Showing 45001 words to 48000 words out of 157517 words
cikin wata raunananniyar murya
Ɗagowa Humaira ta yi tace
“Hajiya nima wallahi ina ƙaunarsa, kuma wallahi In ba a aura min shi ba zuciya ta bugawa za ta yi na mutu.”.
Tashin hankali, a gigice Hajiya Babba ta ce
“Ba za ki mutu ba Humaira, a kan waye kike magana? Ko waye dole ya aure ki tunda kina son sa, tell me who's that person da har kika mace kan sa”
“Hajiya Yaya Sadauki!...”
Bata bari ta ƙarasa ba ta tura ta gefe tana bin ta da wani irin kallo.
“Lallai Humaira ba ki da hankali ma, mijin ƴar'uwar taki kike so? Abun hauka ne aka ce miki?”
A raunane Humaira tace
“Haba Hajiya, Ni na ɗaura wa zuciyar tawa son sa ne? Allah ne fa ya halicci zuciya ta da son sa, na girma da son sa sai yanzu kawai za a raba Ni da shi? Ba a min adalci ba kuwa” raunin da Muryar ta tayi yasa ta dakata ta juya za ta fice daga ɗakin tana kuka.
“Wait, come here Humaira!” Hajiya Babba ta dakatar da ita, ba musu ta koma bakin Bed ɗin ta Zauna.
“Humaira haƙuri za ki yi kawai, Alhaji Baba ne ya yanke wannan hukunci. Da a ce ma ita Mabrukan akwai wani tsayayye a wajen ta za a iya dakatar da auren amma babu.”
“Hajiya Aunty Mabruka ba ta son Yaya Sadauki, she never get even a single feeling for him, in fact tsawon rayuwa ta da ita ban taɓa jin ko sau ɗaya ta yaba kowa ba sai Captain Hisham wanda tun ba yau ba suke tare, meyasa kuke son raba ta da farin cikin ta? Hajiya don Allah kar ki bari na rasa Yaya Sadauki, idan hakan ta faru I'm useless, ba Zan amfanu ba don ƙarshe ma dai I'll lost my life and....”
Da hannunta ta toshe bakin Humaira tana jijjiga kanta
“A'a Humaira, U won't lost your life saboda namiji, ba za ki mutu ba Humaira, ki yi haƙuri kin ji, zan duba naga yaya abun zai kasance, go and sleep now.” ba tare da ta ce komai ba ta fice sai sauƙe ajiyar zuciya take. Nan ta bar Hajiya Babba cikin kogin damuwa musamman da abun ya kwaɓe mata amma to Allah we belong, sai ta ƙara roƙon sa da ya kawo agaji.
*MORNING*
*Zahrah's POV*
A hankali ta fara motsa yatsun kafafuwanta wanda take jin kamar an ɗaure mata su, can kuma ta fara kiciniyar buɗe idanuwanta da suka yi mata wani irin nauyi, da ƙyar ta iya buɗe su tana mai bin parlourn da kallo sam jikinta babu Kwari ko kaɗan, a haka ta fara ƙoƙarin miƙewa tana tunanin what makes her so dull today. Nan ta fara tariyo daren jiya, da sauri ta koma shagab ta kwanta tana ƙara rintse idon ta.
“Ya Allah!”
Ƙoƙarin miƙewa ta ƙara yi har sau uku tana komawa saboda yada jikinta yayi laushi, da ƙyar ta miƙe ta nufi toilet tana mai bin jikin gini. Bayan ta yi alwala ta yi sallar ta wacce a zaune ma ta yi ta tana mai roƙon Ubangiji da ya kawo wa rayuwar ta ɗauki. Alhamdulillah sai ta ji zuciyar ta ta ɗan yi sanyi ba wai don ta daina jin yadda zuciyar ke zafi ba, sai dai ta ji ƙarfin guiwar coping ma wannan bada moment ɗin da ya zo mata a ba zata.
Bata fita parlourn ba sai da Hajjaty tazo duba ta nan ta tarar da ita jikinta zafi kau, hankalin Hajjaty ta tashi matuƙa da sauri ta fita ta kwaso drugs da kuma abinci ta dawo. Sosai ta ba wa Zahrah kulawar da ta ɗan ƙara ɗauke hankalin Zahrah daga tuna wannan abu. Yinin ranar dai kusan tare suka yi.
