Showing 1 words to 3000 words out of 157517 words

Chapter 1 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5124

[11/10, 12:22 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: Typing 📲

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*


Wattpad: @diamond_bhatool
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._

*Chapter 1: Zahrah settled down at Abatcha estate*

*PAGE* 0️⃣1️⃣

_Assalamu Alaikum, barkanku masoyana na ɓoye da Kuma zahiri, yau Diamond Bhatool ta fere alƙalaminta tare da sabunta shi don cigaba da rubutun littafin *A BABBAN GIDA*, ina fatan masoya zaku bani haɗin Kai sosai ta hanyar sharing da Kuma sharhi ga duk update da na sake muku. Taku har kullum, ITZ Diamond Bhatool 💎._

_Sannan masu son amfani da littafi na ko buƙatar karanta shi, ƙofa buɗe take bayan samun izini daga gare Ni, na gode._

_Wannan shafin naku ne Angels ɗina da koyaushe nake alfahari da ku, Meenal da kuma shaheedah, love U much 💕 😘_





“Maaa..ma...dii...diiiiiiiiiii...diiiina...ceeee”
Daga haka ta faɗi sume. Da sauri Daddy da kuma Laraba suka yo kanta kowa ransa fal tambayoyi.
Daddy da kansa ya ɗaga Hajjaty ya ɗaura ta kan doguwar sofa da ke parlourn. Da hannun yayiwa Laraba alamar ta kawo mishi ruwa. Bayan ta dawo ta bashi, daga nan ya sa ta ta shigar da baƙuwar da basu san sunanta ba ciki, a hannunsa ya shafa ruwa sannan ya shafi fuskar Hajjaty da ke kwance. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana buɗe idanunta don ƙara tabbatar da abunda ta gani, Madina ta dawo gare ta.
A rarrabe ta furta “Ya...U...dai...ta..ta...da...w'plp00lp0liikp8im00oA ɓangaren Zahrah tun lokacin da tsohuwar ta faɗi jikinta yayi sanyi zuciyarta ta k tun daga lokacin ta ji duk wani ƙarfin guiwa nata ya baje, tsoronta ɗaya ne ma kada su ƙi aminta da zamanta, in dai kuwa hakq ta faru ba ta da madogara sai Allah, daman nan ne hope ɗinta, ta nan ne ta ke san ran zaa nemo Mama, to su ma yanzu ba ta da assurance na zama da su ɗin.
Laraba ce ta zo ta kalle ta cike da girmamawa don su al'adar wannan gida haka take, komai ƙanƙantar mutum dole a girmama shi.
“Ƴan mata Alhaji ya ce a kai ki masauƙi, ki biyo ni”
Miƙewa Zahrah tayi ta bi bayan Laraba, dogon corridor suka bi, bayan sun ƙare suka tsaya dai-dai wata ƙofa, ita dai Zahrah ido ne kawai nata, Laraba da kanta ta buɗe mata ɗakin ta ce “ki shiga ki watsa ruwa ki huta, ni bari na je na kawo miki abun taɓawa”
Da kai ta bata amsar tana shigewa cikin ɗakin wanda tana shiga sassanyan iska mai cike da ni'ima da kuma daddaɗan ƙamshi ta bugeta. Lumshe idanuwanta tayi ta ce “Allah yayi duniya da kayan morewa, kamar ba za'a mutu ba!” sai kuma ta ajiye Ghana must go nata a gefe tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo, dontunda take bata taɓa ganin ya shi ba a rayuwarta kai ko gidan Ammin Badi'a da take ganinsa mai kyau ko rabin wannan bai yi ba. Ɗan taɓe fuska tayi kamar zata yi kuka. “Allah sarki Mama na ko ina kike?, yaushe zaki dawo gare Ni? Waige-waige Zahrah ta fara tana neman ƙofar da zata Kaita toilet ɗin don ta watsa ruwa kafin nan, ƙofar da ta hango yasa ta nufi wurin.

