Showing 171001 words to 174000 words out of 210924 words

Chapter 58 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22865

shi d'in sarki ne Mai cike da madafan iko, d'aya daga cikin manyan sarakunan arewa masu tutar daular Shehu Usman...
"Kai a k'asa Annah ta soma fad'in" Allah shi taimake ka, ni ce nafi Cancanta na mik'a godiya ta WA Rabbil Izza wanda ya zab'e ni a matsayin wacce zata raini Yarima d'an Babban sarki ta kuma shayar dashi, hak'ik'a wann ba k'aramin d'aukaka bane, Modibbo yaron arziki ne, Modibbo d'an arziki ne snn mijin arziki ne, Shakka babu jinin dattako na yawo a jijiyoyin jikin sa.... " Ubangiji ya kare ku daga sharrin mahassada da abokan gaba, Allah Ya ja zamanin babban sarki da Yarima, Allah Ya nuna mana d'iyoyin Yarima nan bada jimawa ba.....

"Mai Martaba ya kasa resisting murmushin girman dake kwance saman fuskar sa, tun bayan rasuwar Suhaima mahaifiyar Jalal ya jima baiji kalaman da suka kwantar masa da hankalk suka saka sa nishad'i irin kalaman wann baiwar Allah ba.... " Baisan sanda ya bud'e murya yana fad'in" Ameen ya Rahmanu ba.....

"Mai Martaba ya kai duban sa ga Zubaidah dake zaune gefen Annah kanta a k'asa yana mai bayyana murmushin iko yake fad'in" Yaki taho nan d'iyata....


"Zubaidah ta mik'e cikeda ladabi had'i da kunya ta k'arasa gaban Mai Martaba ya d'an rusuna gefe guda...
"Jalal sai satan kallon ta yake...
"Mai Martaba kuwa karanto masu Albarka ya shiga yi tareda jero masu addu'o'in samun nasara a rayuwa had'i da zama lafia da Juna da kuma fatan samun zuri'a d'ayyiba...
"Gaba d'aya kunya lullub'e Zubaidah yayi tamkar k'asa ta tsage ta shige ciki.... Su Shattim da Annah kuwa sai amsawa da Ameen suke....
"Wayar Shattima ne tayi k'ara yayi saurin sakata a silent gamida sulalewa ya fice zuwa wani k'ofa....


"Saida yayi wata silent murmushi kafin ya d'aga wayar cikin dakewa....

"Daga d'aya b'angaren Jade suka gaisa da Shattima a matsayin sa na PA d'in Modibbo Cooperation, nan Jade ta sanar dashi Boss d'inta na son yin magana dashi... Kai tsaye Shattima yace ta had'a su...

"Cikin k'ank'anin mintoci Jade tayi transferring call d'in to office din Alh Kasim...

"Ya d'aga sai faman washe baki yake suka gaisa da Shattima, nan Alh Kasim ya buk'aci ko zai iya magana da Mr President...

"Saida Shattima ya murmusa kafin yace " I'm sorry Sir my Boss is a very busy Man..... Ba kasafai ake samun sa ba, yanzu haka yana tsaka da meeting da wasu clients d'insa da suka zo daga Singapore.... Gaskiya bazaka iya samun damar magana dashi ba, you know how you business Men are...

"Alh Kasim yaji babu dad'i yau har shine ake wulak'an ta sa akan ganin wani, koda shike tunda shine mai neman abu he just have to put up with the situation...
"Cikin sauri yace " Okay eh.. Eh... Haka ne, amma dae pls this time around mu samu muyi confidential meeting d'in sabida already kayan sun zama ready....

"Shattima ya murmusa kafin yace " I can't promise you that Mr President, coz my Boss is very committed.... Amma dae I'll try my best na saka a schedules d'insa... Shattima yaci gaba da fad'in" I really have to go Mr President ya kammala ganawar sa,... " Ko me ake ciki I'll get back to you....Daga haka Shattima ya katse kiran yana wata murmushi yana karkad'a kai....

"Alh Kasim ya d'ago yana kallon Barr da ya masa k'uri.... Fuzar da iska yayi kafin yace " Barr ina so a samo min details akan owner na Modibbo Cooperation...

"Barr dai kallon sa kurum yayi kafin yace " Ina muka kwana da zancen Faisal...
"Alh Kasim ya murmusa kafin yace " Mutuwa ce ta kamace sa sabida amfanin sa ya k'are mana. Just get your boys ready, a zak'ulosa duk yanda ya shiga... Alh Maina kuma da matar sa zansan abinda zanyi dasu don nasan babu abinda zai hanasu testifying a kotu, what matters alot now shine mu samu kampanin nan ta farfad'o in two weeks time, I really wanna get rid of that imbecile Honorable.... Daga haka ya wuce ya nufi lift yana neman layin Salim da wuni zubur suna gidan su Tariq...

