Showing 36001 words to 39000 words out of 210924 words

Chapter 13 - ZUBAIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

EYSHAAT   

30 Aug 2024

22876

da rad'ad'i had'i da wani irin ciwo har ya isa gida......





"Tafe suke ita da Annah bayan sun ajiye Kamal a makaranta, don yau Annah mussaman ta d'au hutun aiki sabida Zubaidah tana so suyi spending time sosai, da k'yar Zubaidah tabi Annah saida Kamal yayi ta magiya kafin ta yarda ta rakasu...

"Daga yanda motar ta ke pake ta hangosu zasu shige gida, da sauri ta fito daga motar ta nufo su...
"Zubaidah....... Ta fad'i tana k'arasowa yanda suke, a tare Zubaidah da Annah suka tsaya cak gamida juyawa, cike da mamaki suke Kallon Kausar, Zubaidah kam k'irjinta ne ya shiga bugawa da sauri da sauri.
"Jan hannun Annah ta soma tana fad'in Annah pls mu tafi.....
'Kausar ta k'araso da sauri ta rik'o hannun Zubaidah tace "Don Allah Zubaidah listen to me I won't take much of your time, pls.... Ta d'an dubi Annah tace pls Annah.
"Gyad'a kai Annah tayi cike da mamakin wani magana Kausar zatayi da Zubaidah? Wata zuciya tace k'ila hak'uri zata bata lokacin da tayi kusan kad'eta.
"Toh ku shigo ciki mana Annah ta fad'i.
"Kausar ta girgiza kai tana murmushi har lokacin hannunta na rik'e da na Zubaidah kafin tace " No Annah karki damu ba jimawa zamuyi ba, daga haka taja hannun Zubaidah zuwa benchin dake gefen k'ofar gidan, Annah kuwa tayi shigewarta ciki...



Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:15] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

27

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum... πŸ“–πŸ“š_

*Dedicated To Victims Of Rape...*


"Meye zaki fad'a mun, a ina na sanki, snn me ya tab'a had'ani dake da har kike son yin magana dake...???
"A jere Zubaidah ta jeho wa Kausar wad'an nan tambayoyin.

"Kausar ta karanceta tsaf kafin ta soma fad'ina, "Nasan zaki iya sani na, sunana Kausar Marafa, snn wacce tayi kusan kad'eki da mota sati biyu da suka shige a gidan Alhj Kasim Dasuki dake Maitama close Abuja, still nice Fiancee d'in Salim Dasuki....."Sunan Salim data ambata yasa Zubaidah saurin mik'ewa, Kausar tayi saurin rik'o hannunta.

"Malma ki sake ni na tafi, babu abu d'aya da ya had'ani da zantukan da kike min, idan kuma bugeni da mota da kika kusa yi ne, ba laifinki bane, laifi na ne, don Allah ki tafi ki k'yaleni....
"Kausar ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Zubaidah shin Jalal shi kadai ya maki fyad'e ko harda Salim..???

"Tambayan da Kausar ta mata yasata fara loosing control, cike da masifa ta fizge hannunta daga rik'on da Kausar ta mata" Cikin kuka take fad'in" Leave me alone, bansan abunda kike fad'a ba don Allah ki k'yakeni ki tafi and never come back.... Daga haka ta wuce cikin gida da sauri tana k'ank'ame jikinta, tana jawo rigar ta tana rufe jikinta.....
"Sosai ta bawa Kausar tausayi, da gani kasan pain d'in abun yana damunta zaiyi wuya ta sami had'in kanta a yanzu, cikin gidan ta shige itama da sauri....


"Zubaidah ba tare da tabi takan Annah ba ta wuce d'aki gamida banko k'ofa....
"Jin haka yasa Annah fitowa da sauri daga kitchen, a tare sukayi kicib's da Kausar ta shigo gidan.
"Annah ta kalleta da mamaki kafin ta tambayeta ina Zubaidah Kausar ta ciro wani d'an Card a jakarta ta mik'awa Annah tace " Pls Annah ki bata wann lambar wayata ce when ever she feels ta min magana she can contact me through this number, na gode..... Daga haka Kausar tasa kai ta fice daga gidan... Annah ta bita da kallo har ta fice kafin ta shiga juya takardan hannunta tana kallo.....



"A daidai k'ofar fita daga gidan suka had'u da Jalal, kallon mamaki yabita dashi, ita kuwa k'ak'aro murmushi tayi kafin tace " Jalal kayi wuyan gani, d'an maida mata murmushin yayi kafin yace " Me ya kawo ki nan...

"Kausar ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace " Jalal abunda nake son tambayarka nasan tanada nauyi but please be honest with me and tell me the exact truth.

