Showing 204001 words to 207000 words out of 210924 words

Chapter 69 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22884

"Cikin kuka yaci gaba da fad'in" The Dasuki's are to blame for everything.... Su suka destroying rayuwar kowa, su suka fara jefa kowa cikin k'uncin rayuwa....

"Mum d'in Tariq da Alh Maina dake gefe kuka suke su duka biyun, suna kaicon rayuwar da suka jefa d'ansu ciki kafin ya bar duniya, ko kad'an basu ga laifin Umar ba sai nasu....

"Umar ya d'ago kai yana kallon Zubaidah kafin yaci gaba da fad'in" Zubaidah ki sani I did it all because of you, duk abubuwan da nayi nayisu ne because I love you, snn da zan sami chance na kashe su gaba d'aya i'll kill them all, harda mijin naki wanda nafi tsana fiye da kowa cikin su.... .I loved You Zubaidah And until now I still does , and i'll die loving you.... You and only you.....
"Basu bamu chance mu kasance tare ba, sunyi destroying happy life d'in da muke ciki, sabida son zuciya irin nasu...

"Sosai Zubaidah ke kuka yayin da Jalal ya sadda kansa k'asa kurum hawaye na neman ciko idanun sa....

"Zulaihat ma kuka take kaman ranta zai fita tana mai shafa jaririn cikin ta dake k'unshe a jikin ta... Imam kallon ta kawai yake shima hawaye na neman ciko idanun sa...


"Kotu tayi tsit sai rubuce rubuce da Alk'ali yake...
"Tabbas yau ake yin ta, yaune ranar bankad'an asiri ranar tonan silili....

_'Yan uwa wann na duniya kenan inaga ranar mai gaba d'aya... Ranar da gabb'ai zasu bada shaida, shin mun shirya ma wann ranar....???? Kukan kurciya dai Jawabi ne Mai hankali shi ke ganewa.... Allah ka sa mufi k'arfin zukatan mu ka rabamu da sharrin shaid'an da Zuciya... Ameen_

******

"Alk'ali ya d'ago bayan ya gama rubuce rubucen da zaiyi snn ya furta " The Court Decide.....

"Gaba d'aya kotu ta mik'e kowa ya mik'e don jin hukuncin da za'a zartar....


*Sameena Aleeyou Mrs*

[7:22AM, 2/9/2018] โ€ช+234 809 781 2439โ€ฌ: ๐ŸŒ’๐ŸŒ’๐ŸŒ’๐ŸŒ’ *ZUBAIDAH*

99

*ยฉSameena Aleeyou... โœ๐Ÿพ*


*_Dedicated To All Victims Of Rape..._*



"Hamma da Hadiza sukai sallama da juna, su Zubaidah ma har zasu shige mota suka k'araso yanda suke, kowa sai ya tausaya ma Hadiza da Hamma idan ya gansu, zaka fahimci shak'uwa da soyayyan juna a idanun su... Shakka babu Hadiza ta shiga taitayin ta, ta kuma yarda ita dai duniya budurwa ce amma ta wawa...
"Ta kuma share hawayen da suka zubo mata kafin tace " Nasan Kamal na hannun na gari, Habibu ka yafe mun duk abinda na maka kaida k'anwar ka...
"Hamma ya share hawayen sa kafin yace " Hadiza mun yafe ki tun tuni snn shekara guda kaman kwana guda ne a wajen mai sama, Allah yasan hakan ya zama sanadin shiriyar ki, snn ki sani ni Habibu zan zauna na jira ki har wa'adin fito dake ya cika......
"Suka rungume juna suna hawaye...

"Gaba d'aya jikkunan su Annah yayi sanyi haka Hadiza ta ringa sallama dasu one by one.... Annah ta rik'e hannun ta gam tana hawaye take fad'in insha Allah Kamal yana hannun na gari, ki kwantar da hankalin ki, Allah Ya wuce mana gaba baki d'aya...

"Zubaidah kam lamo tayi cikin jikin Jalal don gaba d'aya babu k'arfi a jikinta, snn sosai take jin zafin abinda ya samu Hadiza duk sai ji take tamkar laifin nata ne, Hamman ta doesn't deserve to go through any of this... Amma hakan Allah Ya k'addara HE is the best planner... Allah yasa hakan shine silan shiriyar Hadiza da masu hali irin nata....

"Sunaji suna gani wata ganduroba ta janye Hadiza aka wuce da ita.....

