Showing 168001 words to 171000 words out of 210924 words
ba...
"Mata ta kad'a kai ta mik'e tsaye, take ta ga gaba d'aya sauran 'yan d'akin sun mik'e, idon Hadiza ya raina fata... Bata ankara ba taji sauk'an duka tako ina harda toshe bakinta sukayi don kar tayi k'ara aji..
"Haka d'ika d'ikan matan nan suka zaune Hadiza sukayita jibga tamkar an kawo masu jaka...
************
"Tana zaune gefensa cikin jikin sa aka gama dressing wajen da bullet d'in ya shige masa, aka nannad'e hannun cikin bandage..
"Zubaidah taci gaba da kuka tana fad'in" It's all because of me, babu Asmah da Amir saboda ni, kowa yana shan wahala saboda ni,.. Why all this, why this had to happen,....
"Hannu d'aya yasa ya rungumota cikin jikin sa gamida lumshe idanu... "Yana jin sauk'an aniyar zuciyar ta... Kafin ya soma furta " Babu abunda zai faru face yana rubuce tuntuni Zubaidah, Allah yafi mu sanin meyasa Al'amra suke faruwa haka. Never doubt what the Almighty can do, the Lord of the worlds Knows how to suddenly change things, He can suddenly Open the doors we never dreamed would open... He is the best Planner.... Ya k'arashe yana sakar mata sassanyar murmushi cikin k'arfin hali
" Gyad'a masa kai ta shiga yi da sauri tana goge hawayen idanun ta... Cikin wani irin murya mai rawa sosai take fad'in" I was so.... Scared, I thought I was going die,,... "It reminds me of that nigh 🌘..
" Shiiihhh" Jalal ya katse ta da fad'in haka kafin yace " Don't speak Baby,, Ina tareda ke babu abunda zai sake samun ki da izinin Allah, Duk tsananin bazan tab'a rabuwa dake ba, It's a promise .!!! Cikin zuciyar sa kuwa tsannin k'una da zogi yake masa wanda har yafi wanda yake ji a wajen ciwon sa.. " Ji yake da zai kama Umar tabbas da yayi masa kisan gilla...
"Dad'a matse ta yayi tana mai ci gaba da koke bak'in cikin ta... " A hankali ta iya furta " Duk sanda nake tareda kai Ya Jay I feel secured pls don't leave me kaji....
"Murmushi yayi gamida sumbatar kanta kafin yace " I love you Zubaidah bazan tab'a barinki ba till my very last breath, so ki daina tunanin akwai abinda zai sa ni Jalal na rabu dake, babu shi.. ...
"Ta kuma rungume sa tana mai tuno kalan ibtila'in dake kan faruwa dasu wanda daga wann sai wancan.
"A haka Dr ya shigo ya tadda su, ya masu prescribing magani su duka biyun kafin ya sallame su.
"Suna fitowa sukayi kicib'is da polisawa suna son d'aukan statement d'in Zubaidah, ga Journalist sunyi chaa tun daga waje...
"Ta kalli Jalal tana girgiza masa kai alamun bazata iya ba...
"Matse yatsun hannunta yayi sosai cikin nasa yana gyad'a mata kai kafin yace " You can do it, Ina tare da ke...
"Ta d'an sakar masa murmushi kafin suka k'arasa can wani rumfa 'yan sanda suka d'auki statement d'inta...
"Suna fitowa suka hangi Annah da Shattima.. Cike da mamaki suke binsu da kallo don basuyi tsammanin Shattima yazo ba...
"A tare Annah da Shattima suka k'araso yanda suke, Idanun su cike da tsantsan tausayi...
"Shi kuwa Jalal murmushin k'arfin hali kawai yake yi...
"Zubaidah ta k'arasa da sauri ta rungume Annah, hawaye na kwararo mata, Annah kuwa fad'i take" Ya isa Zubaidah, mu gode ma Allah... Allah kuma ya tsayar haka, Allah Ya bamu ikon cin jarabawar mu...
"Shattima ma k'arasawa yayi ya d'anyi hugging Jalal ta gefen sa maras ciwon kafin suka soma gaisawa, Shattima yai masa yaya jiki had'i da jaje da kuma addu'ar Allah ya tsayar haka..
"Jalal ya amsa da ameen had'i da tambayar sa su Ummah, Shattima yace " Duk suna lafiya sunce a gaida ku..
"Jalal ya murmusa kafin yace " Muna amsawa kuwa, mun gode sosai,
"Zubaidah da Shattima suka soma gaisawa sanda Annah ta tafi ta rungume Jalal d'inta....
