Showing 33001 words to 36000 words out of 157517 words

Chapter 12 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5146

ya fara yasa yayi wa Alhaji Baba sallama kana ya ja masa ƙofa. Alhaji Baba har cikin ransa yayi farin ciki da abunda yake shirin ƙullawa ganin yadda Yaya Sadauki ya nuna goyon bayansa ɗari bisa ɗari, wani sashe na zuciyarsa kuma na ƙara tausaya masa.

*Flash back*
Bayan wannan ƴar tarzoma da aka yi a ɓangaren Hajiya Babba, kowacce mijinta ya ja mata kunne akan kada ta ƙara shiga sabgar Hajiya Rukayya balle su kai mata raini, ita ɗin ba sa'ar su bace, abun ya ƙonawa kowaccensu rai har ta kai ga kowa ta ɗauki alwashin samarwa kanta maslaha game da hakan. Haushin su bai wuce ma yadda mazajen nasu ke matuƙar ba wa Hajiya Rukayya girma ba, ko faɗa suka yi ba sa bin bayansu sai na Hajiya Rukayya, that's what make them took a pledge to destroy her.

Ɓangaren Mommah ta ƙudiri aniyar hana auren da Alhaji Baba ke shirin ɗaurawa ko da kuwa zata yi yawo tsirara ne ba wai iya rasa aurenta ba sakamakon huɗubar shaiɗanci da ƙawayen ta suka yi mata ita la ta hau kan keken ɓera.

*Ci gaba*

Kai tsaye ɓangaren su ya wuce don ya samu ya huta, har ya fara taka staircase ɗin ya juyo jin Mommah na ƙwalla ƙiransa.

Juyowa yayi sai a lokacin ne idon sa ya sauƙa a kan Daddy. Ƙarasawa yayi yayi hugging Daddyn yana faɗin
“Daddy na, yaushe ka dawo?”

“Wato ma ina maka magana Aliyu ka tafi wurin ubanka saboda Ni bani da muhimmanci a wurinka ka bar Ni Ni ga mahaukaciya ko?”

Dafe kansa yayi yana faɗin
“I'm sorry Daddy, Ina yini ya hanya?”

Fuska sake Daddy ya masa da “Alhamdulillah Lafiya ƙalau.” sai kuma ya haɗe fuska har ya zartawa Yaya Sadauki a iya kamewa. Kallon Mommah da ke haki yace

“Wuce ki shiga ciki ki jira Ni, Aliyu go and rest”

“Ok Daddy, bye Mommah, bye Daddy.”
Ya keɓe ta zai wuce da sauri ta tsayar da shi
“Ba kiranka nake ba?” ta faɗa a harzuƙe.

“Let him go Sughrah in ba Haka ba you'll see the other side of me, ALIYU go.”

Ya ɗaga ƙafa zai tafi Mommah ta ƙara tsayar da shi.
“Other side of yours na nawa, nace na nawa Daddyn Ra'ees?, Aliyu if you dare go sai na saɓa maka.”

Ransa ne ya fara ɓaci da abunda Iyayen nasa ke yi a gabansa, shiyasa baya spn zaman part ɗin su tunda yayi wayo. Fuskarsa ɗaure sai kuma ya kwantar da murya yace
“Haba Mommah, why kike son rigima ne ke kam? DADDY na miki Magana kin ƙi bin umarninsa how do you expect me to obey your orders?, Mommah not me alone in baki daina musu da Daddy a gaban mu ba har su Ra'ees sai sun daina bin maganar ki. Please calm down ki bi umarnin DADDY.”


Ba ƙaramin tasiri kalaman sa suka yi a ranta ba, hakan yasa ta sake hannun Yaya Sadaukin ta wuce zuwa Bedroom ɗin nata. Sai da yaga shigewarta tukunna yayi wa Daddy sai da safe.

Bai ɓata lokaci ba kamar kullum yayi wanka ya saka kayan bacci sannan ya fashe jikinsa da turare, daga nan ya shinfiɗa praying mata yayi shafa'i da witri kana ya nufi bed ɗin sa yana mai kashe bedside lamp ɗin da ya kunna. Ya so bacci ya ɗauke shi amma tunanukan da suka yi wa zuciyarsa ƙawanya sun ƙi barin hakan, bahaguwar rayuwar da iyayensa ke yi ya fara isar shi coz tunda ya tashi yayi wayo bai taɓa ganin an yi zaman arzikin a gidan ba, Mommah ko kaɗan ba ta daraja Daddy shiyasa ma ya Hajjaty ta nema masa auren Aunty Amarya.