***********


"Ansar ne ya shigo da wasu lauyoyi sukayi ta'aziya wa Mumsy, ya tambaye ta Kausar fah, Mumsy tace tana can parlorn sama ku k'arasa..
"Ansar ya amsa mata kafin yayi jagora ma sauran 'yan uwan sa lauyoyin...


"Zaune ya hange ta fuskar nan nata very pale, watery eyes d'inta na lumshe tana k'udundune cikin ash hijab wanda yake har k'asa, cazbaha ne a hannun ta da alama tazbihi take...

"Ansar ya d'an sa hannu ya k'wank'wasa k'ofar, ta d'ago ido suka kalli juna... "Yayi k'arfin halin sakar mata murmushi kafin yace " May I...

"Tashi tayi ta zauna sosai tana gyara zaman hijabin ta da ya d'an zame kwantantun suman gishin ta suka fito.. "Gyad'a masa kai kurum tayi ba tareda tace komai ba..
"D'an k'arasowa gaban ta yayi cikin parlorn kafin yace " Ina su Mardiyan yaya suka barki ke kad'ai bayan nace masu ke d'in amana na bar masu., gashi sun barki those tears suna sake zuba..

"D'an murmushi kawai tayi na k'arfin hali kafin tace " Sun d'an fita ne amma suna dawowa...

"Ansar ya d'an murmusa, shima kana ganin sa kasan kurum juriya da k'arfin hali yake, he needs to be strong for Kausar and Mumsy.. Sann yace " Okay colleagues d'ina zasu maki ta'aziyya...

"Gyad'a masa kai tayi kafin tace " Bismillah su shigo.. Ta k'arashe tana goge ragowar hawayen ta....

************

"Su Annah da Zubaidah tuni an masu masauk'i a wani tangamemen section yayinda Jalal ke durk'ushe gefen Mai Martaba, Shattima na daga Side...

"Mai Martaba yaci gaba da fad'in" Insha Allah gobe ni zan koma Abdullah zai raka ni sai ya juyo, ya d'an ja fasali kafin yaci gaba da fad'in" Modibbo ka sani daga yanzu ba kai kad'ai bane, kanada Mu kanada gatan ka, babu mahaluk'in da zai kuma tauye maka wani hakkin ka, ko na bari ya muzguna maka, ba kai kad'ai ba, dukda iyalan ka baki d'aya, ina so ka sake dani kaman yanda Abdullah ya sake dani, Allah Ya baka lafiya ya kuma sa zakkan jiki ne....
"Jalal kai a k'asa yace " Na gode Ranka shi dad'e...

"Mai Martaba ya murmusa kafin yace " Ka kirani Abbah...

"Jalal ma d'an murmusawa yayi kafin ya furta ABBBAH "

"Farin ciki maras misaltuwa ya wanzu a zuciyar Mai Martaba, yau gashi ga gudan jinin sa, Allah Ya cika masa burin sa.. Yakai kallon sa ga yatsun k'afafun Jalal wanda babu abinda ya rabasu da nasa, yanda suke a kwance dogaye...
"Shattima kuwa sai murmusawa yake...

"Mai Martaba ya k'arada " Modibbo ka tabbata ciwon nan baya damun ka,..
"Jalal ya d'an murmusa kafin yace A'a Abbah da sauk'i sosai...

"Mai Martaba ya jinjina kai yana murmushi ya kasa d'aga idanun sa daga barin kallon Jalal, ji yake anya zai iya bari har sai nan da sati biyu su iso Fadah...

_Lallai wann rana akwai babban biki inji Sameena, kar ku bari a baku labari.._

"Basu suka bar gidan ba sai bayan sallan isha, a hakan ma da Abbah yaso su zauna a nan gidan sa gaba d'ayan su, Amma da yaji labarin Ansar sai ya amince masu su koma chan saidai zai wadata su da securities, Jalal dai duk ba son irin wad'an nan abubuwan yake ba, amma babu hali ya musa ma Abbah, Charisman sa ya wuce gaban wasa...


"Wani sabon tashin hankalin suka tarar sanda suka isa gida suka tarar babu Hadiza, Kuka Hamma da Kamal suke an rasa me rarrashin wani cikin su..
"Hankalin Zubaidah sosai ya tashi ganin Hamman ta da Kamal a wann yanayi wanda hakan ya tada hankalin Jalal sosai, ko kad'an baison ganin hankalin Zubaidah a tashe ...