"Mum d'in Tariq ce ta k'araso wajen tana mai goge ragowar hawayen ta da hankacif, cikin muryar kuka take duban Zubaidah tana fad'in" Zubaidah ki yafe wa d'ana Tariq snn muma ki yafe mana, da ace tun farko bamu bi son zuciya ba da bata kawo mu ga haka ba.. Ki yafe mana don Allah.... Jalal kaima ka yafe mu...

"Zubaidah ta rik'e hannayen ta tana hawaye kafin tace " Wllhi na jima da yafe ma Tariq, na sani he wasn't like them, and he was about to confess... Ba laifin sa bane denying d'in da yayi, da ace beyi hakan ba na tabbata da tuni kuma Alh Kasim ya halak'a ku, yin hakan da yayi yayi daidai... Snn insha Allah yanzu zai fi samun kwanciyar hankali, Allah Ya gafarta masa da sauran musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.... Tana kaiwa aya Mum ta rungume ta sosai tana hawaye...

"Jalal ya d'an murmusa kafin yace " Mum ina mai k'ara maki ta'aziyan aboki na... Allah yakai haske makwancin sa ya gafarta masa laifukan sa...

"Mum ta murmusa kafin tace " Ameen Jalal, Allah Ya albarkace ku ya azirta ku da zuri'a d'ayyiba... Gaba d'aya har su Annah suka amsa da Ameen....

************

"Yau dai duk gidan Talabijin d'in da ka kunna labarin kenan... Finally yau an gama da shari'ar da mutane suke ta son jin k'arshen sa...Allah Ya kawo k'arshen shari'an.


"Zahidah da Kausar kuwa tunda suka had'u haba nan fah Abuja ya kuma yi ma Zahidah dad'i... Kwata kwata batasan Kausar dasu Jalal sun san juna ba... Hakan yayi mata dad'i sosai tunda yanzu an zama tamkar 'yan uwa..

"Zahidah ta dube ta kafin tace " Babe kice kema you're part of the story..

"Kausar ta murmusa kafin tace " Ai labarin ZUBAIDAH ya had'a da mutane da dama... Ko wanne da irin nasa k'alubalen da ya fuskan ta...

"Zahidah ta gyad'a kai kafin tace "Wann hakane 'yar uwa... Allah Ya amfanar damu da darussan dake ciki..
"Kaman daga sama suka jiyo muryar Zubaidah tana fad'in "Ameen..

"Gaba d'aya suka juyo suna kallon ta suna masu sakar ma juna murmushi..

"Kausar tace " Zuby nifah zan rubuta labarin ki idan kin min izini...

"Zahidah tace " Kaman kin shiga raina friend..

"Zubaidah ta zauna cikin d'aya daga cikin kujerun kafin ta d'anyi Far da idanu tace " Bayan duk wanda Samyn mu ta rubuta kuma...

"Suka murmusa gaba d'aya kafin suka ce kuma fah haka ne.. Our Samy wrote everything, ba naki kawai ba ma harma da namu...
"Suka dara gaba d'aya kafin Zubaidah tace " Wann haka ne... Ubangiji yasa rubutun ta Ya amfani Al'ummah..

"Muryan Jalal, Ansar da kuma Shattima suka jiyo suna amsawa da "Ameen"...

"Suka juyo suna kallon su gaba d'aya kowa na kallon masoyin sa...

"Kausar tace " Ah ashe dai an kasa mana kunne ne anata sauraren mu..

"Ansar yace " Gulmar ta isa haka maza ki tashi mu tafi is getting late already, Mumsy might be worried...

"Kausar ta d'an turo baki tace " Kai Big bro, fah ba gulma muke ba tad'in mu ne na mata...

"Shattima dake danna wayar sa yace " Ai tad'in matan kenan real name d'insa gulma, kuyi addu'a kafin ku tashi...

"Sukayi dariya gaba d'aya.... Basu ankara dasu Zubaidah da Jalal ba tuni ya sure ta sun shige d'aki yanai mata rad'i a kunne da " Baby someone's in need of you....
"Kaman ta k'walla ihu haka taji amma bata so taja hankalin mutane wajen su snn tasan bazai ajiyetan ba, yin shirun shine rufin asirin ta...

"Ansar ya wani sha mur cike da umarni yake magana ma Kausar.... Haka ba don taso ba sukayi sallama da Zahidah da alk'awarin Zahidar zata je mata gobe kafin su wuce Gombe....

"Har waje Shattima da Zahidah sukai masu rakiya kafin suma suka jero suna hiran su ta masoya....