"Jalal ya tambaye su yaya jikin su Kausar da Ansar, Annah tace " Ah Alhamdulillah, duk sunyi tawakkali, dukda pain d'in na cikin jikkkunansu, Yanzu haka ma daga can gidan Haj Raliyan muke, 'yan uwan Amir sun iso daga can Katsinan, Hafiz ma yana taredasu a can...
"Jalal ya d'an girgiza kai sanda tunanin Tariq ya fad'o masa, A hankali ya furta, Allah Ya maka rahama friend, Allah yasa kwanciyar hankalin ka knn...
"Ameen" ya jiyo muryoyin su suna amsawa...
"Gaba d'aya motar Shattima dake pake a parking space suka nufa..
"'Yan Jarida kuwa sukai masu chaa suna so suji ta bakin su, musamman Jalal da Zubaidah...
"A mota Shattima sai jansu da hira yake yana so ya d'an mantar dasu damuwa..
"A haka har ya d'auki hanyar Asorock ba tareda sun lura ba..
"Jalal ya d'an dubesa yace " Kasan dai bai kamata mu wuce gidan rasuwa a haka ba, ka kaimu gida first mu d'an kintsa..
"Shattima dai bai ansa ba sai d'an slow da yayi yace " Annah wai dama da inaso ku d'an gaisa da Abbah na ne don gobe zai wuce ba jimawa zaiyi a garin ba...
"Annah ta murmusa tace " A haba Baba na ai babu komai, mu k'arasa tunda ka biyo damu hanya...
"Shattima ya amsa da yauwa godiya nake Annah, kafin yaci gaba da driving da confidence..
"Jalal kuwa wata duniyar tunani ya tafi, wani Abbah Shattima yake nufi, yadai san Mahaifin sa Baba yake fad'i masa, snn Yakan kira Mai Martaba da Abbah, toh shin Mai Martaban ne yazo ko kuwa.... Haka kurum yaji ya tsinci kansa da fad'uwar gaba mai tsanani.. Daidai lokacin da Shattima yayi horn a wani wagegen Mansion wanda gate d'inma kawai abin kalla ne...
"Wow inji Sameena sanda Shattima ya saka hancin BMW dinsa a cikin a wagegen gidan. Tsayuwa fad'in tsarin gidan b'ata lokaci ne, guards ne tako ta ina suna tsaron gidan... Daga waje baka hango gidan dukda ginin bene ne dashike kaman yayi gidan kaman yayi slope, kwalta kuwa ya ratsa ko ta ina a cikin gidan, wasu tankama tankaman Parking lots ne har guda biyu suna facing juna wanda ko wani guda d'aya zai d'auki motoci ak'alla goma. Saida na soma hangan moticin ciki ne nace Masha Allah, idan bakayi bani waje inji hausawa, shak'e parking lots d'in suke da Luxurious Cars, Kama daga kan Mercedes da dai sauran su.. Kai Masha Allah dai kawai....
"Shattima na gama parking suka soma fitowa saida Shattima ya taimaka ma Jalal da Bud'e k'ofa sabida hannun sa..
"Gaban Jalal kuwa sai fad'uwa yake ya rasa dalili.. Harta Annah saida taji wani irin yanyi sanda suka iso gidan...
"Securities masu tsaron k'ofa suka shiga bubbud'e masu k'ofofin alfarman suna masu kwasan gaisuwa....
"Abbah na zaune a parlorn nasa wanda yasha ado da furniture na alfarma daga center.... A hankali ya mik'e tsaye Sanda Shattima ya shigo ya baro su a waiting parlor...
"Kallon Shattima yake yana mai k'arasowa tsakiyar parlorn yake fad'in" Abdullah ina Modibbo, kar kace min wani abu ya kuma gifta tsakanin mu, kace min zan sake ganin sa...
"Shattima kai a k'asa yake murmusawa don gaba d'aya bai saba da wann canzawan na Mai Martaba ba... A hankali yace " Allah Ya taimake ka Abbah, tare muke da Modibbo da family d'insa, idan ka min izini zan masu iso...
"Mai Martaba na murmushi da bai tab'a irin ta ba, siriryar hawaye tana sauk'o masa a idanun sa guda, kumatun sa suka lotsa kaman yanda na Jalal yake kafin ya shiga gyad'a kai yana fad'in" Bismillah bismillah Abdullah...
"Shattima ya rusuna yayi godiya kafin ya mik'e ya k'arasa ya masu iso....
"K'iraje suka shiga bugawa, jikkuna suka shiga samun sauyin yanayi, zuciyoyi suka shiga girgizawa, Idaniya suka shiga kallon Al'ajabi..
"Takowa ya ringa yi yayinda Jalal ma ke takawa cikin parlorn yanajin wani babban Al'amri a tareda shi, harta k'afafuwan sa da k'yar yake iya d'agasu.
