Showing 117001 words to 120000 words out of 210924 words
yanayin gadon maras lafiya yanda yake bashida girma, ta d'an d'ago idanu tana dubansa kafin tace " Ai zan tak'ure ka Ya Jay....
"Hannunta ya kamo kafin yace " Pls Baby I just want you here by my side, don't say no kinji...
"D'an murmushi tayi wanda iyakacinsa fatan baki kafin ta d'ale gadon k'irjinta naci gaba da bugawa da sauri da sauri, abune wanda bata tab'a yinsa ba kwanciya gado guda da namiji, gashi gadon tak'urarre wanda tasan dole jikkunan su Ya manne dana juna, haka ta kwanta cikin runtse idanu.... Ahankali taji yana zame hijabin dake jikinta, wayyo Allah Zubaidah ji tayi gaba d'aya ta soma shaking...... Cikin kunnenta yake rad'a mata "Calm down Baby I got you..... Ji tayi Ya sakalo hannunsa gamida rungumeta tsam cikin jikinsa ba tareda yayi la'akari da ciwon dake jikinsa ba.... Haka k'irjin Zubaidah ya ringa bugawa da sauri da sauri, gaba d'aya ji tayi baccin ya kasa zuwa mata... Shima Jalal abubuwa ne da dama sukayita ziyartan sa, a hankali yana shak'an daddad'an k'amshinta bacci ya soma d'aukan sa, cikin kunnenta Ya rad'a mata " Goodnight baby I love you"""
"Har cikin b'argo da tsokan ta taji kalaman nasa, a hankali ta kuma lumshe idanu gamida sakin murmushin da batasan daga ina ya bijiro mata ba... A haka bacci mai dad'i yayi awon gaba dasu....
_Nima Sameena nace "Asuba ta gari *ZubyJay*π"_
**************
"K'arfe shabiyu na talatainin dare tana bugawa Tariq ya sauk'o daga saman gadon sa da k'yar, tabbas yasan by now polisawa masu tsaron k'ofar sa sunyi bacci , Hood sweater d'insa Ya d'auko ya saka a hankali sanda yaji motsin Dad d'insa a bathroom kafin ya sad'ad'o zuwa k'ofa cikin sand'a ya Bud'e k'ofar.... Yakai dubansa ga securities d'in ya tabbata bacci suke, a hankali ya d'aga kai sama yana duban CCTV Cameras, cikin sauri yaja hular sweater d'in ya rufe kansa da fuskar sa gaba d'aya kafin ya soma tafiya sauri sauri yana rirrik'e gefen cikin sa..... Yana ficewa daga corridor d'in Dad ya fito daga toilet, nan yaga wayam babu Tariq, a tamanin ya fito waje yana neman d'auki, ai a sittin polisawan nan suka ware idanun su, cikin sauri d'aya ya danna intercom d'in dake hannunsa ya sanar a gate, kafin suka fice gaba d'aya harda Dad.... Nan da nan asibitin ya kaure da k'aran security Alarm.......
"Ta k'ofar baya yayi niyan fita saidai ina securities sun samu labari, k'ok'arin tsere masu yake yana so ya haye garu saidai sabida ciwon dake jikinsa bazai iya ba,... D'aya police d'in kuwa fad'i yake pull right there, stop or I'll shoot.... Dad cikin tsananin tashin hankali yake fad'in" Tariq ka tsaya ka tsaya pls son kar su harbe ka..... Kan kace me sun capke sa.... Sai faman buge buge yake yana fad'in" Let me go, let go of me, I'm not a criminal, just let me goooo....
"Cuff him d'aya police d'in ya fad'i lokaci guda yana magana da ogan su da intercom d'in dake hannunsa..... Dad yanaji yana gani aka saka ma Tariq handcuffs... Nan Ya zube yana rirrik'e cikinsa wajen da aka mai aiki.... Nan da nan asibiti ta bada ambulance ba'a zarce dashi ko ina ba sai asibitin cikin prison.....
"Washi gari kan kace me labari ya baza garin Abuja.... Asmah ce take sanar da Ansar sanda suke waya suna kan hanyar su ta zuwa asibiti wajen Jalal.... Ansar ya jinjina lamarin kafin ya sanar dasu Annah da Shattima... Zancen suka ringa yi har suka isa asibitin......
"Jalal ma sosai ya jinjina lamarin, Zubaidah kam bata tofah komai ba, Jalal yanata santa kallonta don yasan dole mood d'inta ya canza tunda babu abunda ta tsana kaman taji labarin su, k'arshe ma ficewa sukayi ita da Annah ko breakfast d'in da suka kawo bata ci ba, dole ta d'aga Annah kan ta rakata su d'an zaga waje....