Can wajen yamma Yaya Sadauki ya shigo Part ɗin, ko da ya tambayi Laraba nan ta kora masa bayanin ai Zahrah ce ba ta da lafiya Hajjatyn take wurin ta. Nan take zuciyarsa ta bada wani irin sauti, da sasaarfa ya ƙarasa zuwa room ɗin Zahrah, handle ɗin ya murɗa ya yi wa kansa iso.
Bayan sun gaisa da Hajjaty ya maida dubansa ga Zahrah, gaban sa ne ya faɗi saboda yadda ta rame kamar wacce ta shekara tana jinya.
“Hajjaty why ba a Kai ta asibiti ba? Bari na kai ta asibiti yanzu, look how she's been wasted!” ya faɗa a ɗan kiɗime yana kai hannunsa zai ɗauki Zahrah wacce take bacci.
“A'a ai ka bar shi ma Sadauki an, ta riga ta ji sauƙi” Hajjaty ta dakatar da shi. Noo ba zai iya ba, ba zai bar amanar sa a haka ba, dole ya kula da ita. Kamar bai ji Hajjatyn ba ya sunkuci Zahrah yayi waje da ita sai cikin mota, daidai lokacin da motar Ammir ta wuce ta wurin. Bai ma kula da su ba ya tayar da motar sai wani private hospital na Indians da ke kusa da estate ɗin. Abunku da ƙwararrun likitoci tuni suka karɓi Zahrah hannu biyu aka fara duba ta.
Har wajen ƙarfe 8:00 na dare ba su bari ya shiga kallonta ba don kuwa gwaje-gwaje sun kai shida aka mata. Can bayan sun kammala physician ɗin ya ce da Yaya Sadauki su je zai yi magana da shi, he's eager to know what's wrong with Zahrah ai da sauri ya bi bayan doctor ɗin. Bayan sun gaisa ya fara masa jawabi.
“Maras lafiyar da ka kawo yanzu haka bacci take don tana da buƙatar hutu sosai, zuwa gobe za mu sallame ta.” ya faa cikin harshen Ingilishi.
“To me yake damunta?” yaya Sadauki ya tambaya.
“Honestly speaking Mr. Kuna gab da rasa ta matsawar ba za ku ba ta kulawar da ya dace ba, at this her age ta Yi ƙanƙanta da samun heart attack, to be sincere with you in ba a ba ta kulawa to condition ɗin will worsen, thank God ma an yi diagnosing early.”
Cike da mamaki da kuma damuwa Yaya Sadauki ke kallon Dr ɗin, har sai da ya gama jawabin yace
“Ok Dr. Yanzu dai takamaiman shi me yake kawo Heart attack ɗin?”
Dr ya gyara zaman glass ɗin sa ya fara magana, bayan ya gama masa bayani nan Yaya Sadauki ya fice fuskarsa ɗauke da damuwa. Wayarsa ce tayi ringing da ba zai ma ɗaga ba sai kuma ya duba, ganin Dude ɗin sa yasa ya ɗaga, bai ce komai ba sai kuma can yace
“BHAAT SPECIALIST”
Can ya Kuma cewa “Ok”.
Reception ya koma ya zauna har Yaya Khalil yazo. Da yake su tsarin asibitin babu patient relatives, ba a zuwa dubiya saboda suna rendering care yadda ya kamata ga patient. Da ƙyar dai aka bar su suka shiga da sharaɗin kada su yi motsin da zai tayar da patient ɗin. Fitowar su kowa fuskarsa ta sauya wanda hakan ta yiwu yana da alaƙa da yadda suka ganta, daga nan suka wuce tare. Da suka isa sai da suka samar da Hajjaty tukun hankalin ta ya ɗan kwanta, da cewa ma tayi sai dai a kai ta taga Zahrah, da suka mata bayanin tsarin asibitin yasa ta haƙura.