"Gaba d'aya su Annah kallon ikon Allah suka tsaya yi....
"Saida suka k'araso daidai tsakiyar parlorn k'asar k'wan wuta mai geza Kafin suka tsaya cak su duka biyun... Bugun zukatan su ya k'aru..
"Tun daga d'an yatsar k'afar sa Mai Martaba ya soma kallon sa har ya d'ago zuwa fuskar sa, k'walla tab idanun sa, Tabbas shine, wann d'ansa ne Lamid'o..... Jalal dai sai kallon buwayar Ubangiji yake ba tareda ya iya furta koda kalma guda ba, yanayin da ya tsinca kansa maras misaltuwa ne, ganin wann mutumi ya jefasa cikin wani yanayi...
"A hankali Mai Martaba yakai hannunsa dake kan faman rawa ya d'an janye bandage d'in da aka d'aure hannun Jalal dashi....
"TAMBARIN ya gani, Tambarin masarautar su.... Kukan da yake rik'ewa shi ya kufce masa.... Ya shiga shafa fuskar Jalal dake tsaye babu alamun kuzari a jikin sa yana fad'in" Lamid'o dama kana raye, dama zan sake saka ka a k'wayan idanu na... Modibbo meyasa ka tafi ka barni nake rayuwa cikin k'unci na rashin ka da Mahaifiyar ka a tare dani.... Ya k'arashe yana mai Rungumar Jalal idaniya naci gaba da zubar da ruwa....
"Kuka ne ya b'alle masu gaba d'aya ba Jalal kawai ba....
"Cikin wani irin murya mai cike da shauk'i da tausayi had'i da kuka Jalal yake fad'in" Abbah, kaine Abbah na, Abbah ka jefar dani, Abbah meyasa... Meyasa kuka jefar dani....... Kuka yaci k'arfin Jalal...
"Shattima ya k'unshe bakin sa ya fice wani k'ofa yana mai fitar da kukan sa wanda yasan shakka babu na farin ciki ne....
"Annah da Zubaidah suma suka rungume juna suna nasu kukan..
"Mai Martaba ya shiga shafa fuskar Jalal yana fad'in " Ko kad'an, ko kad'an Masoyi na, duk iya tsawon rayuwar da nayi nayisa ne cikin k'aunar ka da sake son ganin ka, nasan watarana Allah zai kuma had'ani da kai.... Ina sonka muna sonka Lamid'o, bamu tab'a dainawa ba... Ya k'arashe daidai sanda suka rungume juna a tare shida Jalal...
RANAR ALKHAIRI, RANAR DATA GOGE BAK'IN CIKIN, RANAR DA ZUKATA SUKA CIKA DA FARIN CIKI.
***************
"Barr ya dubi Alh Kasim dake kan bincikan wasu files don ko zarafin yima employees d'insu salary basu samu ba., yace Ka saurare ni Alh Kasim ko kasan har yanzu ba'a sami Faisal ba, thank Goodness mun b'uya a inuwar Umar don yanzu gaba d'aya hankalin police na kansa. Amma ka sani duk randa suka kama sa toh fah za'a zak'ulo mu tunda Faisal za'a soma nema...
"Alh Kasim yaja wata doguwar tsaki yana rik'e da k'irjinsa dake masa zafi kad'an kad'an kafin yace " Barr wai kashe kaina ne kake so nayi, how many times do I have to tell you kasan yanda za'ayi a zak'ulo that imbecile Faisal wanda baisan aikin sa ba, that jerk deserve nothing but to die... I want him dead, idan ya mutu thing might be easier for us...
"Babban damuwa na yanzu shine na samu na rabu da wann d'an iskan Honorable d'in don naga alama bashida ta ido, bazan bashi k'ofa yayi destroying d'ina ba, da zaran munyi had'akar kasuwancin nan da Modibbo Cooperation kaga ahiknn, zan samu na watsar da d'an iska..
"Barr ya fuzar da iska kurum ba tareda ya furta komai ba, Don yasan akwai k'ura a gaban su, tun daga yanda PA d'in president na Modibbo cooperation yake masu yawo da hankali, don har rana mai kaman ta yau da PA kawai suke communicating basu daman magana da Mr President ba....
*********
"Da k'yar saida wata 'yar sanda ta shigo ta kwaci Hadiza a hannun matan nan wa'enda suka saba da shiga rikici iri da kala...
"Ko d'aga hannun ta ta kasa balle ta iya tashi, idanunta kuwa haka ya kumbura suntum, bakinta kuwa uwa shantu haka ya koma sabida yanda ya kumbura yayi tsayi suntum..