Sameena ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿพ
๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜๐ŸŒ˜ *ZUBAIDAH*

89

*ยฉSameena Aleeyou...โœ๐Ÿพ*

_๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATION ๐Ÿค_


*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Jalal Ansar ku zauna a gida kawai ku kula da gida ni zan fice neman ta, zan wuce police stations na sanar da 'yan sanda ko Allah zai sa a dace, don kunsan tunda ba'a kama Umar har yanzu ba komai ka iya faruwa...

"Shattima ya gyad'a kai kafin yace " Haka ne, I'll go with you..
"Jalal da Ansar suka rako su har parking space, suna addu'an Allah yasa a dace.
"Cikin gida kuwa Annah da Zubaidah sai faman lallashin Hamma da Kamal suke...


"Motar Shattima sukayi anfani da suka fice. Bayan fitar su Ansar ya juya ya nufi d'aki dun gaba d'aya baya jin dad'i. Jalal ya take masa baya yana d'an d'ingisawa sabida ciwon sa...


"K'ofar d'akin Ansar ya tura ya shiga da Sallama...
"Zaune ya hange sa yana kallon hoton Asmah a cikin wayar sa, d'aya hannun sa rik'e da hoton family dinsa...

"Da sallama Jalal Ya shiga gamida zama gefen Ansar , har lokacin Ansar bai d'ago kai ba ga dukkan alamu hawaye ke zuba a idanunsa...

"Jalal ya d'anyi still kafin ya dafa Ansar da hannun sa maras ciwo, kasa ce masa komai yayi sabida tausayin sa dake ratsa zuciyar sa....
"Da k'yar ya iya furta " Friend kayi hak'uri......

"Cikin muryar kuka Ansar yake fad'in" No matter how hard I tried bro, but I just couldnt help.... Duk sun tafi sun barni Jalal, meyasa mutanen da nake so the most suke tafiya su barni, why why Jalal.... Ya k'arashe yana mai kifa kansa da gwiwoyin sa.....

"Jalal ya kuma dafa sa kafin yace " Kalan taka k'addaran da jarabawan knn friend, Allah Ya bamu ikon cin jarabawar mu baki d'aya... " Ka sani Ansar, we are all here for you, together we would overcome this horrible tragedy, snn insha Allah Umar bazai tsere ma jami'an tsaro ba, duk iya gudun sa akwai ranar da Allah zai kama sa, and he'll pay for all the crimes he's committed...

"Ansar ya d'ago Face d'insa da jajayen idanun sa had'i da d'aura hab'ar sa saman hannayen sa da ya dunk'ule waje guda...
"Cikin wani irin siga yake fad'in" Ba zallan aikin Umar bane, I'm quite sure the Dasuki's are behind this, na sani wnn aikin Alh Kasim ne, shi kad'ai ne yake farautar rayuwa ta, That imbecile took everything away from Me.... I swear, na ranste I won't rest until he's locked up in jell.... Da shi da 'ya'yan sa duk sai sun tafi prison snn a lokacin zai d'and'ani zafin rashi.... Ya k'arashe siriryar hawaye na gangaro masa....

""Jalal ya d'an basa light hug cike da tausayawa
***********

"Da k'yar ya samu jinin ya tsagaita, sai ciccija leb'e yake, a haka ya hangi wata motar kaya ta yo jidon doya zata shigar k'asashen north east, wato Arewa maso gabashin k'asar nan, yankin da Jihar Gombe take...
"Da dabara ya samu ya d'ale cikin doyan nan ya kwanta abinsa ba tareda kowa ya gansa ba...
"Mai trailer kuwa yana zuwa yaja motar sa ya d'au hanya....


"Da k'yar Faisal ya samu ya fice daga warehouse d'in da ya b'oye, da cizge baki da dabaran gujewa jami'an tsaro ya samu ya iso Dasuki Holding....

"Daga gate d'in baya ya kira wayar Barr ya sanar dashi halin da yake ciki yana buk'atan treatments amma yasan muddin ya tafi asibiti police will arrest him...
"Barr yayi wata murmushi yana kallon Alh Kasim kafin ya katse wayar yace " Ta zo gidan sauk'i abin farautar mu ya kawo kansa gida, ..
"A tamanin Alh Kasim ya mik'e yana fad'in" He shouldn't be here, idon 'yan sanda na kanmu... Babu shiri suka nufo waje suna neman sa ba tare da sanin kowa ba..

"Faisal kuwa daga yanda yake rakub'e ya hange su, ya fito cikin sauri ya nufesu yana jan k'afar da k'yar...

"Yana isowa yanda suke Alh Kasim ya d'auke sa da wani wawan mari... Kafin yace " This is exactly the reward of a Jerk like you.... Daga haka ya zaro k'aramar bindiga a gefen business suit d'insa yayi pointing Faisal dashi...