Moreso, tunanin sakamakon rayuwarsa yake, ya zata kaya yaya zai yi? Ga kuma auren sadaukarwa da yake shirin yi saboda Hajiya Babba da amininsa kuma ɗan'uwansa, ga kuma tunanin ƴar'uwarsa Zahrah da ya rasa dalilin da yasa ya kasa manta ta daidai da na second ɗaya ne, amma ya alaƙanta hakan da kyautatawarta gare shi. A haka a haka dai har ɓarawo bacci ya sace shi.
(Good night Yaya Sadaukin mu).

*Other side of the house, Hajiya Babba's apartment.*

Yammacin ranar bayan Aunty Mabruka ta dawo daga court Hajiya Babba ta titsiye ta gaba akan al'amarin da ya faru a karo na ba adadi. Hawayen da Aunty Mabruka ke yi yasa Hajiya Babba daka mata tsawa har sai da Nasreen ta Zabura ta fito parlourn.

“Ki faɗa min gaskiya Mabruka in ba haka ba ranki zai ɓaci.”

Tsabar takaici da ya tokare mata maƙogwaro yasa ta kasa cewa komai sai zubar da ƙwalla da take.

“Don't let me repeat myself Mabruka, can Dama akwai wata alaƙa tsakanin ki da Sadauki ne har kike bashi damar shiga ɗakinki? Allah yasa dai baki bashi kanki ba ma.”

A zabure Mabruka ta buɗe baki ta fara magana har wa lokacin kuma hawaye bai daina zuba kan fuskarta ba.

“Haba Hajiya, idan kowa bai shede Ni ba ai ke kika haife Ni kuma kika raine Ni, kin san me zan yi kin san meye ba zan yi ba. Shekarata yanzu ashirin da bakwai a duniya, duk da cewa bani da aure hakan bai sa ina bin maza ba, ke kan ki kin san bana mu'amala da su ko da kuwa a lokacin da nake ji da tashen balagar tsuntsaye ban aikata hakan ba sai da nayi hankali? Ku duba al'amarin Hajiya Babba, kullum amsar da zan baku ba zata wuce babu abunda ya faru tsakani na da shi ba, hasali ma shi kansa akwai abinda aka bashi in ba Haka ba ke kanki kin san Yaya Sadauki ko kallo ban ishe shi ba.”

*Some of you will wonder why all these is happening, menene dalilin mutanen gidan na tsanar Hajiya Babba kuma meyasa ita da abokan zamanta suke zaman lafiya.?*
*A tunanin ku za a yi auren nan ko kuwa? Kuna tunanin ƙiyayyar da uwar miji ke nunawa? Anya Hajiya Turai zata amince? Leka see.*
*Duk amsoshinku na tare da ni, ku ci gaba da kasancewa da ni don jin yadda zata kaya.*


[12/29, 10:16 AM] Diamond Bhatool:

*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*


*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_


_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow

*PAGE* 1️⃣6️⃣

_This page is dedicated to my troublemaker and joy giver (Rouhy🦋). ILYSM🦋💞_

                                  ﷽

“Abun da ban fahimta ba kenan, tabbas al'amarin nan akwai sarƙaƙiya and whoever is behind this akwai target ɗin shi kan ki Mabruka. ”

“Hajiya In Sha Allah duk wanda ya nufe ni da sharri ma kansa zai koma.” ta faɗa a raunane, duk irin biris ɗin Hajiya Babba yau she shows her empathy on her daughter, for the first time ever.

“Haka ne, ki shirya jin sakamako daga Alhaji Baba, though ni ba lallai na aminta da zaɓin ba.

*Ina Rumana?*

Tunda ta isa part ɗinsu ta iske Ammie a parlour, tashin hankali ƙarara a fuskar ta, ɗan kukan da take ƙoƙarin riƙewa ne ya ƙwace mata nan ta faɗa cinyar Ammir.

“Ke Rumana lafiyar ki kuwa? Me ya faru?” Ammie ta tambaya cikin tashin hankalin ganin ƴar ƴar'uwarta da take matuƙar so da ƙauna cikin yanayi na damuwa. Shiru Rumana bata amsa ba sai ma ƙara volume ɗin kukanta da tayi.