******

"Tunda aka shiga mota Kausar ta turo baki gaba ko yayi magana bata amsa sa...

"Murmushi yayi cikin ransa yana mai yaba komai nata na burge sa... Bai kuma ce mata komai ba har suka iso gida..

"Yana gama parking tasa hannu zata bud'e motar, yayi saurin sakata a lock...

"Cikin sassanyar muryar sa yace " Lil Sis are you mad at me..??

"Ba tareda ta kalle sa ba tace " Ba kaine ba, just k'arfe takwas ne fah, kuma this is our first time da muka had'u da Zahidah in person..... Kum....

"Karkatowa sosai yayi yana kallonta jin ta kasa ci gaba da maganar nata, ba komai ya hanata ba, illa k'warjinin da ya mata...

"Ansar ya fahimci hakan ya murmusa kafin yace " Toh I'm sorry, kinji lil Sis... Amma kinsan abinda yasa nayi hakan, ever since that tragedy happened Mumsy bata so muna kaiwa dare a waje... Idan kin tuna ko ni kad'ai na fita da dare tana damuwa balle harda ke.... Hakan ma bai dace bane Lil Sis amma dai kiyi hak'uri kinji I apologize..

"Murmushi ta d'an yi kafin yace " Kinyi hak'uri...

"Tana mai murmushi take gyad'a masa kai shima murmushin yayi kafin ya bud'e masu mota suka fito...

"Fitowarsu keda wuya security guda daga cikin masu tsaron gate ya k'araso yana gaidasu kafin yace " Ma'am dama wani aika aka kawo ya k'arasa parking lot yana yaye wata hamshak'iyar Lamborghini da aka rufeta da tampol..... Daga Kausar har Ansar kallo suka bisa dashi...

"Ansar yace " Wa ya kawo snn Hajiya ta sani..???

"Security ya girgiza kai kafin yace "Aikan daga Senator Ali Ali ne yace wai zai kira k'aramar Madam sabida aikan nata ne, snn Hajiya bata sani ba, don lokacin da aka kawo duk baku gida ni kuma ban sanar da ita ba...

"Ya k'arashe yana mai mik'a wani takarda da key ma Kausar kafin yace " Ma'am wai zakiyi signing a nan...

"Harara kawai Kausar take galla masa tama rasa me zata ce...

"Ansar kuwa sai huci yake fizge takardan yayi ya keta lokaci guda.... Kausar ta bisa da kallon mamaki bata tab'a ganin sa cikin yanyin ba...

"Wrathfully yake fad'in" You're very stupid, uba wa yace ka karb'a..... Kasan yanda zakayi ka fitar da wann motar daga gidan nan kaji na fad'a maka wllhi bazai kwana a gidan nan ba....

"Cike da tsoro security ke kallon Ansar, zaiyi magana yace " I'm done talking, get this whatever outta this house, if you don't want to get yourself fired.... Snn daga yau kar ka sake amsan wani abu nasa... ... Daga haka ya nufi cikin gidan yana huci..

"Kausar jiki a sanyaye ta bisa da kallo kafin tabi bayan sa....


"A k'ofar da zai sadaka da cikin gidan ta had'u dashi sai faman huci yake...
"Kaman wata munafuka haka ta k'araso wajen..... Cikin wani irin huci yake fad'in" Since when...?? Since when mutumin nan ke maki waya...??

"D'an jim tayi kafin tace " About a month...

"Ansar ya fuzar da iska kafin yace " Shine baki sanar dani ba, why why... Meyasa baki sanar dani ba...

"Ganin yanda ya hayayyak'ota yana mata masifa yasata saurin fad'in" And why must I tell you.... Sabida bana son shi banga dalilin da zaisa na sanar da kai ba...... Cikin sauri ta nufi cikin gida...

"A tamanin ya take mata baya.... Curus suka yi da Mumsy dake tsaye jikin window ta gama ganin komai....

"Ku k'araso ta fad'i tana mai k'arasawa cikin parlour...

"Kafin su soma mata bayani ta soma fad'in" Ansar kayi daidai da kace a maida masa motar sa.... And you Kausar ki sani Ansar is only trying to protect you ne, he's like a brother to you.... You shouldn't have disrespected him, ba hanaki zaurawa zamuyi ba amma dole musan su waye maneman ki ... Oya bashi hak'uri..

"D'an kallon juna sukai kafin ta basu hak'uri dukan su... Komai ya wuce... Mumsy tace tayi serving nasu dinner... Babu musu tayi yanda Mumsy ta sakata...