"Faisal yana girgiza kai cikin rashin yarda da abinda yake gani yake fad'in" Boss no.... No Boss kar ka min haka, ni ne Faisal babban yaron ka...

"Alh Kasim ya tintsire da dariya kafin yace " And also babban idiot, A jerk like you bai kamata yaci gaba da rayuwa ba, rayuwar ka na nufin mutuwa na, kaga idan ka mutu banida sauran damuwa zanci gaba da b'uya a inuwar Umar, baka raye balle idan yabada statement d'insa ayi tunanin zak'ulo ka ni kuma ka zak'ulo ni, snn kayi failing aikin ka tunda har yau Barr Kumo na numfashi.. So I'm sorry but you've to go..... Daga haka ya d'auke kan Faisal da harsashi...

"Shida Barr suka fashe da wata dariya, Barr yana nunsa yana dariya yake fad'in baka da kyau, kayi amfani da mutum ka yar dashi... Alh Kasim ya kuma murmusawa kafin ya hura bakin bindigar yayi ido masu James kafin suka k'araso, ya Kalli James yace " Get rid of this mess... Daga haka suka nufi motocin su shida Barr....

***************

"Saida suka zaga station uku kafin suka ci karo da case d'in Hadiza, 'yan sanda suka fad'a masu yanda abin yake, tun daga zuwan ta banki da kuma dalilin kawota cell...

"Ba Hafiz kawai ba harta Shattima saida yayi mamaki, toh me zai had'ata da Dasuki's... Suka kasa nemo amsar gaba d'ayan su ...
"Babu yanda basuyi ba a basu belin hadiza 'yan sanda sun k'i yarda, suka ce case d'in ba nasu bane, Alh Kasim tuni yayi pressing charges...

"Hafiz yayi shiru yana nazari kafin Shattima yace " Ai sai mu k'arasa can gidan muji ko akwai wani abinda suka sani gameda batun....

********

"Gaba d'aya mamaki ne ya ishe su, Hadiza da Alh Kasim toh ma ina zataga check, kai kurum Zubaidah ta shiga girgizawa tana fad'in" Bazata daina hali ba, ni na tabbata wani abin take k'ullawa tareda su a bayan idanun mu reshe ya juye da mujiya.
"Jalal ya sauk'e ajiyan zuciya yana tunanin toh me matar nan zata k'ulla da Dasuki's..
"Annah kuwa girgiza kai kurum tayi kafin tace " Yanzu abinda ke gaban mu shine muyi k'ok'arin sanin me take k'ullawa dasu ko ta samu ta kub'uta daga hannun 'yan sanda..
"Hafiz ya fuzar da iska kafin yace " Nifa abin ma wllhi ya dame ni ko kad'an na kasa gano me zai had'ata da wad'an nan mutane...

"Zubaidah ta d'an girgiza kai kafin tace " Idan dai Yaya Hadiza ce kunga kad'an, halin ta ne bazata canza ba, ni na tabbata wani abin take k'ulla min tare dasu, ina tausayin Hamma na, da Kamal,.... Ta k'arashe tana goge hawayen idanun ta... "Jalal ya d'an yi amfani da hannun sa guda ya d'aura saman yatsun hannun ba tareda kowa ya lura ba yana mai mata alama da idanu kan she should be strong...

"Annah ta bud'e murya tace " Aiko ko kusa kar ayi Hamma yaji wann zancen.... Kaman daga sama suka jiyo muryar sa yana fad'in"

"Na sani nasan bazata daina tsanar k'anwata ba, na sani wani abin take k'ulla mata tareda wad'ancan azzaluman mutanen. Kuyiww Allah kar ku karb'o ta, ku dubi girman Allah ku k'yaleta a can ta koyi darasin ta... Ta sha fad'i min inada nakasu a hallita na.. Amma ko kad'an ban d'auki hakan nak'asu ba don ban zamto tamkar ko wani namiji ba..
" Allah Ya gani a iya zaman mu ban tab'a tauye mata komai na rayuwa ba, ta zalunci Zubaidah tun tasowar ta, Na sani Allah bazai barta haka kurum ba taita aikata zalunci a bayan k'asa ba.. "Ya k'araso gaban su sosai yake kuka duk ya jik'a hannun rigar sa sabida goge hawaye kafin yaci gaba da fad'in" Zubaidah kin ga yanda Allah ke canza Al'amran sa koh,.... Duk hassadar da take maki kullun ci gaba kike, ki yafe ni k'anwata babu yanda na iya ne tuntuni...... "Bai kai aya ba Zubaidah ta k'arasa ta rungume sa tana fad'in " Hammaaa.... Kuka ya kufce mata, sosai shima yake kuka..
"Gaba d'aya suka tausaya masu...


"Bayan wasu mintoci Shattima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login