar na Yamma Nasreen da Zahrah suka fito don miƙawa amaren Dinner ɗinsu, amma yau sun ci alwashin sai sun shiga gidan kowacce ko ana ha maza ha mata. Daidai harabar filin da ke kusa da Part ɗin wadda zai sada ka da titi suka tsaya suna gyara riƙon 2-2 baskets ɗin da ke hannunsu. Basu ankara ba sai ji Zahrah tayi an bangaje ta saura kaɗan basket ɗin ya zube. Da sauri ta ɗago idanuwanta don gani wani gwanin ne, idonta ne ya sauƙa kan fuskar Rumana da ke cike da murmushi irin wadda ake ƙira murmmushin mugunta yayin da take tauna chewing gum ƙaƙas ƙaƙas Kamar wata tsohuwar kilaki, hakan ba ƙaramin hasala Zahrah yayi ba, ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta ajiye baskets ɗin gefe ta nufi Rumana. Tas! Ta ɗauke ta da mari wanda yasa Nasreen ƙarasowa tana faɗin "Ki barta Zahrah ba girman ki bane wannan."
A hasale Zahrah tace "Don ba ki da hankali idan abincin ya zube jikina ya ƙona Ni fa?" Hannun Rumana da ta gagara cirewa daga fuskar ta saboda tsantsar mamaki da kuma tsoro da ya dira mata lokaci guda tace "Ni kika mara?"
"An mareki, ki rama in kin isa."
Ba ta Raman ba amma a hasale tace "Wallahi kuwa zan Raman, za ki san kin mare ni a lokacin da kika ga an ɗaura aure na da bugun zuciyarki." Daga haka ta ja ƙafafunta ta bar wurin.
Tsaki kawai Zahrah ta sauƙe tare da nufar basket ɗinta ta kwasa daga nan suka wuce, sun ci Sa'a kuwa Ya Khalil ba ya nan, hakan yasa suka shige bayan wacce ke kula da gidan ta buɗe musu. Lokacin da Nainarh ta gansu tsabagen farin ciki wani tsalle ta daka tare da ƙarasowa kusa da su. Harara Zahrah ta aika mata tare da faɗin "Dakata mana Malama, kya jira mu aje shirgin hannunmu ai, don in muka ƙone kema sai mun ƙona ki."
"I'm sorry, tsabagen farin cikin ganin ku ne, ke fa Madam? Daga ina? Ko har kin fara yawo ne?"
"Kya jira dai mu ɗosana mazaunan mu kafin ki tsare mu da tambayoyi." Daga haka suka nemi wuri suka zauna gabaɗayansu. Nainarh da ke son jin dalilin ganin Zahrah nan yasa tace "Malama wai har kin fara fita ne?, ya jikin naki?"
"Da sauƙi uwar magana, to Ni ai ba a kai Ni gidan mijin ba tukun, kya jira in an kai Ni sai ki tambaya."
"Don Allah dai cire Ni cikin duhu."
Nasreen ce ta kwashe komai ta sanar da Nainarh, Allah sarki ya Ishaq yau ya sha zagi a wurin Nainarh, ba su jima ba suka wuce.
A can gida kuma Yaya Ishaq, Mom da kuma Dad ɗinsa suka zo, an tarbe su kuma kamar babu abunda ya faru, daga nan kuma suka fara faɗin dalilin zuwan nasu. Tabbas an sha mamaki da jin al'amarin da kuma yadda ya faru, nan aka jajantawa juna daga nan kuma aka koma wata hirar, shi dai Ya Ishaq damuwarsa ba ta wuce rashin Zahrahn ba sai dai ko giftawarta bai gani ba bare ya samu damar ba ta haƙuri kan abunda ya faru. Daf da za su tafi sai ga Zahrah da Nasreen sun shigo, idonta a kan Ya Ishaq ya fara sauƙa wanda hakan ya haddasa mata yanayi irin na fargaba, shima kuma a nashi ɓangaren haka ne ta faru, it has been long since ya sanya ta cikin ƙwayar idanunsa sai yau, ta ƙara kyau kamar ba ita ba, alamu kuma sun nuna ba ta tare da wata damuwa. Ita ta fara janye idanunta sannan ta ƙarasa suka gaisa da Dad da Mom, haka Nasreen ma haka. Suna shirin miƙewa Mom tace "Ai gara da ba mu tafi ba, tunda kin dawo zauna a yi gabanki tunda abun da ya shafe ki ne ake tattaunawa."