Ko da ta shiga toilet ɗin da ƙyar ta iya sarrafa bayin saboda bata taɓa amfani da kwatankwacinsa ba, in taƙaice muku dai Zahrah bata fito ba sai da ta taɓa komai na ciki saboda tsantsar curiousity irin nata. Tana fitowa ta nufi Ghana must go nata ta buɗe, cikin kayan da ta kwaso babu laifi suna da kyau musamman na bibalo da ta juyo ta taho da su. A cikinsu ta cire wata riga da skirt na atampa ta saka, ta yafa veil blue Wanda ya shiga da atamfar.

Kamar wacce akai ma albishir na aljanna haka take murmushi babu ƙaƙƙautawa, knocking da taji ana yi yasa ta gyara zamanta a kan gadon tana faɗin “A shigo”, da ƙyar ta gimtse dariyar da ke cinta saboda yadda wai yau ita ke bada umarnin a shigo. Laraba ce ɗaule da tray wanda aka jera food flasks kusan huɗu sai kuma jug da cup a gefe, plate, spoon da kuma fork sai wuƙa.

A gaban Zahrah ta ajiye ita kuwa Zahrah kamar bata gani ba sai da Laraban ta ce “Ga abinci nan Hajiya ”
“Na gode” ta tsinci kanta da bata amsa. Sai da taji ƙarar rufe ƙofar Laraba kafin ta tashi daga gadon tana juyawa. Tsawon daƙiƙu biyu tukun ta jawo tray ɗin ta zauna kan carpet ɗin da ke Malale a ɗakin. Ɗaya bayan ɗaya ta buɗe flasks ɗin tana zaro ido tare da lashe baki kamar wata mayya.
“Wai wa wai!, yau akwai shagali, Ni Zahrah aka titso ma wannan abinci!” ta faɗa tana riƙe haɓa sai kuma ta gyara zama ta zuba abincin ta fara ci. Sai da ta ƙoshi tukun ta tura tray ɗin gefe sannan ta zuɓa coconut juice da ke cikin jug ɗin a cup ta sha. Ta daɗe bata yi irin wannan cin ba yasa taci tayi nak da ita kafin ta baje sai kuma bacci.

Da azahar ma Laraba haka ta jibgo mata abinci, bayan ta ci ta yi sallah sannan ta kwanta.


**************************

*Toro*
*Jahar Bauchi*

“Sannu baiwar Allah, sannu, sha maganin kada ki zubar fa” Tsohuwar ce ke faɗa yayin da take bawa matar da aka tallafo ta alamar dai ba mai lafiya bace musamman yadda ƴan matan biyun suka dago ta daga kwance.

Kamar ta san me aka faɗa mata bata dawo da ruwan maganin ba, ganin ta sha har ya ɗan tsirga mata yasa suka mayar da ita kwance.
Tsohuwar ta dubi ƴan matan ta ce “ke Balki ɗakko zani a ɗaki ki lulluɓa wa baiwar Allahn nan kada ƙudaje su takura mata.”
“To Inna ” ta bata amsa tana miƙewa tsaye sannan ta wuce ɗauko zanin. Ɗayar da har yanzu ke zaune gefen matar ce ta kyaɓw baki tace “Inna wai don Allah ina kuka samo matar nan?”
Harararta tsohuwar tayi tace “Bani waje Nafisa, ke dai ba zaki taɓa canzawa ba shegen gulma kamar uwarki salamatu” zaro ido tayi jin an haɗo da uwarta sai kuma ta tura baki.
“Kai Inna ai ba gulma bace, kawai tambaya ce, Allah matar ne ta bani tausayi kuma wallahi na taɓa ganin mai kama da ita”
Cike da zumuɗi Inna tace “Matso nafisatu, faɗa min a ina kika taɓa ganinta, wallahi Kinga wannan baiwar Allah mugun tausayi take bani, kinganta wallahi a can wajen kangon nan na layin su Mamuda na ganta kwance, ke nifa na zata aljana ce.”
“To Inna shine sai kika ɗaukota?” Balki ta tambaya.
Inna tace “Kinga Balki rufa min asiri, bayan na ganta sai na ƙarasa na tambaya mutum ko aljan, shine naji shiru, wallahi haka kawai ta bani tausayi saboda kayan jikinta tsaf tsaf suke kamar dai kurciya aka mata. To da Mamuda yazo wucewa cikin Sa'a na saka shi ya kawo ta gida shine nake bata jiƙe-jiƙenmu na gargajiya, amma nayi magana da Malam Sufi yace zai zo ya duba ta.”