"Suna cin abinci yana satan kallon Kausar da har lokacin babu walwala a tattare da ita... Yayi murmushi a ransa kafin ya soma fad'in" Mumsy dama akwai d'an wani abin da nake so ki min...

"Mumsy tace " Me kenan d'ana..

"Ansar ya murmusa kafin yace " Mumsy dama aure nake so kije ki nema min since you're my only parent...

"Ai abincin da Kausar bata had'iye ba kenan, ta ajiye spoon tana duban sa cike da mamaki...

"Mumsy ta fad'ad'a murmushin ta kafin tace " Kai Son, naji dad'i sosai... In fact this is great news.... Ko ina ne kuwa nai maka alk'awarin zuwa koda yakai birnin sin ne....

"Ansar ya murmusa yace " Godiya nake Mumsy, you the best....... Basu ankara ba sai ganin Kausar sukayi ta mik'e zata bar table d'in...

"Ina zaki..? Mumsy ta tambaya...

"Baki a ture tace " Mumsy na k'oshi ne, I lost my appetite...

"Ansar yana d'an satan kallon ta yake murmushi kafin yace " Mumsy nasan matsalan ta, idan wancan Lamborghini d'in ne kar ki damu zan saya maki ko salary na na shekara ne zan tara na saya maki....

"Ni me zanyi da sport car motar maza kawai ni na k'oshi ne....

"Ansar ya ajiye spoon d'insa ya mik'e yana murmushi kafin yace " Lil Sis yaudai fushi kawai kike dani, kiyi hak'uri yau kam ma Apo zan tafi can zan kwana...

"Kukan da take matse wa ya soma zuba mata, ta juya da sauri ta rungume Mumsy tana fad'in" Mumsy kin gani wllhi yanzu Big bro bai damu damu ba, wai tafiya zai yi, tun kafin yayi auren ya soma barin mu, what if yayi aure... I'm sure matar rabamu zatayi dashi....

"Ansar sosai abin ya basa dariya, daga shi har Mumsy k'unshe dariyar su sukayi...

"K'arasowa yayi daf da ita kafin yace " Inace baki so nayi auren ne, toh ki kwantar da hankalin ki na fasa, duk abinda lil take so ayi shi za'ayi......


"Tura baki tayi ta wuce stirs da sauri.....

"Ya bita da kallo yana murmushi.... D'an juyowa yayi Ya dubi Mumsy gaba d'aya sai yaji kunyar ta Ya rufe sa...

"Mumsy ta k'arasa cikin parlour ta zauna.... Ansar ya tako a hankali Ya zauna a gaban ta saman carpet, yayi irin zaman rak'umi...

"Tattaro nutsuwar sa yayi gaba d'aya kafin ya soma fad'in " Mumsy thank you, thank you for everything...... Kin dawo min da soyayyar mahaifa da na rasa... Thank you for accepting me into your family... I know I owed you alot....

"Mumsy tana murmushi take kallon sa take giriza kai kafin tace " You don't owe me anything Son.... Ni yafi cancanta na mik'a gidiya ta ga Allah daya blessing d'ina with a Son like you Ansar ...... All I want shine na ganku kun sami abokan zama na gari... Both you and Kausar....

"Ansar ya d'an shafi k'eyar sa kafin yace " Thanks Mumsy...... Snann ya d'ora da.... Dama... Dama Mumsy there's something I want to ask of you.....

"Mumsy ta gyad'a kai kafin tace " Ina jinka Son go ahead...

"Idonsa naga Carpet yake fad'in" Mumsy if you may allow me... Ina son na nemi auren Kausar....

"Murmushin dake fuskar ta ya kasa gushewa, hawayen farin ciki suka ciko idanun ta....

"Jin tayi shiru yasa sa d'ago kai cike da tsoron amsar ta... Ya maida kansa k'asa k'irjinsa naci gaba da fad'uwa...
"Muryar Mumsy ya tsinkaro tana fad'in" Ansar da zanfi kowa farin cikin kasancewar hakan... But Son.... Kausar bazaura ce while on the other hand kai baka tab'a aure ba, shin kana ganin hakan yayi maka...

"Ansar cike da jin dad'i yake murmushi had'i da gode ma Allah kafin yace " Mumsy, I love her for who she' and I promise to take care of your Baby, cherish her and give her all the love that she deserves..... All I want is your blessings Mumsy.....

"Kausar dake lab'e saman Staircase... Wani farin ciki ne taji ya mamaye ta...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login