Daga nan kuma Yaya Sadauki ya wuce Part ɗin su don yana bukatar hutawa, wanka ya yi ya Saka wasu soft pyjamas blue colour, kamar kullum yayi shafa'i da witr sannan ya nufi Bed ɗinsa, bayam ya Yi addu'a ya ja Blanket yana mai lumshe idanunsa. Tunani yake me yayi causing wannan sickness na Zahrah, he later concluded it as dalilin rashin Mama ne. Hakan ya sa ya ƙuduri aniyar da safe zai ƙara tunkarar abokin aikinsa Inspector Wada Usman kan batun.
Ba ita ta farka ba sai wuraren 3:00am, a hankali ta fara bin ɗakin da take da kallo, hannun ta ta ɗaga sai taji igiya like a jiki, da sauri ta mayar da duban ta ga hannun, zaro ido tayi ganin cannula ce ga Kuma wani ƙatoton I.V fluid da aka maƙala mata. Sai a lokacin ta fahimci cewa a asibiti take, gabanta ne ya faɗi don bata san ya aka yi ta zo asibiti ba, shikenan asirin ta ya tonu?
Ƙarfe 6:30am na safe yayi parking motarsa a harabar makeken asibitin saboda saurin da yake yi ya dubo Lilynsa. Masu kula da asibitin suka tsayar da shi har sai da ya mayar da motarsa wurin da aka tanada domin parking. Yana gamawa ya fito da basket ɗin daga booth ya nufi cikin asibitin. Ko da ya isa reception Nan ya sanar da su wurin patient ɗin sa ya zo, da ƙyar suka bar shi ya shiga saboda irin yadda ya musu kwarjini.
Lokacin da ya shiga ya tarar da Zahrah kwance sai dai da alama ba bacci take ba amma idanuwanta a lumshe suke, alamar buɗe ƙofar yasa ta ɗan buɗe idonta don ganin waye. Cikin rashin Sa'a suka haɗa ido da Yaya Sadauki wanda ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi da sai da ji zuciyarta ta buga.
Kujerara ya ja ya zauna yana bin ta da kallo ba tare da ya ce mata komai ba, ita ma sai ta mayar da idanuwanta ta kulle. Can dai yayi murmushi ya ce
“Jira kike na fara miki magana ko Lily?”
Bakin ta ta ɗan turo gaba tace
“To ai Ni ce ba Ni da lafiya kai za ka gaida ni”
Mamaki da al'ajabi suka cika shi jin zancenta sai ya danganta hakan da larurar ta.
“Is alright good morning Lily, ya jikin ki?”
Baki ture ta amsa da “Da sauƙi”
Murmushi yayi ganin dai yau tabbas da rigima ta tashi
“Ok speedy recovery dear, an jima za mu koma gida, kin shirya?”
*React please and help me share this update please.*
*I'm alerting you with my precious 2025 story Ruɗin Zamani which I'll be starting May be tomorrow or day after tomorrow, sai dai paid book ne, amma In na samu reactions daga gare ku zan mayar da shi free, soyayyar ku kaɗai nake buƙata.*
[1/12, 11:52 AM] Diamond Bhatool:
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 2️⃣2️⃣
﷽
Yamutsa fuska tayi tace “Uhm” daga haka kowa yayi shiru, nashi ɓangaren yana tunanin why is Lilyn Yaya so quite nata ɓangaren tana ƙoƙarin koyawa zuciyarta cire soyayyar sa da ta shige shi ba zata.
Abincin ya fara fitarwa sannan ya ɗaura a bedside locker, bayan ya zuba mata papper soup ɗin da Hajjaty ta yi mata ya ce “O Yah Lily tashi, hope kin yi salla ma”
Kai ta gyaɗa masa
“Ok tashi ki ci abinci” da sauri ta miƙe saboda yunwar da take ji. Kaɗan taci daga nan ta sha fruits ɗin da ya ke miƙa mata. Sai da tayi nak tukun tayi ƙoƙarin komawa ta kwanta.
“No Lily, Bari abincin ya gama shiga kada ki ce za ki kwanta kin ji?”