Ba musu su biyun suka zauna, Mom ce ta fara magana cikin Dattaku irin nata, nan ta kwashe komai ta sanar da Zahrah. Abunka da mace, macen ma mai rauni tuni ta fara share ƙwalla haka Nasreen ma, Dad ne ya dakatar da Su da faɗin "Ya isa, kukan ba shi da wani amfani a yanzu, ku yi haƙuri ku rungumi ƙaddara kawai."
"Haka ne," Hajjaty ta ƙara a kai "Sai dai mu ce Allah ya kiyaye gaba, ya ƙara kare mu daga sharrin maƙiya, ke kuma Zahrah kin ji komai, ki yi haƙjri ki yafewa Yayanki."
Cikin sanyin murya tace "Babu komai, Allah ya yafe mana baki ɗaya."
"Amin" suka amsa tare. Daf da maghrib suka yi haramar wucewa, ganin za su tafi kuma bai samu ya yi magana da Zahrahn ba in person yace "Eh Zahrah, please ki ba Ni ko two minutes ne don Allah"
"Ok" kawai tace, jin yayi shiru yasa tace "ina sauraronka"
Diridiri yayi kamar marar gaskiya yace "I'm sorry again and again, I'm sorry for hurting U, don Allah ki yafe min."
"Babu komai Yaya, na daɗe da yafe maka."
Fitowar Mom da Dad yasa ya mata sallama daga nan suka wuce.
Bayan sun yi dinner Zahrah ta tambayi Nasreen ra'ayinta game da Yaya Ishaq ɗin a halin yanzu da gaskiya ta zo musu, a hankali tace mata "Ai na haƙura da shi tun tuni."
"Wallahi ba ki isa ba, in dai har don Ni ne ai na yafe masa, kuma kinga ai ba shi da laifi, abunda muke zargin nan dai ya tabbata, amma dai bari mu murmure sai mu fara aiki a kai."
"Ai kuwa dai" Nasreen ta ba da amsa a gajarce
"Malama nifa ki faɗa min gaskiya, ke ko ba kya so ma sai an yi da shi, wallahi ma Hajjaty zan faɗawa."
Da sauri Nasreen tace "Rufa min asiri Zahrah, ba wannan ba, kin san meye?"
"Kin ji me Rumana tace ɗazu?"
"Eh fa, na ji ta, amma Ni ba Ni da lokacin shirmenta."
Numfashi Nasreen ta sauƙe tare da gyara zamanta, in a serious tune tace "Ba shirme bane Zahrah, wallahi ina zarginta."
"Zarginta na me kuma?" Zahrah ta tambaya cike da ƙaguwa.
Sassauta muryarta tayi a hankali tace "Cewa fa tayi wai sai ma kin ga an ɗaura aurenta da abun ƙaunarki, anya ba ta da hannu a cikin fasa auren nan da aka yi?"
Jim Zahrah tayi kafin tace "Kamar dai, kin tuna saƙon da ya turo min? Muryar mace naji amma ba zan iya tantance waye ba."
"Zargi ya tabbata, wallahi mu sa wa yarinyar nan ido, Ni dama can ban yarda da ita ba. Kin san dama ai an ce tsintacciyar mage ba ta mage, wallahi Zahrah mu sa mata ido, Ni dalilin ta ma yasa na ji ina son Ya Ishaq ɗina" ta faɗa babu fargaba
Dukan wasa Zahrah ta kai mata tare da faɗin "Za ku mugun dace kuwa, Allah dai ya tabbatar da alkhairi."
"Amin" Nasreen ta amsa mata "To yaushe za ki haɗa Ni da shi?"
"Ni kuma? Ke nifa matar aure ce yanzu, ba zan na kula maza ba, amma zan yi wa Mamah magana tunda naga ɗazu bayan tafiyarsu ma ya kira ta."
"Yauwah my sweet sister. Sai yanzu na ji batun, wallahi sai na ci uban yarinyar nan Rumana."
"Calm down Duk cikin kishin ne?" Harararta Nasreen tayi tare da faɗin "bar Ni kawai, Na ƙagu naga mijin nan naki, wallahi jikina yana ba Ni kamar na san shi " ta Idasa cikin sigar zolaya.
"Ke kika sani dai, Ni kai na ba saninsa nayi ba talkless of you silly creature, Ni tsoro na ɗaya ma kar Yace a'a ba ya so na."
Da sauri Nasreen tace "Ba a yi irin mijin nan ba, wallahi sai dai ya faɗa a baki, amma santaleliyar yarinya irinki ta wuce haka."
"Ni yi min