"Jalal kam yaji dad'i ficewar nasu don dama yana so su sami Time shida Ansar su tattauna, Shattima ma sallama ya masu don yanada uzuri...
"Ya rage daga Jalal sai Ansar, nan suka soma tattauna lamarin..... A haka wasu police guda biyu suka shigo don interrogating Jalal.......
Sameena ce ππΎ
[1/23, 22:26] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
67
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_πKAINUWA WRITERS ASSOCIATION (United We Stand Divided We Fall) π€_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Where are you my Shawtyπ this one's for you sweetheart.... ππ*
"Zaune suke saman d'aya daga cikin kujerun shak'atawa da aka k'awata asibitin dasu, jefi jefi mutane suke wucewa kasancewar wajen Amenity ne ba kowa da kowa ake kwantarwa ba kaman general...
"Zubaidah taci gaba da fad'in" Annah zan dropping charges d'in nan kurum kowa ya huta, ever since I pressed charges abubuwa suka dad'a rincab'e mana, I'm afraid Annah ... Nasan they Won't Leave us alone idan ba janye k'ara nayi ba....
"Hannayenta Annah ta rik'o kafin tace " Zubaidah Allah yana tare da mai gaskiya kar ki mance... Snn wann gwagwarmaya da kike yi bama kanki kurum kike ba, wa matan duniya kike yi, snn Alh Kasim ya zalinci mutane da dama wanda na tabbata ta dalilin wann sharia naki da ake yi Allah zai toni asirin duk wani muggan ayyukan sa... Kar ki damu daughter nasan you worried so much about Jalal, but he's doing this for us, ko kin janye k'ara ko baki janye ba The Dasukis Won't Leave us alone as they promised, kar ki mance yanda har cikin gida Labib da guards d'insa suka shigo sukayi cin kashinsu son ransu, Allah ma yace ka nemi hakkin ka, kinyi hak'uri da irin bak'in ciki da k'unci da suka jefa rayuwar ki, kinyi hak'uri lokacin da suka Aura maki mijin da ba zab'i ne a gareki ba... "Da sauri Zubaidah ta d'ago tana duvanta jin tace Mijin da ba zab'inki ba....
"Annah ta murmusa kafin tace " Na sani a yanzu shine zab'in ki, ina nufin a lokacin da abun ya kasance, a lokacin da bakisan wanene Jalal ba, a lokacin da baki gane duk duniyar nan bayaga Hamman ki bakida masoyi tamkar Jalal.... Annah ta d'an murmusa kafin tace " He has a big heart he's... just an incredible.....
"Murmushi kawai Zubaidah tayi tana duban Annah kafin ta hangi polisawa suna fitowa daga bakin ward d'in.... Mik'ewa sukayi gaba d'aya suka nufi d'akin Jalal d'in......
*****************
"No... No... No this can't be, Balele da gaske kake Baffah na babu.... Umar Ya fad'i sanda siririyar hawaye take gangaro masa...
"Daga d'aya b'angaren Balele yace " Umar itadai duniya budurwa ce amma ta wawa, babu abinda zan iya k'ara fad'i maka iyaka nace mun riga mun sallaci mahaifinka mun kaisa gidan sa ta gaskiya, don kuwa wasiyar sa ce cewa bai yarda ka sallaci gawansa ba, ni nayi nawa tunda na fad'a maka, kana iya zuwa idan kaga dama...... Daga haka ya katse wayar.....
"Gijiiff Ya zauna saman couch yana maida numfashi a hankali, wann wani irin rayuwa ce, shi bai sami albarka iyayensa ba, shi bai sami Zubaidah ba, uwa uba he's running out of cash.....
"Girgiza kai ya soma tamkar tab'ebb'e ya soma fad'in" No... No I won't let mutuwan Baffah ya b'ata mun plans d'ina ba... All that I planed... I won't back down until I take Zubaidah back, she's mine , tawace ni kad'ai babu wani mahaluk'in da ya isa ya mallaketa alhalin ina nunfashi, I'll take her back and kill them all one by one.... *Sune Sila* sune *Sanadin Rabuwar mu* *Su suka ja min* na rasata... They are all monsters, *Jalal* ya furta a hankali kafin yace " He's my biggest enemy, that coward must die...... Ya k'arashe yana hangan kwalbar giyan da Zulaihat ta bari a parlorn...... Cikin sauri ya k'arasa ya suri kwalban..... Ya jima yana juya kwalban yana tuno ranar shiga kotu ta farko da ya hangi irin kallon soyayyar da Jalal da kuma Zubaidah suke aika ma juna wanda duk iyaka zaman su da soyayyar da suka sha a baya bata tab'a masa ba....... Da k'arfin gaske ya finciki marfin yayi jifa da ita saida ta daki glass d'in window kafin ya d'aga sama ya soma kwankwad'a this is his first time don bai tab'a Sha ba... Wata uwar tsami yaji ta ziyarci saman harshen sa..... Runtse idanu yayi da k'arfin gaske Ya ringa kwankwad'ar barasan nan tamkar aikosa akayi..... Saida ya d'aga kwalba guda yana sunbatu shi kad'ai....... A haka bacci ta kwashe sa a wajen.....