Ba a daɗe ba aka yi discharge nata, bayan ya gama settling komai da taimakon sa suka fice sai Abatcha estate. Daga nan kuma ya damƙa ta hannun Hajjaty saboda yana son a haɗa lefen bikin sa ta hannun Mommy Nasiba wacce take matsayin ya ga Mommah.
Ba shi ya dawo ba sai da yamma, ko da ya shigo bai tarar da kowa ba, direct bedroom ɗinta ya nufa and luckily yana nocking yaji ta bashi amsa da “Come in”
A kwance ya tarar da ita, ganin shi ne sai ta turo baki gaba, sarai ya ganta amma sai ya sake kamar bai ga ba. Sai da ya zauna gefen Bed ɗin yace
“In kina tura min bakin nan Lilyn Yaya zan yanke shi”
Kamar bata ji ba ta ƙara tura bakin wanda hakan ya shagaltar da shi ga kallonta ba tare da kifta ido ba na tsawon minti guda da wasu sakanni. Kallon nasa da taga ya yi yawa yasa ta langwaɓe kai tana faɗin
“Ni ka bar kallo na Yaya”
Kansa ya kawar gefe ya haɗe fuskar nan sannan yace
“Wa ya ce miki kallon ki nake, ina duba yanayin jikin ki ne ko akwai progress, ba wannan ba ba na son Wasa Lily, ki faɗa min gaskiya me yake damunku, wace damuwa kike da ita da take shirin jefa ki ga wani yanayi na daban?”
Shiru tayi tare da mayar da kallonta ƙasa, a ɗan kausashe yace
“Kin ga Lily, bana son Shirun Nan, don't let me repeat myself”
Fuska a shagwaɓe tace
“Yaya babu komai fa”
Hararar da ya banko mata yasa ta mayar da hankalinta.
“Eh ah ah Yaya ba komai da gaske nake nima kawai zazzaɓi nake”
“Will You shut up?” ya dakatar da ita
“Idan ba ki faɗa min ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daɗi, Ni sa'an ki ne?”
Jiki na rawa tuni hawaye suka wanke mata fuska, ta ya ma za ta iya ce masa soyayyar sa ce take shirin hallaka ta?, That's impossible.
Ganin hawaye a fuskarta ga kuma yadda ta tsorata yasa yace
“Is ok, daina kukan tunda ban dake ki ba, faɗa min me ke damun ki”
“Mama ce har yanzu ba ta dawo ba, kuma ina so na kalle ta.”
Nan ya fara lallashin ta yana ce mata Mama ta kusa dawowa in Sha Allah. Daga nan yace ta faɗi me take so zai siyo mata. Daga haka ya fice.
*Ina Mommah?*
Mommah dai har yanzu tana kan bakar ta na a fasa wannan aure wanda tuni har an fara shirye-shiryen sa. Ya ma za a yi a yi mata haka? Nan da nan ta tada hauka bisa zigin Aminanta, Daddy har tsoron shigowa gidan yake saboda bai san tsiyar da zai tarar ba. Abun nata har ya wuce nan ta kan shiga har sashrn Hajiya Babba ta mata tijara daga nan kuma ta nufi sashen Hajjaty nan ma ta sauƙe kwandon tsiyarta.
*A week later*
Cikin satin nan Zahrah ta koma makaranta sannan ta mayar da hankalinta ga karatun ta, ba wai don ta daina son Yaya Sadauki ba Amma a halin yanzu tana iya ɓoye feelings ɗin ta a game da shi yayin da kusancin su kuma ya Karu, kulawar da yake bata ta ninku.
A yau talata Zahrah, Nasreen, Zakiyya, Nainarh da kuma Rumaysa suka je amso ɗinkinsu daga wurin tailor. Sun ci Sa'a kuwa ɗinki ya kammala. Duk an ɗinka, ankon Dinner, Yini da kuma Family and friends day duk an gama. Nan ƴan matan suka biya tailor daga nan suka dawo gida.