“Kin ga Rumana ki nutsu ki sanar da Ni damuwarki, wani abun ya faru ne?” ajiyar zuciya Rumana ta sauƙe tana rage sautin kukanta.

“Ina jin ki Rumana, hankali na gaba ɗaya ya tashi, don Allah ki faɗa min ne ya faru?” cikin wata raunananniyar murya Rumana tace
“Ammie kin dai san yadda nake son Yaya Sadauki...” dakatawa tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta.

“Talk Rumana, me ya samu Sadaukin?”

“Ammie kin san wannan yarinyar? Jikar Hajjatyn nan yanzu na gan su tare alamun daga wani wurin suke, Ammie Ni fa ko kallo bai ishe Ni ba, wallahi na tsani yarinyar nan kamar mutuwa ta.”

Cikin tashin hankali itama Ammie ɗin tace
“Wai Zahrah kike nufi?” kai Rumana ta gyaɗa.
“Ki kwantar da hankalin ki daughter, ko ana ha maza ha mata ke ce matar Sadauki, burin mu Ni da ke sai ya cika, yanzu dai ki share zancen yarinyar nan don maganar da nake miki Alhaji Baba....”

Nan ta bata labarin halin da ake ciki.
Tashin hankali wai ba a sa masa date! Rumana dai har da sumarta jin wata na shirin wuf da abun harinta.
(Allah Sarki Rumana...)

*MORNING.......*

Yau ma dai Zahrah ce ta girkawa Yaya Sadauki breakfast sauran Kuma Laraba ce tayi, Hajjaty sai ɓaɓatu take mata wai tana sakalta Yaya Sadauki, idan ta fara zuwa school ta ga yadda zai yi ai. Ita dai Zahrah dariya kawai tayi tace “Hajjaty ai duk abinda zan yi wa Yaya ban faɗi ba, ya cancanci fiye da hakan.” kyaɓe baki Hajjaty tayi tana faɗin “Ai sai ki yi.”

Bayan sun yi breakfast ya shigo looking so breathtaking and awesome, hairstyle ɗin shi kawai ya sauya amma wani irin kyau da ya ƙara ba a magana. Cike da girmamawa suka gaisa da Hajjaty, ita ma Zahrah ta gaida shi, ba tare da yace uffan ba ya nufi dining, zugum-zugum Zahrah ta bi shi. Tana serving nashi ta wuce don shiryawa.

Wanka ta ƙara yi a gurguje daga nan ta shirya tsaf cikin wata Maroon Egyptian cotton Abaya wacce ta matuƙar amsar farar fatarta, gashinta ta tufke before ta saka Black hula sai kuma tayi rolling black veil na abayar. Sosai ta fito kamar ba ita ba, In ka hanta ba ka yi zaton ɗiyar hausawa bace, sai ta fito sak a balarabiya....black wristwatch ta Sanya wadda kana ganin sa ka san ba na wasa bane kana ta janyo Black handbag da kuma takalmi ta saka.

Ma sha Allah, kiran da Hajjaty ta ƙwala mata yasa ta fesa turare a gaggauce kuma ta fice parlourn.

“Yayanku ya fita”
Da sauri Zahrah ta bi shi tana farin cikin yau zata koma karatu bayan wani dogon zango. By the time ta fita da sauri ta ƙarasa motar ta buɗe gidan gaba ta zauna. Nan motar su ta fice daga estate ɗin.

Ganin shirin ya yi yawa yasa Zahrah ta saci kallon Yaya Sadaukin, and to her observation, he looks so worried...

“Yaya” ta faɗa a hankali, ba tare da ya kalle ta ba yace
“Uhm”

“You look so worried, wani abu na damunka, ko ba ka da lafiya ne?”
Abun da mahaifiyar sa bata taɓa fahimta a tattare da shi kenan, bata san damuwarsa ba ba kuma ta damu da damuwar tasa ba sai ma tsananin son kai da take da, always putting her priority over na wasu, amma yau ga yarinya ƙarama har takan iya fahimtar yana cikin wani hali. Ko ba komai kulawarta gare shi yasa ta ƙara samun matsuguni cikin zuciyarsa.