"Can gida kuwa a tunanin su Hamma Hadiza na tare dasu Annah ne....
Sameena ce 👌🏾
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
88
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Desiccated To All Victims Of Rape...*
*Maryam Ahmad Paki dearest Inlaw... the chapter is yours sweetheart😍 Allah Ya bar k'auna, Alkhairin Allah Ya Kai maki🤝.... ❤*
"Kallo take ta faman bin Imam dashi yanda yake ta kaikomo a asibitin nan sabida Innah, K'walla mazu zafi suka kuma ciko idanun ta, Kai her whole life bata tab'a ganin mutum irin Imam ba, his generosity is extra ordinary, despite duk abinda ta masa he didn't turn his back on her, he's still here for her..... "
"Har Imam ya k'araso kujeran gefen ta Ya zauna Zulaihat bata san ya iso wajen ba, tayi nisa duniyar tunani da kaico na rayuwa, lokaci guda hawaye na bin pale face d'inta, ... " Hannun sa ta hango yana mai mik'a mata hanki...
"Ta d'ago ta dubesa cike da jin nauyi kafin tasa hannu ta karb'i hanki d'in tace " Na gode... D'an jimm yayi kafin yace " Do you need something? Are you hungry...??
"Girgiza masa kai tayi alamun a'a kafin ta soma fad'in cikin muryar kuka " Imam na gode, na gode da duk d'awainiyar ka dani, Allah NE kawai zai iya biyan ka, ...... "Da sauri Imam ya katse ta da fad'in" Ki daina fad'in haka Zulaihat I beg of you kinji, nasha fad'a maki ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, when ever you needs me , I'll be right there.... It's a Promise, snn ko gobe ne ma kike neman wani taimako na don't hesitate to tell me right away kinji......
"Girgiza kai ta soma tana share hawayen ta kafin tace " Imam ya kamata kayi nesa dani don ban cancanci mutane irin ku, ni mayaudariya ce, mai mance Alkhairi wacce zuciyar ta bai cika da komai ba face abinda take so take muradin samu ta ko wani hanya..... "Imam don Allah ka tafi kayi nesa dani, insha Allah wann shine k'arahen taimakon da zan nema daga gare ka....
"Imam ya kafe ta da idanu tausayin ta na ratsa zuciyar sa, so yake yayi hugging nata ko rad'ad'in dake zuciyar ta zai ragu amma babu hali....
"Murya a hankali ya soma fad'in" Zulaihat d'ago ki kalle ni.... Kasa d'agowa tayi sai share hawayen ta da take kan faman yi.... Ya kuma kiran sunan ta a hankali....
"D'agowa tayi tana duban sa with her watery eyes....
"Imam ya d'an muskuta don baison aminta da abinda zuciyar sa ke fad'a masa tunda matar wani ne....
"A hankali ya soma fad'in" Everything is happening for a reason, bamu ke tsara rayuwar mu yanda muke so ba saidai muyi fata, if to say d'an Adam shi zai tsara rayuwar sa yanda yake so ba Allah ba da duniyar ta gagari kowa, amma shike tsara mana rayuwar mu saidai muyi fatan kasancewa daga cikin bayi zab'bb'u kuma na k'warai.... Ki daina blaming kanki for what's happening, Allah Ya fimu sanin meyasa Al'amra suke a yanda suke yanzu ba..... Ki kwantar da hankalin ki kinji, I won't leave your side har mahaifiyar mijin ki ta samu lafia.....
"Zulaihat ta share hawayen idanun ta kafin ta furta a hankali " You are an Angel.... Daidai nan Dr ya fito yace yana son yin magana da Zulaihat in private...
"Zulaihat ta girgiza masa kai kafin tace " Dr zaka iya fad'a min komai a gaban sa he's my brother...
"Dr ya d'anyi jimm kafin yace " Well fine, mu k'arasa office d'ina, suka bi bayansa a tare...
"Dr ya kalli Imam ya kalli Zulaihat kafin yace " Mahaifiyar ku tanada hawan jini sann bata shan magani, rashin shan maganin da batayi ya haifar mata da kidney problem, I mean gaba d'aya two kidneys d'inta sunyi failing, for now zamu ke mata dialysis (Wankin k'oda) a k'alla a sati sau uku, snn wanki d'aya dubu ashirin ne... Pls ku samo kud'in as soon as possible a soma mata don kuwa her life is in danger.....
************
"Hannun Jalal na rik'e cikin nasa ya kasa saki yake jero godiya da addu'o'in girma wa Annah bisa babban gudumawar da ta bada a rayuwar d'an sa....
"Gaba d'aya Annah sai ji tayi she's not comfortable da irin godiyar da Mai Martaba yake mata, musamman da suka fahimci