Showing 210001 words to 210924 words out of 210924 words

Chapter 71 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22861

a bakin ki.... I don't care.... I love you for who you are.. Ni ke d'in nake so..... Murmushi suka sakar ma juna kafin ya jawo ta had'i da rufa masu bargo masu light off.....

*************


"Zubaidah ta haifi yarinyar ta k'atuwa kyakkyawa..... Ranar suna yarinya taci sunan Maman Jalal wato Suhaima.... Kai Masha Allah... Wann yarinya taga gata da soyayya wajen illahirin dangi baki d'aya... Kowa so yake ya burge uwar yarinya da jaririyar ta....

"Hawan daba mai ji da lafiya aka shirya a garin Gombe na murnan samun wann jaririya....

"Kai Masha Allah... Komai yayi sai Allah son barka...
"Jalal baya sama baya k'asa....


"Suna zazzaune a wargajejen bedroom d'in Zubaidah, Kausar Zahidah da kuma ita kanta Zubaidar sai tad'i ake irin ta k'awaye, Baby Suhaima kuwa tana can sashen Mai Martaba ana saka mata albarka.... Wata kuyanga d'aya ce ta shigo cike da rusunawa ta sanar dasu wata mata tana sallama.... " Zahidah tace maza ta tambayo sunan ta... Jim kad'an Kuyangar ta dawo ta rusuna kafin tace " Tace sunan ta Zulaihat...

"Zubaidah ta saki murmushi kafin tace " Bisimillah a shigo da ita....

"Kausar da Zubaidah ne suka santa.. Basuji mamakin ganin ta da Baby ba, saidai sun tausaya mata sanin Umar yana gidan Yari...

"Bayan sun gaggaisa ta nuna masu babyn ta sann tayi murna ma Zubaidah... Zubaidah ta mik'a hannu ta karb'i Muhammad tana kallon sa... Sosai take murmushi take kallon yaron had'i da yima addu'a da fatan zama d'a na gari... Zubaidah tayi introducing Zahidah ma Zulaihat , nan Zulaihat ma ta labarta masu abubuwan da suka faru da ita, ciki harda auren Imam da kuma mutuwar Umar.... Sosai suka tausaya mata suka kuma mata murnan auren Imam da tayi.....

************

"Mumsy ta saya ma Mummy da Mamy gida mai kyaun gaske har ma'aikata ta sama masu... Haka suka dinga mata godiya suna hawaye..... Nan kuma su Mummy suka sami labarin mutuwar Kasim Dasuki a gidan Yari... Allahu Akbar, shi kuwa Barr Kansa ne kawai ke aiki a jikin sa ko motsa jikin sa bai iya yi...

"Allah ka bamu jarabawan da zamu iya ci a rayuwa.....

"Wa'adin da aka d'ibar ma Hadiza sun cika, an fito da ita daga gidan Yari, Idan kaga Hadiza gaba prison ya canza ta, ta zama mutuniyar arziki, har karatun addini dana boko tayi a prison, sosai Hadiza ta nustu, tabbas gidan Yari, Alkhairi ne a gareta...
"Hamma da Kamal babu wanda yakaisu farin ciki, gida mai ji da lafia Jalal ya sai masu suka koma ciki cike da farin ciki



**************

*Some Years Later*


"Daddy pls let's go for a vacation..... Suhaima 'yar shekara takwas ta fad'i...
"Tura laptop d'in gaban sa yayi kafin ya jawota ya d'aura bisa laps d'insa yace "Angel where do you want us to go..??

"Suhaima ta d'anyi far da idanu ta d'aura d'an yatsan ta saman kumatun ta kafin tace " Let's see... Kaman tana tunani... Can kuma sai cewa tayi yesss.. " Daddy Malaysia pls, I wanna visit Ghenttin Island...

"Jalal ya murmusa kafin yace " Whatever Daddy's Angel want, Daddy will do it right away.... But you see Precious , Daddy is a very busy Man, I got alot of commitments to take care of.... Why not mu bari sai wani hutun...

"Suhaima ta d'an tab'e fuska tana son yin kuka, Jalal sai faman ririta ta yake yana rarrashin ta..... "Zubaidah dake sauk'owa daga stirs rik'e da yaro d'an shekara uku , wand yaci sunan mahaifin ta wato Ibrahim, suna kiran sa Khalil, sai faman mitan sakalta Suhaima da Jalal keyi take....

"Bud'e hannu yayi ma yaron kafin yace " Come here Champ..... Da gudu yaron ya tafi ya rungume sa Jalal ya d'aga sa sama yana fad'in" My Champ is really adding weight, I barely pick him up..... Sai wasa suke da yaran suna d'alewa kansa.....

"Murmushi tayi tana mai kallon su yanda suke cike da farin ciki..
"A hankali ta furta Alhamdulillah....

*Nima Sameena nace wann shine k'arshen labarin ZUBAIDAH..... ina rok'on Rabbi fad'akarwan dake cikin sa ya amfane mu dasu, kurakuran dake ciki ya gafarta mana... Ameen*

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAJ!! ALHAMDULILLAH!!!

*Dukkan Yabo da godiya sun tabbata GA Ubangiji ALLAH wanda ya bani ikon rubuta littafin nan cikin kwanciyar hankali daga farko har zuwa k'arshe.*


*Ina mik'a godiya ta a gareku k'ungiya ta ta KAINUWA bisa jajircewan da kukayi da goyon bayan ku da shawarwarin ku a gareni har Allah yasa na kammala wannan littafi, Allah Ya saka maku da Alkhairi ya kuma k'ara d'aukaka da hazak'a.... Allah Ya barmu tare har a Aljannah..... Ameen😍*

*Queen Samy Novels Forum*
*Kainuwa Fans Groups 1to6*
*ZBI*
*Duniyar Novels*
*Aysha Sada Machika Novels*
*Fadila Talba Novels*
*Musha Karatu na Kausar luv*
*Novel da Zumunci #Maman Sadiq*
*My darling Sis Rally Garba*
*My darling Shawty*

*Na gode k'warai da goyon bayan ku a gareni... Sameena Aleeyou Aka Queen Samy ke maku fata na Alkhairi😍🤝*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login