_(Allah ka rabamu da bak'ar zuciya wanda zata kaimu ga aikin danasani... Ameeen)_
*******************
*Washe Gari*
"Alh Kasim dake tsaye gefen gadon Mummy da take ta d'irkan drip yayi tsaki a hankali kafin ya k'ara trying lambar Barr Munir still jinta yayi a kashe.... Da k'arfi Ya daki gefen gadon yana furta " Damn it... On your phone you idiot....
"zumbur Mummy ta bud'e idanunta tana kallon mijin nata, d'an matsowa kusanta yayi kafin yace " Farha kin tashi... Bata amsa sa ba sai cewa tayi " Salim.... Ina Salim yake, I want to see my boy, pls Call him for me..... Ta k'arashe tana k'ok'arin mik'ewa.....
"Wani tsakin Daddy Ya kuma yi kafin ya maidata ya kwantar yace " Farha wai bakiji abinda Dr yace bane, ki daina saka damuwa ma ranki wai ko so kike ki sami matsalan shanyewar b'arin jiki, idan kin kwantar da hankalin ki an kusa shiga kotu kuma na maki alk'awari this time around I won't let you down, zan kawo maki precious son d'inki har cikin gidan nan, I promise you that kinji Farha nah.....
"Gyad'a masa kai tayi tamkar k'aramar yarinya kafin tace "When's the heroine..???
"D'an jimm yayi kafin ya tsuguna ya rik'e hannayen ta yace soon my love, Salim zai dawo gida soon, and I'll make them pay...... Ya k'arashe yana furta Jalal I'll soon come for you, but sai na gama da incompetent Attorney d'in naku wanda baisan meke masa ciwo a rayuwa ba, Zaku san da waye kuke yak'i little brats...... A hankali duk yayi maganganun nasa wanda sai ka kasa kunne sosai kafin kaji.....
"Jane ce ta shigo da ruwa a glass cup saman d'an k'aramin plate ta gaida Daddy kafin ta ajiye gefen bedside.... Kallon agogon hannunsa ya kuma yi k'arfe 10:30am daidai, ganin Mummy ta koma bacci yasa sa zame hannunsa daga rik'on da tayi masa kafin ya fice zuwa parlorn k'asa ya shiga neman layin Faisal bugu biyu Faisal ya d'aga cike da rusuna...
"Faisal I want you to get me Attorney Kumo cikin awanni ashirin da hud'u, bana so a sami failure .... I confide this mission to you alone, ..... I repeat bana so a sami failure....
"Tamkar Alh Kasim na kallon sa haka ya gyad'a kafin yace " Mission accomplished Boss... Daga haka Alh Kasim ya soma katse wayar yana wani irin huci shi kad'ai..... Gama wayar keda wuya Attorney Munir ya kirasa..... Saida ya rakkaba uban tsaki kafin ya d'aga wayan yana fad'in" Where the hell have you been Attorney..??
. "Daga d'aya b'angaren Barr Munir yace " Calm down Alh Kasim, mu gaisa mana first....
"Tsaki Daddy yayi kafin yace " Ba wann bane a gaba na, get me that idiot right now, yanzu yanzu babu b'ata lokaci....
"Barr ya fuzar da iska kafin yace " I hear you, amma wani idiot kake magana...
"Umar Of course... Daddy yace cikin katse sa....
"Murmushi Barr yayi kafin yace " At your service Alh Dasuki, but first Yaya jikin k'anwata....
"Cike da k'osawa Daddy yace " da sauk'i sosai.... Sai na ganka, ina gida yau coz bazan fita company ba, apparently idon police yanzu na kan company d'inmu, irin wann had'uwar a gida ya kamata mu ringa yinsa.... Daga haka katse wayar yayi kafin ya mike Ya ringa zagaya parlorn shi kad'ai k'unci pal zuciyarsa......