Jugum suka yi suna kallon Inna kowa na jajanta batun baiwar Allahr, gashi kuma tana mugun yi musu kama da wata da suka taɓa gani a social media. Kawar da tunanin suka yi suka ci gaba da hirarsu da kakar tasu.


**********************

*Oxford University of London*

Samari ne biyu zaune kowa na fuskantar ɗan uwansa sai kuma table ɗin da yayi musu shamaki. Kyawawa ne duk su biyun ga kuma tsantsar kama da suke da juna sai dai ɗayan ya ɗara ɗan uwansa kyan fuska da kuma na jiki.

Mai ƙarancin kyau ɗin ne ya dubi agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ce “Sadauki time ya cika fa, we've to go no, Alhaji Baba yace da mun koma na ƙira shi na haɗa ku tunda kai ka rufe wayar ta ka”
Wanda aka ƙira da Sadaukin Kamar ba zai bada amsa ba can kuma sai ya ce “Ok, amma Khalil sanin kanka ne ba don shi na rufe wayar ba ko?”
Baki ya kyaɓe yana faɗin “Wannan kuma kai ya dama Sadauki, na riga nayi iyakar iyawa ta ganin ka rage wannan ƙunci da ka yafa wa kanka amma abu ya gagara, to ya kake so kuma nayi maka?, kaga yanzu dai let's get going, in mun je we'll talk”

Ba tare da ya ce komai ba ya miƙe jiki babu ƙwari yana ɗaukar key da kuma tablet ɗin da ke kan table ɗin, daga haka suka wuce zuwa masauƙinsu kasancewar a hostel suke.

Ko da suka isa Khalil ya ɗauko wayarsa kasancewar ba da ita ya fita ba, number Alhaji Baba ya ƙira, bugun fari kuwa aka ɗaga wayar, da sallama a bakinsa kafin ya ce “To na cika alƙawarin tsoho mai ran ƙarfe, ga Shalelen da ya ɓoye maka kansa nan kuyi magana” daga haka miƙawa Sadauki da ke kallonsa ta gefen ido wayar.

Amsa yayi tare da kara ta a kunnensa sai kuma yayi shiru.
“Sadauki!” kamilalliyar Muryar dattijon ta bayyana. Shiru Sadauki bai amsa ba, sabo da halinsa yasa tsohon ya ce “Kana ji na ko?”
“uhm” ya bashi amsa a taƙaice.
“Tun jiya nake famar ƙiran wayarka amma bana samu, na shiga damuwa sosai” sai a lokacin Sadauki ya ɗan saki fuskarsa tare da sanya wani tsadadden murmushi kanta.
“Ina lafiya Alhaji Baba, Ka daina damuwa sosai a kai na, zan kula da kaina yadda ya kamata”
Alhaji Baba ya ce “Ai ba zan iya ba, musamman da Baban ka ya tuntuɓe Ni da zancen nan, Abinda nake so da kai yanzu shine ka buɗe wayarka, duk wanda ya ƙira ka ka ɗaga wayarsa ka nuna masa babu komai kaji?”
“Ok” ya faɗa a taƙaice lokaci ɗaya kuma fuskarsa ta sauya launi zuwa ja kamar wadda aka daka.
Jin shirun yayi yawa yasa Alhaji Baba faɗin “Tunda baka son magana da Ni Sadauki bawa Khalil wayar”

Ba kunya sai tsoron Allah haka ya miƙawa khalil ɗin wayar shi kuma ya wuce can cikin ɗakinsa tare da zubewa kan gadonsa.


******************************

*ABATCHA ESTATE*

Jerin motoci ne kusan biyar waɗanda dukkansu suka kasance na kallo suka Turo hancinsu zuwa katafaren estate ɗin, makeken gate ɗin guards suka buɗe, nan suka samu damar shigewa ciki. A mai flat wato ɓangaren tsoffin gidan suka yi parking motocin, nan suka fara fitowa.