“Yaya...” ta faɗa kamar za ta yi kuka.
“Babu komai Lilyn Yaya, bacci ne bai ishe Ni ba kawai.”

“Kai yaya” ta faɗa Yana kwaɓe fuska.
“Wallahi a'a, akwai abun da ke damunka kawai dai Ba ka so na sani ne, but always believe in Allah Yaya, zai magance maka damuwoyin ka, I'm always praying for you tun ban taɓa ganin ka ba.” ɗagowa yayi ya kalle ta sai kuma ya maida kallonsa ga hanya.

“You look so beautiful Lilyn Yaya.”
“And you look more handsome than...” Bata ƙarasa ba ganin an wangale musu gate ɗin school ɗin. Ba su wani daɗe ba ya kammala duk wasu matakai na ganin ta zama cikakkiyar ɗaliba, a lokacin kuma ta amshi uniform da littattafai, daga nan aka wuce da ita Form 3...same class da su Zakiyya. Ihun murna suka saki ganin Zahrah suna kuma mamakin ba zatar da tayi musu. Nan suka yi introducing Bata ma sauran ƴan ajin, daga nan fa Zahrah ta ɗame kamar ba baƙuwar ba, har ta yi abokin wai shi Nu'aym, shi ne kuma class rep ɗin su.

Ko da lokacin tashi ya yi ta fito za su tafi da su Nasreen ta hango sayyarar Yayan ta, da sauri ta juya za ta wuce.
Nainarh ta dakatar da ita
“Where do you think you're going, an Zo ɗaukarmu fa.” pointing motar Yaya Sadaukin tayi sa hannu, nan Nainarh ta zaro ido waje tana mamaki, In ba ƙarya tayi ba wannan motar da Yaya Sadauki yau ya fita da ita ne. Bata aune ba ta ga Zahrah har ta kai ga wurin motar, babu yadda ta iya ta nufi motar Baban Salaha. Ko da su Nasreen suka tambaye ta ina Zahrah sai tace musu ai ta tafi. Basu matsa mata da tambaya ba ganin yanayin fuskarta da haka suka wuce gida.

Can wajen Zahrah tana shiga ya ja motar.
“Yaya shi ne ka baro aikinka ka zo, ai da zan koma da su Nainarh.” shiru ya mata bai ce komai ba can kuma yace
“Na san da motar can ɗin ai nazo, kullum kuma Ni zan kai ki na maida ki, don't say anything again....” shiru babu wanda yayi magana har suka isa. Yana daidaita parking ta fito, wannan karon kuma a idon Mami wacce motarta ke shirin barin estate ɗin.

Ko da Yaya Sadauki ya shigo Zahrah ta zo ta tambaye shi ko za ta masa girki? Yace mata a'a zai ci wancan ɗin shima and ta shirya in zai fita zai kawo mata uniform na Tahfiz wacce take cikin estate ɗin.

A islamiyyar suka haɗu, nan suka tusa ta gaba da tambayar waye ya mayar da ita gida, shiru tayi musu, da ta gaji kuma tace musu ai motar su Nu'aym ne, ba tare da sun yarda ba suka ƙyale ta amma suka ce mata kada ta ƙara bin wata motar in ba haka ba sai sun faɗawa Alhaji Babba.
Bayan sun keɓe da Nainarh ne ta kawo zancen ta kuma yi mata jan ido kan ta san waye ne a motar.

“Ya Allah, Sis Nainarh Yaya Sadauki ne fa ba kowa ba, kinga Dama shi ya kawo Ni, ya riga ya gan Ni, In na wuce na bi ku ba zai ji daɗi ba.”

“Then meyasa kika ɓoye min da farko? Ko kina tunanin ba zan so na ganki da shi ba? Ke ma ƴar'uwarsa ce ai.”

“Ba haka ba ne Nainarh...”

“Don't say anything Zahrah, kawai dai na baki amanar Yaya na, don na ga ke ta musamman ce gare shi, ki kasance da Yaya kina ɗebe masa kewa ko damuwoyinsa za su gusa. Nan ta bata labari kamar yadda Nasreen ta bata. Ita dai Zahrah mamaki take, ko me suka ɗauke ta da ta kasance da shi?