Suna dawowa suka tarar an kawo lefen Aunty Mabruka. Bayan sun ajiye kayan su a Bedroom ɗin Zahrah suka dawo parlourn. Mommy Nasiba ce da kuma wasu yayyen Mommah suka kawo. Kaya ne na kuzo mu gani wanda duk idon da yayi tozali da su sai ya tabbatar Naira ta sha wahala. Su Mimie, Aunty Amarya da sauran matan gidan sai yaba kayan suke yayin da Mamie da Ammie ke jin zukatan su kamar su yi bunga musamman da suka ga kayan, kowaccen su cikin ranta tana faɗin da yanzu fa na ɗiyarta wannan dukiya da aka narka.
Basu bari an gama gani ba suka ɗunguma don kai report ga uwar ango, ai kuwa suka ɗaura ta kan layi, ba a jima ba sai ga ta ta shigo parlourn Hajjaty gadan-gadan, biye da ita kuma Ammie da Mamie ne. Tana isa ta ja burki ganin Yayyenta da ƙannenta a parlourn musamman da ta ga akwatunan da ke Baje a parlourn.
Kamar wacce aka hankaɗa ta nufi cikin parlourn sai ka ce mai taɓin hankali.
Sai da ta isa tsakiyar ta nuno Mommy Nasiba da yatsa
“Ashe har da ku ake cin amana ta Yaya? Ke ma har da ku?” ta fara nuna su ɗaya bayan ɗaya.
“Na rantse da Allah ba a isa an mun cin kashin nan ba, har ku ba zan bar ku ba, kuma ku kwashi kayanku don wallahi auren nan ba za a yi shi ba ko zan bar gidan nan.”
Galala Mommy Nasiba ke kallon Ƙanwar Tata musamman in ta tuna dama ba ta da kirki can da amma bata yi tsammanin rashin ɗa'arta ta kai haka ba.
“Haba Sughrah! Ashe ba ki da hankali ke?”
A gadarance Mommah ta rufe ido tace
“E ba Ni da shi, akan haka wallahi ko da me za a ƙira Ni ba zan ja da baya ba, ku kuma ɗaya bayan ɗaya sai na yi maganinku.”
“Haba Sughrah! Meye kike haka kamar marar ilimi?” Hajjaty ta faɗa tana tsare Mommah da ido.
“Ki ƙira Ni da marar ilimin kai tsaye Hajjaty, ai dama can ba so na kike yi ba, har zan ce ba na son haɗin auren amma a ƙi saboda Ni ba Ni da ƴanci? Tukunna ma wai akwai wanda ya haifa min ɗan ne?”
Ba shiri taji an ɗauke ta da mari, ba kowa bace sai Mommy Nasiba.
“Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri! Hajjaty ai ba sa'ar yin ki bane In kin mana mun yi shiru ba zan zuba ido ki ɓata tarbiyyar gidan mu gaba na ba, shashasha kawai”
“Ni kika mara Yaya?”
“Ƙwarai kuwa Sughrah ke na mara”
“Ni kika mara ko yaya?” ta nuna kanta da yatsa har lokacin hannunta na kan kuncinta.
“Wallahi ba a isa ba, ko duniya za ta kifa sai an fasa auren nan, don me ma zan bar ɗa na ya auri matar da ta hana Ni shan iska a gidan aure na, ta toshe min duk wata kafa da zan sarara, wallahi ba zai auri Mabruka wacce ta gama yawon banza ba kam, never! Ɗa na Ni na haife shi saboda haka babu wanda ya isa yayi min iko da shi.”
“Ai ba ke kaɗai kika haife shi ba kuma ba ke kaɗai kike da iko da shi ba.” Muryar DADDY ta sauƙa a kunnenta. A zabure ta waiwayo sai kuma ta kama kunkumi tace
“Ai duk laifin ka ne Daddynsu, na ce bana so dole sai kun nuna min isa akan cikin da na raina na kuma haife har ya zama mutum?, Wallahi ka ji na rantse Umar wallahi sai an fasa auren nan ko kuma ran kowa ya ɓaci don ba zan bari a yi min cin kashin nan ba.”
Mommy Nasiba ce wannan karon take shirin ƙara saukewa Mommah wani marin taji Daddy yace
“Rabu da ita Hajiya Nasiba, ta gama haukarta babu abun da zai fasaya.”
A harzuƙe Momma tace
“Ni Kake cewa mahaukaciya ko Umar? Wallahi za