Cikin waɗanda suka fara fitowa ne ɗayan su ya buɗewa Alhaji Baba ƙofar motar ya fito. Masha Allah, kyakkyawan dattijon ya tako da taimakon ɗaya daga cikin mutanen wanda ke tsantsar kama da shi. Haka sauran suka biyo bayansu zuwa cikin gidan.

Babu kowa a katafaren parlourn wanda ya kasance mai faɗi da yalwa sosai, Wanda ke riƙe da Alhaji Baba ne ya zaunar da shi kan kujerar sannan ya nufi wani ɗaki wanda ya ƙara tabbatar da cewa ɗakin Hajjaty ne. Ganinta zaune kan sallaya alamar dai sallar maghrib ta idar ya sa ya ƙarasa gunta yana risinar da kai ƙasa.
“Sannu da gida Hajjaty”
Ɗagowa Hajjaty tayi tana murmushi ta ce “A'ah Muhammad kun dawo kenan!” fuska sake shima ya amsa mata da faɗin “Eh Hajjaty mun iso kuwa yanzu”
“To bari na sa Laraba ta kawo muku abinci sai ku ci ko”
Ba tare da ya Musa ba suka fito tare da Hajjaty, sauran suma dake zaune ƙass suka miƙa gaisuwarsu ga Hajjaty, fuska sake ta amsa tare da ƙwalla ƙiran Laraba. Abinci ta jera musu kan dogon table da ke ɗauke da aƙalla kujeru hamsin sai kuma ta koma. Ganin lokacin Isha yayi yasa suka wuce masallaci kawai. Suna dawowa kuma suka baje abincin suka fara ciki.

Sai da suka kammala kafin Dattijo ɗazu (Daddy) yayi gyaran murya ya ce “To! Ɗazu fitarku wani baƙon al'amari ya faru har ya kai ga Hajjaty ta suma” sai kuma yayi shiru.
Zuciyar Abba har ta fara bugu don tunaninsa ko wani abu ya faru da matarsa ne da take da shegen jarabar tsiya.
“Akwai wata baƙuwa da ta kusa sati tana jele estate ɗinnan sai dai bata samu damar shiga ba sai yau. Kar na ɓata muku lokaci dai wannan yarinya kana ganinta ka ga jinin gidan nan, suna mugun kama da ƴar uwarmu ƙwaya ɗaya wacce ta ɓata shekarun baya.”

Zuciyarsu ce ta buga a tare kowa fuskarsa ta sauya musamman Alhaji Babba wanda duk cikinsu ya fi yin sabo da ƴar uwartasa kafin ɓatanta.
“Yanzu dai babu wani ɓata lokaci ko jan magana, ina ga za'a iya ƙiranta yanzu a ji daga bakinta daga ina take idan har ta tabbata jinin mu ce sai a haɗa taro gobe in Allah ya kaimu”
Kowa yayi na'am da maganar Daddy shi yasa Hajjaty da ɗauki da kuma anxiety suka lulluɓe ta ta ƙwalla ƙiran Laraba, nan ta sanar da ita tana son ganin baƙuwar ne ta ƙira ta.

*Me kuke tunani game da wannan labari mai cike da cakwakiya, ƴan uwantaka, munafurci, soyayya da kuma saran ɓoye (na billyn Abdul)*

*_Yanayin yadda naga kun amshi littafi na biyu ta hanyar yi min sharhi shi zai sa na ci gaba da muku typing babu ƙosawa, mutane na na channel kuma idan bana ganin reactions zan daina kawo muku shi baki ɗaya, sannan kada a mance ake taya Ni sharing zuwa wasu groups ɗin, wannan ma salon ƙauna ne, ina so saƙon ya kai inda ya kamata, ku sani DIAMOND BHATOOL taku ce!🤗😍😘_*

[12/10, 7:56 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎:
*_Typing 📲_*

🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family 🏠)_
★TAKUN ƘARSHE★
[Labari/Rubutawa]
*Fadimatu Adamu Hassan*💎
*A.k.A Diamond Bhatool*
*(Famanté)*