**********************
" Whatt..! Kana nufin Barr Kumo baya gari, where the heck did he go..... Okay okay fine kazo gida Maitama straight, ..... Daga haka ya katse wayar yana tsaki... Juyowa yayi yana duban Barr da ya had'e hannaye biyu yana kallonsa kafin yace " I just can't believe this, dukansu biyu basa nan, ka sake kiran Umar ka fad'a masa bana wann game d'in dashi, idan yana son kansa da lafiya yazo gidan nan yanzu yanzu....
"Tab'e baki Barr yayi kafin yace " Ubansa ne fah ya mutu aiko kaga dole ya tafi ...
"Wani uban tsaki Alh Kasim yayi kafin yace " Uwar tasa ma ta mutu for all I care.. Lambar Umar Ya shiga latsawa lokaci guda......
*Kuyi hak'uri na rashin jina kwana biyu... Wllhi I'm pretty much occupied ne kwana biyun nan, you know how New Year is....biki everywhere, but just bear with me for the meantime, insha Allah I'll make it up to you by updating everyday..... Just stay tuned guys... ππ*
[1/23, 22:27] βͺ+234 803 619 0581β¬: ππππ *ZUBAIDAH*
68
*Β©Sameena Aleeyou...βπΎ*
_πKAINUWA WRITERS ASSOCIATION π€_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Driving yake yana kuka tamkar yaro, he couldn't help it, zuciyar sa gab take da tawarwatsewa.... K'aran da wayarsa tayi ne yasa sa rage speed kafin ya duba, ganin mai kiran nasa yasa sa sakin wani mugun tsaki kafin ya ajiye wayar.... Kiran ta kuma shigowa, a hasale ya d'aga yana fad'in" Me kuke nema a wajena,...???
"Daddy Ya murmusa kafin yace " Where are you, ina son ganinka right now..
"Murmushi takaici Umar yayi kafin yace " I thought I have made my self clear, stay out of my life, Kai ka jawo na rasa mahaifina if only ban biye ma son zuciya irin naku ba..... "Katse Alh Kasim yayi da fad'in" Shut the hell up you idiot, on the contrary kai ka zab'i hakan ma kanka, .... Wait a minute, kar kace mun zaka giving up, well koma meye kake shiryawa a cikin zuciyar ka I have to remind you this.... You can't run away from me, how do times do I have to tell you, already kana cikin mess d'in nan, yanzu duk ba wann ba, abu guda nake so ka min, aikin da ka soma you must accomplish it, Apparently Jalal yana babban asibitin garin Gombe, kasan yanda za'ayi ka k'arasa aikin ka, what I mean finish him once and for all, kasan na riga da nasan little secret d'inka, so just go ahead and kill him... Sorry for your lost..... Daga haka ya katse wayar....
"Jifa da wayar Umar yayi kafin ya soma magana shi kad'ai.... " That imbecile is still alive, murmushi yayi mai cike da ma'anoni kafin yaci gaba da driving d'insa.....
****************
"Annah pls don't say no, Ya kamata ki koma gida, hankalina bazai tab'a kwanciya ba muddin nidake duka muka zauna a asibitin nan alhali bamu tare da Zubaidah, Annah ke kad'ai ce nasan zaki kula min da ita, pls kiyi hak'uri ku tafi bana so tayi missing jarabawarta sabida ni, just go pls kinji Annah na, don't worry about me, I'll be fine insha Allah, snn I'm not alone here, akwai Shattima da Family d'insa, pls kinji Annah.......
"Sauk'e ajiyan zuciya tayi tana kallon fuskar sa kafin ta shiga gyad'a masa kai a hankali tace " Shikenn Jalal zan tafi kaman yanda ka buk'ata but as soon as Zubaidah ta gama da jarabawan ta zamu dawo....
"Murmushi yayi kafin yace " Before then ma anyi discharging d'ina insha Allah... Ya rik'o hannayenta yana murmushi kafin yace " Always remember that I love you... You are the best Mum on Earth..... Rungume juna sukayi nan k'wallan da Annah take mak'ewa ya fito.... Shafa fuskar sa ta ringa yi tana masa addu'an samun lafiya....
"D'ago kai yayi ya kalli Zubaidah da kanta ke duk'e a k'asa, Annah ta kai duvanta ga yanda ya kafe idanunsa, a hankali tasa bayan hannunta ta share k'wallan ta kafin ta fice ta basu waje.....
"D'an sauk'owa yayi daga saman gadon yana d'ingisawa kafin ya k'araso gaban ta..... Bai iya ce mata komai ba sai rungumeta da yayi sosai cikin jikin sa.... Nan Zubaidah tayi bursting cikin wani