Bayan an tashi daga islamiyyar a gajiye ta koma, amma duk da haka she prepare dinner for him. Lokacin da ta shiga wurin Alhaji Baba ne taji ana zancen aure, amma bata fahimci na waye ba. Ko da ta dawo sai ta ji ta rasa sukuni amma haka ta daure, a yau kam ba su yi wata hira ba da Yayan ta, tana gama serving nasa ta wuce ba tare da ita ta yi dinner ɗin ba.

*Washegari*

Kamar yadda ya faɗa ɗin shi ne ya kai ta school da kansa, haka kuma ya ɗauko ta. A hanyarsu ta dawowa ya kawo mata zancen aurensa. Dim ƙirjin ta ya buga, amma sai ta masa Allah sanya alkairi duk da bata ji daɗin zancen ba, amma ta ta'allaƙa hakan ne da sanin ba son auren yake yi ba saboda ta san mata ba sa gabanta.

A sukwane ta ƙarasa yinin ranar, ko a islamiyya sisters ɗin ta babu tambayar da basu mata ba amma tace babu abinda ke damunta kawai gajiya ce. Bata fasa masa hidima ba tayi masa dinner. Bayan ta yi sallah ta ɗan kwanta kan sallayar ta da niyyar ba zata ma fita waje ba coz ji take kamar ta rausa kuka haka take ji idan ta tuna da maganar. (Yarinya don't know that she's in love....).

Tsawon sati guda tana bin motar gida gudun kada su haɗu, In an tashi ma da wuri take kaɗe ma su Zakiyya hankali su wuce, cikin satin nan ba ƙaramar rama ta yi ba, and bata Zama a parlour ma gudun kada su haɗu da kowa, she's always fund of isolating herself saboda ta fi jin daɗin hakan, duk yadda ƴan uwanta suka matsa mata da tambaya ko uffan ba ta cewa sai ma ta basu waje.

Ɓangaren Yaya Sadauki kwana biyu in ya zo sai Hajjaty tace masa Zahrah ta bi su Nasreen saboda kada ta makara, a rana ta uku ya bar mata sallahun lallai lallai ta jira shi da safe gobe coz zaman part ɗin Hajjaty ma daina shi tayi ta koma Part ɗin Hajiya Babba.

Babu wadda ya fahimci dalilin Zahrah na sauyawarta daga yadda take zuwa Silent Zahrah. Allah sarki Yaya Sadauki ya fi kowa damuwa da rashin ganinta, ta riga ta sabarwa zuciyarsa da rayuwa da shi and yanzu take gudunsa, ya Yi tunanin har ya gaji kan me ya mata amma ya kasa fahimtar komai. Lokacin ya fara fahimtar cewa ita ɗin ƙarfin guiwarsa ce, dole ta dawo gare shi don cikar burinsa da ya ɗauri aniyar cimma su.

Alhamdulillah ya fara aiki kan neman Mama, an kama kawu wanda ke hauka tuburan daga ƙarshe dai aka sake shi ganin ba information ɗin da za a samu wurinsa. Baba Amarya da ɗiyarta Bibalo Are no where to be found. Yadda yadda so abun ya zo masa sai yake ƙoƙarin ba shi wahala and supporter ɗinsa ta guje shi, ba shi da wata maslaha da ta wuce ya dawo da ita gare shi.

Yau juma'a kuwa ya ƙuduri aniyar sanya ta a idonsa ya kuma tanadi tambayoyin sa da zai mata, dole ta amsa masa su kuma in ba haka ba.....


*Allah sarki little Zahrah Kuma Lilyn yayanta an zurma tun kafin a je ko ina, anya kuwa za ta samu cikar burin ta a yadda ta sanya damuwa cikin ranta? Kai jama'a....team Zahrah kuna ina? Yau reactions ɗin ku kamata yayi ya zo da emojin 😥 nan. Ni dai ina taya Yaya Sadauki murnar samun mace wayayya kamar Barrister Mabruka. Ko ba komai za mu yi anko, ke kuma Zahrah ki kashe kanki tunda baki da hankali....Ina team Rumana? Ku ma an doka ku, haka team Kausar ku ma ana shiri.*
*Ko wanne shiri su Mami ke yi, sun ma san me ake ciki kuwa?*
*Allah Sarki Rayuwa, Allah ya kawo ma kowa sauƙi.*

*Kada a mance for any inquiries ga number ta +2347061707238, ƙofar gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login