Wattpad: @diamond_bhatook
Arewabooks: @diamondbhatool

_Ƙirƙirarren labari mai cike da ƴan'uwantaka, gwagwarmayar rayuwa, makirci, mugunta, hassada, munafurci, rashin tausayi da kuma dauwamammiyar soyayya maras iyaka_

_Creative work of love vs. societal expectations., family bonds and loyalty, Identity and self-acceptance, Hypocrisy and jealousy's destructive power._

*Chapter 1: Zahrah settled down at Abatcha estate*

*PAGE* 0️⃣2️⃣

_Sadaukarwa gare ku masoyan asali, boyayyu da kuma wanda suka bayyana a zahiri, Allah ya bar ƙauna Ameen_

*Masu Neman labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan zaku samu:*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

*Join my WhatsApp group 1*
https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66

*Join my WhatsApp group 2*
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB





Hajjaty da kanta ta ƙwalla ƙiran Laraba da ke kitchen, nan ta faɗa mata saƙon da zata isarwa Zahrah, ko da ta faɗa mata ta ja ƙofar ta rufe mata, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata yayin da wani irin fargaba da tsoro suka lulluɓe ta. Cike da ƙarfin hali ta miƙe tare da goge hawayen sannan ta nufi ƙofa.

Taron jama'ar da ta gani wanda mafi akasarinsu maza ne kuma da gani manya ne yasa ta ɗan dakata tana dafe ƙirjinta. Kanta ta sunkuyar ƙasa sakamakon jin Muryar Hajjaty tana faɗin “Ƙaraso nan yarinya”. Babu musu ta nufi wajensu zuciyarta ba bugawa da sauri da sauri, Dukkansu kowa idonsa a kanta yake hakan yasa har ƙafarta ta fara harɗewa kamar zata faɗi, a tare zukatansu suka buga sai dai maganar Alhaji Baba yasa duk hankaulansu dawowa gare su.

Hajjaty ne ta nuna mata gefenta sai dai ko da ta ƙaraso sai ta zame ƙasa ta zauna a kan carpet dai-dai ƙafar Hajjaty. Cikin murya mai ɗauke da zallar izza da nutsuwa Alhaji Baba yayi sallama suka amsa masa. Gyaran murya yayi yace.
“To ba komai ya tara mu nan ba sai batun da na riska bayan dawowa ta daga tafiya. Ɗan dakatawa yayi tare da mayar da dubansa ga Zahrah wacce kanta ke ƙasa a takure.
“Baiwar Allah kin zo cikin wannan ahali da abun al'ajabi sai dai mu nan bamu san ke wacece ba, idan babu damuwa muna son sani.” Ya idasa yana ƙara kallon Zahrah da yake ji kamar ya rungume ta saboda tsantsar kamanninta da ɓatacciyar yarinyar su.

Ba tare da Zahrah ta ɗago ba ta goge hawayen da suka zubo mata tare da jan hanci, “Da farko suna na Zahrah Abdulkarim Kuru, na zo ne tun daga jahar Bauchi saboda saduwa da ku. Ni ɗin a taƙaice ba kowa bace ga wannan ahali face jika!”
Gabansu ne ya faɗi jin furucinta, sai dai ita Zahrah murmushi kawai ta yi tunawa da baƙar ranar da aka rasa Mama.
“Eh Ni ɗiyar Madina ce, tabbas ita ce mahaifiya ta, tabbacin hakan kuwa shine kamanni na da ita, ban kwaso komai na mahaifi na ba sai yatsu.”
Nan dai ta fara basu labarin ɓatan Mama Wanda a ainihi guduwa tayi kamar yadda tayi mata bayani a kwanakin baya, guduwarta zuwa wurin Abbanta, auren su, haihuwarta, mummunan kisan da aka yi wa Abba, daga nan ta hau bada labaron auren Mama da kawu, wanda ya kasance dan uwa ga Abba, irin zaman auren da suka yi, har zuwa ɓatan Mama. Tuni jikinsu yayi sanyi gabaɗayansu. Hajjaty kuka take shaɓe-shaɓe tare da rungume Zahrar a ƙirjinta kamar wacce za'a ƙwace ta daga gare ta.
“Ni dama na sani,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login