"Jalal ya kuma binta da kallon mamaki kafin yace "Umhun inajinki go ahead.

"Jalal nasan ku hud'un nan ba'a raba ku, kai Salim Labib da kuma Tariq, Don Allah ka fad'amun gaskiya " Are you the rapist or all of you, pls tell me if Salim was involved?... I was told that you're the guilty one, pls ka fada mun iyakar gaskiyarka....

"Take idanunsa suka kad'a sukayi ja, tambayar data masa yayi matuk'ar sosa masa rai, but he don't want to ruin everything, he's doing this for the girl..
"D'agowa yayi ya dubeta kafin yace " Gaskiya suka fad'a maki Salim ya fad'a maki iyakar gaskiyarsa, now that you learned the truth kar ki sake dawowa nan pls kinji na rok'eki....

"Kausar da jikinta yayi sanyi ta gyad'a kai a hankali kafin tace " Bazan sake daowa ba insha Allah, your wife told me thesame...... "Da sauri ya dubeta kafin yace " You mean you talked to Zubaidah????

"Gyad'a masa kai tayi a hankali.......


"Fuskarsa cike da damuwa ya furta "Oh nooo, cikin sauri ya shige gidan Kausar ta bisa da kallo har ya b'ace mata kafin ta nufi yanda ta paka ride d'inta......




"Bai samu kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye d'akin Annah ya nufah......

"Yanda ta gansa ya shigo parlorn cikin sauri yasata k'walla wani irin k'ara ta tak'ure jikin garu tana k'ank'ame jikinta..... A hanzarce Annah ta nufo parlorn, shi kuwa Jalal ko motsi ya kasa sai kallon da ya bita dashi.....


"Annah ta watsa masa mugun kallo kafin ta k'arasa ta rungume Zubaidah tana rarrashinta....

"Jikinsa a sanyaye ya ajiye b'akar ledan da ya shigo dashi kana ya fice, d"akinsa ya wuce gamida zama bisa katifa...
"When will all these end?? When? When????? Kwanciya yayi bisa gado tausayin kansa da rayuwar da yake fusakanta suka cika zuciyarsa.....


"Wayanta ta ciro tayi dialing lambar Asmah snn ta saka a speaker... Bugu uku Asmah ta d'aga.

"Hello Barrister kina gida ko school??

"Daga d'aya b'angaren Asmah tace " Ina school, akwai wani abu ne, ??

"Okay shiknn sai kin dawo gida we need to talk ASAP.

"What for, maganar me bani hint you sounds serious....

"Okay amma driving right now, when I get home I'll call you back....

"Wait driving, ina kikaje da safen nan, ?

"Suleja naje...

"Suleja, suleja, wajen wa, Asmah ta tambaya cike da mamaki.... Kufa Journalist d'in nan kuna da bin diddigi don kunfi mu lawyers ma...

"Kausar tayi murmushi kafin tace "We will talk at home...

"Okay bye...

"yeah see you then...... Daga haka tayi hanging up zuciyarta cike da jin dad'i at least yanzu tasan Salim d'inta is innocent, zata ci gaba da shirin biki da k'warin gwiwarta........



"Ko office bai fice ba sabida zafi da k'irjinsa ke masa, ciwo kaman wasa babu yanda Mami batayi a kira Family Dr dinsu ba Alhj Jamil yak'i yarda, Labib ne ya shigo fuskar sa cike da damuwa ya k'arasa ya d'an zauna gefen gadon da mahaifinsa ke kwance, ya dubi Mami dake k'ok'arin had'a masa tea kana yace " Wai Mami har yanzu yak'i yarda a kira Dr d'in, mik'ewa yayi yana k'ok'arin ciro wayarsa a aljihu yake fad'in "I'm calling Dasuki Hospital Mami, bazamu biye nasa ba..... "Bai gama yin shiru ba yaji Dad d'insa ya rik'e hannunsa, juyowa yayi yana dubansa da alama bakinsa ya karkace.... Hannun Mami ya rik'o ya had'a dana Labib, cikin muryarsa da bai fita sosai ya soma fad'in
"Na bar maku amanar junan ku, Labib kabi mahaifiyarka snn kema ki kula dashi and pls protect him........ "Baki na rawa Labib yake fad'in" No no Dad pls stop saying all this, you gonna get better, we taking you to the hospital right away, Mami kam ta kasa nagana sai k'unshe bakinta da tayi tana kuka..... Labib duk ya daburce ya rasa wanne zaiyi, k'walla kira ya shiga yi wa ma'aikatan gidan, Alhj ya kuma rik'e hannun Labib gam kafin yace " Be careful with your uncle son..... Daga haka suka ji kaman yana salati dukda muryar ba sosai take fita ba.... Cikin mintuna k'alilan suka ji difffff komai ya tsaya........





Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:16] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

28

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum... πŸ“–πŸ“š_

*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Jijjigasa ya shiga yi da iya k'arfinsa yana fad'in " Dad Dad, no pls wake up Dad....! Kuka mai k'arfi ya kufce masa sanda ya rungume Dad d'insa da k'arfin gaske yake kuka yana ambatan sunan sa, bai kula da Mami ba da tuni ta sume, ...

"K'aran kukan Labib da suka jiyo yasa sata nufo d'akin d'akin babu shiri, Iya Dala ta Saki salati ganin Alh Jamil tamkar maras numfashi ga Labib na kuka rungume dashi, wani k'arin tashin hankalin shine hango Mami datayi zube a k'asa tamkar bata numfashi.
"A tamanin Iya Dala ta fice ta nufi gidan Alh Kasim...


"Yanda Mummy ta ganta gaba d'aya a rikice yasa hankalinta mugun tashi, gankalinta bai gama tashi ba saida taji labarin da Iya Dala ta kawo mata....
"Momy duk ta rikice da k'yar ta iya duban Jane tace ta kira Company a fadawa Daddy ya dawo gida babu lafiya, a tare suka nufi gidan Alh Jamil ita da Iya Dala,...

"Tsaye yake a saman penthouse(sashensa) d'insa ya hangi Momy da alama bata san yanda take jefa k'afafunta ba, ai babu shiri ya sauk'o ya nufo su..

"Momy lafiya meke faruwa? Salim ya tambaya cike da damuwa ganin hawaye a fuskar Momyn tasa.. . Rungumesa tayi tana kuka take fad'in" It's your uncle Salim.... "Gabansa yayi wani irin fad'uwa,
"A hankali ya furta "My uncle, what.... What happened to him Momy...
"Jawo hannunsa tayi suka nufi gidan tana fad'in I don't know Salim, let's go and find out......



"Sosai hankalinsu ya tashi da irin abinda suka gani, Mami dai ta farfad'o da aka yayyafa mata ruwa, Alh Jamil kam sa'i yayi don kuwa ya amsa kiran mahaliccinsa,...

"Rungume gawar mijinta tayi tana kuka mai tsuma zuciya, " Jamil kar ka tafi ka barni, bazan iya juran rayuwa cikin rashinka ba, don Allah kar ka tafi ka barni mijina.... Momy da itama hawayen take ta k'arasa ta rungumeta tana rarrashi...

"Labib yana ganin Salim suka rungume juna yana fad'in" Salim tell me my Dad is'nt dead, tell me he will wake up, tell me he can go through this, tell me I'm not gonna loose him.... Sosai Salim Ya rungumesa hawaye shima na k'ok'arin kufce masa....


"A kid'ime Alh Kasim da Dr suka shigo cikin d'akin, Alh Kasim tamkar mutumin arziki ya k'arasa kan d'an uwan nasa yana fad'in" Jamil my brother, what on earth is happening to you?? Dr ne ya matso ya shiga yin aikinsa, ya buk'aci su d'an basu waje, gaba d'aya suka fice parlour....


"Alh Kasim da Barr Munir sai kai komo suke saika rantse har ransu abin damunsu yayi....

"Dr ne ya fito daga d'akin jikinsa a sanyaye, gaba d'aya suka nufo sa suna son jin ba'asi.....
"Alh Kasim yace " Dr ya d'an uwa na, wani hali yake ciki, kafin Dr ya bud'e baki Labib ya rik'o hannunsa yana hawaye yake tambayarsa" How's my father Dr, tell me I can see him right now and he can talk to me.....

"Sauk'e ajiyan zuciya Dr yayi kafin yace " I'm sorry there's nothing I can do, sorry for your loss....

"Tashin hankali maras misaltuwa suka shiga idan ka d'auke Alh Kasim da Barr Munir Wanda hakan ba k'aramin farin ciki ya jefasu ba, burin Alh Kasim na mallakan Dasuki Holding ba tareda k'aninsa ba ya cika, matansa da d'ansa kuwa abune mai sauk'i....


"Abunka da babban mutum kan kace me an yad'a a kafafun watsa labaru, kan kace me gidan ya cika fal da jama'a....





"Suna zaune a barander suna tsinkan zogale itada Annah, dukda bata san dadin uwa ba amma tabbas tana jin dadin zama da Annah, tana jin kaman ta sami wani abu ne wanda a da bata samu ba a iya zamanta da Hadiza, jefi jefi Annah take janta da hira.

"Kamar wacce aka wurgota haka Hadiza ta diro masu aka kunnenta manne da Radio sai faman k'ara murya take tana fad'in" Kuji k'anin Alh Kasim Dasuki, Alh Jamil Allah ya masa rasuwa yau da safen nan..... "K'irjin Annah ya yanke ta shiga karanto innalillahi..... A b'angaren Zubaidah kuwa ko kad'an basu bata tausayi ba tunda tasan mahaifin Labib ne, k'arshema tashi tayi a wajen ta shige d'aki abinta, Hadiza tabi bayanta da kallo don yanzu ko maganar arziki bai shiga tsakaninsu.....




"Alh Kasim na zaune at the center a babban parlonsa da aka wangame gaba d'aya don Karb'an gaisuwa, mutane sai tambayan Labib suke suna so su masa ta'aziya, ciki harda su Alh Marafa da sauran tawagansa na siyasa, da kuma tawagan Ministoci da sanatoci da dai manyan 'yan kasuwa masu fad'i aji a garin Abj,
"Daddy ya kalli Salim yace " ina d'an uwanka?
"Salim yace " Yana penthouse d'ina, Daddy ya gyad'a kai yayi kafin yace "Okay Daddy ya nufi sashensa.....


"Zaune ya taddasa ya k'urawa aquarium d'in dake gefen closet d'insa ido, bin kifayen ciki yake da kallo amma hankalinsa gaba d'aya baya wajen, Maganar mahaifinsa na k'arshe ita tafi yawo cikin zuciyarsa *Be careful with your Uncle* meyasa Dad zaiyi wnn furuncin, tabbas idan ya gano Alh Kasim has anything to do with his father's death, he will kill him for sure... Dafasa da Salim yayi ne ya katse masa tunanin da yake.

"Kallo d'aya ya masa ya watsar, Salim ya d'an zauna gefensa gamida jero masa kalamai masu taushi "
"Labib you need to be strong for your Mom, idan kai namiji ka kasa jurewa ya kake tunanin mahaifiyarka zatayi, she needs you now, she needs you more than ever, pls be a Man I know you can go through this, besides you are not alone, you have us all, together we will through this as a family, tashi muje people are waiting for you to give you their condolence greetings, Daddy yace ka fito they are all waiting for you....


"Jin ya ambaci Daddy yasa sa kallonsa kaman zai mik'e sai kuma ya zauna yana girgiza kai yake fad'in" Kaje kawai Salim banjin dad'i, pls ka rufe mun k'ofa idan ka fita....
"Da mamaki Salim ke kallonsa kafin yace " Haba Labib daurewa zakayi mekake tunanin zanje nace wa manyan mutanen da suke jiranka, haba haba, saikace wani k'aramin yaro.....

"A harzuqe yace " I said leave me alone Salim, I f go out there, I'm pretty sure I'll see that Bastard and I assure you things are gonna get out of control, so leave pls, go tell them what ever you think.... Daga haka ya koma gaban window ya shiga kallon waje......


"Da mugun mamaki Salim yake dubansa, zaiyi magana knn Tariq ya shigo don yaji shirun yayi yawa daga fitan Salim yaje ya shigo da Labib sun kwashe mintoci....

"Kallon Labib dake tsaye bakin window yayi kafin ya dubi Salim, alamun tambaya ya masa da ido, Salim ya ware hnnaye gamida bud'e idanu alamun bai sani ba.....


"Tariq ya k'arasa ya rik'o kafad'un Labib yace " Let's go Labib, . "D'ago kai yayi ya dubi Tariq kaman raqumi da akala haka ya soma binsa, Salim ya d'an fuzar da iska gamida bin bayansu, cike da mamakin maganganun da Labib yayi, a iya saninsa Labib kwana biyu bai tari fad'a da kowa ba toh ko da waye yake yi sai Allah.......




"Har ya gama gaisawa da illahirin mutanen dake parlorn idonsa akan Alh Kasim yake, banda watsa masa mugun kallo baya komai, kai k'arshe har Labib ya bar parlorn idanunsa na kan Alh Kasim, gaba d'aya Alh Kasim yasha jinin jikinsa da irin kallon da Labib ke masa, a hankali ya saci jiki yabi bayan Labib.....





Sameena ce πŸ‘ŒπŸΎ
[1/23, 22:16] β€ͺ+234 803 619 0581‬: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*

29

*©Sameena Aleeyou...✍🏾*

_Queen Samy Novels Forum...πŸ“–πŸ“š_

*Dedicated To All Victims Of Rape...*



"Har aka gama kwana uku basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login